Showing 27001 words to 30000 words out of 46406 words

Chapter 10 - HAMDAH part 2 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

7627

mangoro gwaiba dabino kwara kwakwa da kuma tupa,
gasunan kasa-kasa. gindin bishiyoyin kuwa yashine fari soll amalale agurin kamar an share gurin babu ko datti har zuwa bakin gaɓar ruwan.
daga gurin bishiyoyin zuwa bakin gaɓar ruwan da ɗan tazara kaɗan,
kafin ai nihin babban ruwan akwai wani ruwa a ɗan gaban bishiyoyin sai dai shi ɗan kaɗan ne da alama dai ruwan idan yayi yawa yana haurowa har gurin idan ya koma kuma sai ragowar ya tsaya a ɗan wannan ramin.
ruwan fari soll kamar babban ruwan kogin nan da yake gudu....

A hankali natako zuwa gun yashin nan wato karkashin bishiyoyin nan,
na sauke su Naseem na zaunar da su,
da sauri cikin jin matsananciyar kishin ruwa na nufi in da wannan ruwa ɗan kaɗan ɗin yake na sun kuya na saka hannuna narika ɗiba ina sha,
sai da nasha na koshi,kana narika ɗibawa da hannuna ina zuwa in da su Nasmah suke na basu suka rika sha,
haka narika kai wa da komowa ina ɗiba ruwan a hannuna ina kai musu suna sha,
haka narika yi har sai da na tabbatar da sun koshi,kafin na kyale su.
na koma gurin ruwan nayi al'wala na dawo in da suke nayi sallar azahar da nake tunani yanzu lokacin sa yayi.
ina idarwa na mike lokacin rana yafito sosai na ɗago Naseem na tuɓe masa kayan jikin sa da yayi wani irin datti dattin har ya wuci misali,
na ɗauko shi muka taho bakin wannan ruwan da muka sha nakuma yi al'wala da shi, na saka hannu cikin ruwan kasan cewar rana yafito hakan yasa ruwan yaɗan yi ɗumi sai narika ɗiba ina wanke masa jikin sa na wanke shi sosai kana na ɗago shi na goyashi,
na ɗauko Nasmah ma itama na tuɓe mata kayan ta itama da yayi matukar datti kamar bana ɗan adam ba,
na wanke mata jikin ta sosai kana na rungume ta muka koma gindin bishiyoyin,
nan da nan kuwa sukayi bacci ina zaune rungume da su,tabbas datti wani sashi ne mai hana ɗan adam sakewa da jin daɗi ɗan rage musu dattin jikin su nayi sai gashi sunyi bacci cikin kankanin lokaci.
ɗankwalin kai na, na cire na shin fiɗa a kasa kana na kwantar da Nasmah dake hannuna,
sannan na kunce Naseem na shinfiɗa zanin goyon su na kwantar dashi sannan na ɗago Nasmah a kan ɗankwali na na mai data kan zanin goyon kusa da shi,
hijabina na cire na rufe su da shi kana na ɗauki ɗan kwali na na ɗaura.
gurin ruwan na koma na wanke musu kayan da na tuɓe musu na shanya kan yashin gurin, kana na tuɓe kaya na na wanke jikina duk da ba soso ba sabulu amma naji da ɗin saka ruwan a jikina.
na wanke kayan su da na tuɓe musu na shan ya kan yashi.
sannan
na dawo in da suke na kwanta a gefen su wani nannauyar bacci yaɗau keni.
bacci ne mai nauyin gaske yaɗauke mu dukan mu ban farka ba sai can dadaɗe wa koda na tashi na fahimci cewa yamma tayi sosai dan guri yayi duhu,
al'wala nayi nazo na gabatar da sallar la'asar,
ko da na idar tagumi nayi a gaban su na zuba musu ido,
sun rame sun dishe wagasu kananun kuraje da suka fito musu duk jiki,
ido na rumtse yayin da tausayin su ke daɗa rasa ni har sai da wasu zafafan ƙwalla suka zubo min batare da nasan da fitar suba.
nakai hannu nashare ina cigaba da kallon su a raina nake faɗin
"Ya Allah ka tseratar da su ka fidda su a cikin wannan kungurmin daji"...

