Showing 9001 words to 12000 words out of 46406 words
kuma son ta sana diyya ta naza mo silar barin Ummi na gidan mu,na gwammace nayita yawo cikin duniyar nan har rayuwa ta takare na koma ga mahaliccina".
shiru nayi sakamakon muryata da ta sarke sabo da kuka.
ido Mama mai awara tazuba min,niko a hankali nashiga jan shashsheka.
dakyau ta zuba min ido cikin alhini tace
"Ke ko ƴar nan wani irin mummunar laifi kika ai kata haka,har mahaifin ki yayi fushi da ke irin haka?".
kai nashiga girgizawa cikin muryar kuka nashi faɗin
"Wlh Allah ban ai kata abun da suka faɗa ba, kuma wlh Allah cikin nan nasa ne".
na karasa cikin kuka sosai,
cikin tsananin mamaki tamai da idanunn ta kan cikina dana ɗaura hannu kansa,kana ta mike tadawo kusa da ni ta zauna tare da jan hijabi na ta zuba wa cikina ido,
kana tace
"Ba shakka ga ciki nan wanene mai cikin? yanzu ƴar nan wannan abu kika ai kata akan yaya iyayen ki bazasuyi fushi dake irin haka ba ciki ciki".
tafaɗa tana tafa hannu.
kai nashiga girgiza wa
nace "Wlh ban ai kata zina ba cikin nan na Ya SALEEM ne".
hannuna ta ruko cikin rashin fahim ta tace
"Waye shi ɗin ta ya akayi yayi miki ciki to in ba zina ba menene?? kiyiyo ciki a waje kice ba zina kika yi ba to menene sunan shi??".
ta jero min tanbayo yin ida nunta a kai na cike da fargaba da son jin ba'asi.
wasu hawaye masu zafi da kuna na share kana a sannu nashiga bata labarin rayuwa ta,tun daga san da nafara sanin koni waye, har abun da yafaru dani yafito dani daga gida har kuma yau da nake zaune a gaban ta.
kuka sosai nake har numfashi na yana fizga abun da yafaru da rasuwar Inna yadawo min sabo fil a zuciya,cikin muryar shashsheka nace
"Allah ka kashe ni nahuta,kaɗauki rayuwa ta ko zuciya ta zata sami sassauci!!!!".
numfashi ta sauke cike da tsananin alhini da al'ajab.
Tace "Akul kidai na faɗan haka babu kyau Allah yafiki son kanki, yakan jarabci mutum dan yagwada imanin sa,
hakika mahai fin ki ya yanke hukunci cikin fushi sai dai duk wan da hakan yazo masa rana a saka dole yaji babu daɗe,shi kuma mijin ki ya kama ta yayi tunani ko da a ce hakan yafaru da gaske aure yabashi,amma tun da yace bai amin ce ba bai kuma karɓi cikin ba to shi kenan, ƴaƴa nawa suka rayu batare da uba ba, Allah sauke ki lafiya yataya ki rukon abun da zaki haifa,su kuma waɗan da sukayi ruwa sukayi saki wajen ganin sun ɓata aure, Allah yanuna musu buwayar sa da izzar sa na kwatar wa wanda aka zalinta hakkinsa tun anan duniya,
zaki zauna tare da ni a nan har zuwa lokacin da zuciyar mahaifin ki zai sassauto daga fushin da yayi."
Nan tarika yi min nasiha takuma nuna matukar tausayar ta gare ni,har sai da taga na dai na kukan.
nan take faɗa min ita ɗaya ce a gidan mijinta ya rasu tun da daɗe wa,
ƴaƴan ta uku sai dai tun suna kanana suka rasu dukan su.
Duk da halin da nake ciki amma na tausaya mata dajin bata da ɗaya.
Batabar ɗakin ba har sai da taga na dai na kukan gaba ɗaya.
can an jima ta kuma dawowa tace na fito tsakar gida zama Ni kaɗai zai daɗa kara min damu wa...
tun daga ranar Mama ketason gusar min da damuwa ta, sai dai banajin har na mutu damuwa da ɗacin dake raina zai yaye gaba ɗaya.
