Showing 12001 words to 15000 words out of 46406 words
kallo kenan idan na gana haka sai na shige ɗaki.
karaso wa in da muke yayi yana faɗin
"Mama ban shigo da wuri ba Allah dai yasa an ajiye min".
murmushi Mama tayi tace
"Ai kuwa yau Sagiru gaba ɗaya na mance da ma HAMDAH ce ke tuna min waɗan da ake ajiye musu ai kuwa yau ban ajiye wa kowa ba na man ce gaba ɗaya dan ita mai tunin bata nan bata jima da shigo wa ba,
Sai dai kuyi hakuri sai na dare kenan".
tsayuwar sa ya gyara tare da dubana yace
"Shine yau baki tunawa Mama ba ai da kafin ki fita kin tuna mata da ta ajiye min kinga dai yanzu laifin kine".
"Laifi na kuma?".
yace "Eh ai kece baki tuna mata ba".
Mama tace
"To an jima kam zata yi min tuni sai na ajiye maka".
yace
"Yauwa to Allah yakai mu".
Sai kuma ya ɗan sosai bayar keyan sa ya dube ni kana ya mai da duban sa kan Mama yace
"Mama zaki bani wan nan ɗiyar taki mai rashin tunin nan".
da sauri na ɗago jin abun da yafaɗa, Mama ko cewa tayi
"Wa wai HAMDAH kake faɗa?".
tafaɗa tana duban mu duka da shi.
yace
"Eh ita" Mama tayi murmushi tare da faɗin
"To ai matar aure ce kai baka ganta da ciki ba haihuwa tazo dan mijin ta soja ne kaga bazai yiwu ta haihu a can ba shiyasa tazo gida".
Ido ya waro tare da buɗe baki da mamaki yakai hannu yarufe bakin yana faɗin
"Matar soja Innalillahi wlh ban taɓa luraba sai yau duk shigo war da nake,wai Allah ya rufa min asiri da kafata ta ɓalle sabo da sallen kwaɗo inayi ana zuba min bulala,a gafar ceni wlh rashin sani ne ki tai make Ni kada ki faɗawa yallaɓoi,
wlh Ni sai yau naga cikin ni duk gani na da ita ban taɓa lura da cikin ba".
yakarashe maganar yana dubana da haɗe hannayen sa guri guda alamun roko.
Murmushi nayi dan kullum idan ya shigo da hijabi a jikina kuma azaune yake sami na,nasan shi yasa bazai ga cikin ba.
yace
"Um bari na tafi wata kila ma tsautsayin wahala ne yashi go da ni,amma da zanyi ido biyu da jarumin sojan nan da na jinjina masa dan ya iya zaɓe kwarai,ko da zai sani sallen kwaɗo sau goma sabo da na tayashi murna".
Mama tace
"Ah to gara dai ka tafi".
"Ai natafi ma". yayi waje yana dariya....★
A can cikin garin birnin Bauchi'n Yakubu kuwa,
A halin ABDULLAHI TURAKI na hango motocin su suna fitowa daga cikin airport,motocine guda uku suke tafiya a jere, cikin mota na biyu wan da yakasan ce shine na tsakiya a ciki na hango su Abbu da Mamie, fuskokin su ɗauke da farin cikin ganin su a kasar su kuma garin su........!★
Mommyn twins ce
Cike parlour'n yake tam da ƴan uwa da abokan arziki,
kowa sai juya tsara bar da aka basa yake cike da jin daɗi.
Mamie bin cikin parlour'n da mutanen cikin tayi da kallo a karo na ba adadi,
yau kwana biyu ke nan da dawowar su amma bataga HAMDAH acikin masu zuwa yi musu sannu da dawowa ba,ko a airport kuwa da a kaje tarar su ba ta cikin waɗan da suka je tarar tasu,bata kawo komai a ranta ba dan tasan iyanzu kam cikin yakara girma ko shi zai hanata,sin tiri kan hanya.
