Showing 39001 words to 42000 words out of 46406 words
min na hanzarta mushirya a kwai kaya acikin ɗakin muyi amfani da su, nace to.
na ɗaga su Nasmah na basu abinci nima na ci, sannan mukayi wanka ,muka kimsa cikin kayan da naganau cikin wardrobe ɗin ɗakin lafiyayyun kaya na manya da yara.
muna gama shirin akayi knocking na kofar koda na buɗe wasu mutane ne maza guda biyu sukace min muje,
To. nace sannan na koma cikin ɗakin na kamo hannun su Nasmah mukabi bayan mutanen.
acan waje muka haɗu da su Bappa nan muka shige mota mukayi gaba.
ido nazubawa hanya a raina nake faɗin
"Yau kuma ina za'a yi da mu?"....★
tundaga bakin get ɗin da yanzu muka iso na fahimci airport muka zo a bakin get ɗin muka haɗu da Mahmoud,
muna isa tuni sojoji sukayi ciki da mu.
direct in da jirgi yake suka nufa da mu,
lumshe idanuna nayi tare da kuma buɗe wa lokacin da na ɗaura kafata kan step ɗin jirgin, sai nake ganin komai tamkar a mafarki.
"To ina kuma yanzu za'ayi da mu a cikin jirgi?".
nayiwa kai na tambayar......!★
Ayi hakuri da typing error busy over👌🏻
*Wlh na fiku matsuwan ganin na kammala littafin nan hausawa sukace in aski yazo gaban goshi yafi zafi insha Allahu mun kusan isa.*🤦🏻♀️
*Ina barar addu'ar ku wacce tagoye ni tamkar mahaifiya aguna Allah yayi mata rasu*😭😭😭😭
Mommyn Twins ce
A sannu narika taka matattakalar jirgin, har muka shige ciki,
Kujerar da ke kusa da window wani mutum ya nuna min yace na zauna anan.
kana ya ɗago su Nasmah da Naseem ya ɗaurasu kan kujerar da ke gefe na,
ya janyo sit belt ya sarkafe su da shi.
tun shigar mu cikin jirgin hankalin jamar cikin da ma'aikatan jirgin duk yadawo kaina,
sai nuna ni suke suna magana wan da ni bajin me suke faɗa nake ba,
sai dai yanzu na fara tsarguwa da yawan kallo da nuna ni da mutanen suke.
ina zaune shiru sai raba ido nake a cikin jirgin, Allah mai iko wai yau nice gani a cikin jirgi wan da da sai dai na hangosa daga nesa in muka yiwa su Abbu rakiya in zasu tafi Saudi.
sai gashi yau gani a cikin sa ko ina za'a kuma kai mu yau oho, ina kuma za'ayi da mu acikin jirgi?.
Kamar Bappa yasan abun da nake ta sakawa cikin zuciya ta,ya mike daga kan kujerar da yake yatoho in da nake, da ƙagan sa kasan yana cikin matsanancin farin ciki, bashi kaɗai ba hatta Mahmoud tun ɗazu bakin su yakasa rufuwa, yakaraso in da nake cikin matukar farin cikin da yagama mamaye ilahirin zuciyar sa
Yace "HAMDAH Allah yayi miki albarka Allah yadaɗa karawa rayuwar ki albarka, hakika rayuwar ki mai cike da ɗinbin albarka ne,
yau gashi ta sana diyyar ki zamu tafi kasa mai sarki".
Amin nace cikin rashin fahimtar in da maganar Bappa yadosa,
"Kasa mai sarki?".
nayi maganar da fuskar tambaya da kuma rashin fahimta.
da sauri Bappa ya gyaɗa kansa kana yace
"Eh kasa mai sarki zamuje Saudi zamu tafi yau da yardar Allah, domin kuwa shugaban kasa yace can zamuje a canza yagama duk wani abun da yakama ta duk wani abun da ya dace adalin shugaba nagari ya gudanar da shi,
zamuje can a can zamuje a canza, do min yace a can za'a fi canza shi da farashi da daraja mai kima a can sunfi mu sanin daraja da kimar Lu'ulu'u, bugu da kari kuma yace a nan babu isasshen kuɗin da zai canza waɗan nan Lu'ulu'u'n duka, dan a yanzu tsaron kasa ya sa a gaba,
Shi yasa yayi magana da masarautar Saudiyya can za a kai musu su zasu canza insha'allahu, Allah dai yayi miki albarka yakarawa rayuwar ki albarka da ke da ƴaƴan ki baki ɗaya".
