Showing 30001 words to 33000 words out of 46406 words
shiru idan suka cigaba da kukan sai nima nacigaba da tafiya ta in da nake jiyo kukan su daga can nesa sosai.
nayi tafiya har na godewa Allah.
ina zaune a gindin wata bishi ina hutawa gaba ki ɗaya jikina yayi sanyi dan tun ɗazu da shanu sukayi kuka basu kuma ba,
har nafara cire rai da sake yin kukan nasu zunbur na muke jiyo sautin su daga can kasa kuma yanzu nafi jin murtar nasu yafi kusa dani akan na ɗazu.
da sauri na mike na soma tafi
ɗan tafiya kaɗan nayi da sauri naja
burki ganin rami a gabana,
in da nake tsaye kuma tudune mai tsawon gaske,
dan saura kiris na zurma kafata kasa.
daga can kasan shima duk daji ne da bishiyoyi,
daga kan tudun in da nake tsaye ina hango shanukai ɗin can da nisa suna ta kiwo kasan cewar a kan tudu nake.
kallon kasa nayi mai uban nisa da tsawo
"Taya zan iya sauka a nan gurin".
nafaɗa ina daɗa kallon kasan.
a hankali nafara bin gefe tacan ɗaya ɓarin gefen dama na,
ganin tacan ɗin bai kai in da nake tsawo sosai ba,
a hankali nafara sauka ina takawa a hankali,sam naki yar da na kalli kasa sai naga ya daɗa yi min nisa kaina kuma sai yarika juyawa sabo da nisan sa,
nayi rabin saka daga saunin sai kawai kafata ta sule na zame muka rika gungurawa kasa tuni su Naseem suka saki kara mai karfi,
kan kace me Naseem ya suɓuce a hannuna ya ganaga can yafaɗi kasa,
Nasmah da ke baya na kuwa mukarika gungurawa da ita, cak numfashi na ya tsaya dan ganin ina kokarin isan kasa da baya kamar an juyani sai kawai na faɗi da gefe a kan hannuna.
kara dukan mu muka sake da karfi cikin azabar jin yadda na faɗi kan hannuna tamkar hannun zai ɓalle yabar jikina.
nayi-nayi na tashi na gagara tashi nafi minti goma kwance ko kyakkyawar motsi na kasa, ina kallon
Naseem yashe a can gefe yana ta zandara ihu,
Nasmah ma sai ihu take tana goye a bayana har lokacin...
Nayi ta yunkurin tashi na kasa da kyar na kai ɗaya hannuna na kunce zanin goyon ta kwanta gefe tana cigaba da tsala ihu duk jikin ta ya kwakkwar jane,
hannuna da na faɗi a kansa na ɗagosa da kyar kana da kyar na iya mike wa zaune.
yayin da hannun da na faɗi a kansan ke min wani irin zugi da raɗaɗi,
da kyar na yunkura na mike ina ɗingishi nazo gun da Naseem yake kife a kasa yana ihu,
na zauna na ɗago shi da ɗaya hannuna mai lafiyar,
nashiga kakkaɓe masa jikin sa ina jijji gashi,
shima duk ya kukkuje a.
Nasmah ta rarrafo tana kuka ta zo in da muke na janyo ta na cigaba da rarrashin su,
duk abun da nake cikin dauriya kawai nake dan nima duk jikina a kukkuje yake,zafin raunukan jikina bai kai na hannun da na faɗi a kan sa ba.
duk raunukan jikin yaran sai jini yake fidda wa.
rungume su na yi tare da fashewa da kukan azabar da hannuna yake min, ko matsi nayi da hannun sai naji zafin har cikin raina.
Mun jima zaune agurin jin tamkar karamin zafin ake a hankali na lallaɓa da kyar na mike,
na kamo Naseem da hannun na mai lafiyar na ɗagoshi da kyar na iya goya shi, dan shi yafi Nasmah jin ciwo.
ina matse idanuna hawaye na zuba cikin jin azaba,
sannan na ɗauki Nasmah na rike ta
a ɓarin hannuna mai lafiyar,
gefe na na waiga in da ɗankwali na dana ɗaura musu duwatsun wasan su yafaɗi can gefe shima na isa na ɗau ka da hannuna mai ciwon,
Jin wani irin zugi da hannun yayi min sai na sake ɗankwalin kasa,
na juya ina faɗin
"Naseem Nasmah bazan iya ɗauka muku abun wasan kuba hannuna yana min ciwo idan na samu wasu zan ɗiba muku a hanya".