Sai dai nakan yi iya bakin kokari na wajen ganin na ɓoye damuwa ta ganin tana nuna kulawa da son ganin na kwantar da hankali na,na sawa zuciya ta salama.
nakan faki idon ta a duk san da zuciya ta tatuno min da abun da yafaru sai na shiga bayi nata kuka har sai naji zuciya ta taɗan sami sassauci, haka ma idan natuno da Ummi na ko wani hali take ciki yanzu,nan ma bayin nake shiga nayi kuka na.
mama
bata taɓa barina na nazauna a ɗaki ni kaɗai,da zarar taga nashiga ɗaki naɗan ɓata lokaci zata leko tace na fito,
wani sa'in ko makota zata shiga sai tace nazo muje.
idan aka ganmu tare a ka tan bayeta wacece Ni sai tace ƴar kanin tane tazo daga garin su Yola..
....★
Da misalin ƙarfe 4 na yamma zaune muke a tsakar gida,
ina surfe wa mama waken kosan gobe,
Ita kuma tana wanke waken awara,
yanzu tare muke yin ai kin kosai da awar duk da hanani yi datake,wani sa'in ma Ni nake soya mata tun idan naji hayaki kai na da ido na suyi ta ciwo har yanzu na saba,wani sa'in kuma ita zata rika suyan Ni kuma na rika zubawa masu siya.
Juye waken mama tayi cikin robar kai markaɗe ta mike tana faɗin
"Yau baza ayi awarar dare ba gaskiya jiya dukan mu bamu yi bacci da wuri ba gashi yau da safen ma bamu huta ba,yanzu daya kamata ace hutu muke gamu gaban wake,kullum ai kin kenan kuɗi kuma ba taruwa yake ba".
Jinjina kai nayi Allah sarki Mama kullum haka take faɗa wai sai dai mukare a gindin wuta amma bamu aje wani ribar kirki,bayan da ribar muke ci musha da sauran bukatu.
Murmushi nayi nace
"Mama ayi kawai tun da an sa har Da waken yau,kuma anjima zaki ga anata shiga nima".
tace "To shike nan ai badun an jikan bakam gaskiya da mun huta yau".......!★
Mommyn twins ce
Tun waye war garin yau nake jin tashin zuciya da warin magani a jiki na,
yau kwana huɗu kenan nake ta fama da irin wannan yanayin,sai dai nayau yafi na sauran kwanakin, shiga na bayi sau uku kenan inata wanke jikina wai ko dun zan dai jin warin da kuma tashin zuciyar,
amma sai ji nake kamar karuwa yake.
Sabulun da Mama ta siya min mai kamshi wan da tun ɗazu shi naketa wanke jikina da shi na kuma ɗau kawa yanzu na fito tsakar gida,
yawun da ke kunshe a bakina naje can gefe na zubar,
fuska na yamutsa jin zuciya ta naci gaba da tashi kamar zanyi amai,
Mama dake jajjagen kayan miyar abincin rana ta dube ni da kyau tace
"Ya dai HAMDAH".
"Bako mai Mama".
nafaɗa ina daɗa yamusa fuskar,
ganin yan da nake ta zubda yawu yasa mama bani goro tace nasa a baki na zai ɗan rage min yawun.
boket nakuma cikawa da ruwa na shiga bayi nayita mulke jikina da sabulun sai da na kusa karar da salun kafin na fito,bawai kodun na dai na jin abun da nake jin ba sai dai dun gajiyar da nayi.
ina shiga ɗaki nayi wurgi da sabulun na sulale sakiyar ɗakin na zauna,
kai na na dafe jin yadda aman ke ta kokarin tahowa,sai juya kai nake.
da sauri na janyo akwati na na buɗe cikin hanzari nakifa fuskata cikin akwatin ina shaƙar ɗan guntun kamshin turaren Ya SALEEM,daya zauna ciki sabo da kayana da ke ciki sai kamshin yazauna jikin akwatin duk da na wanke kayan cikin yafi akirga amma yar yanzu akwatin yana ɗauke da ragowar kamshin, duk da bawani kamshi mai yawa bane sai naja numfashi sosai nake jiyo kamshin.
