Showing 21001 words to 24000 words out of 48162 words

Chapter 8 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah

10 Jul 2024

3358

ina fatan kin ja?a duk abunda ya dace*
Am gaskiya babu samu ,sai kuma tayi shuru ganin wani abu mai kama da Document yana ta faman bude wa akan screen din laptop din gabanta
Cak ta tsayar da idanun ta akan rubutun
*GZJ* da ma'anar sa
*Gidan zubda jini*
Abayyane ta karanta
Good taji ya fa?a daga cikin wayar ,''saura ?ayar kalmar ,shuru tayi tana zazzare idanu kamar tana gaban sa ?irjinsa sai bugawa yake
Ina jinki ya sake fa?a ras ras ras gabanta ya fa?i zuciyar ta kamar taza faso ?irjinta
Muryar taji kamar ta wani makusancinta ?it taji ya kashe wayar..............



Kuyi ha?uri akoy typing error a ciki na makara banyi editing ba ????




Ajiye wayar tayi tana ?ara Maimaita ma'anar kalmar, Mamaki take yaushe ta samo ma'anar
Ita dai tasan a ranar da ta ajiye tap din bata sami wani information akai ba, kuma yanzu ta gani Kamar ita ta ajiye
Hankalin ta maida ko zataga ne ta inda bayanan suka shigo ta
Wani rubutun tagani yana kan hanyar budewa, dan jinkirta wa tayi dan ganin mizai biyo bayan wancan ma'anar.
Can taga ya ?ude saidai layin Farko na rubutun baya ganuwa sai hazo_hazo take gani , ga Rubutu amma haske ya hana ta gane haruffan da akayi anfani da su wajan Rubutun
Layi na biyu ta duba *K*: *Kabiru* ta gani
Mi kenan idan tinanin ta ya bata daidai to ma'anar *Mk* ne anan
*K* tana nufin Kabir to *M* din fah , har yanzu mamaki take , ta yadda ta yadda akayi ta sami wa'yannan jawaban


A ?ayan ?angaren tunda ya katse kiran wayar yake nazarin bayanan ta, to Miyasa ta rufe wajan fa?a masa bayanan , ko taji wani abu ne na daban a tattare da shi
A'a kawai yanayi ne, ya bawa kansa amsa
Dama a tsaye yake ya jingina da Motar sa , ciki ya koma ya data ya bar wajan zuciyarsa duk ba ?adi

Agogon dake manne a falon ta kalla, taga ?arfe sha biyu da yan mintuna tasan duk inda yake yanzu yana hanyar sa ta dawowa gida
Tashi tayi tashi daki dan yin wanka
Shigar ta toilet ba jimawa taji shigowar motar sa gidan, a falo ya yada zango da ledoji a Hannunsa
Kujerar data tashi anan ya zauna, hannu yakai ya ?auki wayar ta da ta bari da tap dinta a kan hannun kujera
Jujjuya yayi yana murmushi yace na yau kawai zaki iya magana da kowa naki, wannan kyauta ce daga Muhammad.


Gidan Dady
Momy ce zaune kusa da Hajiya tana gaishe da kawu, ya Amsawa tare yana tambayar ta sauran mutanen Gidan , tace lafiya alhamdulillah
Inna tana bacci, jiya mura ta hanata ta kwonta shine yanzu take ramuwar bacci
Ita kuma Ru?ayya tana makaranta yau suna da exam ne

Kawu yace'' masha Allah , Allah ya bata Lafiya ya taimaka ya bada sa'a, ya wajan ita Maryama din , Momy tace '' ai ku zamu tambaya da ita kawu, Allah dai ya ka mana agaji cikin wannan lamari
Da Amine kowa ya amsa kafin kuwa yace'' gaskiya ne ai insha Allah komai yazo ?arshe , a yadda shi Almustapha yake mini bayani, nasan ya fa?a muku gobe zasu dawo ko??

Momy tace eh ai yanzu muka gama waya dashi yake cewa jiki yayi sau?i sosai,dan har yana tafiya amma da sanda, '' eh hakane ai shi so yayi su?an ?ara zama har ya ?ara samun ?arfin jiki kafin su dawo , ta shi Hussainin ne ya matsa akan su dawo gida
To alhamdulillah ganin ana samun Nasarori ta kowane ?angare yasa na ce kawai su dawo din