A hankali na mike tsaye jin cikina na murɗan yunwa na sinko ƴaƴan itatuwa da yawa wanda na sani har da wan da bansan su ba duk wan da na sinko na gusura najisa da zaki sai na kama ci,
nan su Nasmah suka farka da kuka na ɗago su na basu abincin su suka sha wanda sai dai susha ne kawai bawai kodun ya koshar da su ba.
suna rungume a jikina a haka guri yarufa sosai lokacin tuni sun koma bacci sai nayi musu addu'a na kwantar da su naje nayi al'wala bayan na idar da sallar magriba da isha sai na kwanta gefen su.
Washegari naji daɗin bacci a gurin sosai bakamar na sauran kwanakin da mukayi a cikin dajin ba,tabbas nan gurin da muke zaune wata rahama ce dan kuwa anan muna samun ruwan sha da ƴaƴan itatuwan da zance,da ruwan da zanyiwa ƴaƴana wanka da kuma ni kaina duk da bada soso da sabulu muke yin wankan ba.
da waɗan nan abubuwan mukayi ta rayuwa a gefen ruwa har na tsawon wata guda.
gurin ya zame mana tamkar gida kuma ɗaki,
a gurin na kan iya ajiye su na ɗan zaga ta bayan bishiyoyin nan na sinko mana wasu kalar kayan itatuwan nakawo mana dan yanzu har su Naseem ma ci suke mu samman abu mai ɗan laushi....★


Zaune muke bayan na musu wanka suna kan kafata ina ta yi musu wasa sai ɓarkewa da dariya suke,
cikin dabara na sauke su namike naje nayi wanka kayan su dana wanke musu ɗazu da nayi musu wanka nashan ya kan yashi yabushe na ɗauko nazo na sa musu.
ina zaune a gefen su Naseem ya lankwasa kafar sa ya rarrafo yazo in da nake,
cikin tsananin farin cikin ganin yau yaron ya fara rarrafe nashafa kansa ina dariya da faɗin
"Iye lallai Naseem wato kayi wa Nasmah wayo ko kai ka fara iya zama shine kuma zaka riga ta iya rarrafe ko,
amma dai zaka barta ta iya da wuri itama ko?".
baki yawashe kamar yasan abun da nake faɗa,
na kama kuma tun Nasmah ina faɗin
"Kema ki dake kinji kada yarika yi miki wayo da yawa".
nayi maganar cikin shauki,
itama dariya ta saka min duk na rungume su ina dariya,
a take kuma naji wani kuka yazo min sai kuma na fashe da kukan.....
cikin ƴar dar Allah bayan sati ɗaya kuwa Nasmah itama ta fara rarrafe.
tun da naga rarrafen su yafara yin kwari, sai bana yin nesa da su dan gudun kada su rarrafa suje su shiga cikin ruwan nan idan zan je tsinko mana abun da zamuci sai na ɗauke su mu tafi tare,
ko bacci nake ji har idan idon su biyu bana yar da natafi na barsu su idan su biyu,
dan duk lokacin da naje na musu wanka Naseem yarika zillewa yana son shiga ruwan yarika bori da shure kafafu wai sai dai na barshi yashiga ruwan,
shi yasa nake jin tsoro kada wata rana nayi bacci yace zai je yashiga ruwan bugu da kari ma zai iya tunkarar babban kogin nan,
to haka zan yi ta zaman gadin su har sai sunyi bacci kafin nima nayi.....


