Showing 1 words to 3000 words out of 76752 words

Chapter 1 - ZAFIN RANA COMPLETE HAUSA NOVEL

ayusher   

26 Aug 2024

8558

*ZAFIN RANA*

*_Shafi na Daya_*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*



*Masarautar Biram*



Ta ko ina ya rurufe kofa da window din dake cikin dakin, kallan juna sukai hankalinsa a tashe yace "Yaya!"

Kusa dashi ya zauna tare da rike hannunsa, wanda ya kira da yaya ya kalleshi cikin matsanancin jin jiki, hannunsa ya matse yace "Abdul-Salam!"

Da sauri yace "yaya."

Yaya ya kalleshi yana magana dakyar, yace "Abdul-Salam ga Amanar Junaid nan, ka kula dashi, in da dama ka fitar dashi daga masarautar nan, dan sam
Bana sanshi da mulki."

Cikin mamaki Abdulsalam ya kalli yayansa yace "yaya? Wani irin magana kakeyi bayan Junaid shi kadai ne dan da ya cancanci ya gajeka? Shikadai ne danka namiji, babu wanda ya dace da mulki sai shi."

Kai ya kadamai da sauri yana magana a hankali yace "A'a kai kayi mulkin, dan Allah ka barshi yayi rayuwar da ya dace dashi, kasanshi yaro ne mai ilimi, da san kwanciyar hankali, banaso ya taso cikin wannan yanayin wanda rayuwarsa ma take cikin garari."

AbdulSalam yace "yaya to ya kakeso ayi?"

Idanunsa ne suka shiga lumshewa, rigarsa ya riko yace "ka kula da Junaid dan Allah Abdul-Salam, na barma mulkin nidai ka barshi da rayuwa............."

Yanda yanayin jikinsa ke rawa ne ya hanashi karasa magana, zuciyarsa ce ta daina bugawa, numfashinsa ya tsaya, wanda hakan ya nuna rai yayi halinsa.

Hankali a tashe AbdulSalam ya dinga jijiga yayan nasa wato Sarki Zubair.

Fitowa yai jikinsa duk a mace, bayi da kuyangun dake tsaye a gun ne suka kalleshi.

Matar da ta taho tana kokarin shiga gun mai gidan nata ne tai turus tana kallan sa.

Idanu ya runtse sannan ya girgiza mata kai alamar babu.

Nan bayi suka fara kukan rashin Sarki da akai, ja da baya da baya ta fara yi, tana girgiza kai, da sauri ta matso tana neman shiga gun mijin nata? Matsa mata yai ta shiga, a kwance ta ganshi wanda hankalinta ya tashi da sauri ta sa hannu ta jijigashi, sai dai ganin jikinsa ya koma ya kwanta yasata ta saki wani irin kuka.

Kan kace me zance ya shiga lungu da sako na cikin masarautar, harma cikin gari inda mutane suke, ta ko ina tururuwa ake ana zuwa ana mika gaisuwa, gidan ya cika makil.

Washe gari....
Matansa da yaransa wadanda duk mata ne kowa ya hallara, yaro ne dan shekara 8 zaune kusa da mahaifiyarsa, kuwa kallan tausayi suke mai, wasu kuwa kallan soko suke masa, shikam yana makale da mahaifiyarsa har ganin ana neman yima mai martaba sallah yasa ta kalleshi tace "Junaid aje za'ayima Mai Martaba sallah."

Kuyangar dake kula dashi ta kalla tace "kuje."

Nan ya mike yai waje.

Yana fita wata tace "yanzu ya za'ai da Junaid?"

Sarauniya wacce itace mahaifiyarsa ta kalleta, yanda ta mata kallan ne yasa taja bakinta tai shiru.

Anyima mai martaba sallah kowa sai gaisuwa yake yima Abdulsalam, a wannan lokaci babu wanda yabi takan Junaid, duk mutanen da ke zuwa gunsa da kula dashi yau suna can gun Abdulsalam ba wanda yabi ta kansa.

Shikam da yake yaro ne, mikewa yai yace "zan koma gun Mamana."

Bawan daya rako shi gun ya bude mai hanya suka juya.

Yana zuwa bakin kofar bangaren Mahaifiyar tasa, yaji ana kwalla mai kira "Yarima Yarima."

Waigawa yai ya kalli mai maganar, da sauri ya karaso inda yake cikin gudu, yana haki, sai daya dan huta sannan yace "Hakimi AbdulSalam yana nemanka."

