Showing 18001 words to 21000 words out of 46406 words

Chapter 7 - HAMDAH part 2 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

7622

iso in da su Mama suke tsaye da ɗaya daga cikin Dr ɗin da sukayi wa HAMDAH CS,
ɗaya daga cikin nurse ɗin tadubi mama tace
"Tun ɗazu muketa nemanki Ina kayan babys da sauri mama tamika musu ledan dake hannunta su shige labour room domin su kimtsa babyn.
Mama ta dubi Dr tace
"Likita ya ita mai jegon dai?".
Dr ta juya tashige room ɗin dake gefe da labour room tana faɗin
"Babu komai in sha Allah har an fito da ita ma tana wannan room ɗin".
wuf Mama tayi zatabi bayan ta tayi saurin cewa
"A'a tsaya tukun akwai likitoci a kanta suna ai kin su bari su gama tukun".
tafaɗa tana shigewa cikin room ɗin.
ajiyar zuciya Mama ta sauke tanayiwa Allah godiya,
taja gefe ta tsaya idanunta akan kofar da akace HAMDAH na ciki.


Bayan wasu ƴan mintuna likitoci'n suka fito Mama na ganin da sauri ta matso in da suke tana tambayar su ya jikin nata,
sukace zata iya shiga yanzu.
cikin hanzari ta juyo zata shiga cikin room ɗin tajiyo Muryar nurse's ɗin da suka karɓi kayan jariri suna faɗin
"Yauwa mun gama ga baby's ɗin".
da sauri ta juyo da mamaki take kallon nurse's ɗin dukan su rike da baby,
sai tasa hannu takarbi guda daya na hannun wacce take kusa da ita tajuya zata wuce,
sai ɗayan nurse din tace
"Baki da me taimaka miki ne ga ɗayan fa,
ko kin bar min ne".
tafaɗa tana murmushi ɗayar tace
"Ai kuwa nima yaran sun tafi da ni Wlh ni ban taɓa gyara kyawawan baby twin's irin waɗan nan ba kallesu fa wlh ko ƴaƴan turawa bazasu nuna musu komai ba kai ni sai nagama sunfi min ƴaƴan turawan".
da maki Mama ke kallon su da jin abun da suke faɗa
tace
"Kuna nufin yanbiyu ne ta haifa duka waɗan nan ƴaƴan ta ne?".
tayi maganar cikin matukar mamaki.
dariya sukayi mata ganin yanda take maganar bilhakki,
Nurse ɗin ta mika mata ɗaya babyn tana faɗin
"Duk natane,yauwa na mijin shi aka fara cirowa kafin macen".
rungumar yaran mama tayi a kowani hannunta guda tajuya cikin tsananin farin ciki har da kwalla tanafadin "Alhamdullilahi Allah mun gode maka".
cikin hanzari tashige dakin da aka kai HAMDAH.
dasauri takarasa inda take kwance da yaran a hannunta tana fadin
"HAMDAH bude idon ki kiga abin da kika haifa".
jin Muryar mama yasani buɗe idanuna a hankali,
asannu nashiga juya kai na saiji nayi kamar an ɗaɗɗaure ni,
dasauri mama tamatso kusada ni ta ajiye yaran dake rike a hannunta a gefe na,tana cigaba da faɗin
"Allah mai iko kai sannu HAMDAH sannu kinji".
asannu najuyo kaina da kyar kallon yaran da mama ta ajiye a gefe na nayi kana daƙyar nabude baki murya can kasa nace
"Mama waƴannan yaranfa?".
sai da ta maso sosai kafin ta iya jin abun da nake faɗa,
fuska ɗauke da yelwataccen murmushi tace
"Dukkansu nakine".
cikin tsananin farin ciki da murna Mama ta ɗago ɗaya daga cikin yaran ta karkato shi saitin fuskanta
tana faɗin
"Kalli kyakkyawar mai gidan nan nawa
da sukayi ta baki wuya,ga kawata ma nan".
ido na kurawa jaririn yayin da naji wani irin mummunar faɗuwan gaba ya ziyarci zuciyata,
fuskar Ya SALEEM kaɗai nake hangowa kan fuskar jaririn,
idanuna na rumtse da karfi tare da kuma buɗe shi kan fuskar jaririn,
mai mugun kama da Ya SALEEM tamkar an tsaga kara.

