Showing 24001 words to 27000 words out of 46406 words

Chapter 9 - HAMDAH part 2 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

7632

fasinja acikin motar.
abun da tadaɗa bani mamaki ma shine motar batayi kama da na fasinja ba,ban kuma lura da hakan ba sai da nashiga motar.
lafiyayyiyar mota ce irin na shiga kawai. shiru nayi ina bin motar da kallo motace mai kyau tabbas batayi kama da motar ɗiban fasinja ba.
wani irin tsalle zuciya ta tayi dai-dai lokacin Naseem da Nasmah suka zabura lokaci guda suka kankame ni Naseem dake rike a hannuna yajuya kansa tare da kife fuskar sa a kirjina sai ya shiga sauke numfashi,
leka fuskar sa nayi sai naga yana bacci,
Saukar numfashin Nasmah nakeji a bayana itama a hankali.
Idanuna na lumshe tare da kuma buɗe su,
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un"
nafurta kan laɓɓana batare da nasan da fitowar sa ba.
yayin da yanayin da nake jinsa a tun motar farko da na rika ji ya karu matuka,
sai dai har lokacin nakasa gane kalar yanayin.
haka mukayi ta tafiya yayin da tsalle da bugawar da zuciya ta take ke karuwa a kowani dakika,jin zuciyata nacigaba da azalzala ta sai nashiga nanata kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un.
tafiya muke tafiya mai nisar gaske nayi mamakin ganin garin Yola da irin wannan nisar wajen karfe 6 muna kan hanya can muka iso wata kungurmin daji danake hangosa daga nan kan hanya.
a sannu direban yaɗan sakai ta godun da yake yafaka motar a gefen titi sakamakon kiran da ya shigo wayar sa,
yajuyo ya kalleni yace
"Bari na amsa waya ina zuwa".
jiki a sanyaye nace masa "To".
ya sauka da sauri ya mai da murfin ya rufe, yaɗa masa can gefe yana wayar,
gabaki ɗaya hankali yakuma mummunar tashi tsoro mai firgitarwa ya lulluɓe ni, bugu da kari ganin yanayin da Naseem da Nasmah suke ciki duk da bacci suke amma sai zabura suke suna kankame ni.
daɗa kankame ƴaƴana nayi ina ambaton sunan Allah,
magana yake yana kallon motar a hankali nakai hannuna nayi kasa da glass ɗin gefen da nake a hankali batare da na saukar dashi duba.
naɗan maso jikin kofar na kasa kunnena..

A hankali nake jiyo sautin maganar sa duk da bana fahimtar abun da yake faɗa
sai dai yanayin iska dake kaɗa wa yana ɗan ɗibo maganar zuwa inda nake.
"Yes oga yaukam nayi babban kamu wata yarin yace da ƴaƴa biyu a ajiye min kuɗi na ayi musu kyakkyawar ajjiya ina zuwa a damka min su,
ina faɗa maka rai uku da babba da yara kananu guda ku a dana min kuɗi na kawai munkusa isowa,ina faɗa maka yarin ya ce gatanan inaga budurwa ce da yara guda biyu ai yau kam fitar sa'a nayi, haba oga ai kai ma kuɗin da zaka karɓa akan su bana wasa bane jinin su ma kaɗai makudan kuɗi ne bare sauran sassan jiki".
wani irin masifaffen tsalle zuciyata tayi tamkar zata faso kirji na ta fito,
da karfi na dafe kirji na yayin da kai na yayi wani irin mummunar sarawa,
jikina yaɗauki ɓari kamar mazari kallon mutumin nake cikin matukar firgita da masifaffen tsoro.
Naseem na kuma rungume wa da karfi a kirjina,
cikin matsanancin tsoro hawaye yafara sauka a idona,
a hankali na masa ɗaya ɓarin hannun na rawa naɗaura jikin murfin motar na buɗe a hankali, nazuro kafafuna waje namike,
na mai da marfin a hankali har lokacin yana tsaye yabaiwa motar baya yana ta kan wayar,
cikin sanɗa narika tafiya ahankali-ahankali narika tafiya na gangara gefen titi nashiga cikin dajin dake gefen titin a hankali cikin sanɗar narika shiga cikin dajin.
ina shiga cikin dajin narika gudu ina kankame da Naseem gudu nake babu ko kakkautawa da iya kafina ban kuma sanin inda nake jifa kafata cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa,
gudun nake da iya karfina na sai da na isa gindin wata ƙatuwar bishiya kafin natsaya a gun na rakuɓe jikin bishiyar,
ina mai da numfashi,
muryar mutumin najiyo daga can yana faɗin
"Ke ina kike ina kika shiga?".
cikin wani irin kaɗuwa da firgici nadaɗa rungume Naseem na rakuɓe sosai ajikin bishiyar, jikina na cirawa...

