Showing 42001 words to 45000 words out of 46406 words
ta ciki yafara kwari ne da zaran yafara girma zaka fara hutawa da laulayi,to kin ga kuwa kin kusa hutawa kenan".
rass. taji gaban kirjin ta ya buga shiru ta ɗan yi tare da tafiya cikin tunani a kasan zuciyar ta.
sai kuma da sauri tadawo da kallon ta san sa jin yana faɗin
"Wannan cikin dai ina ga shine a ke ciwa mai bin jiki,to ina ga shima yabi jikin ki ne gashi dai har watan sa huɗu amma bai fara bayyana ba,wata kila in yafara girma yanuno kansa nan zaki ɗan ji daɗi".
hannu ta mika taɗauki yankakken Apple takai bakin ta tana tauna cikin nuna rashin jin daɗin abun da take ci tace
"Ni wlh tsabar wahalar da cikin nan yake bani bansan har yashiga wata huɗu ba".
tayi maganar yayin da zuciyar ta ke tunano mata lallai wannan watan ne yayi dai-dai da cikin watan sa huɗu kenan.
murmushin gefen baki yayi kana ya mai da idanun sa kan wayar sa da ya ɗauka kan hannun kuje rar da yake kai.
sannan yace
"Ai abu na jikin ki ma kina mance kwanakin sa? tun lokacin da na sami labarin cikin nake lissafin sa".
ɗan dimm tayi sai kuma tayi saurin kawar da maganar da faɗin
"Wlh ni ina jin kwaɗayin gwaten gauta, ina ga abu mai ɗan ɗaci-ɗaci yafi gyara min baki".
"Gwaten gauta kuma to ke meye zakiyi da wani gwaten gauta?".
yayi maganar har lau idanun sa nakan wayar sa.
tace "Allah ni shi nake jin sha'awar na sha zan dai na jin bakina ba daɗi, kasan fa tun ranar da Raliya tayi ta kawo min na sha ranar na wuni ban zubda yawu ko amai ba,har nakuma ci abinci lafiyar Allah babu jin rashin daɗin nan,
gashi yan zu Raliya batanan tayi tafi bansan yaya zanyi ba,
bansan wama zai yi min in sha ba."
cikin fara gajiya da surutun ta da son sashi yawan magana da take yace
"Kiyi da kan ki mana har sai wani yamiki kafin kisha, tun da ciwon bai kwantar da ke ba kina iya tashi mai zai hana kiyi da kan ki, sai a samo miki gautar kiyi ai,
ko kuma kisa Rufa'ila tayi miki ko sauran ma'aikatan gidan".
yana gama faɗa ya mike tsaye yana rufe system ɗin sa.
Ido tawaro tace
"Rufa'ila? Rufa'ila'r ce zata yi min girki wlh bazan ci girkin Rufa'ila ba, kawai kasa dai a yimin".
takarashe maganar tana bubbuɗe kofofin hanci.
da ɗan mamaki yajuyo yakalleta ganin yan da tayi maganar a tsaye kana yace
"To wa kike so ya miki ni kike so naje nayi miki? babu masu girki ne a cikin gidan da sai na nemo masu yi miki?".
ganin yan da ya sauya fuska sai kuma ta shagwaɓe fuska tana faɗin
"A'a kai kuma haba dai kadai sa ayi min dan Allah my SALEEM ina so na sha".
"Wa kenan zan sa yayi mikin?".
yafaɗa yana kokarin barin gurin.
da sauri tace
"Dan Allah kayiwa Mamie magana dan nasan ita zatafi iya yin gwaten tun da dai abincin gargajiya ce, ita zatafi yin mai daɗi ma dan Allah kayi mata magana sai tayi min".
bai kuma cewa komai ba har ya juya zai bar gurin sai kuma ya ɗago wayar sa ya laluɓo lambar Mamie ya dan na kira.
bayan sun gaisa yaɗaura da faɗin
"Mamie wai Na'ima ce ke son shan gwaten gauta ko zakiyi mata".
daga cikin wayar Mamie tace
"Yanzu ma haka shirin fita unguwa nake, tasa ma'aikatan ta suyi mata mana in bazata iya yi da kan taba, kaganni nan fita ma zanyi".
