Showing 3001 words to 6000 words out of 46406 words

Chapter 2 - HAMDAH part 2 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

7619

goggo Hauwa ta farka tace
"Amma lallai SALEEM a gaishe ka sabo da haka zakace ka haramta kan ka da ita sannan kuma ciki ba naka ba? zancen banza kenan mata nawa suke da ciki kuma suna jinin al'ada ai ba akan ta aka soma ba in ba ka sani ba kasani".
Maganar sa ce yasa goggo Hauwa yin shiru da nata maganar cikin ɗinbin mamaki kowa ke kallon sa
yayin da shiko ya karkata hankalin sa gurin Abba da son bashi amsar tambayar da yakuma yi mishi yanzu kan cewa da yayi mishi "Dalilin ka kenan?".
kan sa ya girgiza kana yace
"Bayan tafiya ta akwai wani wan da yake zuwa gurin ta ɗazu ma ai katan gida na suka tabbatar min da haka".
wani irin zabura su Ummi suka yi suka haɗa baki wajen cewa
"Wani yake zuwa gurin ta??".
Abba kam hular kansa ya cire yashiga yin fifita da shi,niko ido na daɗa kura masa kamar tv...

Zaman sa ya gyara kana yasoma sanar musu duk abun da baba Mai gadi da Habu mai shara da Sani direver suka sanar masa, kana ya ɗaura da ganin da Na'ima tace tayi mana a kan gado da wan da Habu shima yace yagani.
salati parlour'n ya kaure da shi tuni hawaye yashiga wanke fuskar Ummi,
cikin takai ci Abba ya dube ni yana faɗin
"Abun da zaki saka mana da shi kenan ki ɓata mana family kin tozarta shi tozarci mafi muni me kika nema kika rasa a rayu HAMDAH me muka gaza miki wacce gatace bamu baki ba sakayyar da zaki yi mana kenan!".
kai narika girgizawa hawaye na zuba a idona na buɗe baki zanyi magana Abba ya daka min tsawa.
kana ya dubi Ya SALEEM yace
"Tashi ka kaje hukuncin da ka yanke shine dai-dai ta haramta a gare ka kuwa tabbas".
a sannu ya mike yafita da sauri na mike tsaye kamar mai tashin aljanu na bi bayan sa kafin na iso shi har ya isa farfajiyar gida da gudu nasha gaban san sa na ruko hannunsa na ɗaura kan cikina cikin muryar kuka da fizgar numfashi na da nake ji kamar zai ɗauke, ina kallon fuskarsa nace
"Ya SALEEM Ya SALEEM wlh abun da ke cikin kinan nan naka ne kai ne uban sa, wlh babu wani na mijin da ya taɓa rike koda bakin mayafi nane bare har ya sanni ƴa mace bayan kai Ya SALEEM ɗan kane cikin kane wlh babu wani wan da yake zuwa guri na".
fizge hannunsa yayi kana ya dube ni da kyau yace
"Kada ki sake dan ganta abun da ke cikin ki da Ni ni ba uban sa bane, ke kinsan uban sa ai jeki haifa ki kai masa abunsa in yaso ki kashe shi tun a ciki tun kafin ya fito duniya a san halin da kike ciki, asan wacece ke mutum a fuska kawai,
In dai irin wannan ɗan ne zai zamo nawa har abada bana so!".
yana kaiwa nan ya juya yashige motar sa yafice a gidan..