Zaune nake na buga uban tagumi nayi shiru ina lissafa kwanakin da mukayi a cikin daji tabbas yau idan ban mance ba kimanin watan mu biyu kenan acikin dajin,
wasu hawaye ne suka zubo min na share su.
Ikon Allah haka zamuyi ta rayuwa a cikin daji har mu mutu karshe namun daji sucinye mu,
tausayin kaina da na ƴaƴana ya kamani sai na rungume su na fashe da kuka.
ganin sunyi bacci na shin fiɗa musu abun kwanciyar su wato zanin goyon su,
na janyo hijabina na lulluɓe su,
na mike na soma tafiya..
kallon sama nayi hadari ya haɗu bakikkirin daga can kasa sai walkiya ake da rugugin tsawa da alama dai anata zabga ruwa daga can da nisa,
ina tsaye ina tsinko abun da zan ci daga can nesa narika jin kugin ruwan nan yana karuwa sosai ba kamar nasauran kwanaki ba ƙugi ne sosai mai matukar amon sauti sosai.
da sauri na juya na fito daga cikin bishiyoyin na nufi in da su Naseem suke kwance cikin hanzari.
Daga can na hango ruwan yana wani irin gudu da kugi daga can da nisa yana wani sama da kasa.
Huff na ɗaga Nasmah na goya ta kana ɗauki Naseem da gudu na juya ganin ruwan
yana haurowa a hankali inda muke yanata taruwa a hankali har ya wuce idon sawu na,
daga can cikin kogin kuma yana wani irin gudu yana yin sama da kasa sai ruwan ya haɗu da junan sa ya fansalu sai yayi sama sannan ya koma kasa.
gudu nake da iya karfi na nayi bayan dutsai cikin sansanin tashin hankali galin ruwan ya iso inda muke zama ya mamaye gurin wan da yake gudu daga can kuma sauran kiris yakaraso,
bayan dutsai da na ɓoyen ma tuni ruwan ya iso har gurin,
cikin kaɗuwa da tashin hankali nasoma hawa kan dutsan da ko a mafarki ban taɓa tunanin zan iya hawan sa ba sai gashi na haura kan sa da goyo da kuma wani ɗan a hannuna can kuma saman sa sosai.
kan kace me ruwan yataho da wannan kugi da ambaliyar da yake,
gurin da muke zama yadawo tamkar cikin ainihin kogin hatta bishiyoyin nan sai da ruwa yahaye kansu,
duk da girma da tsawon da dutsai ɗin nan yake dashi sai da ya kusa haurowa sama in da nake tsaye jikina na cirawa,
rumtse idanuna nayi nakuma buɗewa cikin ruwan da yake wani irin gudu da kugi, ina ambaton sunan Allah, yau kam nasan mutuwa ce yazo mana babu makawa ruwa ce zata zamo ajalin mu,zata tafi da mu mu kuma mutu a cikin ta.
kankame ƴaƴana na kuma yi nagama sadakarwa na mika wuya ga mutuwa gaba ɗaya.
wasu irin halittun ruwa narika gani daban-daban wani abun ma idan nagani rufe idanuna nake da karfi har sai ya wuce kafin na buɗe,haka sukayi ta wucewa a kan ruwan,
wani abun da yadaɗa firgita ni da bani tsoro daga can najiyo guɗa mai karfi a can tsakiyar ruwan guɗa mai tsawon gaske babu jan numfashi ko sauke wa,
ido na zuba sosai daga can in da guɗar ke tashi sai dai banga komai ba sabo da sakanin mu da nisa kuma da alama daga can kasa abun ke wuce wa.
sai narika jin kamar iska tana jana kuma karfin iskar tacikin ruwan ne,kuka na fashe dashi na durkushe kan dutsai ɗin na kankame jikina,ina ambaton sunan Allah.
har lokacin ban fasa jin iska na kokarin jana ba,
a hankali guɗan da ake yarika raguwa alamun yana yin nesa da ni,
iskar da ke jana kamar zai faɗar dani cikin ruwan sai yarika sassauta, lokacin da na dai na jin sautin guɗar nan gaba ɗaya iskar ta tsaya.
abun tun sassafe sai yamma can kafin ruwan yafara sassauta gudun da yake, yana sassauta yana yin kasa-kasa,
a hankali yarika yin kasa yana wuce wa har ya dawo in da yake,
Numfashi mai cike da zallar tsoro na sauke a sannu narika bin gurin da kallo har zuwa gurin da muke zama,
yashin ya daɗa wankuwa yayi fari soll sai dai har lokacin da jikan ruwa sosai a hankali nafara kiciniyar sauka daga kan dutsan nayi matukar mamakin yadda akayi na iya hawa saman dutsan,
daƙyar na iya sauka kasa.
a hankali narika takawa in da kafata har yana lumewa cikin saka sabo da har lokacin da dam shin ruwa,
a hankali na matsa can gefe in da shima akwai damshin sai dai ba kamar in da muke zama ba.
ranar a nan muka kwana cikin ciyawa,
sai dai ban yar da na rumtsa ba dan gani nake kamar ruwan zai dawo....

