Showing 36001 words to 39000 words out of 46406 words

Chapter 13 - HAMDAH part 2 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

7625

duk maganar da Mahmud da Bappa su ke da tsare-tsaren da Mahmud yake na yan da lamarin zai tafi cikin sauki,
ban iya cewa komai jikina yayi sanyi natuno wani sashi a rayuwa ta, tun isowar Mahmud da yayi sallama cikin gidan inadaga ɗaki sai da naji gaban kirjina ya yabuga, jikina sai ya kama ɓari muryar sa tamkar muryar Abba har na fara tunanin ko Abba ne sai da naji Mero tana faɗin
Oyoyo Yaya Mahmoud.
ko yanzu da muke zaune ganin fuskar sa shima ya sani shiga wata yanayin, kamannin sa irin na Abba yana matukar kama da Abba.
sai dai shi baikai Abba girma ba shekarun sa bazai wuce 38 zuwa 40 ba,
kira ce tashigo wayar sa da sauri ya ɗaga kiran kana yakara wayar a kunnen sa "Ok godiya nake".
abun da yafaɗa kenan tare da sauke wayar.
maganar sa naji a sama yana faɗin
"Tun jiya na nimi ganawa da gwamnatin jihar nan, gashi da ikon Allah cikin sauki an bani tabbacin ganawa da shi cikin sauki in sha Allah, wa gwamnati za'a siyar domin samun cigaban kasa".
ya mike tsaye yana cigaba da faɗin
"Bappa mu hanzar ta."
tun kan ya rufa baki Bappa yamike yana faɗin
"masha Allah hakan yayi".
bukkar sa yashiga zuwa can yafito yana gyara babbar rigar da yasa ka kan kayan jikin sa,tuni Mahmud yayi waje Bappa na fita ya shige mota suka ɗau hanya...
kwance nake a kan gado Nasmah da Naseem suna gefe na sai wasa suke,Mero ta shigo nace ta ɗauke su sufita dan kaina ciwo yake min sai kuma dami na da surutun su suke, suna fita na gyara kwanciya ta,gaba ɗaya yau tunanin gida da ya dame ni tun ganin da nayiwa Mahmoud tunanin family na ya addabe ni,ina kwance shiru a haka har bacci ya ɗauke ni...

Bappa sun isa cikin Adamawa batare da ɓata lokaci ba suka sami ganawa da Gwamnan jihar su, saboda muhimmin abun da ke tafe da su.
bayan sun gabatar da abin da ke tafe dasu, shi kansa Gwamnan yayi mamakin yawan Diamond ɗin, yace gaskiya wannan Daimond ɗin kam sai dai a jingina da shugaban kasa. sabo da babu kuɗin da zai iya canza wannan Diamond ɗin a fadar jahar.
batare da ɓata lokaci ba yayi magana da fadar shugaban kasar Nigeria, kana ya haɗa su da wasu jagororin da zasu tafi tare, sannan yace dole sai sun tafi da wanda yasamo Diamond ɗin sabo da za'a iya bukatar hakan acan fadar shugaban kasar.
da yamma lis suka baro cikin Adamawa suka koma rugarsu da jagororin da aka haɗa su da su, da sojoji mota guda waɗan da zasuyi musu rakiya, dan acewar gwamnar komawar su cikin daji da wannan abu yana da haɗari sosai dole sai an haɗasu da jami'an tsaro.
mota uku ne motar Mahmoud sai na jagororin da aka haɗa su dasu motar su guda sai motar sojojin.
motar su Mahmoud ne a gaba na jogororin a tsakiya na sojojin na biye da su...
bayan sallar Isha
muna zaune a tsakar gida muka jiyo jiniyar sojoji,
Ido Inna wuro ta waro tare da faɗin,
"Sojoji kuma shanun wa aka kuma kaɗawa yau?".
batakai ga rufe bakin taba muka ji jiniyar ya tsaya daf kofar ida,