Bappa yarika zabgamin addu'a da samin albarka.
Mahmoud daga can yana zaune sai washe baki yake,
Ido na waro tare da furta
"Bappa Saudi fa Saudiyya zamuje yanzu?".
nayi maganar cikin muryar dariya mai bayyana matukar farin ciki,
Bappa kam kai yashiga gyaɗa wa yana faɗin
"In sha Allahu".
Wani irin matsanancin farin ciki ne ya lulluɓe ni wai nice zanje Saudi nice a jirgi da zai kaini Saudi.
har lokacin Bappa na tsaye yanata zabgamin addu'a da sanya albarka har sai da ma'aikatan jirgin suka ce yazo ya zauna lokacin tashi yayi.
nan ne ya koma mazaunin sa.
Nan na'ura tafara bada sanarwar jirgi zai tashi kowa ya kimsa.
duban Naseem da Nasmah nayi tare da gyara musu zaman su murmushi nayi ina faɗin
"Nasmah Naseem kunsan in da zamuje kuwa yara makka zamu".
nafaɗa ina dariya suma baki suka washe.
Batare da ɓata lokaci ba jirgi ya ɗaga da mu,
cikin yardar Allah da buwayar sa.
Idanuna na lumshe tare da kuma buɗe wa ina yiwa Ubangiji buwayi gagara misali godiya, lokacin da na ganmu muna keta hazo, tabbas Allah mabuwayi ne kuma mai izza,
sai baza idanuna nake cikin gajimare ina kallon wasu da ke cikin jirgin har sun sami da mar yin bacci,
ni kam zunzurutun farin ciki da murna ko ɗigon bacci bana jin sa a cikin idona.....★
Da misalin ƙarfe 3:15 jirgin mu yasauka a kasar Saudi wayyo Allah, zo kuga farin ciki da murna bakina kasa rufuwa yayi daga Ni har su Bappa bakin ko wannen mu a buɗe yake.
bayan saukar jirgin da kamar minti 15 nan aka umurci fasinjoji da su sauka, bayan murfin jirgin ta buɗe da kanta.
A hankali na mike ina kokarin cire belt ɗin jikin su Nasmah,
da sauri wani ya iso in da muke cikin hanzari yayi abun da nake shirin yi tare da ɗaukar Naseem, daga can wani shima ya karaso da sauri ya ɗauki Nasmah kana sukayi gaba nikuma na bisu a baya.
su Bappa suna gaban mu, tunkan mukarasa sauka daga saman matattakalar jirgin sojojin kasar Saudi suka buɗe murfin motacin su da ke pake a cikin airport ɗin.
Lumsh idanuna nayi lokacin da na sauke fafafuna kan kasar Saudi tare da yiwa Ubangiji tasbihi,
a ɓangaren su Bappa ma haka abin yake Bappa kam har sai da ya ɗaga hannunsa sama yanayiwa Ubangiji da ya halicci wannan sarkakakkiyar kasar godiya da ya nufesa da zuwa cikin sa.
daga can sojojin kasar saudi sanye da uniform ɗin su, suna tsaye jikin motocin su,
tun kan mukarasa sauka sukayi hanzarin nufo in da muke,
Nan suka samu a gaba mu da jagororin da shugaban kasar mu yahaɗo mu dasu,
sauran sojojin da ke tsaye jikin motar sukayi hanzarin buɗe mana mota, muna karaso wa muka shige ciki, yayin da Ni Bappa Mahmoud Naseem Naseem, muke mota guda sauran motocin kuma jagororin mu suka shige ciki.
batare da ɓata lokaci ba sukaja motar mukayi gaba,
Ido nayi ta bazawa kan shahararren titin da muke tafiya kansa da kayatattun guraren da muketa wucewa,
Kai jama'a na rantse babu kasar da takai Saudi kyau duk tafiye-tafiyen ka duk wani yawon buɗe idon ka zuwa wasu kasashe daban-daban har in bakaje Saudi ba,
to Tabbas bakayi kallo ba, baka kuma baiwa idanunka abinci mai kyau ba.....