Dur kushewa nayi a gurin ina wani irin kuka mai tsuma rai, na daɗe durkushe jin jiri na fisgata na mike da kyar na koma parlour in da su Ummi suke har lokacin Ummi na hawaye sai dai ta kasa furta ko da kalma ɗaya ce, goggo Hauwa da Aunty Halima sunyi jugum.
ina saka kafata cikin parlour'n Abba ya takatar da ni da faɗin
"Kada ki sake ki tako cikin parlour'n nan maza ki tafi kiyi nesa da mu domin zama da irin ki acikin family tamkar rugujewar ahali ce,
kisani idan zuciya ta tabuga to kece sila kuma bazan taɓa yafe miki ba,bana kaunar nakuma buɗe idanuna na ganki fita min a gida kitafi duk inda zakije amma ki sani ban yarda kije gidan ɗaya daga cikin dangi naba har in dangi nane fita min a gida nace!".
yafaɗa cikin karaji baya nashiga ja inajin maganar Abba tamkar saukar ruwan dalma a zuciya ta.
mikewa Ummi tayi hawaye taf idon ta tace
"Ina zataje Abba'n Fauzan ka bata lasisin shiga duniya kenan? bata da in da yafi nan in kuma kace ta tafi to sai dai mutafi tare".
Ummi ta nufo ni tana cigaba da faɗin
"Ɗiyar ka mace zaka jefawa duniya sai dai in mutafi tare".
cikin fushi Abba yace
"Fatima idan kika fita daga cikin parlour'n nan to ki tabbata nayafe ki".
ido na waro cikin tsananin tashin hankali nashiga girgiza kai da karfi nace
"Ummi dan Allah dan Allah karki fita Ummi ki koma na rokeki Abba kayi hakuri ni zan tafi".
ganin tana ta daɗa matsoni yasani tahowa da gudu na rungume ta cikin muryar kuka nacigaba da faɗin
"Ummi ki koma dan Allah karki fita".
sai kuma na zame jikina da sauri na saka hannuna biyu na share hawaye na nakuma kai hannu kan fuskar ta nashare mata hawaye tare da yin wani murmushi ina duban ta yayin da wasu zafafan hawaye suka zubo min nace
"Ummi duk inda nake a faɗin duniyar nan ko a muce ko a raye addu'ar ki itace zata zame min garkuwa in nazamo silar fitar ki a gidan nan bazan taɓa yafewa kai na ba".
Najuya na dubi su goggo Hauwa da tuni suma hawaye yagama wanke musu fuska na haɗe hannaye na biyu nace
"Dan Allah goggo Hauwa Aunty Halima kada kubar Ummi na ta fita dan Allah".
da sauri na juya nafita a cikin parlour'n na ɗau jakata dana yar dashi a tsakar gidan da sauri na nufi kofar fita ina waige ko Ummi na biyo ni.
sauri na rika yi har na fita daga layin mu.......!★






Mommyn twins ce




Sauri nake kamar zan tashi sama duk da nafita daga layin unguwar amma hankali na bai kwanta ba,tafiyar nake ina ta waige-waige,sai gani nake kamar Ummi zata biyo ni.
tafiyar kawai nake batare da nasan in da zani ba kokuma sanin in da na nufa ba.
Karar ababen hawa da naji ya karaɗe ko ta ina shine ya dawo dani cikin hayyaci na,nayi mamakin ganin in da nake
Duk da kuwa tazarar dake sakanin unguwar mu da in da nake yanzu
wato winte.
Gefen titi na zame nashiga cikin mutanen da nagansu zazzau ne kan bence wasu ko nata harkokin gaban su.yayin da zuciya ta keta azalzala ta ji nake idan naci gaba da jan numfashi acikin garinnan tabbas zuwa anjima numfashi'n kwacewa zaiyi yatafi abun sa.
maganar da naji kusa da nine yasani ɗagowa wani ɗan yuniyon ne tsaye a kanmu yana faɗin
"Yauwa motar ku yanzu kam yacika kowa ya kawo kuɗin sa".
gafen da nake ya kalla kana yace
"Ƴan mata ke ma a wannan motar kike?".
tsintar kaina nayi da gyaɗa masa kai,yace
"To kawo kuɗin ki mota ta cika".
idanuna na mai da kan akwatin da ke gaba na tabbas nasan bana da ko sisi dan ban fita da ko biyar daga gida ba, hasali ma babu abun da na iya ɗauka in ba wannan akwatin ba,ganin yanata amsar kuɗin mutane sai na kai hannuna kan zip ɗin bayan akwatin ina ɗan wasa da shi a raina nake faɗin
"To ko ince masa yakarɓi akwatin a bakin kuɗin motar ne, Ni har da kayan cikin ma in dai zasu ɗauke Ni suraba ni da garin nan".
yadda nake wasa da zip ɗin sai yana ɗan zugewa da mamaki nakurawa aljuhun jakar ido ganin bakin kuɗi ya baiyana, da sauri na idda zuge zip ɗin nazaro kuɗin ina juyashi a hannuna naira dubu biyu sabbi dar.
tunanin ta yadda akayi kuɗin yashigo cikin a kwatin nake,
nan take na tuno lokacin rasuwar Inna ina zaune a cikin bedroom ɗin Ummi taciro kuɗi cikin wardrobe zatayi aika kasuwa daga cikin kuɗaɗen dubu biyu suka zubo,nakwashe ina mika mata tafita da sauri tana faɗin na ajiye bari tazo,a lokacin kuwa kasan cewar ina zaune ne kusa da akwatin sai naja zip ɗin a kwatin nasaka ciki kan cewar in tashigo zan cire na bata,gaba ɗaya nagama mance wa a she dai ban bata ba..