Mama ta mai da yaron ta kwantar ta ɗago ɗayar tana faɗin
"Ga kawata nan tabar kallah masha Allah".
hancin babyn ta lakata tana washe baki da cigaba da faɗin
"Ikon Allah wannan girman ciki yayi yawa ashe dai kune kuka baje ciki".
kai na na rausayar gefe da kyar,
jin wasu zafafan hawaye sun zubo min kokarin danne zuciya ta daketa son fama min mikin dake cikin ta nake,
rumtse idanuna da karfi nayi duk yan da naso danne zuciya ta sai da na tuno.
fahimtar yanayin da na shiga yasa Mama tayi ta jana da hira duk da bana ammsa mata da ido kawai nake binta.
haka tayita kokarin gusar min da damuwar da take hangoshi cikin idona,
har sai da taga na saki raina,
har naɗan juyo da kaina ina kallon yaran,
Allah mai girma da ɗauka wai duk waɗan nan ƴaƴan a cikina a ka ciro su.


Mommyn twins ce



Ranan Azaune mama ta kwana rike kuma da yaran idan ɗaya yayi motsi sai ta aje na hannunta taɗau ki ɗayan,
duk san da na farka sai na ganta zaune tausayin ta yakama ni,
na tabbata tun da rana dana fara labour batasa komai a bakinta ba har kuma yanzu, domin gabakinta abushe,
haka tayi-tayi dayaran har gari yawaye.
washegari da safe
Zainabu suka zo da ita da wata makociyar Mama,sukazo mana da abun karyawa niki-niki.
suna rike da yaran a hannunsu kowa sai sanbar ka yake,
Zaunabu data kurawa ƴa macen ido tace
"Oh ikon Allah jibi waɗan nan yara wazai gansu yace tagwaye yara katin-katin dasu kamar haihuwar ɗaya,
kai sannu HAMDAH gaskiya kinyi kokari waɗan nan kam ai sai dai CS ɗin".
murmushi matar da sukazo da ita tayi tace
"Wlh kam yara tabar kallah ga wayo ni dai tun zuwan mu idanun su abuɗe suke".
Mama tayi dariya tana faɗin
"Waɗan nan awaye kazan birni ai tun jiya idanunsu a buɗe yake suna jin motsi zasu juya ido gun kamar masu jin magana,
kunga wannan bakyauyiyar kawar tawa idanunta a kan fanka, shi ko angon ido yakurawa kwan wuta".
dariya duk suka saka ai kuwa sai yaran suka shiga raba ido kamar sun san me ake faɗa,
Zainabu tace
"Ai kuwa yaran akwai wayo ga yan da suke kokarin juya kai suna jin magana"...

Haka suka yi ta kallon yaran cikin ban sha'awa.
nan mukata hira dasu sai kusan azahar sukatafi.
mama ta rakasu tadawo tana dawowa daga rakiyarsu nadubeta cikin yanayin gajiya da kwanciyar da tun jiya ban motsa daga in da aka kwantar da ni ba,
nace
"Mama dan Allah ki dagani nikam nagaji kokuma injuya gefe".
Mama tace
"Sunce bayanzu ba". dasaura nace
"To Mama kishin ruwa nakeji dan Allah kibani ruwa nasha".
dubana take cikin tausayawa da tsigar rarrashi tace
"Kiyi hakuri HAMDAH su sun fimu sanin dalilin da yasa suka ce kada a baki komai tun da ai kin sune ki kara hakuri dan Allah kibari likitocin suzo tukun".
kai kawai najuya cikin gajiya da kwanciyar guri daya gamugun ƙishin ruwan da nakeji...
karfe
huɗu na yamma har lokacin ina nan kwance duk yadda naso Mama ta ɗagani ko taban ruwa nasha fir taki.
kuka nasaka mata ina faɗin
"Ni dai nagaji nagaji ƙishin ruwa nake ji".
Ido Mama ta zuba min tana jijjiga baby boy ɗin dake ta zandara ihu tun ɗazu,ta bashi ruwa yafi a kirga da zaran ta cire fida a bakin sa sai ya sa kuka.
Ana cikin haka sai ga ɗaya daga cikin
Doctors ɗin da sukayi min CS yashigo,
yace
"Mama mai kikayi wa pationt din mu ne haka take kuka".
yafaɗa da murmushi yana karaso wa bakin gadon da nake,
Mama tace
"Wallahi tuntini wai so take a ɗaga ta tagaji kuma wai kishin ruwa take ji shine nace tayi haƙuri sai kunzo".
murmushi Dr yakuma cikin kwarewa da iya tafiyar da mara lafiya ya dube ni yace
"Idan zaki iya tashi to tashi".
nayi yunƙurin tashi naji Nakasa sai ji nayi kamar cikina yana buɗewa in da aka min CS ɗin,
ido na matse sai ga hawaye sharr.
Ido yaɗan kura min kana yace
"Sorry bari nurse's suzo su tai maka miki".
yafita ba jimawa nurse suka shigo suka ɗagani suka goge min jiki suka kimtsa ni,
kana suka cewa mama takawo ruwan zafi kadan a kofi akabani nasha,
sannan sukace na gwada kwanciya da kai na in zan iya,nan ma na kasa,su suka mai dani
suka kwantar dani. sukace wa mama taringa haɗa min milo inasha duk bayan awa daya domin zai taimaka
min yakawo min ƙarfi ajikina.
tace to insha'allahu nan suka fita...