Juyawa yai suka koma, mutumin daya gani cikin mutane sosai dazu yayi mamakin ganinshi a cikin bangaren Sarki mahaifinsa shi kadai a wannan lokacin.


Yana shiga Abdulsalam ya kalleshi, Junaid wanda ya shiga kif kif da ido kawai yasa kuka, da sauri ya matso ya rungumeshi, Junaid ya shiga yin kuka yana cewa "Kawu wai Baffana ya rasu?shine wanda akama Sallah dazu?"

Abdulsalam ya rungumeshi cikin tausayawa yace "Junaid."

Kuka sosai Junaid yakeyi kafin ya tsagaita.

Abdulsalam ne ya kalleshi yace "yanzu zamuje a kaishi makwancinsa, nazo ne da sauri dan na sanar ma wani abu."

Junaid sam bai fahimta ba sai dai kallansa kawai da yakeyi.

Abdulsalam yace "yanzu zaka bi wannan, ya fada yana nuna saurayin daya kirashi dazu, tare zamu tafi dakai sai dai kai zakabi wannan zakuje wani guri, wanda ba dadewa zakuyi ba zanzo na daukeka."

Kai ya jinjina alamar to, sannan yace "kar kuma ka fadawa Mamanka, kadai ce mata zakaje inda za'akai Mai martaba."

Kallansa yai ba tare da wani zargi ba ya daga kai, nan ya juya ya fita, wannan saurayin yabi bayansa.


Shiru Abdulsalam yai, indai yanaso yai yanda Sarki yace to lalai dole ne ya fita da yaran nan ana cikin hargitsin nan, dan inhar ya bari sai an lafa to ko za'a mutu mahaifiyarsa bazata taba yarda da wannan lamari ba, shiyasa tun a daren jiya shi da yaran nan wanda yake jarumi ne shi sannan mutumin ne wanda ya yarda dashi, suka fita cikin dare dan neman inda ya dace yaran ya zauna, ya debi kuyangu ya kaisu, da sassafe da bayin da zasu kula dashi.


Junaid ya je gun Mahaifiyarsa, sai dai yawan mutanen dake shigowa yi mata gaisuwa ya hanashi karasawa kusa da ita, sai dai hangoshi datai daga nesa, saurayin ne ya kalleshi yace "Yarima lokaci yayi."

Junaid ya kalleshi yace "muje in na dawo na fada mata."

Nan ya juya ya fita, sam yayinsa ma da suke mata ba wanda ya damu dashi, kowa najin haushin shi kadaine namiji dole ne kuma ya gaji mai Martaba.


Sun fito suka shiga cikin jerin masu kai Mai Martaba gidansa na gaskiya.

Ana kokarin shiga inda za'a birneshi, saurayin yaja hannu Junaid suka bar gun, Junaid ne ya kalleshi sannan ya kwace hannunsa suka fara tafiya yana cemai "ina zamu?"

"Ba dadewa zamuyi ba can kauyen ne, yarima ai kanasan hawa doki ko?"

Da sauri Junaid yace "eh sosai ma."

Saurayin yai murmushi, dan wani kauye suka nufa, wani gida ya shiga sai gashi ya fito da doki.

Junaid cikin murna ya kalleshi yace "aikuwa da gaske kake."

Nan ya hau da Junaid gaba shi kuma ya hau suka harba doki sukai gaba.......

Sundanyi tafiya mai nisa kafin su isa wani kauye, Junaid cikin sha'awa yake kallan mutanen kauyen, ta ko ina kowa hada hadar sa yakeyi, kallan saurayin yai yace "sai yau na taba shigowa cikin mutane haka, zanci wancan.."
Ya fada yana nuna mai wani abu da suke saidawa, kamar mazarkwaila.

Saurayin yace "Yarima kayi hakuri in munje zansa a zo a duba maka mai kyau ba irin wannan ba."

Junaid yai dariya yace "ina binka bashi kenan."

Sauka sukai akan dokin suka karasa dan karshen kauyen kadan.

Gini ne wanda kana ganinshi kaga gini na sarauta, mamaki ya kama Junaid ya kalleshi yace "gidan waye?"

Saurayin yace "gidan Sarki Zubair ne."

"Babana?"
Ya fada cikin mamaki, saurayin ya daga kai, yana murmushi dan shi kansa bai taba ma sanin kauyen nan ba sai a daren jiya da sukazo da Abdulsalam, wanda Sarki zubair ya sanar dashi inda kauyen yake da gidan dayasa aka ginama Junaid tun sanda ciwo ya fara kamashi, wato shekara biyu da suka gabata.