Mamie na gama faɗar haka ta kashe wayar.
duk abun da suke Na'ima na ji dan wayar a speaker yasa ka,
batare da yajuyo ba yace "To kinji abin da Mamie tafaɗa bata nan zata fita so kawai kisa ayi miki".
yafaɗa tare da gyara rukon system ɗin sa ya nufi bedroom ɗin sa.
wani irin kololon bakin ciki ne ya tirni ke ta,
wato koma damuwa baiyi ba, shidai yakan nuna yana son cikin amma irin rawan kafa da yake nunawa lokacin cikin HAMDAH sam bayayi a kan cikin ta.
tsaki taja ta tare da mike wa, sai gatanan ta ware tana tafiya normal bakamar irin yanda ɗazu tayi da taje zubda yawo cikin toilet ɗin parlour'n ba.
ta nufi side ɗin ta da sauri ta shige ɗakin ta tana shiga,
ta ɗau wayar ta takira kawarta Raliya, Raliya na ɗagawa tace
"Aminiya ya kike ya gida ya cikin mun dai?".
Raliya tayi maganar da dariya
dariya duk suka saka kana Na'ima tace
"Him kedai bari aminiya ciki yana nan, ke ni ba na mance ba ashe dai cikin yashiga wata huɗu ni bana gama sakarkancewa ba kwata-kwata ni na ma mance da lissafin ashe ɗan batalikan nan yana nan yana rike da lissafin".
dariya Raliya ta fashe da shi.
tace "Ke da abu ke jikin ki baki rike lissafin sa ba".
Na'ima tace
"Himm ke dai bari ai ni na wasar da lissafin tun wancan ranar ashe dama haka mukayi lissafin cikin yanzu yake cemin wai cikin wata huɗu kenan yanzu yakusa shiga biyar kenan,
to idan yashiga biyar ba'aga ciki yana tashi ba yaya kenan, karfa asiri ya tonu".
Raliya tace "Haba dai sai kace ba Na'ima da na sani ba ya kike wani abu kamar ba kece Na'ima ba,ta ya za'ayi ya gane da zaran cikin yakai wata biyar in yaga baigirma ba sai muyi hanyar da zamuyi sai kawai ace ya zuba".
"Kwarai kuwa haka za'a yi kawata kin kawo mafita amma bazai taɓa zuba ba sai ya bani miliyan 5 ɗin na yanzu ma zan shirya in ce masa zanje awo ina zuwa kuma zan kira sa in haɗa sa da Dr Hashim Wargi in tsara masa yan da tafiyar zata kuma ci gaba".
kuma shekewa da dariya sukayi, Raliya tace
"Kai kawata kina fa tsula tsiyar ki".
tace "Yan da nake so kuwa in juya acikin gidan yanda naga dama".
sai kuma taɗan sassauta maganar tare da cigaba dafaɗin
"Amma ki san meye aminiya?".
Raliya tace "Sai kin faɗa". tace
"Allah yanzu ina son cikin nan da gaske narasa yan da zanyi ne kawai kinsan rannan naje gurin boka nace mishi yasake duba min yagani anya kuwa bazan haihuba, yace min maganar kenan fa ɗaya tas koyayen haihuwa ta na gama da su,wai ashe sauran sa kenan zuwan mu akan mahanar kuɗin da nake so SALEEM ya banin nan, yabaiwa aljani durkus jinin duk cikin da zanyi nan gaba kin san wai ashe bayan dawowar mu da wata biyu nasami ciki banko sani ba aljani durkus da akayi masa sadakar jinin yaɗauke cikin yaje ya shanye jinin,
dama wai shike nan ya rage duk na wanke sauran tun muna makaran ta,to ni yanzu abun yafara dami na kin gafa SALEEM yana son haihuwa yana son yara,
narasa yadda zanyi kinga fa ta sana diyyar ganin hankalin shi naga yafara komawa kan yara idan abokan sa sukazo da yaran su karkiga yan da yake yi da su,
gudun kada ya tunu cikin wancan ɓatacciyar shegiyar yarinyar nan HAMDAH da kuma abun da zata haifa ko ta haifan ko ta mutu da cikin oho mata shiya sa fa na laune nace ina da cikin nan, sabo da kawai hankalin shi yadaɗa dawowa gare ni,
yanzu tsohuwar sa ma wai an kira ta dan rainin wayo nace inaso nasa gwaten gauta kinsan me tace? tace wani wai zata fita unguwa to in yi da kai na mana,
kiji matan nan lokacin da wannan ɓatacciyar HAMDAH'N take nan kullum ita ke mata girki tasa akawo mata,
amma wai yanzu nace inaso nasha gwaten gauta tace wai nayi da kaina,wato ko da ɗanta ya narka min cikin da gaske haka zatace kifaji matar nan".