Sai anan Safwane yasan gobe su Dady zasu dawo yace '' Allah ya kaimu goben lafiya, anan kowa ya amsa da amine
Kawu yace'' nayi Magana da Abubakar anjima za'a kawo komai na anfani , sai ku duba idan da wani abinda Ba'a kawo ba sai kuyi Magana
To insha Allah kawu daya ke ma da sauran komai ai ba'ajima da kawowa ba yace '' to shikenan bar a na tafi akwai daurin auren da zan halarta bayan Sallar azahar cewar kawu da yake ?o?arin mi?e wa tsaye
Safwane yace to abaki tsara bar taka fah ko har gida za'a kai maka , '' ashe kasan sauran zancen, da ban zo gidan ba ai bansan kazo ba
To mini afuwa mai ran ?arfe insha Allah zaka ganni, kai dai ta tanadi man ?ulli da man shanu na tarbar ba?o
Kamar gaske cewar kawu da ya tashi yana ?ara babbar Rigar shi , sallama tayi wa su Hajiya da take ta kallon su tun ?azu , farin ciki ya cika mata rai , jin gudan ?anta ?ollin ?ol zai dawo cikin iyalansa,da har ta fidda rai
Bazata gaji da yiwa Dady da iyalansa godiya ba, da adu'ar gamawa da duniya lafiya
Tabbas Dady ya taimake su a rayuwa , da taimakon Allah da taimakon Dady ake juya dukiyar Marigayin mijinta har yanzu, ya ?auki ?anwarsa ya bawa ?anta aure,har bayan ta rasu bai bar kulawa dasu ba ,shi mutun ne nagari abin koyi
Allah ya albarkaci rayuwarsa data iyalansa baki ?aya
Tana wannan tunanin har kawu yabar gidan bata sani ba

?arfe biyar da rabi na marece ta iso ?ofar gidan, yau duk agajiye take
Dayake motar ta ta sami matsala sai direba ya Kaita makaranta da safe , yanzu kuma da aka tashe su sai bata kira direba ba ta shigo adaidai ta sahu ya kata har ?ofar gida, biyan sa tayi tana ?o?arin shiga gida

Wata mota mai rai da nunfashi tagani ta nufo ?ofar Gidan nasu daka tawa tayi da shiga dan ganin ko waye, dan ita atunanin ko Maryam dinta ce
Horne matu?in Motar yayi a bakin ?ofar gidan
Security ya le?o dan ganin ko waye har kusa da motar ya iso
Sauke glass din motar Matashin Saurayin yayi yana yiwa security bayani, kafin yayi masa nuni da dayan motar '' sannu da zuwa Hajiya ya fa?a yana komawa dan bu?e musu ?ofar

Ru?ayya data sume atsaye ganin wannan Halittar da ta gaji da tsaruwa ,sai masha Allah kawai take fa?a a cikin zuciyar ta ,bata ankara ba har motar ta shige cikin gidan


Daga ?afar ta tayi ya fara takawa kamar kazar da ?wai ya fashe mata a ciki ,gajiyar ta taji ya nunku, ganin farko da tayiwa gayan, ya tafi da duk wani kuzari nata
Bata ta?a jin hakan akan *Sadik* din taba


Ihun *Ihsan* ya dawo da ita cikin asalin tunanin ta
Oyoyooooooo tanti

?aukan ta tayi ta shiga juyi da ita a Farfajiya Gidan Suna dariya, '' ke Yarinya ta kun iya surprise keda wa kuka zo ?
Nu na mata wajan da Maman ta take tsaye yarinyar tayi

Tunda suka fito daga motar yake tsaye yana kallon ta , shida ya fito da niyyar ya sauke musu kaya sai ya ?uge da kallon Gimbiyar zuciyar sa a cewar sa , dan har yayi mata kyakkyawan masauki,ya kuma bata babban matsayi a cikin zuciyar sa.


Koda ta kalli wajan sai idanun su ya sar?e da juna , ko wannan su sai da zuciyar sa ta harba da ?arfi

Anty Ramatou da Iskancin su ya ishe ta tace '' Iskancin banza zaku mu shiga ciki ko na barku anan , cikin jin kunya yace '' Anty kawai kije abunki ai nima nasan hanya

Hararar wasa tayi masa tana gyara ri?on ?aramin ?anta *Nasir*
dake bacci tun suna hanya tace kadai bini a hankali dan wallahi sai na hanaka kasan zan iya
Cikin marairai cewa yace habawa Antyn mu, Matar Big Brother ai ke din ba ruwan ki Ni nasani ,ta ?a?a zaki hana Autan gidan ku abincin ruhin sa

?ar dariya tayi tana barin wajan dan tasan idan ta biyewa *Abdoul_Wahid* to zasu kwana anan , shine Auta a gidan su Mijinta

Iyayan su ri?a??un yan boko ne wanda suka ga ?arshen biro da takarda
Yanzu haka Papan su Ambassador n ?asar Nijar ne a ?asar Garmany , su biyu kadai garesu
*Abdul Rahman* wanda shine mijin Anty Ramatou sai kuma shi *Abdoul_wahid*
Ba Hausawa bane yan ?abilar Zarma ne dan ko Hausa bata gama zama a bakin su ba sai Zabarmanci


Falon ta shiga ba kowa duk sun shiga ?akunan su dan yin Sallah, sai yar aiki guda daya da take jera kayan abinci a ?asan carpet
Tun lokacin da Momy ta lura da Hajiya da Inna basa san cin abincin a daining, sai tace ana a jiye wa a carpet
Zama tayi a ?aya daga cikin kujerun falon da mismillah a bakin ta ,ta kwontar da Nasir a gefen ba.