Ina jin Muryar sa yana ta matsowa in da nake daga in da nake ɓoye ina kallonsa ya gangaro har yazo kusa da ni yana ta waige-waige yana cigaba da faɗin,
ke Ina kike. numfashi nane yasoma yin sama-sama tamkar zai fice a jiki, ganin sa daf da Ni.
dubana nakai kan Naseem da ya buɗe ido yana kokarin yin kuka kai nashiga girgiza masa tare da ɗaura hannuna kan bakin sa narufe da karfi.
mutumin
ya ɗau lokaci agun yana dube-dube kana yayi tsaki tare da faɗin
"Kash ga samu ga rashi taya ma akayi har tafita ban ganta ba".
yakuma jan dogon tsaki yajuya yakoma gon motar sa.
ina ganin haka nakuma sa gudu narika kusawa cikin dajin, gudu ne irin na ceton rai ko ina ce rayuka,
bana ko ganin gabana.
ga lokacin tuni guri yasoma yin duhu sai dai hasken farin wata daya haske ko ina...

Tuntuɓe nayi da wata katuwar kututture da bansan tana gaba na ba,nayi luuu zan faɗi sai nayi baya tangal-tangal kaɗan yarage na faɗi da baya,
Naseem ya suɓuce a hannuna yafaɗi kasa timm,bayan da nayi kuwa hakan yayi sana diyyar kan Nasmah ya garu da jikin wata bishiyar dake baya na,
a tare suka saki kuka Naseem kam tun da yasaki wani irin kara mai karfi tun da yasaki karan nan bai kuma yin motsi ba.
cikin tsananin firgici da tashin hankali nayi kasa naɗa go
Naseem da ko matsi bayayi na rungume shi a jikina da karfi nashiga girgiza shi da kiran sunan sa,
"Naseem Naseem Naseem katashi dan Allah katashi katashi Naseem".
narika faɗa ina girgiza shi da kiran sunan shi amma ko motsi baiyi ba,
cikin rasa abin yi na zube kasa ina cigaba da girgiza shi,
babu ko alamar nunfashi tare da shi, hankali na yakuma mummunar tashi ga Nasmah sai zandara ihu take.
wani kuka nasake da karfi ina girgiza shi da karfi,
ɗankwalin kai na na ciro nashiga fifita shi ina kiran sunan shi,
nan ma shiru rungume sa nayi da karfi ina faɗin
"Naseem ka tashi dan Allah kada ka mutu, ka kabuɗe idon ka dan Allah Naseem kada ka mutu Naseem Naseemmmmmmm".
Nafaɗa da karfi cikin muryar kuka...

Duk yan da nayi ta jijjiga shi da kiran sunan sa da kuma yi masa fifita yana nan a inda yake babu numfashi a jikin sa,nayi ta kuka kamar raina zai fita ina kankame dashi,kamar an zabure Ni na ɗagosa da sauri na shin fiɗa shi a kasa na mike da sauri nashiga duba gefe da gefe na ko zan ga ruwa na yayya fa masa ko Allah zai sa ya tashi,
bazan mance ba ɗan goggo Hauwa yataɓa yin irin yan da Naseem yayi sai dai shi ba faɗuwa yayi ba rashin lafiya yake sai numfashin sa yaɗauke lokacin sun zo gidan Inna sai naga Inna ta ɗibo ruwa tayi ta yayyafa masa sai ya farfaɗo numfashin sa ya dawo.
da gudu nayi gaba narika ɗan zaga gurin babu alamar ruwa agurin,
da gudu na dawo in da yake na ɗago shi
nashiga hura masa iskar bakina a fuskar sa, narika hurawa ina kiran sunan shi.
mun kai minti 30 agurin ina abu ɗaya babu kuma sauyi,
da sauri nasaka bakina kan bakin sa narika hura masa iska da karfi,
wani nannauyar numfashi ya sauke tare da sakin kuka mai karfi ya kankame Ni,
nima kukan na kuma fashewa da shi na rungume shi ina faɗin
"Alhamdulillh Allah na gode maka".
da sauri na kunce Nasmah da take ta kuka tun ɗazu na haɗe su duk na rungume.
nayita rarrashin su sai da naga sun yi shiru,
nakuma basu abincin su nan ma sai da naga sun koshi,
kana na ɗago Naseem wannan karo shi na goya shi narike Nasmah a hannu.