Raliya tace
"To ai yanzun ma na gaskiyar ce tun da koshi uban gayyar bai isa ya karyata ko yagane karya bane,
kirabu da ita kawai kin san har yanzu sunajin abun aransu sai dai bazasu iya yin komai a kai bane".
Na'ima tace
"Ah to sumayi mana ai sai dai abun yakashe su a ransu amma zancen suyi magana kam karyansu,
SALEEM yarigada ya zama nawa ni kaɗai idan sukayi wasa ma sai na rabasu da shi in ga ta faɗin su".
dariya suka saka dukan su
Raliya tace
"Yi hakuri dai kada ki raba su bassu a haka kawai aje zuwa tun da babu abun da aka rage ki da shi".
tace "Kwarai kuwa SALEEM nawane yazamo nawa, amma kinsan maye ne,
Raliya inason magana da ke kizo gida muyi ta, Raliya inason ɗa".
Raliya tace
"Kinason ɗa kuma?". tace "Kwarai kuwa ina son ɗa ɗan da zai zamo da na SALEEM duk da nasan ni bazan taɓa haihuwa ba,amma ina son ɗan da zai zamo na SALEEM kuma a madadin ni nahaife shi magajin SALEEM yashe zaki zo?".
Raliya tace "Zan shigo gobe dan yanzu bana ma gari nayiwa wani saurayi na rakiya, yanzu haka ma muna hotel ne da tun ɗazu kika kira ma bazan sami damar ɗagawa ba,nashiga wanka ne ma yanzu shine kiran ki yake shigo wa."
Na'ima tace
"To shike nan yanzu yaushe zaki dawo".
tace "Gobe ko jibi zamu dawo".
tace "To Allah yakai mu kida gobe dan Allah tabbas ina son ɗa wan da zai gaji dukiyar SALEEM".
Raliya tace "To an gama ina hanya kuwa".
nan sukayi sallama.
bayan da Na'ima ta sauke wayar daga kunnnen ta zama ta gyara tare da faɗin
"SALEEM dole zan samo ɗan da zai zamo naka yakuma gado min dukiyar ka".
tayi maganar a fili yayin da take girgiza kanta alamar yar da da duk wani shirin da ta tufkeshi yanzu a ranta....
a ɓangaren Mamie kuwa
tun lokacin da sukayi waya da SALEEM tana zaune a ɗakin ta, bawai fita unguwar zatayi kamar yan da tafaɗa mishi ba, tafaɗi hakan ne kawai dan a ranta tanajin bazata iya girkawa Na'ima abun da zataci ba koda ƴaƴan cikin ta sunkai guda goma ne.
tana zaune gan ɗeɗiyar mata da ita wai tana laulayin ciki har da niman mai yi mata girki duk da tulin ma'aikatan da ke gidan su.
kai Mamie ta girgiza "Wato dan taga lokacin na HAMDAH ni ke mata girki ko,
to ai HAMDAH yarin yace karama tana bukatar tai mako".
Mamie tayi maganar a can kasan ranta.
yayin da take jin Na'ima wata annoba ce acikin rayuwar su sai dai babu yan da suka ɗiba suka iya da ita.
Mamie na nan zaune har Abbu yashigo yakaraso ya zauna a bakin gadon da take zaune,
ya dube ta cikin kulawa tare da faɗin
"Yaya dai Hajiya Maryamu na ganki shiru haka".
murmushi tayi kawai tana faɗin
"Babu komai".
amma acikin kasan ranta tabbas tunanin HAMDAH ce yazo mata.
shima kuwa a ɓangaren Abbu haka abun yake dan tun shigowar sa da yaga tanayin ta shima yashiga irin yanayin datake cikin wan da baki baya iya furtashi sai dai yayi ta kona zuciyoyi...
a can cikin part ɗin Ummi kuwa
zaune take a kan sallaya kamar koda yaushe tana jan jarbi,
bayan tagama yiwa ɗiyar tata addu'o'in samun kariyar Allah a duk in da take.
Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela kasan cewar yau Saturday ne duk suka tattaro da ƴaƴan su sukazo gida wuni, duk suna part ɗin
Ummi da ƴaƴan su, suna zaune suna ta tayata hira,
Ummi dai na zaune tana jin su wan da rabin hankalin ta ma baya tare da su.