Isowa tayi da Ihsan a hannun ta zata gota ta inda yake , '' dan Allah a mini afuwa idan har nayi laifi, amma ban cancanci shariya daga wajan Gimbiya taba ba
Cak ta tsayar da ?afafuwan ta, zuciyar ta tana bugawa da sauri sauri, batasan lokacin data ce '' sannu da zuwa fatan kunzo lafiya ya hanya ?
Amsata yayi cikin sauri
Bata bar wajan ba sai da ya gama fito da kayan daga mota ya fara shigar dasu cikin falo, sai a zuwan ?arshe suka shiga a tare


A daren Ranar haka suka yi ta firar yaushe gamo da yaya Safwane su duka a falo hada su Momy

Sunyi waya da Dady ne yake cema ta jibi idan Allah ya kaimu zasu dawo, to shine ta ro?i mijinta da yabar ta tazo gida taga isowar su Abban
Da dashi zasu zo sai ya sami kira daga sama ,za suyi tafiya da ministan ilimi a washe garin ranar, shine na hannun daman ministan

Da yake shi Abdoul_wahid anan Niamey yake zama a tare dasu ,

Mamma da Pappa ka?ai suke zaune a Garmany, saidai suna ziyartar su lokaci bayan lokaci
To sai yace su tafi da ?anansa,
da a jirgi zasu zo , sai aka sami matsalar hazo, shine yayi driving nasu har Zinder a mota

Kwana suka yi suna waya da Ru?ayya, dan tuntuni suka yi musayar number,kuma duk akan idanun Anty Ramatou, ba tare da sun san tana ankare dasu ba



Gidan Muhammad

Koda ta fito daga wanka shiryawa tayi cikin riga da zani na atanfa , feshe jikin ta tayi da turare kafin ta nufi falo


Ba yanan, sai ledojin daya shigo dasu kawai tagani ajiye
Kicthing ta nufa ta dauko plate din din da zata sauye musu abunda aya shigo dashi, cups din da zasu sha ruwa , frige ta bu?e ta ?auko da ruwa swan na babbar roba , kayan fruit ta ?an ?ebo musu a wani plate din na daban ta dawo falon

A zaune ta gansa da jalla biya a jikin sa , kenan ?akin sa ya huce daya shigo ta fa?a a ranta lokacin da take ?o?arin ajiye kayan dake hannun ta
Amsa yayi ya ajiye yana mata sannu kamar wacce tayi wani aikin a zo a gani
Kallon ta kawai yake yana yabawa da Halittar ubangiji, shi ke rabawa ya bawa wanda ya so , kuma a lokacin daya so, shikam ya kashe ya bashi, abun da ya da?e yana kauna da muradin Mallaka
Maryam ita ce mafarkin sa, burinsa kuma farin cikin sa dana ahalin sa baki daya .

Busa masa fuska tayi da iskan bakin ta mai sanyin kamshi , sai da ya lunshe ido, wani sanyin da?i yana ratsa shi , tace '' wannan kallon fah an sauya Ni ne ?
'' Eh ai ke kullum kamar sauya ki ake Sayyada ta

Shuru tayi bata ce komai ba , dan a irin wannan lokutan ne halin da suke ciki yake fa?o mata arai

Shi ya zuba musu abincin kuma ya ciyar da su
Kayan itatuwan suka ?an ta?a kafin ya tattare komai daga wajan, yana bata mamaki a lokuta dadama
Baya banban ce tsakanin aikin Namiji dana mace , ko wanne idan ta raya masa yi yake

Dawowa yayi yana hamdallah ga Ubangiji daya ni'im tar dasu, sukaci abincin da dubban mutane suke neman wanda bai kai yashi ba amma basu samu ba ,
Alhamdulillah alaa kulli halin ya sake fa?a lokacin da yake zama a kusa da ita .