A sannu narika waige-waigen gefe na nashiga kallon kungurmin dajin da muke ciki ciki kaɗuwa da tsoron ganin guri yagama rufe wa yayi duhu ga daji bakajin motsin komai sai na tsuntsaye da wani irin muryoyi da numfarfashin abubuwan da ban taɓa jin irin suba,
da sauri na juya hanyar da nafi tunanin tanan nabiyo nashigo cikin dajin nabi da sauri narika tafiya sai dai abun mamaki nayi tafiya mai tswon gaske ban ga alamar titi ba,
firgici da tashin hankali yaku baibaye ni ganin kamar daɗa kusuwa cikin dajin nake ga wasu abubuwa masu firgitarwa da razanar wa da nake ta gamuwa da su a hanya.
da sauri na ja na tsaya ganin wani abu saman sa haske kasan sa duhu mai tsoratar wa,
cikin firgici da kiɗi ma najuya da sauri mai haɗe da gudu na koma da baya jikina na cirawa,
sai da natafi da nisa sannan na tsaya,
gefe da gefe na na kalla ina tunanin ta wace hanya ce nabiyo nashigo cikin nan,
a kiɗime na kama wata hanyar ta daban wan da nake ganin ko ita zata fidda ni bakin titi,
nayita tafiya har na godewa Allah amma ita ma babu alamar titi a gaban ta.
nakuma canza wata hanyar haka nayi yawo har guri yagama rufawa gaba ɗaya..


Zuwa yanzu kam kuka na fashe da shi ina ambaton sunan Allah duk inda na juya gabar da yamma kudu da arewa daji ne.
Wani kututture da ke gefe da in da nake tsaye ina iya hango shi sabo da hasken farin wata na isa na zauna a kai tare da kuma sakin kuka cikin muryar kuka mai haɗe da tsantsar tashin hankali da kaɗuwa nake faɗin
"Ya Allah kakashe ni na huta Allah ka tsiratar da waɗan nan yaran Allah ka gani basu ai kata laifin komai ba,
ya ALLAH ni ka ɗauki raina su ka tsiratar da su kasan basu ai kata komai ba".
kukana ne ya tsananta lokacin da na ɗaga kai nakuma bin dajin da kallo,
najima sosai a zaune naci kuka har na godewa Allah...........!★




Mommyn Twins ce



Ina zaune a kan icen shiru ina ta girgiza su Nasmah dan bana so su rika kuka dan idan suna yi sai na rika jin motsin abu kamar yana tahowa in da muke,
ina nan zaune babu alamun bacci ko gyangyaɗi a idona sai tarin ɗinbin tsoro da tashin hankali.......
ganin guri ya ɗan yi haske ba kuma hasken farin wata ba,
hakan ya tabbatar min da gari ne ya waye
wato dai mun kwana a zaune kenan.
a hankali na mike tsaye ina bin kungurmin dajin da kallo,
duba na nakai karkashin kututturen da muka kwana a kai jin motsi da huci,
a kiɗime cikin kaɗuwa nayi baya da sauri yayin da hantar ciki na yayi wani irin kaɗawa ganin ƙatuwar maciji tana fitowa daga karkashin iccen,
juyawa nayi da gudu narika gudu cikin matsanancin tashin hankali sai da nayi gudu mai nisan gaske kana na tsaya, ina maida numfashi da gyara rukon Nasmah da tuni suka saki kuka dukan su,
najuya ina wai gen baya na.
kukan nima na sake nakasa rarrashin su sai kukan dukan mu muke.
a galabaice na zube kasa na zaunar da Nasmah a kasa kana na kunce Naseem shima na ajiye shi gefe har lokacin duk kanin mu kuka muke ina binsu da kallon tausayawa,
sai na rungume su duka nakuma fashewa da kuka.
sai da nayi kuka mai isata kana na ɗago su na basu abincin su,
sai dai na san basu koshi ba dan har lokacin basu dai na kananun koke-koke ba tabbbas dole bazasu koshi ba banciba bare su su samu abinci a jikina, ni kai na yunwar nake ji mara misaltuwa.
wasu zafafan hawaye na share kana na mike tsaye,
ina ɗan kalle-kallen in da muke zaune, gindin bishiyar mangoro ne ga mangorori sunata rito kasa-kasa,
na ɗau wani kara da ke gefe na a kasa na mika hannu nayi tsalle na buga mangorori guda uku suka zubo kasa,
ɗaya ja biyun kuma duk basu yi ba haka na ɗauka nayi ta shan su kaf sai da na shanye su.
kana nayi taimama,
waige-waige nashiga yi dan bansan inane gabar ba,ina zan fuskanta nagabatar da sallar ba, sai kawai na nafiskanci gabana na gabatar da sallar asuba.
ina idarwa na kuma goya Naseem da tun jiya da ya faɗi jikin sa yayi zafi rau har kuma yanzu jikin nasa da zafi sosai,
sannan na ɗauki Nasmah muka cigaba da tafiya...