Da daddare nurse's ɗin suka kuma zuwa,
yanzu kam cewa sukayi na tashi da kai na daƙyar na iya mikewa zaune, bayan sun gama gyara min jikina sukace na kwanta da gefe in zan iya shima nakwanta,
Washegari ma da kaina na tashi nurse's suka gama ai kin su suka fita,
Mama tasa min pillow a baya na na jingina dashi,
bayan nagama shan tea mai zallar milo da Mama ta haɗa min,
tadube Ni tana faɗin
"To tun da kin koshi kibashi nono yanzu kam kin ga dai tun jiya kuka yake,
ga ƴar'uwar sa ma yau ta tashi da kukan, yunwa duk suke ji".
Baki na tura dan tun jiya take ta bina nabashi nono toma ni ta'ina ma zan fara,
miko shi tayi taɗaura shi kan cinya ta sai dai bata sake shiba tana rike dashi ta ɗan gyara shi ta inda bazai fama min ciwo ba,
tace
"To ɗan gyara sai ki bashi"...
yana kama nonon nayi saurin fizge nonon a bakin sa tare da sakin ƴar karamar kara,
na yarfe hannu ina faɗin
"Wayyo zafi".
ai ko shima sai ya saki kuka yana cusa hannunsa cikin baki,
Mama
tace "Daure ki bashi kinji".
sai da Mama tayi ta lallaɓi na kafin na yarna na maida masa nonon bakin sa ina matse ido harda kwalla.
bayan yasha ta kwantar da shi ta ɗauko ta ita ma tasha.
kana tayi musu wanka
nan da nan kuwa sukayi bacci....★


Kwanan mu uku a asibiti kullum sai Zainabu ta ai ko mana da abinci.
zuwa yanzu kam jikina Alhmdllh dan har ina sauka na taka da kaina,
Muna zaune Mama nata jana da hira yayin da take ta yiwa yaran wasa.
Malam musa yashigo da sallama bayan an gaisa yake
tambaya haryanzu baban yaran baisamu isowa bane?
Mama tace
"Eh. a takai ce.
ƙasa nayi da kai na ina wasa da yatsun hannuna yayin danaji wani abu yataso yatokare zuciyata nan take naji ƙwalla yaciko min ido dasauri namai dasu,ta hanyar ambaton sunan Allah a cikin zuciya ta,
Har yanzu mutanen da suke hulɗa da Mama basusan ko wacece niba,
har yau Mama bata sanar musu koni wacece ba abun da kaɗai suka sani takuma sanar musu Ni ɗiyar kanin tane kuma mijina soja ne yana bakin ai ki haihuwa nazo,
rumtse idanuna nayi yayin da kwallar da naketa mai dasu suka zubo,
nakai hannuna nashare batare da nabari sun gani ba.
Malam Musa yace
"Ayya to Allah yataimaka yaune kwanan su uku ko? yakamata a musu huɗuba gashi kuma har yanzu bai samu isowa ba".
da sauri Mama tace
"Haka ne kuma inaga zuwan sa kam ma zai kai har bayan suna ai ko baza'a jira har sai yazo ba za'a yi musu huɗu ba,
Malam ayi musu huɗu ba kawai, yoo yaushe za'a zauna zaman jiran sa".
Malam musa yace
"To babu damuwa, shin yafaɗi sunan daza a sa ma yaranne?".
mama
tace "Eh". takalleni tare da faɗin
"Yayama sunan daya faɗa miki?".
shiru nayi kaina a kasa,
sai da mama ta kuma mai-maita
tan bayar kana nace
"Idris da Aysha"
tabbas babu sunan da ya dace da yaran face sunan Abbu da Inna, sun nuna min so da kauna da kuma gata. bakuma zan taɓa mancewa da su a rayuwa taba.
Malam Musa yace "Masha Allah yara zasuci manyan suna".
gyara rukon baby boy din dake hannusa yayi kana yazura hannunsa cikin aljuhu yaciro dabino,
Nan yayi Masa huɗuba da suna Idris kamar yadda addini yakoyar,
kana ya mikawa Mama shi yace
"Allah yaraya Idris bisa Sunnah".
Mama tace "Amin".
ta kwantar da shi ta dauko baby girl din ta Mika masa Nan ita ma yayi mata huɗuba,
kana yamikawa Mama tare da fadin
"Allah yaraya Aysha".
Mama takuma amsawa da Amin Amin,tare da masa godiya.
Nan yayi Mana sallama yatafi.....
Mama ta dubeni da murmushi dason gusar min da damuwar da take hangoshi kan fuska ta, ta kalli yaran tana faɗin
"Masha Allah kinwa Inna takwara ne ko wa kanki?".
ta faɗa tana murmushi,
ido na tsurawa babyn kana nace
"Wa Inna nayiwa takwara kamar yadda nima naci sunan ta".
dariya Mama tayi tare da lakata hancin babyn tana faɗin
"Kaga Aysha ɗiyar Aysha kakar Aysha uban giji yaraya ku da imani,
to me za'a rika kiran su yanzu kuma?".
tafaɗa tana duba na fuska ɗauke da murmushi.
shiru naɗan yi alamar nazari zuwa can nace
" *NASEEM DA NASMAH*"
baki Mama ta washe tana faɗin
"Iye Ah gaskiya sunan yayi kama dasu".
yanzu kam sai da mama tasani murmushi idanuna a kan yaran ina duba kamar da tace sunan yayi da su....★