Masarautar Biram.....
Nasan duk wanda yaji sunan Biram zai fara tunanin ina ne? Sai dai nasan wasu daga cikin mu su san sunan.

Biram shine asalin sunan garin Hadejia wanda mutane suka fi sani a wannan lokaci, gari ne wanda aka gima shi tun asalin hausa bakwai da banza bawai, gari ne wanda ya kafu tun Alif Dubu daya da dari takwas da takwas (1808)

Yana daga cikin kasashen da Bayajidda ya kafa, gari ne na hausa da fulani, gari ne wanda suka taso suna shuke shuke, kiwo da sauransu.





*Ayusher Muhd*



*ZAFIN RANA*

Haske Writers Association 💡

Na Ayusher Muhd🏹


Shafi na biyu



Junaid suna shiga ya shiga kallan gida cikin tsananin jin dadi, dan abin ya birgeshi, yaje zai shiga cikin falo ne ya hango kuyangun gidansu.

Mamaki ne ya kamsashi ya nufo gun yana cewa "Hari kece?"

Juyowa tai da sauri jin muryarsa, ta nufo inda yake tace "Yarima!"

Kallanta yai yace "me kike anan?"

"Da sassafe aka kawomu nan akace mu zauna zaka zo."
Ba tare da yai tunanin komai ba yace " ke dawa?"

Nan ta shiga kiran ragowar kunyangun, yana ta dariya, cikin gidan ya shiga yana tattaba abubuwa, mamaki sosai yakeyi ta yanda duk wani abu dayake fadawa Mahaifinsa yanaso akwaishi a wannan gidan, kallan saurayin nan yace "kai ya sunanka?"

"Azi sunana Yarima."

Junaid ya kalleshi yace "Ali ko Azi?"

Yace "Azi."

Dan dariya yai sannan yace " kace zaka sa a siyomin wannan abin?"

Azi yace "eh yarima amma sai ka zauna anan ka kwana baka kuka ba."

Ba tare da damuwa ba yace "to, amma in mun tashi zamu gun Mamana ko?"

Azi yace "in munyi bacci sau haka, ya fada yana nuna yatsun hannunsa.

Junaid ya kalleshi yace " to."

***********

A can masarautar Biram kuwa anata shige da fice wanda ya hana Gimbiya Azeema samun nutsuwa harya fahimci dan nata baya nan, har sai zuwa dare bayan anyi sallar magrib ta kalli kuyangar dake kula da ita tace "Kicema Yarima yazo yaci abinci anan."

Da sauri tace to, Gimbiya Azeema ta zubama tiren abincin ido, bata taba kawo Sarki Zubair zai rigata rasuwa ba, yanzu ya zatai da rayuwarta? Tun tana yar mitsitsiya aka aurar da ita gareshi, ta taso shine mahaifinta, mijinta kuma abokin shawararta yanzu ya zatai?


Kanta ta kwantar a jikin gado, zuciyarta duk ba dadi, Duk yawan mata da kwarkwarorin dayake dashi baya damunta sam, saboda a koda yaushe yana nuna musu matsayinta.

Dole ne ta mike tsaye ta kula da kanta kodan rayuwar Junaid, bazata taba yarda ace Abdulsalam shine yahau mulki ba alhalin asalin sarauta ta Junaid ce, dole ta jajjirce taga wannan al'amari ya faru.



Shigowar da Kuyangar tayi ne yasa ta kalli kofa da sauri tana jiran ganin Junaid.

Ganin har kuyangar ta karaso bata ganshi ba yasa ta kalleta, kuyangar tace "Gimbiya baya bangarensa."

Batai mamaki ba tace "ki duba bangaren su Hanna, da can babban gida."

Da sauri tace to, juyawa ta ta fita, Gimbiya ta mike daga kan sallayar ta zauna a bakin makeken gadonta wanda aka mai ado.

Da gudu wannan kuyangar ta shigo, ran Azeena ya baci ta mata wani kallo wanda ya sata saurin tsayuwa daidai, Barira ta kalleta sannan ta maida kanta kasa tace "Gimbiya ba'aga Junaid ba, kowa na tambaya sai yace shi tun rana a gunki ba wanda ya ganshi.

Mikewa tai da sauri tace "ina ya shiga?"
Muje in duba da kaina, nan suka fito ta shiga bi ta ko ina tana nemansa, tun abin bata maidashi na tashin hankali ba, sai da duk inda taje nemanshi suma su fito dan tayata nema, taga an hadu dayawa sai dai ba wanda ya ganshi.