Numfashi na sauke a hankali na furta
"Alhamdulillah".
dai-dai lokacin kuwa ɗan yuniyon ɗin yake faɗin
"Kawo nake".
duka kuɗin na mika masa sai naga ya zare dubu ɗaya yakai hannu aljuhu yazaro ɗari biyu sai ya haɗa da dubu ɗayan nan ya mika min dubu ɗaya da ɗari biyu kenan.
karɓa nayi ina juya kuɗin a hannuna "Wato kuɗin motar garin da zasu ɗari takwas kenan?".
nayi tan bayar a raina,
ganin duk wan da yabada kuɗi sai ya shige cikin motar dake gaban mu sai nima na mike nashige cikin motar ina rungume da akwatina.
Ina alla-alla motar ta tashi duk da kuwa bansan motar wani gari zata ba ban kuma da mu da duk inda zaije ba ni dai burina nafita a cikin garin nan, bana kaunar na buɗe idanuna nakuma ganina cikin garin bana kaunar narika shakar iskar garin naji na tsani garin gaba ɗayan ta.
numfashi na sauke tare da yin hamdala lokacin da motar ta hau kan titin taɗau hanyar fita daga cikin garin......★

★★★


A nan cikin garin Bauchi kuwa,
kan kace me labarin abun da ya faru yakaraɗe ƴan uwa,
su Aunty Jaleela duk sun taho gidan cikin tashin hankali,
Aunty Rafee'at da yanzu isowar su ita da Dr Farooq ko jiran ya dai-dai ta parking batayi ba tafito cikin tsananin tashin hankali tanufi ciki.
Nan ta iske ƴan gidan dukan su zaune cikin parlour'n Ummi har da wasu ƴan uwan su,
da sauri tashigo cikin parlour'n cikin muguwar tashin hankali tana faɗin
"Ummi ina HAMDAH tatafi ina tasani batasan ko ina ba".
Ummi da har lokacin kwalla basu dai na zuba a idon taba takai hannu ta share wasu zafafan hawaye,bata iya ce komai ba
sai kwallar da ta cigaba da sharewa.
cikin share kwalla goggo Hauwa tace
"Tatafi bamu san in da ta tafi ba".
tafaɗa tana sharce hanci.
Kuka Aunty Rafee'at ta sake da karfi cikin muryar kuka sosai tace
"Wlh cikin Ya SALEEM ne wlh cikin sane wlh na shaida HAMDAH bazata taɓa ai kata abun da ake zargin ta ai kata ba".
da sauri
tayi gun Dr Farooq da yanzu yashigo tariko hannunsa tare da faɗin
"Wlh Allah cikin nan na Ya SALEEM ne Abba'n Adeel kai shai da ne".
sai kuma tasaki hannunsa tayi gun goggo Hauwa tace
"Goggo Hauwa kema shai da ce Ya SALEEM shine mutum na farko da ya taɓa sanin ta ɗiya mace,wlh na rantse HAMDAH bata ai kata abun da ake zargi ba wlh sharri a ke mata".
takarasa maganar cikin shashsheka..
Aunty Jaleela ma nagefen Ummi takasa cewa komai sai kwallar da take ta share wa,
parlour'n yayi shiru cike da jimami da sautin kukan Aunty Rafee'at......★


Ido na zuba wa hanyar da bansan na wani gari bane,duk tafiyar da motar yake gani nake baya sauri,
munyi tafiyar da yakai na a wa 2,wata matar da take gefe na tabuɗe murya tace
"Direba nakusa sauka ni a Narkuta zan sauka".
direban ya amsa mata da to.
tafiya kaɗan muka kara muka iso wani gari mai kyau da tsaruwa a dai-dai farkon shiga garin motar ta tsaya direban yace
"Mun iso masu sauka a Narkuta".
kasan cewar Ni ina ta bakin kofa ne yasa dole sai da na sauka kafin matar tafita,
maganar direban naji a sama
"Ƴan mata kema a nan zaki sauka ne".
firgigit na dawo daga tunani da natafi sai kawai na sinci kai na da gyaɗa masa kai,
"No wahala"
yafaɗa tare da jan motar sa yayi gaba.

