Showing 6001 words to 9000 words out of 46406 words

Chapter 3 - HAMDAH part 2 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

7630

shiga jikina har ya zamana bana jinta sai dai cikina sai yayi ta murɗeni abun cikina yayi ta motsawa,idan naji kishin kuwa sai na bazama yawon niman kofar gida mai panpo na tara da hannuna nashi,
ina sha kuwa sai nayi hawaye sabo da murɗan da cikina zai yi ta min...
Zaune nake akofar wani gidan da nake tunanin a nan yau zan kwana dan yamma tayi sosai ana daf da kiran magriba,
kishin ruwa ne ya dameni tun ɗazu sai dai nayi yawo a layin da nashigo yau ban sami wani gida mai panpo a kofar gidan ba,sai dai na fuskanci wannan unguwar na marasa karfi ne dan gine-ginen su ma kaɗai kagani zakasan unguwar talakawa ne.
a hankali na mike na janyo akwakina nacigaba da tafiya ko zan sami ruwa dan ina jin kishin sosai,
ina sharar wata kwana can na hango rijiya mutane na tsaye a kansa anata jan ruwa a cikin sa,
da sauri na nufi gurin dan ruwan da nafi muradi kenan,ina isa gurin na tsaya gefe da wata ƴar dattijuwar mata nace
"Dan Allah a sammin ruwa".
matar ta juyo kana tace
"Sha zakiyi ne?".
kai na gyaɗa mata tace "Ai ho". wani ɗan kara min roba ta janyo ruwan ta zuba ciki tace
"Ɗauka kisha".
To nace da sauri na ɗauka nasoma sha nasha sosai sai da naji cikina ya cika sannan na aje robar tare da yi mata godiya,ta ɗau ruwan ta tatafi a hankali naji cikina na ɗan murɗa min sai dai ba kamar na duk lokacin da na sha ruwan panpo ba,a hankali nasoma tafiya naɗan yi nisa da rijiyar kaɗan sai na zauna kan wani bulo dake gefen ciyawa jin cikin bai dai na yimin murɗa ba.
kai na na cusa sakankanin cinyoyi na inajin yan da cikin ke ci gaba da murɗa ni,
da sauri na ɗago kai na jin abu na tafi a kafata,wani irin waro ido nayi cikin firgici da razana ganin maciji a saman kafata,cikin zafin nama na mike tsaye tare da kwalla kara na yarfe kafar da karfi macijin ya faɗi can gefe yashige cikin ciyayin dake gurin,
da iya karfina nake ihun ina yarfe kafar....