Yau Zainabu da kanta takawo mana abincin dare da kuɗi naira dubu 5.
nan take cewa Mama malam Musa ne yabata rance,
ranar da tazo niman kuɗine tayi wa malam ɗin magana ko yana dashi,
yace
Wlh baya dashi sai yau ya samu shine yabata takawo.
Mama tayi ta mata godiya tace dan Allah tayi masa godiya kuma in sha Allahu zata biya da hannunta da yar dar Allah.
Nan da nan kuwa takai ragowar kuɗin da ake binsu a asibitin.
Washegari da safe aka sallame mu....
ranar da muka dawo gida a ranar mama tafara awara,na tausaya mata kwarai,
ranar sai da nayi kuka dan nasan dan ni ta fara sana'ar a yau wan da yakama ta ace hutawa take da ɗawai niyar asibitin da ko baccin kirki batayi, sai gashi muna shiga gida tasoma wani ai kin...
ana gobe suna da yamma bayan Mama tayi wa yaran wanka muna zaune ina cin abinci,
Mama na goye da Nasmah yayin da Naseem ke rike a hannunta tanata jijjiga shi, Mama ta dube ni tace
"Wannan mai gidan fa in baiji motsi a bakin sa ba baya gane wa".
fuska na kwaɓe nace
"Mama yanzu fa suka sha".
"To yaro shi ina ruwan sa ciki kawai yasa ni gama dai kiba shi yasha,
ga kawata ma na kan motsi".
Kamar na kurma ihu haka naji,
yanzu suka sha babu jimawa gashi yanzu wai suna nima,
cikin tura baki nace
"Allah kaɗan zan basu anjima kuma abasu kunu".
Mama tace
"Kunu kuma?".
nace "Eh". dariya tayi tace
"To shike nan yanzu dai ki basu susha".......