Wani kayataccen masauki aka sauke mu,
bayan munci munsha munyi su wanka, Bappa yace muje masallaci muyi sallah,
wasu sojoji uku sukayi mana rakiya zuwa Masallaci sai bayan sallar isha muka dawo masaukin mu a gajiye dan munyi sallole kam ba iyaka, tun a cikin masallaci su Naseem sukayi bacci,
a cikin parlour sojojin suka dire su saman kujera,
ɗaukar Nasmah nayi na nufi ɗakin da a ka sauke ni ɗazu,
shin fiɗa Nasmah da ke hannuna nayi kan lafiyayyen gadon, da ɗan sauri na juyo jin an turo kofa,
Mahmoud ne rike da Naseem, gefe na ja tare da soma cirewa Nasmah takalmin kafarta, ya karaso bakin gadon ya shin fiɗa shi,
Ina ɗagowa muka haɗa ido da shi, saurin kawar da kaina nayi,na lura tun a mota yake ta satar kallo na sai ya rika niman yimin magana musamman idan muna hira da Bappa sai ya rika saba ki ciki, yana fara sa baki cikin maganar ni kuma zanyi shiru haka kawai nake jin mogun nauyin sa,
gefen sa na bi ina kokarin wuce sa yace
"Shima kicire masa takalmin zai masa nauyi ai".
yafaɗa tare da nufar kofa yafita, a sannu na isa na cire masa takalmin, zubewa nayi a gefen su dan bacci ne tam ido na..
Washegari bayan mun dawo daga masallaci muka tadda an cike mana parlour da breakfast kalolin abinci iri-iri irin na gida Nigeria da kuma irin na nan kasar Saudi,
bayan munci munsha mukayi su wanka, aka kuma ɗiban mu da sojoji jama'a sai gamu a fadar Saudi,
Ya ilahi ya lillahi na ga karrama wa naga karamci daga gurin larabawa, gaskiya larabawa akwaisu da karrama wa,
nan da nan ina za'a saka akarika yi da mu tamkar mu wasu ne, anawani kafa-kafa da mu.
Nan da nan aka cike mu da kayan cime-cime irin na larabawa....★
Bayan maganganun da ya gudana sakanin fadar Saudi da jagororin kasar mu da shugaban kasar mu yahaɗo mu da su,
nan fadar ta bukaci ganin Diamond ɗin,
nan Bappa ya ciro sa cikin lajuhu wan da suke ɗaure cikin laida ya mikawa ɗaya daga cikin jagororin mu,
kana shikuma ya mikawa wani na kusa da shi sannan shi kuma yamika wa da dukkan alamu hukuma ne, ya karɓa kana ya taka zuwa sakiyar katafaren parlour'n saman table ɗin dake gaban wani farin dattijon balarabe yana zaune cikin kamala da dattako fuskarsa ɗauke da annuri,
ya aje laidar, tare da yin magana cikin harshen larabci.
shugaban shima yayi magana cikin harshen larabci da sauri wani da ke zaune a kasa kusa da kafar sa ya mike ya shinfiɗa wani farin gyalle kan table ɗin kana yashiga kunce laidar,
ya juye Lu'ulu'u'n kan farin gyallen.
wani dake tsaye taɗan can gefe rike da wani ɗan karamin a kwati ya maso da sauri tare da buɗe ɗan karamin a kwatin,
yaciro wani na'ura kana yamaso kusa da table ɗin,
ya ɗaura na'urar kan Lu'ulu'u'n nan na'urar ta kawo haske tare da bada ɗan sauti, idanun mutumin tar a kan na'urar, yaɗau mintuna da ɗan dama kana yaɗago,
cikin garshen larabci yayiwa wan da nafi tunanin shene shugaban magana,
kai ya jinjina tare da duban mu da murmushi ɗauke a kan fuskar sa,kasan cewar bama jin bama jin larabci shima bayajin yaren mu, sai ya juya cikin harshen turanci yake magana,
"To a binciken da akayi yanuna wannan asalin *LU'ULU'U* ne muna tayaku murna".
yafaɗa fuskarsa ɗauke da yelwataccen murmushi,
ai ko gaba ɗaya gurin yakace me da hayaniya kowa yana faɗar albarkacin bakin sa, sai faɗi ake wai wanene yasamo Diamond kuma wai a Nigeria.
mutanen saudi suke maganar, nan jagororin mu suka nuna ni, nan aka rika nuna Ni a na faɗin nice nasamo diamond ɗin, sai kawai nadawo abun kallo, sai nuna ni ake wasu kam ma sai sun zo har kusa dani suna tayani murna,
wasu cikin harshen larabci suke magana sai dai bana fahimtar su gara waɗan da suke magana cikin harshen turanci suma ɗin dakyar sabo da harshen su yanuna da Larabci turancin nasu da kyar nake iya ganewa.