"Wane ne waye a nan?".
naji murya daga can ana tan baya,cigaba da tan bayar a kayi ana motsawa in da nake,niko sai ihun nake ina tsalle da yarfe ƙafan,
jin an dafa kafaɗa na ana faɗin
"Subhanallahi ƴar nan menene?".
da sauri narike hannun matar da naji tana tan baya na da karfi cikin sananin tsoro nace
"Maciji maciji maciji".
nafaɗa da karfi ina cigaba da yarfe kafar,
a kiɗime matar tace
"Ya cije ki ko au da ma kece? me yazaunar dake a nan tun da kinsha ruwan basai kiyi azamar tafiya gida ba, kyazo gidan macizai kizau na ba'azo in da suke Bama ana tare-tare dasu acikin gida bare kinzo nan cikin su,maza zo muje a samiki magani tun kan dafin ya haura miki,wani irin zuwa unguwa ne har guri ya rufa baza'a koma gida ba".
tafaɗa tana janyo hannuna,sai lokacin na gane matar itace wacce na roketa ruwa ta bani nasha ɗazun nan.
ta janyo hannuna ina ɗangala kafar, tana cigaba da faɗin
"Dage kiyi sauri muje tun kafin dafin ya haura miki,waɗan nan abu ai sai a hankali har gida suke shiga mana dan ma yanzu da sauki muna saka musu magani shine suke ɗan yin nesa da gidajen mu".
dai-dai lokacin muka isa kofar wani gida muka shige ciki, murya ta buɗe tashiga kwaɗa sallama tare da faɗin
"Zainabu zainabu matar gidan nan tana nan kuwa".
wata mata tafito daga cikin ɗaki tana amsa sallamar tace
"Ina nan, a'a Mama mai awara kece tafe".
Matar da muke tare da ita tace
"Eh,malam Musa na nan kuwa ko har yatafi masallaci?".
Zainabu tace
"Yana nan yanzu yake shirin fita yazaga ne, yauwa gashi ma yafito".
tafaɗa tana kallon hanyar bayi,
mutumin da a ka kira da malam Musa ya dube mu yana faɗin
"Sannu Mama mai awara ku ne da yammacin nan".
tace
"Eh wlh malam Musa maciji ne ya cije ta dan Allah a sa mata magani kafin ya haura mata".
ya dube ni da har lokacin ina masar kwalla
yace
"To subhanallah garin yaya?".
Mama mai awara tace "Can gefen fadama tabi kasan kuwa kamar gidan su ne".
"Kwarai kuwa Allah yasa ba mugayen bane".
yafaɗa yana shige wa cikin ɗaki mama mai awara tace
"Amin dai". ni dai ina nan itana masar kwalla ban iya cewa komai ba, matar malam Musa wato Zainabu tashiga tafito da taburma ta shin fiɗa tace muzauna,ba jimawa kuwa malam Musa yafi ɗauke da wata ƴar karamar jaka ya zauna gefen taburman kana yadube Ni yace na miko kafar da yaga ina ta girgiza shi,na mika masa yazuge zip ɗin jakar yaciro kayakin magungunar sa ya zaro wani farin gyale ya gyara zaman sa da kyau ya ɗaura ƙyallen saman kafata kana yaɗauko wani magani acikin kwalba yaɗan ɗiga kan ƙyallen dake kan kafar tawa.
yazubawa ƙyallen ido
sai kuma ya ɗago ya dube ni yace
"An ya nan ne kuwa".
kai na gyaɗa da sauri cikin matsar kwalla nace
"Allah nan ɗin yahau".
nafaɗa ina daɗa girgiza kafar dan ji nake kamar har lokacin yana kan kafata,
Maganin yadaɗa ɗigawa kan gyallen kana ya dubi mama mai awara
yace
"Babu wani alamun dafin maciji a tare da ita gashi nan dai kina gani".
sai ya mai da dubansa gare ni yace
"Amma yaya kikaji da ya sare kin?".
nace "Ganin sa nayi a kan kafata kawai ban san yan da akayi yahau ba".
kai malam Musa ya jinjina kana yayi murmushi da faɗin
"Allah ya tai make ki wata kila wucewa zaiyi ke kuma kika tsaya masa takan hanya yabi takafar ki yawuce batare da yasan kina ma gurin ba da taimakon Allah".
mama mai awara ta sauke numfashi da karfi tace
"To Allah ya taimaka ina gama macijiya ce dan su matan basu fiye yin saraba sai sunji matsi".
Zainabu dake gefe tace "Haka ne kam Allah dai ya daɗa karewa".
suka amsa da amin nidai ido naketa cirewa cike da tsoro.
mama mai awara ta mike tana yiwa malam Musa godiya tayi wa zainabu sallama tayi waje nabi bayan ta.


Muna fita ta dube ni tace
"Allah ya kare mugayen basu cije kiba,ai wannan mai maganin har wasu garuruwa suna kawo masa jin yan sarar maciji dan shi gada yayi tun iyaye da kakani,idan maciji ya cije ka to da wannan kyallen yake gane kalar macijin da ya sare ka,sai ya baka magani,idan yasaka kyallen dai-dai in da maciji yazuba dafin sa to kyallen zai canza kala yakoma kalar jikin macijin,kinga ai yan da yaɗau ra kyallen a fari a farin sa ya ɗaga,babu rabon wahala Allah ya kare,
Maza kiyi gida yanzun nan muje na nuna miki hanya mai sauki da zaki fita bakin hanya,jirani a nan na ɗauko miki jakar ki".
kai kawai na gyaɗa mata yayin da naji wasu zafafan hawaye sun zubo min,yanayin yan da matar take magana yasa ni tuno da Inna ta,
"Allah sarki Inna na tabbata in da kina numfashi bazan taɓa hofanta ba".
Kwalla na kuma share wa lokacin da matar tadawo gaba na tana mika min a kwatina,
tace
"Maza ki tafi gida dare yayi ke bakya tsoron kije gida iyayen ki su miki faɗa, Allah ma ya takai ta ai da sai dai a kai ki gida da raunin maciji,
yi sauri muje na nuna miki kinga har na makara markaɗen awara nafito ɗauka wa shine na jiyo kururuwar ki da yanzu na dafashi har na tsane".