a sannu na soma tafiya ina ɗaga kafata ahankali-ahankali,
sai kuma na tsaya a raina nake faɗin
"To yanzu idan na tafi na bar ɗankwali na anan a ina zan samu abun da zan ɗaura a kaina idan na cire hijabi na na rufe su Nasmah da shi?".
nayiwa kai na tan bayar,
idanuna na rumtsa nasan idan na ɗauka hannuna zai min zafi.
a raina nake ayyana na kunce Duwatsun na zubdasu sai na ɗauki ɗan kwalina nasan shi bazai min nauyi ba.
na koma in da yake na ɗauki ɗan kwalin ina kokarin kuncewa nayi nayi na kunce na kasa saboda da hannu mai ciwon ne jin hakan yana daɗa kara ramin zugin hannuna ne sai na bari.
na zaunar da Nasmah a kasa Sannan naɗan kunce zanin goyo na cusa ɗan kwalin sakanin bayana da jikin Naseem,sai na mayar na ɗaura,
kana na ɗauki Nasmah muka fara tafiya a hankali.
dan yanzu bana iya tafiya da sauri dan duk jikina ciwo yake min ga su Naseem har yanzu suna ta kuka.
Idan muka ɗan tafi kaɗan sai na sauke su na huta kana muku ma ci gaba,
Abun mamaki munyi tafiya mai nisa amma har lokacin bamu iso in da shanun nan suke ba, daga can saman tudun da muka gangaro da nake hango su banyi zaton zanyi irin wannan tafiya mai ni haka ba kafin na iso su.
a haka dai nayi ta tafiya har na iso kusa da su,
wasu matasa Fulani ne guda biyu suke kiwon shanun,suna tsaye can gefe sai dai na lura basu san da zuwa na gurin ba duk da dai sakanin mu da ɗan tazara,
a sannu na isa gindin wata bishiya na zauna kana na sauke su Naseem,
nayita rarrashin su Nasmah har sukayi bacci.
muna nan zaune a gurin har yamma sai sannan makiyayan nan suka fara kaɗa shanukan,sunayin gaba,
Ganin haka na mike da sauri na ɗauki su Nasmah narika bin bayan su duk inda sukayi ina biye da su,idan suka tsaya na tsaya idan suka cigaba da tafiya nima na bisu.
haka dai mukayi ta tafiya har naji badaɗi gashi babu halin nace zan tsaya na huta sutafi su barni,
tafiyar nake ina matsar ƙwalla sabo da tsaɓar gajiya gajikina da ya daɗa kara yin tsami,
muna nan muna tafiya har guri yafara rufawa.
can naga shanun sun tsaya kana a sannu naga sunayin kwana can na hangi bukkoki gefen bukkar cikin wani gurin da a ka zagaye shanun suka shiga, nan makiyayan suka fara ɗaure su,
a sannu na karaso gurin sai na tsaya gefe da garken shanun ina ta raba ido,
Fulani mazaunan gurin sunata harkokin su wasu daga kusurwa daban-daban suna ta ɗaure shanukan su da alama suma yanzu suka dawo daga kiwo,
numfashi na sauke tare da yin murmushi cikin zubda ƙwalla gani na acikin mutane wan da nagama fidda sammanin yiwuwar hakan,
a hankali na tako na tsaya kusa da garken shanun....
wani dattijo ne yafito daga cikin wani gidan da ke gefe da garken shanun,
kana yashiga cikin shanun cikin girmama wa da ladabi matasan makiyayan nan suka shiga gai dashi cikin girmamawa,ya amsa cikin sakin fuska
kana yashiga tayasu ɗaure shanun.
jijjiga Naseem da yake ta musu-musu a bayana nashiga yi dan nasan yagaji ko kuma jikin sa ya masa tsami dan yabugu sosai,ina matse ido hawaye na zuba,
tuni Nasmah ma ta saki kuka, sai na cigaba da gargiza su ina hawaye,
yan da nake girgiza sun hakan yasa hannuna ke girgiza zafi har cikin raina.
da sauri dattijon nan yafito daga cikin garken shanu yana ɗan waige-waige da alama dai kukan yaran yaji yasashi fitowa duba da yan da yake ta ɗan waige-waige,
nan idanunsa ya sauka kanmu da mamaki yake kallona kana yace
"Ke wanene me kike yi a na?".
yayi maganar idanunsa a kaina cikin hausar sa da bata tsaya ba,
banyi magana ba sai masar ƙwalla nake,
"Ke wanene nace me yasa mi yaron?".
cikin zubda ƙwalla nace
"Munfaɗi ne shine yaji ciwo kuma yunwa suke ji".