ido na baza kan titin kowa na ta harkokin gaban sa,
a sannu na masa gefe kan wani kwalbati da ya kasan ce hanyar shiga wani layi na zau na, tare da aje akwati na a gabana,
yayin da masu a dai-dai ta da mashina suke ta tsayuwa suna tan bayana ina zani,wasu nace musu babu wasu kuma nayi musu shiru.
najima sosai zaune a gurin.
Har guri yafara rufawa yayin da ababen hawa suka yawaita kowa yana kokarin konawa gida,
Ina nan zaune a kan kwalbatin,
shafa cikina da naji yana ɗan motsa wa nayi yanzu kam naji ina jin yunwa akasin ɗazu da banajin ko ɗigon yunwa,duk da wunin yau bansa ko ruwa a baki na ba, dan ko breakfast banyi ba.
a hankali na mike nanufi gurin wata mai sai da abinci da nake hango ta can gefen titin,kuɗi na mika mata nace
"Abani abinci".
sai kuma na dubawa kuɗin da nake mika mata ido da mamaki ganin naira ɗari biyu ne bayan nasan dubu ɗaya da ɗari biyu ne a hannuna,
waige-waigen gefe da gefe na nayi ko dubu ɗayan yafaɗi kasa ne amma babu ko alamar sa.
maganar
matar naji tana faɗin
"Babu abincin 200".
nace "To abani drink".
ta miko min gora na amsa na juya a hankali hanyar da na bi nabaza ido ko zanga kuɗin amma har na'isa in da akwatina yake babu alamar sa,
kurɓa uku zuwa huɗu nayi wa drink ɗin sai naji cikina na murɗa ni sai na rufe gorar,
A sannu na ɗago jin karar mota ta tsaya daf da Ni dai-dai lokacin aka zuge glass ɗin motar kasa, wani matashi ne zaune a cikin motar sai busa sigari yake,yayin da wani ke zaune a gefen sa,kai na na kawar da sauri jin hayakin sigarin yana isoni, matashin ya dubi abokin tafiyar nasa yace
"Maye wannan fa ta haɗu musala zata rage mana dare sosai".
Kai ya gyaɗa cikin cakewa da kayan mayen da yake ta shaka.
matashin ya dubeni yace
"Ya ƴanmata shigo muje mana mubaki masau ki muhuta kihuta sosai".
yafaɗa yana latso laɓɓan sa,
nan take maganganu Inna da tarika yimin lokacin tana kwance a gadon asibiti suka fara yimin yawo a ƙwaƙwalwa ta.
rumtse idonuna nayi da karfi,sai na
kuma kawar da kai na batare da nako kalle in da suke ba bare na furta wani abun.
ɗayan dake zaune gefen mai zaman banza yaleko tare da ɗaga murya yace
"Zazzafa ce fa nawa za'a biya ki?".
nan ma banko juyo ba dan na fahimci ƴan iska ne inajin ɗayan yana faɗin
"Muje gaba akwai irin su, biyu zamu ɗiba dan mu huta sosai".
ɗayan kuma yace
"Ta haɗu fa duk da tana cikin hijabi".
"Shiyasa take taja mana aji manya masu zaren take so muje kawai".
haka sukayi ta magan ganunsu sukaja motar su sukayi gaba.
numfashi na sauke tare da cigaba da ambaton sunan Allah azuciya ta da nake,
tafiyar su dakamar 5mn wata mota takuma tsayuwa gefe na wannan karon sai da naji gaban kirji na ya faɗi,da sauri na juyo jin muryar wan da yake cikin matar
"Shigo na sauke ki a gida mana da alama dai kin rasa abun hawa ne".
saurayi ne shima sai dai baiyi kama da irin waɗan can da suka wucen ba yana zaune cikin kamala, murmushi yayi min kana yakuma faɗin
"Naga kin jima zaune a nan da alama dai jira kike azo daga gida a ɗauke ki in bazaki damu ba muje na sau keki a gidan".
da sauri na girgiza kaina tare da faɗin
"A'a Nagode kaje kawai".
kai ya jinjina yadube ni da kyau tare da faɗin
"To in ma bazaki shiga motata ba to ina mai baki shawara daki nimi mai abun hawa kihau ki tafi gida".
murmushi yayi cikin maganar da yake kana yaci gaba
"Duk wani wanda yagan ki zaune a nan to zai yi miki kallo irin kallon da waɗan can samarin da suka yi miki yanzu suka wuce,gashi dai duk mai tunani idan ya ganki bakiyi kama da irin mata masu tallen kansu ba duk da dai basa da kama,
bai kamata kici gaba da jira a kan wannan hanyar ba dan yana da haɗari sosai,
akwai matasa marasa ɗa'a su basa jiran amincewar mace ko kotaso ko kar taso zasu ɗauke ta da karfi su kai ta ɗaki su kulle idan suka gama kwanakin da zasu yi dake suje su yasar da ke,a irin wannan lokaci suke fitowa, babu kuma wan da ya isa ya dakatar da su domin ƴaƴan manya ne,zai fi miki kyau kitari abin hawa kitafi gida".
ido na waro ina kallon sa har yakai karshen maganar yayin da tsoro ya lulluɓeni sai nashiga gyaɗa masa masa kai,shiko murmushi yakuma kana yace
"Ko za'a bani aron number?".
mikewa tsaye nayi
cike da jin tsoron da ya ɗarsa min a zuciya na bashi baya ina ta ɗan kalle-kalle.
ina jin sa yakuma maimaita tan bayar sa ganin bani da niyyar amsa shi sai yaja motar sa yayi gaba.