Duk abun da take faɗa sama-sama nake jinta wani irin kuna da raɗaɗi zuciya ta ke min sai sharar kwalla nake.
muna fita gaban rijiyar nan da hannu ta nuna min hanya tace
"Ki mike nan hanyar ta ɓulle har titi Allah bamu alheri".
kai na gyaɗa kana a hankali nasoma tafiya,ita kuma tabi ta wani hanyar.
A hankali nake tafiyar idanuna a kasa sai gani nake kamar zan ɗaura kafar kan wani macijin,duk da kuwa guri yafara yin duhu lokacin........!★





Mommyn twins ce




*Masha Allah yau Allah yayi ikon sa na dawo Nagode da addu'o'in ku sosai*🥰





Ina ganin shige war matar cikin wani gida sai na rakuɓe kofar gidan da na iso yanzu,
hawayen tsoro ne suka shiga zuba min a ido shike nan Ni nasan rayuwa ta ta kare yau maciji shi zai yi saniyyar barina duni,tun da kuwa garin su nazo,
wani sassanyar kuka na sake mara sauti nasadakar ma kawai macijin yacije ni na mutu ko zan huta da wannan rayuwar kunci da bakin cikin.
Ji nayi an gasko min toci da sauri na ɗago kai na tare da kare fuskata da hannuna sabo da hasken tocin dake haska min ido.
da sauri takaraso in da nake rike da roba mai ɗauke da kullun waken awara a ciki,salati ta doka tana faɗin
"Yau naga ikon Allah ƴar nan ashe baki tafi gida ba,kuma zama anan kikayi,hanyar koma wa gida ne ta ɓace miki kokuwa wani laifin kikayi kike tsoron komawa,in ba haka ba mai zaisa kiki komawa gida,ki zauna kina ta rabuɓe-rakuɓe a nan,
yaran zamani ga iya laifi ga tsoron hukunci,tun da kana tsoron hukunci ai sai ka riƙa gujewa ai kata lai fi,to baki tsoron ki karawa kanki wani laifin ni sam banason yaro irin haka to menene am fanin fitowa a gidan da har zaki ki koma wa gidan ki rakuɓe a nan kinata koke-koke, to in bugun naki za ayi bagara ki koma a bige ki ya wuce miki ba, ka zauna ka karawa kanka laifi,ɗauki jakar maza kizo nan".
tafaɗa tana dubana.


Tana gaba ina biye da ita muka shige cikin wani ɗan ma dai-dai cin gida mai ɗauke da ɗaki ciki biyu sai kitchen da Kuma banɗaki a gefe,
da kaga kidan kasan na talakawa ne sosai sai dai a tsaftace yake babu kazanta ko datti a cikin ɗan ma dai-dai cin tsakar gidan.
tanuna min ɗaya daga cikin ɗakunan tace nashiga,
a kasa kan taburman dake malale cikin ɗakin na zauna,
babu jimawa tashigo ɗauke da kwano ta direshi gaba na tana faɗin
"Ci yanzu muje na rakaki bakin titi kihau abun hawa ki koma gida,
in ban da rashin hankali niyyar guduwa kikayi gaba ɗaya a gidan da kika ɗau jaka?,
Akul karki kuma wan nan ba ta'adar ɗan kirki bane ci maza muje".
wasu zafafan hawaye na share kana da sauri har hannuna na rawa na buɗe kwanon,
tuwon jan dawa ne miyar bushashiyar kuɓaiwa,sai tashi da kamshin daddawa yake,
da sauri na sa hannu na soma ci.
ta fita ta kuma dawowa da kofin ruwa ta aje min,kana ta fita taje tasoma tatar kullun da ta ɗauko markaɗen sa.
cin tuwan nake tamkar na sami nama,yau kwana uku da wuni ɗaya kenan rabun da nasa wani abu mai gishiri a bakina.
naci tuwon sosai dan har nakusa cinye wa kana na kara da ruwa,
bayana na jingina da jikin garu tare da yiwa Ubangiji godiya,
a hankali narka jin murɗar da cikina keyi min yana ɗan raguwa, yayin da abun cikina da tun jiya da cikin ya murɗa ni sai shima naji ya motsa sai ya sauka kasan marana ya dunkule guri guda bai kuma motsawa ba sai yanzu naji yana ɗan motsawa da harbawa a hankali...
can an jima matar taɗa go labule tace
"Zo kiyi sallah kafin awara ta ta dafu sai muje na rakaki".
"Tom". nace na mike nafito rike da lanta da ke cikin ɗakin kasan cewar guri yayi duhu sosai,cikin ɗar-ɗar nashiga bayin nayi sarki nafito kana nayi al'wala na koma ɗakin na gabatar da sallar isha,
bayan na idar ina zaune kan sallaya tashigo,ganin da al'wala tare da ita sai na mike nabata sallayar na koma gefe.