Mero tace "Inna wuro anan suka tsaya".
tafaɗa tana nuna kofar gida, ganin yan da sukabi suka tsorata nima sai na fara shiga yanayin da suke ciki,
har kuma lokacin jiniyar na tashi, nace
"Eh..Eh akofar gida suke".
duk mukayi jigum idanun mu a kofar gida tsoro fal zuciyoyin mu.
bayan haka dakamar minti 15 muka jiyo sallamar su Bappa duk muka mike tsaye tare da amsa sallamar.
suka karaso ciki,tun kan su zauna Inna wuro tace
"Malam lafiya da sojoji a kofar gida?".
ganin duk hankulan mu a tashe yasa Bappa faɗin
"Babu komai fa rakomu sukayi domin su bamu tsaro sabo da abun da muke tare da shi".
tsaguwar sa ya gyara kana yace
"Duk ku zauna". nan muka ɗan sami kwarin guiwa muka koma mazau nin mu,
Mahmoud yacewa Mero ta tashi tazuba ruwa acikin bototi, tana zubawa ta mika masa yakarɓa yafita,yakai wa ba'in da suke tare da su a waje.
Bappa ya zauna kan taburman sa da Inna wuro ke shinfiɗa masa duk dare a bakin kofar sa kana a nutse yashiga faɗa mana yan da sukayi da gwamna kana ya ɗaura da faɗin
"Sai ki shirya tun yau dan gobe idan Allah ya kai mu da sassafe zamu tafi".
kai na gyaɗa cike da mamakin jin abun da Bappa ya faɗa.
Inna wuro tace
"Ikon Allah to Allah ya kai mu sai ki tashi ki kimsa".
to kawai nace dan ni ban san me zan kimsan ba, ba kaya nake da shi ba bare na ce shi zan kimsan, su Naseem ma ba kayan suke dashi ba sai kala bibbiyun da Bappa ya ɗin kamusu.
washegari da sassafe Inna wuro ta tasheni,tace naje nayi wanka taɗaga su Nasmah taje tayi musu wanka,
ta shirya su, ina fita ta bani wani kayan ta mai ɗan haske na saka duk da kayan yaɗan min girma,
Mahmud yashigo yace nayi sauri ni ake jira, da sauri na karasa saka hijabi wan da shima ita ta bani,
Inna wuro da Mero suka rako ni har waje,tuni kowa ya shige mota sojojin nan suna saman motar su sun tasa bindigogin su gaba, da hannu Mahmud yayi min alama da inzo, na karaso gun motar sa na buɗe gidan baya muka shiga ni da Nasmah, Naseem kam tun da yaga Bappa yarika mika hannu yana tsalle Bappa yace a kawo shi..
motar sojojin a gaba yayin da motar mu ke biye da shi sai na jagororin
a baya..
nan muka ɗauki hanyar birnin tarayya Abuja....★


muna isa garin Abuja wani kayataccen masauki aka wuce da mu, nan Mahmoud ke faɗa wa Bappa,
an tabadar da masaukin domin mu ne, ɗakina ni da su Nasmah da ban, ɗakin Bappa da ban sai na Mahmoud ɗin,sai kuma na jagororin da muka taho da su,
sojojin kam suna cin abinci suka juya suka ɗau hanyar Adamawa,dan da ma suma rakiyar sukayi mana yanzu kuma kulawar mu yafita a hannunsu yadawo hannun wasu hukumar da muka tarar da su a nan.
a gayiye na zauna bakin gado Naseem da Nasmah suna zaune tsakiyar gadon sunata wasan su.
bin lafiyayy ɗakin nayi da kallo, numfashi na sauke ashe dai zan sake gani na cikin ɗaki irin wannan, dan ni na fidda sammanin hakan arayuwa ta mai cike da tarin kaddara da jarabta.
kasan cewar mun isa ana kirana sallar magriba, dan da muka iso sai da muka tsaya a wani guri naga jagororin da aka haɗo mu da su, suka tsaya yin magana da wasu, mun ɓata lokaci a gurin kafin muka taho nan.