Bayan sallar Isha Ya SALEEM yashigo cikin bedroom ɗin Mamie tana zaune tana warewa ƴan uwan ta na kan gari waɗan da bata basu tsaraba,
a hankali yakara so cikin ɗakin yazau na kan kujerar da ke cikin ɗakin tare da gai da Mamie,
ta amsa tana faɗin
"Har yanzu baka tafi gida ba".
cikin yana yin nan nasa kamar an sashi dole yin maganar ko kuma mai jin bacci yace
"Eh yanzu zan tafi na shigo nayi miki sallama ne".
tace "Gara kam ka tafi yanzu haka HAMDAH na can tsoro duk ya ishe ta ga Halima ma naga bata koma ba tace min anan zata kwana".
wani irin bugawa kirjin sa yayi da karfi jin an ambaci sunan ta.
shi har ga Allah ma ya mancewa da wata mai suna HAMDAH in ba yanzu da Mamie ta faɗa ba, tun ranar da suka rabu ya goge sunan ta cikin zuciyar sa baya kaunar yaji wani ya ambaci sunan ta,
sai kuwa akayi sa'a a cikin gidan sa uwar gidan tasa wato Na'ima tayi ruwa tayi saki wajen ganin babu wan da yakuma tuno ta bare har arika ambaton sunan ta,dan hakan shine kaɗai zai tai maka wajen ganin ya daɗa mancewa da ita na har abada,
kamar yan da bokan ta yasar mata tatafi bazata kuma waigowa ba
sai dai ma takuma yin nisa da su.
yanzu kuma ba wani zuwa family House ɗin su yake sosai ba,kuma ko da yaje ɗin ma gaisu wa ce kaɗai suke yi yatafi.
da karfi-karfi haka zuciyar sa ke bugawa,har sai da yakai hannu ya dafe dai-dai saitin kirjin sa.
Mamie ta janyo wani ɗan madaidaiciya akwati tabuɗe, dogayen riguna ne da gyale da sauran su zafafa sai gefen cikin akwatin kayan baby ne wanda mace da na miji zasu iya sawa.
murmushi tayi tare da faɗin
"Ga tsara bar ta dana mai gidan dan Ni wa mai gida na tsiya bawa kishiya ba,Abbu ne yayi wahalar siyowa kishiya".
tayi maganar fuska ɗauke da murmushi cike da so da kaunar jikan ta da take saran fitowar sa duniya ko mace ko na miji.
ta cigaba da faɗin
"Da zan baka kakai mata amma dai bari na bari idan tazo sai ta haɗa dana gun Abbu'n ku ta tafi da
shi tun da shi har yanzu bai buɗe jakar saba".
Har lokacin hannunsa na dafe kan kirjin sa a hankali ya mike,batare da yace komai ba yafita,
bayan sa Mamie tabi da kallo bata kawo komai a ranta ba dan tasan halin ɗan nata sarai miskilanci a jinin sa yake.
yana dai-dai ta zaman sa cikin mota yaja gajeren tsaki jin har lokacin zuciyar sa bata fasa bugawa ba,a haka ya koma gida..
Washegari Mamie tayi ta zuba ido ganin zuwan HAMDAH amma shiru har yamma.
A ɓangaren Abbu ma ranar sai da ya tanbayi Mamie wai shin HAMDAH tazo ta karɓi tsara bar tane bata karɓi na amaryar sa ba.
Nan Mamie ke ce masa ai ko sannu da dawowa bata zo musu ba amma dai tasan jikin ne yasoma nauyi...
Bayan sallar magriba,
da sauri Masa'ud yabi bayan Abbu suka shiga gida tare, a parlour suka zauna in da suka tadda Mamie nan zaune,zama Masa'ud ya gyara dan yau yasha alwashin faɗa wa su Abbu abinda ke faruwa duk da Ummi tace kada wani ya sanar musu sai sun daɗa hutawa sosai.
a cewar sa wani hutu yarage musu bayan ƴar uwar su ba a san halin da take ciki ba.
"Abbu Mamie".
Masa'ud ya kira sunan su yana duban su,a kusan tare suka amsa yayin da suka mai da hankalin su kan shi.
Zaman sa ya daɗa gyarawa kana ya nisa yasoma magana,
"Abbu kunsan abun da ke faruwa kuwa?".
A tare suka haɗa baki wajen cewa
"Meke faruwa?".
"Assalamualaikum"
gaba ɗayan su suka juyo jin muryar Aunty Rafee'at tana sallama,suka amsa mata,ta karaso ciki ta sami guri ta zauna tare da gaishe su in da Masa'ud ya gai data.
Mamie tace
"Unguwar dare bakya bari gari ya waye ba".
Hmm. kawai tace dan batajin abun da ke tafi da ita zata iya barin sa sai gobe, kwanaki arba'in da suka shuɗe tayi sune cikin kunci da tashin hankali,
Dr Farooq ma yayi-yayi da ita kan tabari gari yawaye tace a'a yau kam bazata bari maganar yakuma kwana ba,a son ta ma tun ranar da suka dawo Nigeria taso faɗa musu Ummi ce ta hana ta,tun da har yau sun yi kwana uku da dawowa bataga amfanin rashin faɗa musun ba gara su ma susanin.