Bayan ta idar ta mike ta dube Ni tana faɗin
"Taso muje ga dare nata yi ki tabbatar kin koma gida kuma kada kisa ke yin haka
kinaso kishiga fushin iyaye ne fushin su musufa ce yana jefa mutum cikin halaka".
wasu hawaye ne naji sun kuma zubomin
"innalillahi wa'inna'ilaihirra'un".
nashiga nanatawa a raina,shin nima haka zan tabbata da fushin iyaye,shin meyasa iyaye na zasuyi fushi da ni kan abun da ban ai kata ba,me yasa zasu yanke min hukunci kan abun da bana da masaniya a kansa??.
maganar ta naji a sama
"Yau kitashi muje kin tsaya kuka ne,ai har gida zansa mai abun hawan yakai ki, tukunna ma inane gidan ku a wani unguwa kike? dan gobe zanje na tabbatar da kin koma ko baki koma ba,kada ki sake ki kuma laifi kice zaki gudu ni bani son yaro irin haka a ina iyayen ki suke?".
kuka na fashe dashi cikin muryar shashsheka nace
"Ni bani da iyaye bani da komai haka zanyi tabin layi har rayuwa ta ta kare na mutu."
"Zancen banza kai, to tashi ki fita min a gida kije kikare rayuwar naki acan,an ya ma ba yawon duniya kika fito ba?to ita duniya ta ishi kowa riga da wando tun da shi kika zaɓa je kibishi,tashi maza ki fita min a gida ban mayi tunanin ko wacece keba na ɗauko ki na kawo ki har cikin makwanci na,tashi-tashi maza tashi nace".
tafaɗa tana nuna min kofa da babbuga hannun ta,
da kyar na mike tsaye ina cigaba da kuka zuciyata nayi min wani irin mugun zafi,
Na rayawa rai na
tabbas idan nafi bakin titi kan kwalbatin da na zauna ranar da nashigo garin nan zan koma, har idan wani yazo yace na bishi zai bani makwanci da abin ci zan bishi,
to menene am fanin rayuwa ta yanzu ratuwa ta bata da wani am fani yanzu.
idanuna na rumtse da karfi jin bugun zuciya ta ya tsanan ta,a duk san da zuciya ta tafara bijiro min da irin waɗan nan tunanin sai magana ta da Inna na karshe yashiga yimin yawo cikin ƙwaƙwalwa,
"kada rayuwa tajuya miki baya ki mance da uban gijin ki".
ƙwaƙwalwa ta tarika amsa kuwwa da wannan kalmar, sai nashiga nanata kalmar innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un.


a hankali na kai hannu zan buɗe labulen ɗakin na fita tace
"da kata,baki da iyaye ajikin bishiya kika fito?".
juyowa nayi ido taf da kwalla nace
"A da ina dasu ayanzu kuma sun yanke alakar da kansu,yanzu ni bani da kowa na karɓi hakan ne abisa umurnin su".
ina kaiwa nan najuya ina kokarin fita tace
"Zo nan kin taɓa jin yan da iyaye sukace sun yanke alakar su da ɗan da suka haifa?,
in ba wani shirin kike son kullawa ba ƴar kankanuwa da ke kin iya tsara zance".
wani murmushi nayi wan da yafi kukan da nake ciwo kana na dawo na zauna in da na tashi,dubana tayi da kyau kana tace
"Wacece ke kuma suwaye iyayen naki? da kike shirya musu karyar sun yanke alakar ɗa da mahaifa a sakanin ku,sabo da kin kullawa ranki zaki shiga bariki, Allah shi kyau ta wannan rayuwar ba mai ɗaure wa bane zai fi miki kyau ki koma gare su ki nimi gafarar su, kirufawa kanki asiri suyi miki aure kije ɗakin auren ki asirin ki a rufe,
in ban da zamani ma ai mu a da kamar ki ta isa aure, yanzu ne kawai wai sai yarin ya tagama rika a gida kafin ayi mata aure,
da ɗa da dukiya ba'a yi musu mugun ta idan na barki kika fita nasan bagidan zaki koma ba dan haka bazan barki ki fita a gidan nan ba, ni da kai na zan dam kaki hannun iyayen ki,
yanzu dai dare yayi ki kwana gobe idan Allah yakai mu da safe zan kai ki gida da kaina"...