kayan jikina na tuɓe na ɗaura zanin a kirji nashige bathroom naje nayi wanka,sannan na fito na tuɓe su Naseem suma naje na musu, ina fita na shinfiɗa sallaya da nagani cikin ɗakin kasan cewar nayi al'wala nagabatar da sallar magrima.
tuni su Nasmah sunyi bacci sabo da gajiyar mota,
sai na gyara musu kwanciyar su a kan lafiyayyen gadon,
bayan na idar da sallar Isha ina zaune a kan sallaya akayi knocking ɗin kofar,
a sannu na mike na isa bakin kofar na buɗe, wani mutum nagani sanye da uniform irin na masu ai kin hotel, da tray ɗin abinci a hannunsa,
yayi min sannu na amsa,baya mayi na ɗan ja murfin kofar ya shigo ya dire tray'n kan table ɗin da ke tsakiyar ɗakin mai lodin kayan abin ci da drinks kala-kala kana yafita, na mai da kofar na rufe, na koma bakin gado na zauna.
da ma yunwa na ke ji nan na janyo tray'n na soma cin abincin,
inaci ina kallon su Naseem dan na san suma yunwar suke ji sai dai gajiya ya sasu bacci,
ina gama ci naje na wanko bakina na dawo, na kwanta bakin gadon tare da yi musu addu'a nima nayi nagyara kwanciya ta.
washegari bayan nayi wanka nayiwa su Nasmah na shirya su muna zaune,a ka shigo mana da breakfast bayan mun karya.
Bappa yashigo da sallama kan kujerar ɗakin ya zauna,
nan nashiga gaida shi ya amsa kana yake tanbaya ta ya gajiyar hanya?,
nace
"gajiya yabi jiki". Naseem kuwa tuni ya wuce jikin sa yana ta tsalle Nasmah ma tabi bayan sa sunata yi masa gwalaɓe,suna ta shekewa da dariya Bappa shima sai biye musu yake yana ta taya su sai zuba masa surutu suke wan da ma maganar tasu bagane ta ake ba.
zama Bappa yagyara tare da duba na kana yace
"Ɗazun Mahmoud ya zo ya same ni da jagororin da aka haɗa mu da su sun bani tabbacin bazamu sami ganin shugaban kasa a yauba,
zamu ɗan ɗau lokaci sai dai kawai muɗan jira,
idan kuma zamu koma to,amma gaskiya
ni ina tunanin komawar mu domin iyanzu maganar Lu'ulu'u'n nan ya karaɗe cikin rugar mu har da wajen sa, ina tunanin mukoma yanzu mutane basa da gaskiya ɗai-ɗai ku ne masu gaskiya a zamanin yanzu, yan da yashiga kunnen mutanen gari kuwa na tabbata zai fita har wajen gari,
har miyagon mutane suje suji sukawo mana farmaki,
gaskiya bazamu koma ba zamu jira har lokacin da zamu sami ganawa da shi shugaban kasar".
kai na jinjina alamun gamsuwa tabbas,
kuɗi a gida akwai haɗari musamman irin wannan da na ga gwamna yahaɗo mu da jami'an tsaro, nace
"To Bappa duk abun da ka yanke dai-dai ne".
yace
"Gaskiya zamu zauna ko nan da kwana uku ko huɗu ne in dai har zamu gana da shi ɗin yafi mana komawar mu da dukiya kan hanya domin ko a hanyar komawar mu ma kaɗai hatsari ne bane kuma ace mun koma cikin ruga in da babu jami'an tsaro".
nace
"Hakane Bappa muzaunan kawai".
kai ya jinjina kana ya mike yana rike da hannun Naseem, Nasmah da take ta kokarin binsu yace ta zauna ta tayani hira,
zai tafi da Naseem shima ya tayashi hira....



kwaman mu uku a Abuja acikin wannan hotel ɗin, alhamdllh a kwana na ukun bukatar mu ta isa ga shugaban kasa sai dai har lokacin ba'a bamu da mar ganin sa ba, a kwana na biyar,da safe ina zaune akayi knocking naje na buɗe kofar Mahmoud ne yashigo da sallama,
rike da babban laida a hannunsa,
na gaishesa cikin girmamawa ya amsa tare da mika min laidar dake hannunsa tare da faɗin
"Gashi ku shirya kuyi sauri, yau kam in sha Allah zamu sami ganawa da shi koba shi ɗin bama zamu zauna da wasu manya na kusa da shi kuyi sauri ku shiriya ya zama na dai da kuna cikin shiri".
nace "Tom".
na karɓi laidar tare da yi masa godiya yafita.
na zawo bakin gado na zauna tare da buɗe laidar na fara ciro kayan cikin, kayane na sawa,kaya masu kyau narika ɗaga na Naseem da Nasmah masu kyau ƴarkanti, dukan su da takalmar su masu kyau,
da ma tuni na riga da na musu wanka, na cire musu kayan jikin su nasa musu wannan kayan,
yara suka fito shar da su tamkar ƴaƴan turawa, sunyi kyau sosai na tasasu gaba inata kallon su cikin ban sha'awa,
sannan nima na mike na camza nawa dogon riga ne da gyalen sa Ash mai ratsin gold
ɗin duwatsu haɗe da takalmi Black and gold, takalmin mai ɗan tudu ne kaɗan.
nasaka kayan a hankali na isa yaban mirror abun da na daɗe banyi shi ba yau nayi,
nashafa
pawda da nagani kan mirror'n haɗe da man lips kana,
nayi rolling ɗin gyalen a kaina,tsayuwa ta na gyara gaban mirror'n
masha Allah duk da na rame na dishe amma bai hanani fitowa a HAMDAH ta ta daba kaɗan ba,
murmushi nayi ganin yan da nayi kyau a cikin kayan yaɗan ɓoye min rama ta.
da misalin karfe 12 Mahmoud yashigo daga bakin kofa yatsaya yace nayi sauri na zo. sai ya juya yafita ,
cikin hanzari na sakawa su Nasmah takallamar su sannan na kama hannunsu muka fito,
muna fita farfajiyar hotel ɗin,
nan na tadda su, Bappa yana zaune cikin mota gefen mai zaman bamza yayin da Mahmoud ke zaune a mazaunin direba. muka karaso Bappa yana ta kallon mu yana murmushi,
nima murmushin nayi muka karaso na buɗe gidan baya na shiga Naseem kam fir yaki shiga sai da na mika sa wa Bappa.