Washegari yakama ranar suna,
da sassafe Mama tayi min wanka kana tayiwa Nasmah da Naseem,
nashirya cikin doguwar riga ɗaya daga cikin kayana da nazo dashi tun wancan lokacin yaɗan kasa min sabo da ciki sai na ajeshi bana sa shi, shi yana nan har yanzu da ɗan sabon tar sa.
ɗan ribar awara da tasamu na kwana biyu
da shi tayi cefane ta siyi shin kafa ta haɗa da sauran waken kosai suka girka abinci da Zainabu da tun da safe tazo.
da rana makota suka shishshigo,
Mama mai yin biki ne tana da kokarin shiga wa mutane biki, duk wan da take yin biki da su kowa sai da ya kawo mata rigar baby wasu na maza wasu na mata da omo da sabulu har da man shafa wa.
Naseem yasamu kaya kala huɗu yayin da Nasmah ma tasamu kala huɗu.
da yamma kowa ya watse....
Bayan suna Mama tafara niman kuɗi ba kama hannun yaro domin biyan bashin da ake binta,
ba iya sana'ar awara da kosai kaɗai ta tsaya ba har da kayan miya tana sara tana siyar wa,
da duk wani abu na nasa'ar cikin gida da tasan zata sami riba a kansa tana siya ta siyar.
cikin yar dar Allah da ikon sa yadafa mata duk abun da zata taɓa na sana'a sai ta sami riba a kansa...
ranar da muka yi arba'in ranar ta kai wa Zainabu da malam Musa kuɗin su,kamar yan da tayi musu alkawarin bayan suna zata biya su takuma jajirce wajen nima har ta samu,
tayi ta musu godiya.....

Tun daga ranar hankalin ta ya kwanta ta kuma mai da hankalin ta wajen kula da Ni da kuma ƴaƴana,
duk wani ribar da zata samu a kanmu yake kare wa.
yanzu nawar ke garau idan ka ganni bazaka ce CS aka min ba, nakan ji mutane da dama suna cewa jikina mai kyau ne bana da kan jiki.....
Haka mukayi ta lallaɓa rayuwa nakuma daure da juriyar shayar da yaran,sai dai na rame kwarai suko kamar hurasu ake, sunata girma da kuma kara wayo sosai,
lokacin da suka cika wata uku,
Mama ta haɗa musu garin kunu na alkama waken suya da gyaɗa,
nan ne naɗan sami sauki,
da shi muka cigaba da rainon su...

Ranar wata asabar..........!★






Mommyn twins ce



Ranar wata asabar hakan yayi dai-dai da watan su Naseem huɗu da sati biyu,
Zaune muke a tsakar gida, ina rike da Naseem a sakiyar kafafuna dan alokacin suke koyon zama.
Mama na goye da Nasmah tana bacci, ita kuma tana ta ɗan aikace-aikacen ta.
Sallama mukaji daga bakin kofa da karfi, ba Mama kaɗai ba hatta ni sai da naji wani irin muguwar faɗuwar gaba dajin muryar mai sallamar,
yau kusan sati ɗaya kenan Alhaji Mamman sai yayi sallama a gidan kullum sai yazo maganar kuɗin hayar sa, wan da yanzu ya ninku yazama na shekara biyu da rabi.
takuma sana diyyar mune hakan ya faru kula da Ni da ƴaƴana shi ya hana ta ajewa Alhaji Mamman kuɗin hayar sa,
yunkurin mikewa nashiga yi jin yacigaba da kwaɗa sallamar ba ko kakkautawa,
kafin na mike ma ya sako kansa cikin gidan yashigo,
yana faɗin
"Fasuma kinsan dai ba gidan mijin ki bane ba,kuma bamu haɗa kuɗi da ni da shi mun siya ba,
sannan kuma koda ace ma mun haɗa kuɗi da ni da shi mun siya,
kinsan dai yanzu yariga da ya mutu kuma dole a cire min nawa a ciki,
bare kuma gida gida nane ba nashi ba ko bulo ɗaya bai ɗaura a kan gidan nan ba,
bare ki zauna kice kina cin gadon sa,
dan haka kifita min a gida yau babu afuwa babu rangwami,
kifita min a gida yau zan saka ƴan haya acikin gida na,
gasu nan ma munzo tare da su,
ina bukatan kuɗi dan sabo da kuɗi na tara kafin na gina gidan,
ga ƴan haya nan mun iso da su ga kayan su can a moto dan haka ki fita kibasu ɗaki."
yakaraso ciki yana muzurai tare da cigaba da faɗin
"Ganan masu shiga gida sun iso ke kaɗai suke jira kifita kibasu ɗaki,
dan yanzu ɗakunan gida nasune su sun iya biyan kuɗin haka,
sannan kuma
bawai na bar miki kuɗin haya da na ke binki na shekara biyu da rabi bane ba,
ina binki bashin su kuma zaki nimo kibiya ni kaya na babu rangwami acikin watannan zaki biya ni in baki bada ta daɗi ba zaki biya a hannun hukuma."

Cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa na ɗago Naseem dake hannuna na goya shi,
na mike tsaye yayin da Mama tarika haɗe hannayen ta biyu cikin matukar tashin hankali tace
"Dan Allah Yaya kayi hakuri insha'allahu ina nan ina kan tara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login