ido na kurawa cikin layin da nake tsaye a mashigar sa, matasa da magidan ta kowa yana ta haramar tafiya masallaci sallar magriba. Da sauri na sunkuya na janyo akwati na nasoma takawa cikin layin da sauri sosai dan ba karamin tsorata nayi da jin abun da mutumin nan yafaɗa min ba,sai dai ina soma tafiyar naji cikina yayi min wani irin murɗa yayin da kai na yake mugun sara min.
Na yi tafiya mai ɗan nisa sai na zauna kan dakalin kofar wani gida,tare da tafe kai na dake matsa nancin tsaramin, da hannuna ɗaya ɗaya hannun kuma na dafe cikina, tausayin kai na ya kamani sai kawai na fashe da kuka mara sauti.
cikin muryar kuka nake faɗin
"Wayyo Allah cikina kai na wayyo Allah na, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un²".
wani sabon kuka ne yakuma zuwa min Allah sarki Inna banki a yanzu Allah ya ɗauki raina kamar yan da yaɗauki nata ba yafiye min wan nan rayuwar.


nayima ina kuka mai matukar kona zuciya kukun da naɗau lokaci mai tsawo batare da nasan lokacin yakure har haka ba,guri yayi shiru bakajin motsin komai sai haushin karnuka da kukan wasu tsuntsaye, na rakuɓe jikin garo na cusa fuskata sakankanin cinyoyi na,an ce bacci ɓarawo ne to ni dai na tabbata duk iya satan sa bazai iya sace ni a wannan irin lokacin ba,ta ya zai sami narasar saceni bayan ina tangare a dandamalin guri wan da a iya ƴan shekaru na ban taɓa mafarkin kasan tuwa a irin hakaba,ban taɓa rayuwa cikin bakin duhu irin haka ba,ina zaune a haka gari yawaye..
nayi al'wala a panpon da ke jikin gidan da nakwana a kofar gidan nayi sallah.
Koda gari yayi haske jama'a suka fara zirga-zirga a kan hanyar duk wan da yazo wucewa sai ya kalleni ganin na zame wa mutane abun kallo dai na mike naja akwati na,
a sannu narika kusawa cikin unguwar haka na rika zaga cikin unguwar idan na gaji sai na sami guri na zauna in na huta sai na mike nacigaba da tafiyar da ban san in da zani ba.
ranar wuni zubur nayi ina haka yunwa kishin ruwa zafin rana sune abokan rayuwata...

Yau kwana na uku a kan layi nake kwana idan nayi ta yawo har dare ya riskeni sai na sami kofar wani gida na rakuɓe gefe a haka zan kwana a zaune,batun yunwa kuwa tarigada ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login