Masa'ud na ganin yanayin ta yasan abun da yazo faɗawa su Abbu shi ya kawo ta,
yace
"Aunty Rafee'at yanzu da ma zan faɗa wa su Abbu kenan".
da mamaki iyayen nasu ke kallon su Mamie da tun ɗazu da Masa'ud yace sunsan abun da ke faruwa taji gaban kirjin ta ya yanke.
tace
"Wai me ke faruwa ne kam?".
tayi tambayar cikin yanayin fara shiga damuwa da fargaba.
A sannu Aunty Rafee'at tashiga basu labarin abun da ya faru tun daga farko har da korar da Abba yayi wa HAMDAH.
Kamar a mafarki haka suke jin zancen nata,
Mamie kam salati tashiga rafkawa tana tafa hannu yayin da hawaye yafara sauka a idon ta,
Cikin sananin tashin hankali da kunar rai Abbu yaɗaga wayar sa yakira Abba batare da ya amsa sallamar da yake masa ba yace yazo yan zunnan,
yana kashewa yakira lambar Ya SALEEM,
a ɓangaren Ya SALEEM ɗin kuwa yana zaune cikin bedroom ɗin sa Na'ima na gefen sa like da shi,
ganin mai kiran nasa a irin wannan lokacin sai da ta ɗan girgiza,
yana ɗaga kiran
yace
"Duk abun da kake kabari kazo yanzu ina niman ka".
Abbu ya faɗa cikin fusatacciyar murya,
da sauri YA SALEEM ya mike ya ɗau makullin motar sa yafita,
A ɓangaren Na'ima kuwa kasa zaune tayi tarika zagawa cikin ɗakin dan duk abin da Abbu yafaɗa taji, tsoron ta ɗaya kada akan maganar yarin yar nan Abbu yayi masa irin wannan kiran,
"Cabɗi jan lallai kuwa da sakel".
tafaɗa a fili.
Cikin gaggawa Abba ya iso sashin wan nasa do min amsa kiran sa, Abbu
ko zama bai bari Abbu yayi ba ya shiga nuna sa da yatsa yana faɗin
"Me ka ai kata kenan me kayi kenan Idris??
da hankalin ka da girman ka da tunanin ka zaka yanke mata irin wannan hukuncin,
menene amfani da ribar yin hakan ka jefata duniya da kan ka,
akan wani dalilin ka mara tushe da asali,
wani gurin da yafi nan ka bata acan ɗin da ka turatan?,
wani irin rashin imani ne hakan kai kana kwance a makwanci mai kyau kaci mai kyau kasha mai kyau ita tana can awani duniyar da kai kan ka baka sani ba,baka kuma damu da duk halin da zata shiga ba,a kan dalilin da baka da tabbacin sa!!".
Sosai Abbu ke yiwa Abba faɗa tamkar zai rufe shi da duka cikin tsananin ɓacin rai.
Ya SALEEM da yanzu shigo warsa ganin yan da Abbu keyiwa Abba yasa shi karaso wa cikin parlour'n jiki a sanyaye,
da sauri Mamie da tunɗazu take ta sharar kwalla tamike tashi dukan kafaɗar sa tana faɗin
"Yanzu a bun da ka ai kata ke nan SALEEM abun da ka ai kata kenan kai ɗin ka kamata da kan ka da wani acikin gidan kan?
shine har zaka sake ta?
shekaran ta nawa a cikin gidan sai yanzu zata kawo wani cikin gidan".
cikin muryar kuka sosai take maganar tana dukan kafaɗar sa.
hayaniyar da Ummi taji nafita sosai cikin side ɗin Mamie yasata fita da sauri tanufi side ɗin dan ganin meke faruwa haka a cikin daren nan,
a tsakar gida ta haɗu da su goggo Hauwa da Aunty Halima suma jin hayaniyar ce tafito dasu daga sashin Inna da sukayi masau ki can,da sauri sukayi cikin side ɗin hankali tashe jiyo muryar Mamie tana magana cikin muryar kuka.
Suna shiga da sauri Ummi tayi gun Mamie daketa bugun kafaɗar SALEEM shi ko na tsaye ya dukar da kan sa kasa,
hannu Mamie Ummi tarike tana faɗin
"A'a Mamie'n Nusaiba menene haka me yasa hakan?".