Munyi tafiya mai nisa jin na gaji nakuma tsayuwa na huta, kana na kuma ci gaba da tafiyar,
wunin ranar haka na wuni ina tafiya idan nagaji da tafiyar duk inda na samu sai na zauna sai dai ban kuma yar da na zauna kan itace ko sunkuru sosai ba guri mai ɗan fili nake samu sai na zauna,
a duk inda nayada zango na kwatanta lokaci kawai nake sai na gabatar da sallah.
ko yanzu ma a wani guri mai ɗan fili na zauna bayan na idar da sallar isha ganin guri yayi duhu sosai sai hasken farin wata,
ina rungume da Naseem da Nasmah,
cikin tsananin tsoro da kaɗuwa na daɗa rungume su jin matsi da kukan wasu abubuwa cikin wasu irin muryoyi daban-daban.
idanuna na rumtse ina ambaton sunan Allah,
zuwa can da daɗewa sai na rage jin sautin muryoyin,
a haka dai har gyangyaɗi yarika ɗan fizgata nayi ta ɗan gyangyaɗin har gari yawaye...
Washegari ma haka na tashi nayita tafiya in na gaji na huta,
yunwa kishin ruwa zafin rana, zuwa yanzu kam jan kafata kawai nake Nasmah da Naseem sai kuka suke nakuma san suma yunwar ce ke ɗawai niya da su.
yunwa da ta addabe ni tafiyar ma da kyar nake iya yin ta
zuwa yanzu kam duk wani
bishiyar da na haɗu dashi idan naga yayi min kama da na ci sai na sinka naci.
nayi tafiya har na gaji kafata duk sunyi bororo kaya sun kwakkwar janeni bani kaɗai ba hatta su Naseem da kwarjanin kaya a jikin su dan idan muna tafiyar naga wani abun tsoro zan sa gudu ta sana niyyar hakan zasu faɗi ko kuma mu faɗi tare haka zan tashi naɗa ga su na rarrashe su sai in sunyi shiru muka cigaba da tafiyar...

Tafiyar da bansan ina muka dosa ba tafiyar da har yanzu bata ɓulle dani titi da nake sammanin tana gabana ba,
tafiyar kunci da wahala..
Yau kwanan mu biyar a cikin dajin nan,
nagama galabai ta na susucewa nafita hayyaci na,
yunwa kishin ruwa zafin rana,
baci ba sha ba wanka haka mukayi ta rayuwa acikin dajin nan har na kimanin kwanaki biyar.
a hankali nake jan kafata da ta kumbura ganin dare yayi ina ta ɗan sauri dan mufita a cikin sun kurun da muke mu isa ɗan sararin da nake hangowa a can a gabana,
da kyar na karaso gun na sauke su Nasmah muka yada zangon mu agun,
rukon su na kyara kan kafata cikin sansanin tausayin su, na zuba musu ido,
sun rame sun dishe sun dawo abun tausayi.
ina nan zaune yunwa ya hanani sakat,
suma sai kananun kuka suke wan da nasan kuma na yunwa ce,
daƙyar na rarrashe su sukayi bacci,
niko kasa yin ɗan gyangyaɗin da nake yi ɗin ma nayi saboda tsabar yunwa,
haka na raba dare ina zaune..
koda gari ya waye kuwa nacigaba da aiki na wato tafiya....