"Yunwa?".
yafaɗa yana kallo na".
na gyaɗa kai na alamar Eh, yaɗan yi shiru yana kallona,
kana ya kalli su Naseem da Nasmah da kyau sannan yace
"Garin yaya kuka faɗi haɗarin mota ne ina zaku je??".
yajero min tambayar
nace
"Acan kan tudu muka faɗi kuma Yola zamu".
shiru yakumayi alamar nazari kana yajuya tare da faɗin
"Kubiyo ni".
ai ko da sauri na bi bayan sa.
ya shiga gidan tun daga bakin kofa yake faɗin
"Sumaye Sumaye Sumaye".
wata yarin yar dake zaune a tsakar gidan ta mike tana faɗin
"Inna wuro Bappa na kira".
wata dattijo war mata tafito daga cikin bukko da sauri tana amsa kiran sa,
tare da faɗin
"Gani nan Malam".
yace
"Zo ga wani bakuwa nan tazo kuma wai yaron ta ya faɗi a kasa kuma yana jin yunwa bashi abinci yaci".
tace
"Subhanallahi kawo shi nan mugani garin yaya?".
namatso in da take tana kokarin karɓar Naseem dake ta zandara ihu, garin cirosa sa a bayana sai ta bige min hannun,
yarfe hannun nayi tare da faɗin
"Wayyo Allah hannuna".
tace "Ayya Allah kam sansu ke ma hannunka na siwo ne?".
kai na gyaɗa cikin zubda ƙwalla nace
"Eh da muka faɗi ne nima na buga hannuna".
kallon yarinyar dake zaune a gefe tayi tace
"Zo Mero kikarɓa mata yaron hannun ta".
yarin yar ta matso da sauri ta karɓi Nasmah,
tace
"La Inna wuro itama taji ciwo".
Inna wuro tace
"Oh wani irin faɗuwa ne haka sai kace haɗarin mota".
tafaɗa tana roko hannuna tare da cigaba da faɗin
"Ko dai haɗarin mota kukayi ne".
yarfe ɗaya hannun nayi nace
"Wayyo Allah na".
Inna wuro tace
"Malam itama ta buga hannun ta inaga tayi targaɗe a hannun".
"Nima dai haka nace kamar wan da suka faɗi a mota".
yamatso kusa da ni yana faɗin
"Naga hannun".
naɗago haka na mika masa yarike yana ɗan jujjuyawa,
rumtsa idanuna nayi da karfi ina faɗin
"Wayyo Allah wayyo Allah".
yace "Sannu kinyi targaɗe ne".
sai ya saki hannun
"Bari nakawo magani nasha maku".
Bappa yafaɗa yana shigewa cikin bukko,
ni dai yarfe hannun narika yi ina matsar ƙwalla.
yana shiga yafito da wasu robobin mai guda biyu, ya dawo in da nake.
Inna wuro tayi sauri ta ɗauko taburma ta shin fiɗa tace na zauna,
na zauna shiko a kan kujera ƴar tsuguno ya zauna kana yaruko hannuna yaja yaja yajijjiga shi da ɗan karfi, kara na sake cikin jin azaba har cikin kokon zuciya ta, ina shushshure kafafu kasa kamar zan saki fitsari a jikina.
kana yabuɗe ɗaya daga cikin roban mai daya fito da su ya lakato maganin ciki yashafa min a hannun da tuni yahaɗa zufa,kana ya saki hannun yana yimin sannu.
Inna wuro tace
"Sannu zakiji daɗi har kiyi bacci".
kai kawai na gyaɗa mata ina matsar ƙwalla, na matsa baya na jingina da jikin garu ina rike da hannun da ɗaya hannuna...
ya karɓi Naseem yashafa masa maganin dake cikin ɗaya robar a duk kanin ciwukan jikin sa,
yana yi yana ɗan mammatsa jikin sa har ya gangaro kasan kafar sa ai ko yana rike guiwar kafar sa yakara sautin kukan sa yana kankame jikin sa,
kafar yarike da kyau yaja sai ga kafar tayi kass,
Maganin da yashafa min a hannu yashafa masa a kafar yana faɗin
"Gocewar kashi ne".
kana ya mikawa Inna wuro shi ta karɓe shi tana girgiza shi da yi masa sannu,
nan ya karɓi Nasmah itama ya sha fa mata bayan yagama dudduba jikin ta ko itama da buguwa ko gocewar kashin a jikin ta,sai dai ita ba a samu gocewar kashin ba sai dai buguwar kawai...