Kanta ne ya fara juyawa, ta ko ina a cikin daren nan nemansa akeyi, ga gida dama a cike saboda yan zuwa gaisuwa.

Kowa da abinda yake sakawa a ransu, dayawa daga cikinsu kuka sukeyi sai dai kana gani kasan wannan kukan na gulma ne, Gimbiya Azeema kam jitai jiri na debanta wanda ya hanata tsayuwa, kallan Babban yarta tai wacce take kusa da ita cikin rada tace mata rikeni mu wuce.

Riketa ta tai ta mike sosai, tare da yin murmushi tace "kuje ku kwanta ba wani abun, da alama yaje wani gun ne bacci ya kamashi."

Tana fadan haka suka juya a tare, kallan yarta tai wasu Sameera tace "Sameera ina Hakimi yake?"

Sameera a hankali tace "kinsan dare ne ba kila ya kwanta."

Idanunta runtse sannan suka cigaba da tafiya, tana shiga dakinta ta zube a kasa saboda gaba daya kafarta ta gama saki, da sauri Sameera tace duk kuyangun su bar dakin, ta kalli Gimbiya tace "Umma kina tunanin wani abin ya sameshi ne?"

Gimbiya Azeema wacce gaba daya ta gama rudewa tace "Sameera mutane nawa ne suke san mulkin nan?"

Sameera tace "kannan Abba su biyar maza, sanan babban yaran Hakimi AbdulSalam Su shida kenan."

"Kina tunanin zasu bari Junaid ya hau mulki yana karami dashi? Bayan su kansu mutum shidan nan fada suke a junansu?"

Hankalin Sameera ya tashi tace "Umma kina nufin sun mai wani abu kenan?"

Gimbiya ta kalleta idanunta sun ciciko gaba daya kirjinta ne taji ya mata nauyi, rike hannun Sameera tai tace "Sameera munyi kuskure da muka nunawa mutane Junaid baya cikin masarautar nan."

Sameera ta kalleta a tsorace, tacigaba "yanzu duk wanda ma bai sani ba ya sani, kinga wanda yake neman cutar dashi zai iya bi ya cutar dashi ba tare da ansani ba."

Gaba daya hankalin Sameera ya tashi, tace "ya zamuyi kenan?Umma junaid yaro ne, taya dan rashin imani zasu nemi cutar dashi? Nawa yaran yake? Yaran da baisan me ake ciki a duniya ba?"

Azeema tace "shine dalili da zaisa su cutar dashi, saboda baisan me ake ciki a duniya ba, shine zaisa su halaka shi ba tare da wata matsala ba, kina tunani zasu jira ya girma? Bayn sun san in ya girma zai kwaci kansa?"


Sai a yanzu itama wadannan tunani suke zuwa mata, jikinta ne ya hau rawa, tace "meke damuna Sameera? Gaba daya banyi wadannan tunanin ba sai yanzu, Sameera ya zanyi in wani abin ya samu Junaid? Na shiga uku......"

Hankalin Sameera yayi tsananin tashi, ta kalleta tace "Umma yanzu ya zamuyi?"

Gimbiya tai shiru, ganin wannan ragwantar ba inda zata kaita ne yasa ta mike tsaye da sauri, tace "ina mai gidanki?"

Tace "Mahmud yana gida."

"In har aka kai gobe da rana ba'aga Junaid ba, ki aika a kai masa wasika, tunda shi ba lalai mutane su fuskanci halin da yake ciki ba, ya nemo Junaid ta ko ina ya nemo Junaid, mu kuma idan aka tashi da safe muce ya dawo yana daki, kar mu bari a fahimci wani abun."

Cikin mamaki ta kalleta tace "yana daki kamar ya?"

"Idan mutane sun ji yana daki maganar zata lafa, sai muyi dabara duk wani abu da zai nuna musu bayanan mu kauceshi, in yaso shi kuma Mahmud kinga yana can yana nemanshi, nan kuma sai musa Barira ta kara duduba ciki a hankali."

Samira ta jinjina kai tare da cewa "nagane Umma."

Gimbiya Azeema ta zauna a bakin gado tace "malaman da sukazo kwanaki, akan suna yin karatu, kinsansu?"

Kai ta girgiza alamar a'a sannan tace "karatu kamar ya?"

Shikenan, zan sa a bincika, kema cikin dabara ki dinga duba cikin Masarautar tamu."