nawo abun kallo har hotuna sukarin ka ɗaukawa dani, wani zaizo kawai yatsaya yaɗauki hoto da ni,
mutane suka rika shigowa suka rika kallo na ni da yarana suka rika ɗaukar su Naseem da Nasmah,suka rika magana cikin harshen larabci idan suka juya da turanci ne nake ɗan fahimtar su,
sukayi ta yabawa yaran da kokari da gararabba da sukayi a bakin ruwa kafin mu samo Diamond ɗin,
hatta shugaban sai da ya jinjina min.
nan da nan ya umurta aje banki a kawo kuɗi, muna nan zaune har waɗan da sukaje kawo kuɗin suka dawo aka rika shiga da gana masgo-masgo cike tam-tam da kuɗi, aka tarasu a tsakiyar parlour'n.
ido na ware cike da tsananin mamakin ganin yan da ake buɗe gana masgo ɗin ana ciro kuɗi a ciki, kuɗi irin na kasar su.
"Sai kace kasa ko kuɗin ganye, to me zamuyi da wannan kuɗin?".
nafaɗa a fili har sai da Mahmoud dake kusa da ni yajuyo ya kalleni,
wasu larabawa ne suka shigo da sallama,in da shi shugaban yayi maga da harshen da muke ganewa wato turanci yake cewa sune masa na farashin Lu'ulu'u, nan suka ƙiyasta kuɗin Lu'ulu'u'n batare da ɓata lokaci ba.
nan da nan aka fara zuba kuɗin cikin na'urorin kirga kuɗi da suka kai guda goma, wan da duk da su akazo daga banki da kuma ma ai katan bankin. bayan an shafi tsawon awanni ana kirga kuɗin
masana farashin Lu'ulu'u' sukayi magana da shugaban,
kuma umurtar su yayi a koma a karo kuɗin dan basukai kuɗin Lu'ulu'u'n ba,
wannan karon har da zinari aka haɗo.
aka rika kirga kuɗin duk gana masgon da aka kirga kuɗin cikin sa sai a maida kuɗin ciki a rufe a kuma zubuta a dadin kuɗin cikin sa,haka akayi tayi anayi ana rubutawa.
ni dai ido na zubawa sarautar Allah ni ban ma iya kirga tulin gana masgo ɗin da suketa tura kuɗi ciki kamar takardu ba,har naji na gaji tamkar nice na'urar dake kirga kuɗin, da mutanen da suketa sakawa cikin gana masgo ɗin.
bayan da aka gama kirga kuɗin a ka jibgesu a sakiyar parlour'n haɗe da
gwala-gwalai da sauransu....
Wannan dattijon balaraben da ke bada umurnin duk abun da za'a yi, yayi gyaran murya tare da nuna kuɗin kana yasoma magana cikin harshen turanci,
"Wannan shine kuɗin Lu'ulu'u'n".
nan kuma ya bukaci a kira masa shugaban kasar Nigeria,
cikin hanzari na kusa da shi yaɗaga waya ya danna kiran lambar shugaban kasar Nigeria,kana ya haɗa shi da shi,
nan yake sanar masa an ƙiyasta kuɗin Lu'ulu'u'n sannan kuma gashi an kirge shi, nan shugaban kasar mu yabukaci a haɗa shi da Bappa,yace yaya za'ayi da kuɗin,
Bappa yace kawai a sashi a sanunun banki dan bamusan yanda zamuyi da wannan kuɗin ba.
shugaban kasar mu ya turo da number account ɗin da za'a saka kuɗin ciki.
nan shugaban yabada umurnin a tafi da kuɗin banki,
nan da nan aka fara fita da kuɗin,
a ka kwashe su zuwa banki,
a ka zuba su cikin account ɗin da shugaban kasar mu yabada na bankuna daban-daban.....★
masauki a ka kuma mana acikin masarautar, kwanan mu uku a gurin naga halacci iya halacci, nadawo abun kallo har daga waje ana zuwa kallo na duk wan da yazo kuwa sai yayi hoto da ni.
har nayi kawaye ƴan matan larabawa ƴan cikin masarauta.