Mamie tace
"Kyale ni Ummi'n Fauzan idan baije yanemo taba bazan taɓa yafe masa ba,a ina ka ganta da wani kataɓa kamata tana cin amanar auren ka ko ta hanyar magana da wani ko a waya ce??!,
kyale ni Ummi'n Fauzan sai ya faɗa min yaushe yataɓa kamata tana cin amanar auren sa".
sakin hannunta Ummi tayi kamo na Ya SALEEM da kansa ke sun kuye har lokacin yana jin zuciyar sa nawani irin tafarfasa,
ta jashi gefe.
su goggo Hauwa kam tsayuwa sukayi suna kallon yan da Abbu ke yiwa Abba faɗa kamar zai rufe shi da duka.
Rai ɓace Abbu ya juyo gun Ya SALEEM yana wasa masa wani irin mugun kallo,
ganin haka yasa Ummi haɗe hannayen ta biyu tace
"Dan Allah Yaya..."
hannu ya ɗaga mata batare da ya bari ta faɗi abun da zatace ba cikin fusatacciyar murya ya dubi Ya SALEEM yace
"Kai ka ɗaura wa kanka aure da ita da zaka kwance?
yau nayi da nasanin haɗaka aure da ita nayi nadamar abun da nafaɗawa mahaifiya ta cewa kai zaka rike mata jika da gaskiya da amana,
yau nayi nadamar faɗar hakan nayi nadamar saurin yar da da hankalin ka da nayi,
da nasani da tun wancan lokacin nacikawa Inna burinta na haɗa auren HAMDAH da Masa'ud,
ban yi tunanin kiyayyar da kake mata yakai nan ba, bayan ka saketa
kakuma bita da mummunar kazafi!!".
rumtse idanunsa yayi yana jin kansa naci gaba da yi masa mugun sara zuciyar sa na tafarfasa yana jin maganganun iyayen nasa tamkar saukar aradu.
Abbu yaci gaba
"Ka kira ma ai katan gidan ka da duk wani mai hannu a kan maganar yanzu-yanzun nan suzo ina neman su!!!".
yakarashe maganar cikin tsawa da karaji sosai..
A can cikin gidan SALEEM kuwa lokacin da sakon kiran Abbu ya'isa gare su wasu daga cikin ma'aikatan gidan da ka gansu kasan suna cikin yanayin tsoro da fargaba,dajin kira kai tsaye daga sama.
A ɓangaren Na'ima kuwa duk da itama tarazana da jin kiran,sai dai tasan bokan ta bazai barta a rana ba.
batare da ɓata lokaci ba suka nufi gidan su Abbu,
in da Na'ima da baba mai gadi Sani direba Habu mai shara,suka taho a mota guda,sauran ma ai katan kuma suma a mota guda...
Acikin parlour'n Mamie suka tadda kaf ƴan gidan anyi jugum-jugum,suna shigowa Aunty Rafee'at tashiga ai kawa Na'ima harara cikin tsananin tsanar matar,a gefe kusa da Ya SALEEM Na'ima ta zauna,in da sauran ma ai katan suka zazzauna a kasa tare da soma gai da su Abbu,
Ummi da goggo Hauwa da Aunty Halima ne kaɗai suka amsa musu.
gyaran murya Abbu yayi ya dubesu da ɗaɗɗaya da kyau kana yaso ma magana
"A cikin ku su wane ne suka ce sun ga HAMDAH da wani acikin ɗakin kwanan ta har kuma suka bada tabbacin sun gansu a makwanci ɗaya??".
kallon-kallo Na'ima da baba mai gadi Sani Habu suka shiga yi.
yayin da hankalin mutanen cikin parlour'n yadawo kansu tun da kowa yasan cewa sune suka bada tabbacin sun gansu da idanunsu.
Ummi kam kanta ta sunkuyar jiki a sanyaye tana jin kunnuwan ta suna yi mata nauyi da sake jin abun da ɗiyar ta ta ai kata...
Baba mai gadi ya rusanar da kai kasa kana yace
"Gamunan Alhaji, ni da Habu da Sani sai kuma Hajiya Na'ima".
yafaɗa yana nuna ko wannensu da hannu kana yaci gaba
"Ranar da oga SALEEM yayi tafiyar da yaje yayi wata guda a ranar mutumin yafara zuwa".
nan ya zaiyana bayani kamar yan da yafaɗa wa Ya SALEEM a wancan lokacin.
Ido Abbu yazuba masa da kyau yana sauraren sa yayin da jikin sa yaɗan yi sanyi dajin maganar daga bakin baba mai gadi,
baba mai gadi dattijo ne dan ya girmewa su Abbu'n nesa ba kusa ba.