Da sauri tace "to Umma."

"Dole na nemi ganin Abdulsalam, sai dai bansan yanda zanyi ba."

Sameera tace "me zakiyi?"

Kallanta tai kamar zatai magana sai kuma tace "karki damu."

Jekinki kwanta, kar yaranki su nemeki.

Juyawa tai cikin sanyin jiki ta fita.

Gimbiya sai zagaye cikin dakin takeyi gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya, gashi bata san me akeyi ba inza'ai adduo'i dan karatun sallah Sarki ya koya mata shima kadan, saboda aikacin addini baiyi zurfi ba, an iya karatu kadan sai dai ba'a san yanda za'ai addu'oi sosai ba, sai yanzu da malamai ke ta kokari suna yadawa.


***********

Kuka yake sosai cikin daki saboda ya saba duk sanda zai kwanta sai Umma tazo ta dan mai karatu sannan yake bacci.

Jin kukan dake fitowa daga dakin ne yasa Hari tai saurin shiga ciki, yana zaune ya takure guri daya.

Hasken fitilar kwai dake cikin dakin ta kara, sannan ta matso tace "Yarima! Lafiya?"

Da sauri ya kalleta yace "Hari ki kaini gun Umma banasan nan."

Ta kalleshi cikin tausayawa tace "Yarima nima bansan ina bane, rufemu akai a buhu aka kawomu bansan taya mukazo ba wlh."

Yace "kiramin Azi."

Kallansa tai cikin tausayawa tace "Yarima kayi hakuri amma banaji zakaga Umma yanzu."

Da sauri ya kalleta yace "kamar ya kenan?"

Idanunta ne suka ciciko tace "duba da yawan abinci da duk wani abin bukata da aka kawo aka ajiye anan na tabbatar bazaka koma yanzu ba."

"To me zanyi anan?"
Ya fada cikin damuwa, kallansa tai tace "dan haka ka kwantar da hankalinka ka kwanta kai bacci, kai sauri ka ci abinci kai bacci ka girma kila lokacin za'a barka."

Idanunsa ne suka dan firfito, bakinsa ne ya fara rawa kafin ya fara kuka......

Haka dai ya kukansa harya gaji yai bacci.


********

A cikin masarautar Biram kuwa da safe kowa sai shigowa yake dan yin gulma, sai dai duk wanda yazo zai ga takalminsa a inda ya saba ajiyewa sannan ga rigarsa nan ta alkyabba a gefen Gimbiya.

Tana nan zaune, duk wanda ya shigo sai tace "ai kasa barci yai jiya ya tafi dakin Sarki acan ya kwana, baiyi bacci sosai ba shiyasa yanzu ya kwanta.

Wasu sun yarda wasu kuwa jinta kawai sukeyi amma bacci ace tun dazu har yanzu? Kuma baccin yaro ma?



***********
AYUSHER
************



*ZAFIN RANA*

*Haske Writers Association*
Pg 3

Gaba daya yau cir haka Gimbiya ta kwana tana sake sake a ranta, ana sallar asuba ne ta kira Barira tace mata ta je jikin massalaci daga gefe kafin Hakimi ya shiga turakarsa tace "masa a idon na ne."
Barira bata tambayeta ma'anar hakan ba ta fita.

Yana fitowa Barira ta sanar da bawan dake kula da Hakimi shi kuma ya sanar mai.

AbdulSalam yanajin haka ya kalli bawan nasa yace "ku je ciki ina zuwa."
Bai jira komai ba yai gaba, tafiya yo mai dan nisa har ya isa wani dan kango, wanda an fara gini amma ba'a karasa ba kuma da alama ginin ya dade a kangon.

Yana shiga ya taddda ta a tsaye, kallanta yai yace "me kike anan? Ke da zaki shiga takaba?"

Kallansa tai cikin tashin hankali tace "na sani, ina Junaid?"

"Junaid? Baya gunki?"

Wani banzan murmushi tai sannan tace "baya guna? Ka dauka bazansan kai ka daukeshi ba?"

"Azeema me kike san cewa?"

Ranta a bace tace " AbdulSalam ina Junaid, kafi kowa sanina Allah in wani abu ya samu dana wlh kasan abinda zai biyo baya."

Ya kalleta yace " yanzu duk duniya ki rasa wanda zaki zarga da yima Junaid illa sai ni?"
Kallansa tai ta kuramai ido tana san gano ko karya yake mata, saboda tasan AbdulSalam sosai, dan kusan tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login