Nayi taganin abubuwa masu razanar wa da firgitarwa idan naga wani abun ma kasa ihu ko niman gudu nake sai dai na rufe idanuna da karfi ina ambaton sunan Allah, nakuma sadakar da cewa rayuwa ta dana ƴaƴana yazo karshe...
Allah sarki rayuwa dani da ƴaƴana mun sauya kamanni mun rame mun fita hayyacin mu mun dawo wasu irin abu da kama,
mun dawo tamkar mahaukata,
Zuwa yanzu karfina yagama kare wa ɗaukan su yana so yafi karfi na,
idan na ɗauke su mukaɗan yi tafiya kaɗan sai naji numfashi na nayin sama-sama idan na ɗan tafi kaɗan sai na ajiye su na huta sosai kana mukuma yin gaba.
Yau kimanin sati biyu kenan muke rayuwa acikin dajin da nake mana fatan mutuwa dan na tabbata ita zatafi zame mana hutu da wannan rayuwar.
cikin jan kafa da ɗan sauri na nufi bishiyar mangoro danake hangosa can sakanin mu daɗan rata dashi,
da sauri narika jan kafata dan rabon da na haɗu da bishiyar mangoro ko wani abu mai zaki na kai kwana biyar, sai dai naci ƴaƴan itace mai ɗaci ko tsami ko burti.
daƙyar na isa gin din bishiyar ina sauke numfashi da sauri na sauke yaran kasa naɗau san da narika kaɓe mangoron sai da na zubo da su da yawa kana na zauna na tattaro su gaba na,nasunku ya sha ba ko kakkautawa har jikina na ɓari,
ina kallon su Naseem suka ɗauka waɗan da ke kusa da su, suna ta gwaguya ban ko hanasu ba dan suma nasan kalar yunwar da nake ji shi suke ji.
ina gama sha naji cikina yawani irin murɗa wa na kwanta a kasa, na da fe cikin nayita murkususu har da hawaye.
najima zube a kasa ina juyi can naji yaɗan sassauta min na mike na ɗau kesu muka cigaba da tafiya.....

Kamar mahaukata duk kayan jikin mu yayi matukar datti bazaka iya shaida wani irin kalar kaya bane a jikin mu,sabo da tsabar datti,
nawa kamma duk ya yayyage daga kasa.
tun wannan mangoron da muka sha bamu kuma samun wani abun ciba a hanya ba sai da muka kuma tafiyar kwana biyu,
daga can da nisa sosai na hangi wani katon dutsai mai girma sosai gefe da dutsai ɗin wasu bishiyoyi ne ajere,
daga in da nake tsaye ina jiyo wani irin sauti mai kara da kugi mai karfi sosai duk da kuwa ina juyo sa daga can da nesa,
cikin sauri da fatan Allah yasa bishiyar abun cine nakara sauri duk da azaba da zugin da kafafuna keyi,
nanufi gurin dutsai da bishiyoyin nan suke.
duk da dai zuciya ta ciki da zullumi da tsoron jin ina daɗa matso in da kara da ƙugi wato irin sautin gudun ruwa yake,
amma ban fasa nufar in da bishiyoyi da katuwar dutsai ɗin nan suke ba,
kuma nan nake jiyo kugi irin kugi mai amon sauti irin na ruwa mai karfi sosai ɗin nan.
a sannu narika tafiya ina yi ina huta wa har na iso kusa da dutsai da bishiyoyin nan,
wani irin juyawa da tsara wa kaina yayi hango wani katon kogi mai girman gaske,
cikin ɗan ɗar-ɗar na karaso jikin dutsai ɗinan wan da can gaban sa kuma katon ruwa ne yana gudu da sautin kugi mai karfin gaske.
koton kogi ne mai girman gaske ko karshen gaɓar sa bana gani, ruwane mai girman gaske ko a TV ban taɓa ganin irin wannan ruwa mai girman gaske haka ba.
gefe da dutsai ɗin kuwa wasu bishiyoyi ne lif-lif-lif masu kyau sai dai da yawan bishiyoyin ban san ko bishyar menene bane gasunan da tarin ƴaƴa a jikin su wasu jajaye wasu koraye,
daga cikin bishiyoyin kuwa akwai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login