Washegari da safe gurin ya daɗa sha ya tsantsame sai dai har lokacin da ɗan damshin sai dai ba kamar na jiya ba,
sai da rana yafito sosai kana
a hankali na ɗauko su Nasmah muka dawo gurin zaman mu,
ido na kurawa kogin nan ganin yadawo yan da yake da, kamar bashi bane jiya yayi ta hauka Allah mai iko.
ɗan kwalin kai na na kunce na shin fiɗa a kasa kana na zaunar da Naseem a kai ina faɗin
"Zauna kada ka sauka kasa kaji gurin da sanyi".
da sauri na kunco Nasmah da take ta musu-musu tana kuka a abaya,
na zauna na basu abincin su,
sai dai har lokacin bata fasa kananan kuka ba,
jijjiga ta nashiga yi ina faɗin
"Yi hakuri Nasmah nasan wan ka kike so kuma nasan ruwan nan akwai sanyi kibari rana yadaɗa yin zafi idan ruwan yayi ɗumi sai na muku".
nayita jijjiga ta.
zuwa can an jima
jin rana yadaɗan yi zafi sosai sai na tuɓe su na dubi Naseem da ke zaune yana ta wasa da yashin gurin nace
"Zauna na fara yi mata wanka sai na ma ka ko".
na mike da ita a jikina na isa gurin ruwan da muke wanka, ruwan yada ɗa yin fari soll,
kasan cewar rana ya taso ruwan har yana kashe ido sabo da tsabar hasken da ya kara,
a hankali na fara yi mata wankan ina yi ina kawar da kai na daga kallon ruwan saboda kashe min ido da yake, tamkar hasken ranar a cikin ruwan yake.
koda na gama yi musu wankan.
babu jimawa sukayi bacci,
mikewa nayi na koma gurin ruwan domin yin al'wala, na sun kuya ina ta kare fuska ta da hasken rana ke haska cikin ruwan yana kashe min ido, na saka hannu cikin ruwan a hankali na ɗibo na fara yin al'walar, na kuma mai da hannuna a karo na biyu, da sauri na ciro hannun jin na taɓa wani abu,
sai kuma na mai da hannun a hankali jin kamar dutsai ne na taɓan, a raina nake ai yana cewa ai dutsan yashi ne,
na cusa hannuna nakuma ɗibo ruwan sai na haɗo da yashi da wani farin dutsai, ina ɗago hannuna hasken rana ya haska dutsan tamkar wutan lantar ki mai hasken gaske. da sauri na rumtsa idanuna jin hasken har cikin jijiyoyin idanuna, cikin hanzari na watsar da yashin gefe ina mammatse idanuna,
nayi al'walan da sauri na bar gurin...
koda yamma tayi da nazo yin al'walan la'asar lokacin rana tayi sanyi hasken ruwan yaɗan ragu,
ina saka hannuna cikin ruwan nakuma ɗauko dutsai ɗin,
A hankali na ɗago shi narika juyashi a hannunna dutsan fari soll mai kyau da shi sai kyalkyali yake duk da kuwa babu hasken rana,
narika kallonsa gwanin ban sha'awa.
A hankali na mika hannu na ɗauko ɗayan da ɗazu nayi wurgi da shi na haɗa su ina ta juya su cikin sha awa,
nakuma saka hannuna cikin ruwan nayi ta laluɓo duwasun ina ciro su sai da naciro guda takwas na haɗa da biyun hannuna suka zamo guda goma,
bayan na gama al'walar na koma gun su Nasmah a kan abun goyon su na zuba duwasun,
ina zubawa kuwa da sauri har suna rige-rigen ɗauka sukayi ta wasa da shi,
nima ina idar da sallar na zauna nayi ta tayasu wasan da duwasun gwanin ban sha'awa da kyau da ɗaukar ido.
dariya nayi ganin yanda suke wasa da duwasun su ɗauki wannan su wurga sai subi sukuma ɗauko wa,
nace
"Kuma yayi muku kyau ko ai dutsan mai kyau ne nima wlh yayi min kyau kuyi wasan ku da shi".
nafaɗa da murmushi ina daɗa tura musu duwatsun gaban su...