idan naji suna larabci sai nace su koya min, nace an ya ma kuwa zan iya?, sai suce zan iya babu wuya.....★
Acan cikin garin Bauchi kuwa, zaune Ya SALEEM da Na'ima suke a parlour'n sa........!★
mommyn Twins ce
Suna zaune cikin parlour'n Ya SALEEM,
yayin da shi Ya SALEEM ke zaune saman 1str ya tasa system a gaba yana ta faman latsawa,
Na'ima ko na kwance saman doguwar kujera, lodin yankakkun Apple da kankana da abarbane cikin plt a kan table ɗin da ke gaban ta,
daga kwancen take mika hannu cikin plt ɗin tana ɗibar yankakkin Apple da kankanar tana kaiwa bakin ta,
yamusa fuska tayi sannan ta mike daƙyar tana cigaba da yamusa fuskar,
sai kuma ta mike da sauri ta nufi toilet dake nan cikin parlour'n, tazubar da yawon da ta tarashi cikin bakin ta kana tajuyo a hankali,
ɗagowa Ya SALEEM yayi yana binta da kallo, da kyar take ɗaga kafa, tarike kugu da duka hannayenta tana wani tafiya da kyar, ta dawo gurin zaman ta tana wani yamusa fuska,
bin ta da kallo yake har ta zauna ,
zaman sa yaɗan gyara yakuma duban ta tare da faɗin,
"Amai kika kuma?". cike iya kirsa da makirci takuma yamusa fuska kana tace
"Banyi amai ba amma dai inajin zuciya ta na tashi sai dai nakasa yin aman sai yawu da yabi ya dame ni".
yace "Subhanallah duk kayan zakin da kike ta sha ɗin na bai sa kin dai na jin aman ba?".
baki ta yamusa tace
"um to dai gashi ni dai ina jin wannan abun da nake tashan bazai sai da min aman da nake jiba".
"Oh sannu". yafaɗa ya juya tare da ci gaba da abun da yake.
ido ta waro a kanshi ganin ya juya cikin ko in kula da damuwar ta ya cigaba da abun da yake, a kasan ranta take faɗin
"Idan boka na kan tudu ya kasa juya wannan bahagon halin naka, zan kaika wa wani bokan ya juya min wannan halin ko ohon naka".
cike da kwarewa a makirci ta marairaice fuska cikin shagwaɓe murya tace
"Haba My SALEEM iya abun da zakace min kenan,sannu kawai ai yakama ta kayi wani abu nifa wlh wannan cikin yana damu na, ciki da masafaffen laulayi haka, nifa cikin nan yana bani wahala wlh ni kam gara acire shi kawai na huta".
tayi maganar ne cikin kirsa da son gano yan da yake jin son cikin a ransa.
da sauri ya juyo ya kalleta tare da faɗin
"What! azubar fa kikace?".
kai ta gyaɗa cikin shagwaɓa tace
"Wlh ni wannan cikin yadame ni wai ace duk abun da nace baya min daɗi, duk abun da naci sai na rikajin zuciya ta na tashi ni,babu abun da zanci naji daɗin sa kawai ni dai inaga cire sa shine samun kwanciyar hankali na".
da sauri yace
"Ke bakida hankali ne zakice azubar, cikin ne za'a zubar Na'ima?".
kai ta kawar dan ba haka taso ba, har yanzu takasa gane SALEEM duk asirin ta da makircin ta, har yanzu takasa juyashi yan da take so,
yan da taso tarika juya shi yan da take so sai dai har yanzu bata sami damar hakan ba,
duk wani makircin ta da surkullen ta kuwa,
bata taɓa iya juya SALEEM son ranta.
sai dai wani lokacin takan ɗan sami yadda take so daga gurin sa sai dai ba duka yan da take bukata ba.
a yanzu takan ɗan sami nuna kuwalar sa a gare ta,
uwa uba bukatar sa yanzu baya barin sa a jikin sa, kullum sai ya sauke sa a mararta, hakan ba kara min da ɗi yake mata ba dan yanzu ma da kan sa yake niman ta, akasin da da sai ta nima da kanta.
A son ta tana so ya nuna mata kulawa fiye da kulawar da yake nunawa HAMDAH a da,
sai dai ina duk yan da taso hakan bai samuba, ko kwatan-kwatan yan da yake nuna kulawa da rawan kafa lokacin da HAMDAH take da ciki, da kafin ma samun cikin,
baya yi mata.
system ɗin gaban sa yaɗan ture kana yamiko hannunsa yaɗan shafi gefen fuskarta yana faɗin
"Sorry da ma ai an ce duk mai ciki haka take ji har fiye ma da hakan, so hakuri kawai zakiyi har Allah yaraba ku lafiya, yanzu kam ma ai kin kusa hutawa tun da yashiga wata huɗu kenan,
kinga ko kin ɗau gangarar hutawa tun da an ce wuyan