Ina zaune nayi jugum zuwa lokacin kam alhamdllh zafi da zugin da hannuna yake min sai raguwa yake,
ido na zubawa su Naseem da ke jikin Inna wuro sunyi shiru sunata rarraba ido,
Bappa kuwa tun da yagama shafa mana maginin yamike yafiya sai yanzu yashigo rike da kwarya a hannunsa,
ya karaso in da muke ya mikawa Inna wuro kwaryar yana faɗin
"Basu susha dan su daɗa jin karfin jikin su".
Inna wuro ta amsa
tare da faɗin
"Dama yanzu nake shirin aiken Mero taje ta tatso musu madarar".
ta aje kwaryar ta mike da sauri ta shiga bokkar dake gefe da mu tafito da kwarya da ludayi guda biyu,
ta raba madarar biyu ta mika min rabi kana ta zauna tana ɗibawa da ludayi tana baiwa su Naseem,
ai ko suka karɓa suna ta sha,
A hankali na ɗibo nadarar cikin lodayi nakai bakina,
lumshe idanuna nayi jin ɗumi da garɗin madarar ya ratsa ni,ai ko na gyara zamata sai gashi na shanye madarar tass har ina tanɗe baki...
Bappa ya fito da shirin tafiya masallaci ya dube ni yana faɗin
"To ni zan tafi masallaci yanzu ina zakuje tun da naga kun gama shan madarar?".
kaina a kasa nace
"Yola zanje".
suka haɗa baki da Inna wuro wajen faɗar. "Yola??".
Bappa yace
"To ke da zakije Yola me ya kawo ki rugan nan Yola da yake tacan gefe Yola da yake tacan mezai sa kibiyo ta nan?".
ko mai ban ce ba sai kasa da kai na da nayi.
da sauri ya juya yanufi kofa yana faɗin
"Bari na tafi kar na rasa sallah".
a hankali na mike nace
"Ni ma zan yi sallar".
Mero ta mike da sauri ta zubo min ruwa a buta ta mika min tare da nuna min banɗaki.
na je nayi sarki kana nafito nayi al'wala,
koda na fito na samu Inna wuro ta shinfiɗa min sallaya Mero kuma na rike da Nasmah sai wasa da gashin kanta daya cukuikuye take,
bayan na idar da sallar ina zaune kan taburma tuni su Naseem sun yi bacci,sai na gyara musu kwanciya kan taburman na rufe su da abun goyon su.
Mero da Inna wuro ma duk lokacin sun shiga yin sallah..
ina zaune jigum...
Bappa ya shigo da sallama,
na amsa kallon in da su Naseem suke kwance yayi kana yace
"A'a ya zaki kwantar da yara a wannan gurin sanyin ke bakyajin sanyi?".
murya ya ɗagaga yashiga kiran Mero,
da sauri Mero ta fito yace
"Kira Sumaye tazo ta ɗaga yaran nan anan ya za'a barsu cikin sanyi".
da sauri Inna wuro tafito tana faɗin
"Ai kwanciya sukayi ne".
ta dube ni tana cigaba da faɗin
"Ke ma in kin gama ki taso a sanyin nan".
ta ɗauke su ta kaisu ɗaki.
numfashi na sauke wai yau mu ake ce wa mutashi a cikin sanyi kar sanyi ya kamamu Allah sarki rayuwa bayan acikin ta mukayi rayuwar wata biyu da ɗori..
A sannu na mike nabi bayan su muka shiga cikin bukka.
abakin gado gado irin na Fulanuka in da aka kwantar da su Nasmah na zauna.
tace idan ina jin bacci na gyara na kwanta a gefen su,a hankali kuwa na gyara dan kuwa baccin nake ji...
Washegari da safe bayan mun karya da lafiyayyen tuwon gari miyar ɗanyen kuka wan da yaji man shanu, muka kara da kunu.
Bappa ya shigo da madara acikin kwarya mai ɗumi ya bawa Inna wuro yace ta bawa su Nasmah,
guri ya samu a gefe ya zauna kana ya dube ni sannan yace
"To yanzu kam gari ya waye bakuwa idan kika fita zaki sami motar tafiya Yola dan daga nan babu wani nisan kirki sosai".