Washegari ko da rana yafito dukan su na kwasa naje musu wanka Nasmah na goye sai na fara yi wa Naseem ko da na gama mishi, sai na saka hannuna nayita laluma cikin ruwan can na ciro dutsai ɗin guda ɗaya na dunkule shi cikin hannuna na cusa masa cikin hannunsa ina faɗin
"Gashi na karo muku abun wasa dun kule shi a hannunka kar ya kashe mana ido".
na kunce Nasmah na goya shi itama nayi mata wanka kana na laluɓo mata guda ɗaya na saka mata cikin hannun ta nace
"Kema ga naki".....★


Zaune muke muna cin kayan itatuwan dana sinko mana shiru nayi tare da kasa kunne daga can da nisa nake jiyo muryar kukan shanu,
da sauri na mike tsaye ina cigaba da baza kunnena ina son gane in da kukan shanun yake fitowa,
duk da daga ji yana da nisa da mu sosai,
wani irin farin ciki ne da murna ya lulluɓe ni,
dan na tabbata shanu bazai zauna shi kaɗai cikin daji ba sai da mutum.
cikin tsananin farin ciki da murna na sunkuya da sauri naɗau ki Nasmah ina faɗin
"Kuzo muje naji kukan shanu a tacan wata kila mu sami ɗan uwan mu bil adam a gurin".
ina ɗago zanin goyon su duwasun da suke wasa da shi suka zubo kasa,
banko bi ta kan su ba na goya Nasmah da sauri na ɗau Naseem da sauri nasoma tafiya.
har nakusa fita daga cikin bishiyoyin sai na juyo ina juyowa kuwa,
na hango duwasun suna wani irin walkiya kasan cewar lokacin rana yafara tasowa,
Naseem dake hannuna kuwa tsalle yarika yi yana nuna duwasun da hannu yanata kokarin zame wa a hannuna,
murmushi nayi nace
"Oh Naseem dutsunan wasan ku ko bari naje na ɗebo muku".
na juya da sauri na ko ma gurin ɗankwalin kaina na ciro naɗibi duwasun duka na zuba cikin ɗan kwalin na ɗaure na rike a ɗayan hannuna,
na mike da sauri muka kama tafiya.
ta in da nafi zato da tunanin tanan kukan shanun ke fita na ɗau hanyar da sauri.
sai dai munyi tafiya mai nisan gaske amma ban ga wani alamun shanukai ba hasali ma kukan su da nake ɗan ji yanzu na dai na, har na fara tunanin wata kila ma kunnena ne yajiye min ba dai-dai ba.
a gajiye na ja na tsaya tare da waigawa baya a raina nake faɗin
"Zan koma kawai gara rayuwar can ya fiye min na ko ina acikin dajin nan".
ga mamakina sai naga nayi nisa sosai dan ko katon dutsai ɗin nan bana hangowa na juya da zummar komawa bakin kogin sai kuma na hakura ganin nayi nisa sosai.
gashi kuma yamma ta fara yi sai na zauna kawai a gurin a nan gurin muka kwana washegari da safe ina zaune ina ɗan gyangyaɗi dan jiya ban samu nayi bacci ba dan acikin sun kuru muka kwana, kukan shanun nan irin na jiya shi ya farkar da ni firgigit na nimike da sauri.........!★




*Na jiya da gobe na baku*👌🏻😆




Mommyn Twins ce



Zunbur na mike tsaye jin da gaske ba wai ko kunne na bane ke yi min karya kamar yan da jiya nayi tunani,
da sauri na ɗauki Nasmah na goya ta,
sannan na ɗauki Naseem na rike shi,
na ɗauki ɗan kwali na da na ɗaura musu duwatsun wasan su na rike a ɗaya hannuna.
cikin sauri mai haɗe da gudu narika bin hanyar da nafi sammani da tunanin tanan ne kukan shanun ke fi.
nayi ta tafiya idan naji shanun sun dai na kuka sai na tsaya na huta idan duka cigaba sai na mike da sauri nacigaba da tafiya,
haka nayi ta tafiya ina yi ina hutawa duk san da shanun sukayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login