motar mutanen da mukazo da su a gaba namu yana biye da shi a haka muka fita a cikin hotel ɗin, duk san da na ɗago kaina sai mun haka ido da Mahmoud,na lura tun fitowar mu idanun sa a kaina, kawar da kaina nayi gefe ganin sai satar kallo na yake tacikin mirror,
munyi tafiya mai nisa kafin muka isa wani katon gida mai matukar girma da kyau da tsaruwa,
a bakin get ɗin gidan motar gaban mu ya faka a bakin get ɗin Mahmoud ma ya tsaya a bayan sa,
ɗaya daga cikin mutanen ya fito ya isa in da sojoji ke zaune a bakin get ɗin,
yayi magana da su kana ya koma cikin motar,
nam sojojin suka buɗe get ɗin,
motar ta fara shiga kafin mu muka bi bayan sa.
sai da na shiga gidan na daɗa ganin tsaruwa da girman sa,
muka paka a parking lot.
kana mutanen suka fito daga cikin motar,ɗaya daga cikin su yazo yace, muma mu sauko.
daga can wasu sojoji suka taho in da muke,jogororin da muka taho da su suna gaba muna biye da su muka nufi cikin gidan, yayin da sojoji
biyu ke gaban mu.
wani lafiyayyen parlour muka bayyana cikin sa,nan da nan aka cike mu da kayan ciye-ciye da na sha.
munkai kimanin awa ɗaya zuwa can mukaji takun sauka daga step's a hankali na ɗago kaina wani mutum ne ya karaso cikin parlour'n cikin girmamawa gaba ɗaya ƴan cikin parlour'n suka mike tsaye,
a sannu ya karatsa ya zauna kan wani kujera lafiyayye,nan kowa ya zube yana mika gaisuwa,
nima dai ɗan tutsunawa nayi na gaishe sa,
ɗan shiru ne yabiyo bayan gaishe-gaishe sannan mutumin yayi gyaran mursa sannan yace
"Sannun ku da zuwa kune ba'in ko?".
waɗan da muka zo da su suka amsa da Eh.
waya ya ɗaga ya daddanna sannan ya kara a kunnen sa,
yayi magana zuwa can ya sauke wayar,
kana ya mike yadubi su Bappa yace su biyo shi,suka mike da waɗan da mukazo da su ɗin da sojojin da suke tsaye har lokacin a cikin parlour'n suka fita,suka bar ni ni da su Nasmah a cikin parlour'n.
tun da suka fita har akayi sallar azahar ina nan zaune har wajen karfe biyu da rabi, babban damuwa ta ma sallar da banyi ba.
can wani soja ya shigo yayi min magana cikin harshen turanci yace na biyo shi,
na mike na ruko hannun su Nasmah muka bi bayan shi.
muna fita wani mota ya nuna min na shiga,
direba na zaune cikin motar shikuma ya zauna mazaunin mai zaman banza, nan direba yaja motar muka fita a gidan.
tafiya muka yitayi har na fara tsorata da tafiyar,naɗan ji tsoro ganin dukkamsu ban san suba,
ganin mu nayi bakin wani ramɓasheshen get mai girman gaske,
aka buɗe mana get ɗin muka shiga shima tafiya mai tsawo mukayi a cikin wannan get ɗin kafin muka kuma isowa wata get ɗin,
nan mukayi ta wuce get-get kuma ko wanne da sojoji.
wata get muka iso mai kyau da tsaruwa muka tsaya nan kira yashigo wayar sojan, ya ɗaga bayan ya sauke wayan ya dube ni yace na sauko.
nafito jiki a sanyaye,
tafiyar kafa mukayi mai tsawo,
kafin nan muka iso wani kofa,
Hmm in da ranka ka sha kallo tsaruwar wannan guri bazai misaltuba,