Aunty Rafee'at da ke ta danne dan ne cikin wayar ta har tashi gurin adana hotuna,
shiru tayi tare da kurawa hoton HAMDAH sai ga hawaye ya cika mata ido kan kace me yafara gangara kan fuskarta,
ido Jaleela ta waro ganin Rafee'at na share kwalla tace
"Aunty Rafee'at yaya dai?".
fuskar wayar ta nuna mata batafe da tayi magana ba, da sauri ta karɓi wayar yayin da itama kwalla suka ciko idon ta,a fili Aunty Jaleela tace
"Ko ya take?". tayi maganar cikin rauni da damuwa sosai.
"Sai Allah Allah ka kare ta".
cewar Aunty Rafee'at, Ummi ma kwallar ce ta cika mata ido dan tasan mahanar kan HAMDAH suke.
ganin Ummi tayi shiru da alamun bayyanar damuwa sosai a tare da ita.
sai sukayi saurin kawar da zancen da wani hirar da ban...
acan cikin garin Yola kuwa
Mama mai awara na hango acikin family house ɗin su, wan da matar yayan ta ta kanainaye gidan yazamo nata dole da ƴaƴan ta.
tana zaune cikin waɗi ɗan karamin ɗaki karami sosai, acikin ɗakin take zaune da taburman ta.
tazuba uban tagumi, tunanin HAMDAH da halin da take ciki yanzu kaɗai take.
lokacin da ta iso Yola ɗan kuɗin da tazo dashi a hannunta ta aje cikin ɗaki akabi a ka sace ta nima tayi cigiya sama da kasa ta rasa, kuma su kaɗai ne agidan daga matar yayan ta sai ƴaƴan ta, amma tayi tan bayar duniyar nan sai matan yayan tace ta ɗaura musu sharri,
karshe tayi ta mata wulakanci na kin kari,
abincin da take bata ma sai ta daina bata, gashi kuɗin da zatayi kuɗin mota ta koma Narkuta babu tunanin HAMDAH duk yabi ya isheta.
ganan ta da taje dan ta saida shi ma taje ta samu wasu sunci gonar,
duk yan da tayi akan gonar akace sam ba nata bane karshe haka tabarsu da Allah.
wannan ɗakin da take zaune aciki ma tun lokacin da tace kuɗin ta ya ɓata matar yayan nata tace tafita mata a gida da kyar dai tasa mu tabarta tacigaba da zama acikin, wan da da ɗakin kiwon kaji ne zuwan tane ta share shi ta shinfiɗa taburman ta take kwana a ciki.
tana so tazo Narkuta taga halin da HAMDAH take ciki amma bata da kuɗin mota, naira goma wannan yafi karfin arzikin ta,
tayi yawon niman bashi gidajen da ta sani dan ta fara jarin awara a nan ɗin dan tasamu kuɗin motar da zata takoma sai dai bata samu ba,
tana zaune ta zuba tagumi yunwa duk ya addabe ta dan rabon ta da cin abin ci tun jiya da daddare yau kuwa ganin har 12 tayi bata samu abun da zata saka cikin bakin taba sai ta zarce da azumi.
yaron matar yayan ta yashigo da kwano a hannu babu ko murfi ya dangwara mata kwanon abincin a gaban ta, babu girmamawa sai zallar rashin tarbiyya, yajuya yafita.
tuwone tuwon datsa miyar bakar kuka da ko manja babu a cikin sa, tuwon ɗan haka agindin kwano tamkar ɗan yaye za'a baiwa abincin sabar kankantar sa.
kallon abincin tayi kawai ta girgiza kai,
batare da takuma kallon abincin ba ta mike ta ɗau mayafin ta tafita a gidan,
cikin unguwar tasu tashiga can ciki
gidan wasu masu kuɗi dake can cikin unguwar tasu tayi,
tayi sallama a gidan matan gidan suka amsa tashiga, bayan sun gaisa tace
"Dan Allah kan maganar ai kin nan nakuma dawowa ko Allah zaisa na samu, ko shara da wanke-wanke da girkin abinci ko wanki duk wan da na samu zanyi"..........!★
*Kuyi hakuri kwana biyu bana samun lokacin yin editing sai ku karanta da hakuri idan na samu lokaci zan yi editing cikin document*
Mommyn Twins ce
Mama mai awara tayi maganar cikin nuna jaddada rokon ta, har in zata samu ai kin tarika samun kwabon kashewa da kuma kuɗin motar da zata koma duba HAMDAH yau sati guda kenan take yayon zuwa gidajen masu kuɗin unguwar su,ko zata sami ai ki,
wannan gidan da tazo ma,sun mata alkawarin samin ai kinne tun sati ɗaya da ya wuce, shine yau ta kuma zuwa ko zata samu, ko wani irin aiki ne tana jin zata iya har in zata sami kuɗin mota.