A hankali narika sauke numfashi jin aman na lafawa,sai dai har lokacin ban fasa jin warin maganin ba,najima fuska ta na kife cikin akwatin,sai dai har lokacin ina jin warin maganin,
a sannu na mike cike da takaici da kuma tausaya wa kai na dan nasan in kwana zanyi ina shaƙar kamshin turaren sa kaɗai bazai gusar min da abun da nake jiba,
kamshin sa kamshin dake fita daga cikin jikinsa shi nake so shine kaɗai mai iya fidda ni cikin wannan hali,
wasu zafafan hawaye ne suka tsiraro min kan fuska nakai hannu na share,
a sannu nayi kasa da hannuna zuwa kan cikina da sai motsawa abun cikin yake na shafa,
baya nayi na jingina bayana da jikin garu tare da rumtse idanuna,yayin da zuciya ta ke wani irin matsanancin zafi da kuna,
idanuna nakuma rumtse wa da karfi cikin zubda kwalla da ɗacin zuciya nashiga faɗin.
"Shine uban ka yace bashi bane yakore ni bayan yasan jikin sa kaɗai nake shiga na dai na jin warin magani ko tashin zuciya,yasa Abba ya koreni ya nesanta ni da Ummi na da ƴan uwa na,yace kai ba jinin sa bane kada nasake danganta ka dashi,haka zaka fito duniya baka da uba kahaɗu da hantarar mutane waɗan da zasu rika yi maka kallon shege,ina ma da ace Inna ta tana nan da idan na haife ka wa ita zan bawa, na tabbata bazata taɓa bari duniya suyi maka kallon shege ba,na tabbata soyayyar da take min bazata taɓa kin jina ba ko da ya kasan ce shegen ne, na tabbata..na tabbata...na tabbata.."
kukane ya kwace min sai nayi saurin kai hannuna kan baki na na toshe tare da sakin kuka mara sauti.
Muryar Mama naji tana tahowa ɗakin haɗe da kiran sunana,
da sauri nayi kokarin sai da kukan nashare hawaye na cikin hanzari, buɗu labule tayi tana faɗin
"HAMDAH mekike yi ne acikin ɗakin tun ɗazu ko bacci kike ne??".
shiru tayi da maganar nata tare da zuba min ido daga bakin kofar kana tace
"Au abun da kika zauna yi kenan? har sai yaushe zaki sanya wa zuciyar ki salama HAMDAH?,
ko badun ni ba kodun abun cikin ki kya fauwala wa Allah komai dan tsira da rayuwar ki wajen haihuwa,idan fa kika cigaba da sawa zuciyar ki damuwa da yawan ta tuno abun da ya faru ya kuma wuce ke zaki cutar da kanki, do min kuwa yanzu cututtuka sunyi yawa,ba a son mai lalura irin naku ta yawaita shiga damuwa,sai ya iya yin sana diyyar ta ko na abun da zata hai fa agurin haihuwa".
da sauri nashiga girgiza kai cikin son ɓoye damuwa ta nace
"Mama bafa kukan nake ba har yanzu Ban dai na jin aman bane,kuma yaki fitowa sai dai narika jin tashin zuciya sosai".
shiru tayi idanunta a kai na kana tace
"To shike nan na ɗau ka ai kukan kika shigo yi,sa kaya kizo na dama miki kudun tsami wata kila yasa ki dai na jin aman".
To nace,ta saki labulen ta juya dan zuwa dama kunun.
A hankali na sun kuya naɗau kaya nasoma sawa.
Ina gama wa na haye kan sallaya dan dama da al'wala ta na gabarar da sallar azahar kana nafito,
Na tadda har ta dama min kunun garin dawa da ruwan tsamiya sai tashi da kamshin kayan yaji yake,
a gefen ta bisa taburma na zauna tamika min kofin kunun,
na amsa nakai kofin bakina a sannu na soma sha,
a sannu cikin ikon Allah narika jin warin maganin da nake jin nan naraguwa,ina gama shan kunun ta miko min gauta a cikin farin laida tace
"Tun da goron bai miki ba ki gwada cin gautar wata kila shi ya miki,
gobe Litinin idan Allah ya kai mu zaki fara zuwa awu nan cikin asibitin unguwar nan,gashi anata faɗakar wa a gidajen rediyo yakama ta kifara zuwa dan yana da amfani kwarai."
kallon cikin tayi kana taci gaba da faɗin
"An ya kuwa HAMDAH lissafin cikin nan dai-dai kika yi?, cikin wata huɗu kamar cikin wata shida ko bakwai,cikin fari da irin wannan girma haka kuma cikin fari bai fiye girma ba".