Habu da Sani suma sukayi bayani da bada tabbacin ganin su kamar yadda suka faɗa wa SALEEM,
kana daga bisani Na'ima ta ɗaura,
tun da Na'ima ta fara magana Aunty Rafee'at ji take kamar taje ta shaketa ta mutu dan bakin ciki,cikin tsana da jin haushin ta tace
"Wlh karya ne cikin Ya SALEEM ne".
ganin yan da take maganar tana nuna Na'ima da yatsa kamar zata mike,
Aunty Halima ta riko hannunta cikin kasa da murya tace
"A'a Rafee'at zau na kawai".
huci take tana ai kawa Na'ima harara.
Shiru parlour'n ya ɗauko kowa da abun da yake sakawa cikin zuciyar sa,
Ummi kam wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata da sake jin abun da ƴar ta ta aikata,cikin wani sabon tashin hankalin da ta sinci kanta ciki tashiga nanata kalmar
Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
Ya SALEEM na zaune har lokacin bai yi magana ba sai dai bugun zuciyar sa da yakaru tamkar zai fasa kirjinsa yafito,
Abbu ya sauke numfashi sannan yace
"Ina da bukatar bincike akan lamarin duk da kasan cewar ku shaidu har huɗu akan lamarin, zan sako hukuma ciki tayi bincike sosai domin daɗa tabbatar da hakan,
kutashi kuje gobe idan Allah ya kai mu za'a fara bincike domin zuciyoyi su dai-dai ta kan abu guda".
wani irin Rasss gaban kirjin N'ima ya buga da sauri ta mike yayin da sauran suma suka mike sukayi musu sai da safe suka tafi.
Abbu ya mai da hankalin sa kan Abba da Ya SALEEM sannan yace
"Gobe nakeson ganin HAMDAH cikin gidan nan".
yana kai wa nan yamike yayi cikin bedroom ɗin sa....
Hankali tashe Na'ima takoma gida hankalin ta bai kuma mummunar tashi ba sai da ta sami labarin cewa Abbu yace anemo HAMDAH,
washegari ana idar da sallar asuba Na'ima ta fita tanufi gidan bokan ta,
hankali tashe tafito daga motar ta tatube takalmin ta tanufi bukkan malam na kan tudu,
yana zaune gaban kayan tsafin sa ta zube gaban sa tana sauke numfashi kamar wacce tayi tsare,
cikin sauke numfarfashi tace
"Boka akwai matsala".
Dariya ya sheke da shi,
itako cikin tashin hankali da rawar jiki ta cigaba da faɗin
"Boka komai ya kwaɓe iyayen sa sun dawo mahaifinsa yace yau zai faɗaɗa bincike akan lamarin kuma yace hukuma zai sa suyi bincike akai,
sannan yace aje a nemo ta a duk inda take,
boka ka taimake Ni kamar yadda kasaba tai makona".
kai ya jinjina kana yaɗauki wani ɗan karamin tandu da zare mai kauri yace
"Za'a rufa musu baki bazasu kara yin ma maganar ba daga yau,zasu mance da batun kuma koda sun tuno ta, baza su iya yin komai akai ba".
dariya yakuma ke cewa da shi yace
"Haka ya miki?"
da sauri tashiga gyaɗa kai tare da faɗin
"Yayi sosai ma Nagode kwarai malam ai Ni kagama min komai a rayuwa"...
Wani bakin ruwa ya zuba cikin ɗan karamin tandun nan sannan ya shiga zagaye bakin tandun da zare mai kaurin nan, har sai da ya mamaye bakin tandun da zaren yarufe shi ruf,
kana ya jefa shi cikin tukunyar tsafin sa,yadube ta yace
"An gama".
godiya tashiga zuba masa kana tabuɗe jakar ta taɗibo kuɗin da batasan adadin su ba ta zubesu a gaban sa ta hayo motar ta takoma gida...
Tayi ta suba idon ganin hukuma masu bincike shiru har yamma,
har dare tana baza kunne kuma jin wata magana nan ma shiru,
wasa-wasa aka shari kwana uku babu wani labari,
dariya tashe ke dashi tare da buga cinya tana hakimce a bakin gadon ta,
"Ɗa ɗan ku haka gida ma nasa, kuma na haramta wa ƴarku do min ni kaɗai kuka haifa min shi".
tayi maganar cikin nuna isa tamkar da wani cikin ɗakin..
A