ni dai ban iya cewa komai ba sai sharar kwalla nake,har ta fita a ɗakin can takuma dawowa tace nataso na zo,na mike da akwatina nabi bayan ta, ɗayan ɗakin da ke jire da nata ta nuna min tace
"Shiga nan ɗakin ki kwanta na gyara miki gurin kwan ciya".
nace to,tana tsaye sai da taga nashi ga kafin ta wuce taje ta kulle kofar gida tadawo tashige ɗakin ta.
bin ɗakin nayi da kallo,katifa ce a kasa da kaɗan yafi taburma kauri,sai wasu kayaki da kullin buhunhuna a gefe,sai dai ɗakin a share tsaf yake babu ko datti.
a sannu na aje akwati na gefe na zauna kan katifar na janyo pillow da aka naɗe shi cikin tsummar zani akayi masa riga da shi,na gyara na kwanta na rufe jikina da hijabi na,
numfashi na sauke lokacin da nakai hakarkari na kan shinfiɗi da sunan kwanciya,rabon da na kwanta irin haka yau kwana uku, Allah mai girma yau gani acikin wata rayuwa,
saman ɗakin nabi da ido wan da kwano ne kawai rufin sa babu ko silim.
Allah ke nan mai iko mai yin yan da yaso da rayuwar ɗan adam,yau nice kwance cikin ɗakin da babu gado bare wadaceccen katifa babu hasken wutan lantarki bare AC.
a tunanina kwanciyar da nayi zan sami yin ramuwar baccin da ban yishi ba na kwanaki uku amma me sai naji babu ko ɗigon bacci a ido na,tunani damuwa kunci su suko addabi zuciya ta haka na ta kuka sai daf asuba bacci yasamu nasarar sace ni....★



washegari da safe ina zaune cikin ɗakin tashigo
ɗauke da kwano da kofi ta dire shi gaba na, hannuna da nayi tagumi da shi na zare kana na gaishe ta ta amsa tace
"Ki karya sai kiyi wanka ga ruwa can na kai miki banɗaki bari nagama suya sai mu tafi".
to kawai nace. ta fita na janyo kwano da kofin ɗumamen tuwo ne da kunu mai zafi saman murfin kofin kuma awara ne da kosai suma sai turiri suke.
ina gama karya wan na sako hijabi nafito, tana zaune cikin kitchen tana ta suya yayin
yara suka zagaye ta sunata mika kuɗi tana zuba musu,har da matasa ma sunata shigo wa siya.
a sannu na shige bayin na ɗau tsawon lokaci ina wanke jikina da nake jin nauyin datti a fatata.
koda na fito daga wankan akwa tina na buɗe na ciro doguwar riga na material na saka,ina gama sa kayan nazau na kan katifa.
can da jimawa ta shigo da mayafi a kan ta ta dube ni tace
"Taso mu tafi yau wa menene sunan unguwar taku?".
kasa nayi da kai da jikin hawaye ya cika min ido,jin ta kuma mai maita tan bayar sai na ɗago nace
"Ni ba agarin nan nake ba zuwa nayi kuma ni bansan kowa a cikin garin nan ba"...


Da mamaki take kallo na cike da mamaki ta zauna kan ɗaya daga cikin ɗaurin buhun dake cikin ɗakin, ta dube ni da kyau kana tace
"Tanan kika ɓullo kuma?".
kai na jinjina kana
nace "Wlh ni ba ƴar garinnan bace,ban taɓa sanin saba".
kwalla da suka zubo min na share kana nacigaba
"Kada ki mai dani gidan mu domin Abba na yace in nesan ta da su idan na dawo yace bai yafe min ba, bana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login