murmushi nayi nace
"Allah Mama dai-dai nake lissafin kinga lokacin da aka kai ni asibiti watan sa ɗaya ne dai-dai, yanzu kuma an kara wata uku kenan bayan wancan wata ɗayan kin ga wata huɗun kenan".
baki mama tarike tace
"Iye har kin rike lissafin dalla-dalla ikon Allah zamani da ƴaƴan cikin ta".
dariya nayi cike dajin kunya narufe fuskata da tafin hannuna.
ranar gauta da kunun tsamiya na wuni sha cikin yardar Allah kuwa naji sassaucin abun da nake ji.
Washegari da sassafe ina kwance Mama tashigo ta tadani tace natashi na shirya natafi asibiti yin bukin,
bayan nayi wanka na shirya tare da ita muka tafi asibitin,ita tayi ta zirga-zirga da cuku-cuku ina zaune sai dai abun da yakama dole sai nayi da kai na nake binta muje.
Sai wajen karfe 1 muka gama komai har da awun,
Kasan cewar yau ɗin Monday ne hakan kuwa yayi dai-dai da yau ne ranar awun masu cikin fari,dan haka ya zamo ranar zuwa awo na kenan duk bayan wata ɗaya.
A gajiye muka shigo gida ga yunwa,
kitchen na shiga na ɗauko kofin ragowar kunun tsamiya ta da mama ta dama min da safe kafin mutafi,
na fito tsakar gida gindin ɗan bishiyan tsada da muke zama musha iska na zauna kan taburman data shin fiɗa,
ita kuma ɗumamen tuwo ta zubo tazo tazau na tana ci muna ɗan taɓa hira,har ta kammala,
lai dar magunguna da aka bamu a gun awu tajanyo ta fiddo da magungunar,
da sauri na kawar da kai na ganin maganin kaɗai yasa naji zuciya ta yaso ma tashi,
"Karbi maza ki haɗiye kin ji abun da suka ce kada ayi wasa da shan kwayar yana taimako sosai,bari ma na tashi naje na nimo miki ƴan abubuwan da suka ce kirika ci wake kam muna da shi,karɓa kisha na tashi".
juyowa nayi jin abun da take faɗa ji nayi kamar na zandara ihu, maganin ta mika min tare da miko min ruwa tana cigaba da faɗin
"Karɓi mana kada su sha iska".
amsar maganin nayi ban da ruwan nace
"Ni da kunu zan sha bazan iya sha da ruwa ba".
tace "To sha dashi ɗin".
da kyar na haɗiye da kunun ma jin yana kokarin dawowa da sauri naɗau agwaluma da ta siya min a asibitin naso ma tsotsa da sauri.
ta mike tana faɗin
"Bari naje gurin mai kayan miyar can na haɗo cefani".
kai kawai na gyaɗa mata tafita.
Baya na na jikina da jikin bishyar da nake zaune a gindinta,a hankali naci gaba da shan agwalumar,
Ina zaune agun har ta dawo da cefane niki-niki a talakance,
nayi mamakin ganin har da hanta a cikin cefanen,
batare da ɓata lokaci ba ta haɗa min gwaten wake da hanta da ganyen ogu. kamar yan da ma'aikatan asibiti suka faɗa...
duk bayan kwana biyu Mama zata siyo kifi ko hanta ko kwai ta sarrafa min shi,
lurar da nafara yi jarin awara da kosai yafara yin kasa nasan ba komai bane ya kawo hakan sai waɗan nan kayan cime-cimen da take girka min,
wani ranar da zata je yin cefanen har takai bakin kofa nabiyo ta da sauri nace
"Mama ki bar kashe kuɗin nan haka kwanakin baya awara mudu huɗu ake yi kosai mudu biyu, amma yanzu mudu biyu ake yi wani sa'in ma mudu ɗaya da rabi,kosai kuwa yanzu mudu ɗaya ne,kuma fa duk wannan siyan kayan abin cin da aka faɗa a asibitin ne yake cinye kuɗin,Ni dai Allah Mama ki bar siya haka ai naci da yawa ma fiye da yan da suka faɗa tun da sunce kwai ɗaya ma naci ya wadatar,kifi kuwa ko na ɗari ne ba sai lallai an siyi hantan ba".