Matan gidan suka ce mata Eh sun yi shawarwari zasu ɗauke ta ai ki,
amma aikin ba ai kin abinci bane. shara da wanke-wanke da kuma wankin kayan su da na kuma ƴaƴan su, dan suna da mai yi musu girkin,
tace ta Amin ce zata iya insha Allah,kuma yanzu zata fara in dai akwai wankin yanzu.
Nan aka fara fito mata da lodin kayan wanki ɗaki-ɗaki,
ɗakunan gidan kaf sai da suka fito da kayan wanki suka jibgeshi tsakar gida,
sannan sukace tafara da wanke-wanke da shara kafin tayi wanki, nan Mama mai awara ta tuɓe hijabin ta ta sha ɗan mara da shi,
cikin kankanin lokaci tayi wanke-wanke kana taɗa tsintsiya tasoma shara,
tana gamawa sannan ta dukufa wanki mai uban yawa.
Wankin take tun tanayi da karfin ta har karfinta yafara kare wa,
ga azumin da babu suhur yunwan tun jiya da rana, ta kwana da shi takuma wuni da shi.
haka dai tayi wankin cikin mawuyacin hali.
tana gamawa ta zauna zaman jiran bushewar sa, tana nan har wankin ya bushe, ta ninke tabi ɗaki-ɗaki tana kaiwa, kamar yan da taga an fito da kayan cikin ɗakunan gidan.
Wani ɗakin idan ta kai suka duba kayan su gaya mata maganar banza, suke kayan ma bai fita ba.
ɗakin ƴanmatan gidan kam da takai wata yarin ya budurwa da ta karɓi kayan tana dubawa watsa mata kayan tayi a jikin ta,
cikin gatsali da tsantsar rashin tarbiyya da sangarci irin na ƴaƴan wasu masu kuɗi tace
"Wannan kayan ne kin wanke? ke wata irin mata ce wata irin dakikiyar mata ce ke wannan an wanke wannan kawai tsomasa a ruwa kikayi kika ɓata min kaya kawai".
kai kawai Mama mai awara ta jinjina,
cikin takai cin jin yan da yarin ya karama wacce ta haife ta tajuya wai ita take zaginta,
kallon gefen ta tayi mahaiyar ƴar na zaune a gefen su amma tayi kamar bata nan.
"Allah shi kyauta".
Mama mai awara ta faɗa a fili tare da juyawa tabar gurin.
itako budurwar fuska ta yamutsa tare da jan dogon tsaki, tace
"Kayan a kasa zaki barmin kenan kiyi tafiyar ki?".
tayi maganar cikin rashin sanin darajar na gaba.
Mama mai awara batace komai ba ta juyo takwashi kayan ta mika mata, fizge kayan tayi a hannunta tajuya tawuce ciki...
Bayan tayi shara da wanke-wanken yamma daf magriba ta takoma gida,
kafin ta tafi kuwa sai da sukayi mata jawabin gobe da sassafe zatazo,
ko da ta koma gida da tasha ruwa tuwon da matar ƴaƴan ta ta ɗan sakura mata na tun da rana wan da ya wuni abuɗe ma shi tayi buɗa baki da shi.
washegari da sassafen tazo ta gidan masu kuɗin bayan tayi wanke-wanken da shara aka kuma jibge mata wanki har da na jiya da ta wanke aciki tayishi......
tun daga ranar kullum Mama mai awara na kan hanyar zuwa yin wannan aikin,
cikin kaskanci da wulakanci da rashin daraja ɗan adam, wannan gida basa da daraja babba duk da ta girme musu duka amma basa daraja ta ko dun girman ta, suna yi mata kallon kaskantacciya kullum cikin wulakancin su take a haka dai har tayi wata ɗaya a karkashin su,
ranar da tacika wata guda tana yi musu aiki