Kai na akasa na amsa da to,
mikewa yayi yashiga bukkan sa ya fito da robar maganin da jiya ya shafa mana,
ya dawo ya zauna yaɗau ki Naseem yana shafa mishi maganin a guraren da yaji ciwo yace
"Amma kam dai haɗarin mota ne wannan sai yau na daɗa ganin raunukan ashe da yawa ko ɓarayi kuka haɗu da su a hanya suka yi muku duka haka,dan yanzu ɓarayi rashin imanin su gaba yake har yara ma basu bari ba".
ƙwalla naji ya cika min ido tuno da yadda akayi muka ji ciwon, cikin zubda ƙwalla nace
"A'a ba hatsari ko dukan ɓarayi bane faɗowa mukayi daga kan wani tudu".
da mamaki Inna wuro tace
"Ikon Allah garin yaya?".
Bappa yaɗan sakai ta shafa masa maganin yana faɗin
"Garin yaya a ina kuka sami tudu ku da kuke mota ba tafiyar kafa ba kuma kince ba haɗari bane".
nace
"Eh acan cikin daji acan ta wani guri da nisa zamu zan sauka a kan tudun shine na zame shi kuma ya suɓuce a hannnuna ya gungura yafaɗi kasa ita kuma tana bayana tare da ita muka isa kasa shine na faɗo a kan hannuna".
gaba ɗayan su suka zuba min ido alamun na zartata da kuma magana ta kana Bappa yace
"Menene yakai ku cikin daji da har kuka kai ga jin rauni??".
kasa nayi da kai na ina wasa da ƴan yatsu na yayin da gudun hawaye na suka tsananta cikin rawar murya da kuka ke son kwace min.
a hankali nafara basu labarin rayuwa ta tun daga farko har yau da nake zaune a gaban su.
Salati Inna wuro ta sake gaba ɗaya jikin ta yagama yin sanyi har sai da taɗiga ƙwalla cike da tausaya wa rayuwar mu,
Bakin zanin ta takai tashare ɗan guntun kwallar da ya fito mata tana faɗin
"Ikon Allah lallai kinga rayuwa rayuwar ki abun a duba ne, me kika tsare wa mutanen nan da zasu jefaki cikin wannan mawuyacin hali, har ya shafi yaran da basusan kansu ba bare susan mecece duniyar, wannan wani irin zalunci ne".
Inna wuro ta karashe maganar tana jan hanci.
Bappa kuwa kai ya jinjina cike da dattako
sannan yace
"Allah mai girma da ɗaukaka,
lallai Allah shi ke kare ba wansa a duk inda yake, yatsare ku yakuma kare ku da sharrin namomin daji masu cutarwa har kuka fito batare da cutar wan wani dabba ba,".
shiru Bappa yayi tare da zuba min ido na ɗan wani lokaci zuwa can kuma sai ya girgiza kan sa sannan yace
"Mutane dai ko da yaushe burinsu su zalunci ɗan uwan su ko ribar me zasu ci da yin hakan?."
yayi maganar yana mike wa,
da sauri Inna wuro ta ɗago tana duban sa,
in da buta yake yanufa yasun kuya yasoma al'wala yana idar wa ya mike, yashige bukkar sa.
numfashi Inna wuro ta sauke,
tare da mai da duban ta kaina
tace "Allah ya tabbatar da alkhairi".
Amin nace batare da sanin inda batun nata ya dosa ba.
bayan Bappa nabi na kallo ganin yayi al'wala kuma lokacin sallah baiyi ba...
Muna nan zaune can yafito rike da jarbi a hannunsa bakinsa na motsi alamun lazumi yake, in da yatashi ɗazu yadawo ya zauna,
numfashi yaja ya sauke tare da yin gyaran murya sannan yasoma magana
"Hakika asiri akayi miki mummunar asiri ma kuwa,
wanda ya sa akayi asirin da wanda ya ai kata sihirin babu imani azuciyar su,
bakin sihiri ne mai matukar duhun gaske, rashin imanin wan da ya ai kata abun yakai yakawo,
dan kuwa asirin ba zai taɓa karyewa ba har sai shi bokon da yayi asirin ya muku,
mutuwar sa shine lakanin karyewar asirin,
tabbas wan nan yacika mugu mara imani,
babu kuma wan da yasan ranar mutuwar wani sai Allah, Allah Ya takai ta