tace
"Tafi can me kika sani so kike kizo haihuwa kirasa jini sai an yi faman niman jini ko,ai waɗan nan abubuwan da kike cin sune zasu tai maka wajen kara miki jini, ko kin zubda jini gun haihuwa ma baza a sami wata matsala ba dan akwai jinin a jikin ki sosai".
kai na jinjina.
waje tayi tana cigaba da faɗin
"Yo menene amfanin niman kuɗin da baza'a magance damuwa ba lafiya ai yafi kuɗi".
juyawa nayi na koma ciki ina saka yadda zanyi na hanata kashe kuɗin nan da yawa dan yanzu jarin da muka dogara dashi ɗin ma yafara yin kasa idan ya karye gaba ɗaya wace madafar zamu dafa...
Acan kasar India lokacin da Ya Masa'ud yasa mi labarin abun da ya faru,bakara min girgiza da tashin hankali ya shiga ba,cikin matukar tashin hankali yabaro kasar yatoho Nigeria,yayi kuka da hawayen sa da yazo ya iske Abba yakori HAMDAH ba'a masan in da take ba kuma yahana a nimo ta.
lokacin yayi yunkurin nimota Abba yace kada ya soma,bai dai bi na Abba'n ba, ya baza cigiya cikin garin Bauchi sai dai ba'a sami wani alamar da ya nuna tana cikin garin ba.
su Aunty Rafee'at
sunyi yunkurin kiran su Abbu da suke can kasa mai tsarki su sanar musu,
Ummi tace kada su sanar musu su barsu suyi iba dan su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da lumana.
kullum Ummi na kan sallaya tana yiwa ɗiyar tata addu'a da fatan samin kariyar Allah agare ta aduk in da take a faɗin duniyar nan....
....★
After 1 month
Yau da wuri na dawo daga awu dan da sassafe Mama ta tashe ni na shirya ta rakani har cikin asibitin kafin ta dawo, lokacin da muka isa asibitin mutum uku na samu a gabana.
na shigo gida na tadda Mama tana ta suyan awara masu siya sun zagaye ta,
ɗaki na wuce na tuɓe hijabi na na aje laidar agwaluma da na siya da ɗarin da Mama ta bani tace ko zan ga wani abun da nake so na siya,
kana nafito.
in da take na isa nayi mata sannu da ai ki tace
"Har kin dawo da wuri haka an yi miki awun kuwa?".
nace "Eh ai yau mutum uku ne a gaba na".
tace "Ai yafi kaje da wuri ka dawo da wuri wani watan ma da wuri zamu tafi".
kofin kunun tsamiya mai ɗumi ta miko min da alama bata jima da dama shiba,
ta tsamo kosai cikin mai tazuba cikin kwano shima ta miko min na amsa, zan zauna kan kujera tace
"A'a ɗauko taburma ki shin fiɗa kimike kafafun ki".
nace to.
Ko da tagama suya kan taburman da na shimfiɗa tazo ta zauna cinikin da tayi ta zube su kasa muka soma kirgawa,muka cire kuɗin komai da akayi amfani da shi, cikin murnar ganin yau an sami riba har dubu ɗaya da ɗari biyar baki na washe nace
"Kai gaskiya yau kam an sami riba har dubu da ɗari biyar".
murmushi tayi tace
"Ai kam yau alhamdulillah bari na fita nayiyo mana cefani".
da sauri nace
"Yauwa Mama yau ni dai bana jin sha'awar hantar nan gara kifi ma kiyi mana irin miyar waken suyar da ranar kika yi manan nan sai asa kifin kawai a ciki".
Nafaɗi hakan ne dan nasan tana fita ribar da aka samun zai kare wajen yin cefanen girkin da take yi min wai na karin jini har sai ta taɓa uwar kuɗin ma.
tace
"To shike nan sai ayi shi tun da kina so".
sallamar da akayi ne yasa mu ɗagowa dukan mu,
Wani saurayi ne mai suna Sagir dake layin unguwar, kusan kullum sai ya shigo siyan awara,
da ai kowa yake a siya masa amma yanzu da kansa yake shiga cikin gidan ya siya,
idan ya shigo yarika bina da