sojoji ne a tsaye a gun duk kanin su foskokin su sanye da bakin glass,
nan suka shiga saka mana na'ura a jikin mu suna gwada mu,ni da su Naseem,kafin muka haura kan step ɗin da zata sada mu da kofar, nan kofar ma,
tafara bada wani sauti tana ɗaukar hotunan mu,abun mamaki da al'ajabi,
daga bisa ni kofar ta buɗe muka shiga,
sojan na gaba ina biye da shi a hankali,
koda muka kuma isowa wata kofar nan sojan ya tsaya wani sojan da ke tsaye nan bakin kofar shi yayi gaba, yayi min alama da na biyo shi,
koda muka kuma zuwa wani kofar ma, tsayuwa wannan sojan yayi kana sojan da ke tsaye a wannan bakin kofar yayi gaba da ni.
muna zuwa wata kofar mai shigen, kama dana farko yakuma ɗaukar mu a hota,ina tsaye ina kallon ikon Allah abun dai ya fara bani tsoro,
shima still anan sojan ya tsaya sojan dake wannan bakin kofar yayi ciki.
"Innalillahi ya ilahi ya lillahi".
abun da na furta kenan,
wani mashahuriyar katon parlour ne kamar ba a duniya yake ba,
wannan parlour'n muka shiga yanuna min gurin zama na zauna.
sai na janyo ƴaƴana na rungume su dan nasan sun gama gajiya da wannan tafiyar,
munyi zaman da yakai na 30min,
kafin daga can wata kofa ta buɗe wani mutum yafito yayi min alama da nazo na mike nabi bayan sa,
nan muka kuma shiga wani gurin na daban wan da yafi ko ina girma da tsaruwa.
muna shiga gurin can da nisa na hango su Bappa zaune kan wasu tsararrun kujeru,
numfashi na sauke,
cikin tsananin mamaki da kaɗuwa nake kallon wan da yake zaune kan kuje ran dake gaban su Bappa,
da mamaki nake lallon mutumin,
shugaban kasar mu na Nigeria ke zaune gaban su Bappa na karaso in da suke na zauna a kasa har lokacin mamakin ganin sa fal zuciya ta, mutumin da nake ganin sa a TV da mujallu,sai kuma cikin ɓarin baki nashiga gai da shi.
cikin sakin fuska fuska ɗauke da annuri ya amsa gaisuwar,
kai Bappa ya ɗan dukar cikin ladabi da girmama wan da yariga da yafi ka cikin girmama shugaba yace
"Ranka shi daɗe wannan itace yarin yar".
yafaɗa yana nuna ni.
annurin fuskar sa ya faɗaɗa idanun sa a kai na, ya jinjina kansa.
hannu ya miko yayi wa su Naseem alama da suzo, ai ko Naseem sarkin sabo ya mike ganin ya mike sai Nasmah itama ta bi bayan sa,
hannun su ya ruko yana faɗin
"Masha Allah sannun ku jarumai".
yafaɗa yana shafa kawunan su.
baki suka washe kamar sun san abun da yafaɗa shima yabisu da murmushi haɗe da yi musu wasa...
bayan wasu maganganun da yayi da na kusa da shi,
wan da duk kanin mu babu wanda yaji abun da suke faɗa, kana ya mike yabita wata kofa.
ɗaya daga cikin mutanen da suke zaune a gefen sa yadube mu yace wa wasu da ke gefen mu a tsaye sukai mu masauki.
nan muka mike muka bi bayan su wani masauki na musamman a ka kai mu, nan ma kowa da ɗakin sa.
anan muka kwana ɗaya washegari
da safe aka buga min kofa koda na buɗe breakfast a ka shigo da shi wan da ya kawon cikin harahen turanci yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login