Wayarta ya dauka ya mi?a mata yace ki kira su Dady kugaisa

Kallon shi tayi ta kalli wayar kafin tace '' ai koda na kira da layina baya fita , saidai idan da taka zan kira

'' To ki kira da tawan, wayar tana ?aki sai dai idan zaki ?auko

Tashi tayi ba tare da tace masa Komai ba ta nufi Dakin nasa

Kaf ta nemi wayar Amma bata gan taba

Dawowa tayi tace masa itafa bata ganta ba, yace '' kije ki tsaya acan nai'kira da layin ki, idan tayi ?ara sai kiga inda take

Ba musu ta koma tana jiran taji ta inda waya zata yi ?ara amma shuru har kusan minti biyu

Fitowa tayi tana yamutsa fuska ganin yana so ya raina mata Hankali

Karo suka yi da juna shi kuma zai shigo Dakin , kanta ya fa?a saman ?irjin sa

Lumshe Idanun ta tayi tana sha?ar ?amshin turaren sa daya gama zama ajikin sa

A kunne ya ra?a mata cewa ga wayar ya gani, sai da yaji ?ara a al'jihunsa ne ya tuna ashe anan ya saka ta

Cikin Mutuwar jiki ta janye jikin ta daga nasa
Wayar ya mi?a mata bayan yayi dailing number Dady

Ayau fira suka sha sosai har da Abba , nan Dady yake gaya mata gobe zasu dawo
tsabagen murna har batasan sanda ta rungume Muhammad ba tana ci gaba da fira da Abba yana bata labarin asibitin da suke da yadda ya tsaru

Ta rikita masa lissafi wa canja masa tinani sandiyyar rungumar data masa , ai baisan sanda ya amshe wayar ba ya katse kiran
yana sauke mata nunfashin da bata ta?a ji daga gare sa ba , sosai yaso koda zafi ne ya rage amma fur ta?i ta bashi hadin kai , haka ya hakura dan baya so yayi koda kissing nata ne batare da yardar taba


A haka ban gararorin guda biyu suka kwana kowan nan su da murnar su Dady zasu dawo gobe


Washe Gari

Tun safe ake shirye shiryen dawowar su Dady
Zuwa sha biyun rana an gama komai na taryan su

Da sunso su tafi su duka airport dan tarbar su, sai Dady yace babu bu?atar hakan, kawai su zauna a tura musu da mota guda ?aya ta isa, saboda gudun matsala


Bayan Sallah azahar yaya Safwane ya nufi Hanyar airport dan jirgin su ?arfe uku zai sabka
Bai wani jima da isa ba jirgin ya iso,
Ko da yaga Abba masha Allah kawai yake fa?a, duk da bai ganshi lokacin ciwon ba, Amma da gani kasan ya samu lafiya sosai, dan har ?ar ?iba yayi, kuma ya ?ara haske alamar hutu ya ratsa sa


Shiga motar suka yi Abba yana dan ?ogarawa da sandar sa wacce a asibitin aka bashi ita
Suna tafiya Abba da Safwane suna fira, dama can shi ?an gidan Abba ne ,

Dady kam yayi nisa cikin tunani da adu'ar Allah ya kaisu Gida lafiya, dan ya dade da sanin halin miyagun can,dama sanin sa'alin waye shugaban su ka?ai ya rage masa sai hakan yazo a anbku, Amma ko yanzu Alhamdulillah dan Muhammad ya basa tabbacin ya idasa ha?a masa komai, mataki kawai ya rage su ?auka
Yana ta tunanin har suka iso Gida.


Tun daga ?ofar Gida zaka shaida cewa ranar yau ta musamman ce, ko ina tsab an gyara gida masha Allah
A Farfajiya Gidan suka iske kaf Mutanen Gida , inna , Hajiya,Momy,Anty Ramatou da yaran ta, Ru?ayya, Abdul wahid da ?an aiki guda biyu


Kowa sai murnar ganin su Dady yake
Masha Allah kawai Momy take cewa
Falo suka isa aka Zazzau na, nan danan aka cike musu gaba da kalolin abincin da aka shirya saboda su
Momy ta gabatar musu da abinci
A cikin makayi guda ta zuba musu, tataccen lomun kayan itatuwan da Ramatou ta ha?a ta zuba musu a cups


Suna cikin cin abinci kawu da Abubakar suka yi sallama
Kai masha Allah _allh abun godiya gaskiya naji da?in ganin ka a haka
Allah ya ?ara lafiya mai anfani da ?orewa, kawu ya fa?a lokacin da suke zama akan kujera


Nan kowa na ?akin ya shiga gaida Abba da jiki, da adu'ar Allah ya kiyaye gaba
Dady yake amsawa cikin farin cikin dawowarsu cikin iyalansu

Hajiya baki har kunne ta kasa ?oye farin cikin ta sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma rai, sai da tayi mai isarta Ru?ayya tana taya ta, dan itama abun kuka baya mata ?adan
Abdoul wahid sai yaji kamar yaje ya rarrashe ta , duk sai yayi wani abun tausayi kamar zai yi kukan shima
Anty Ramatou tana kallon sa tana masa dariya ?asa ?asa





*Jaune cadre*


Yaya Muhammad dan Allah kayi sauri kaga fah har ?arfe uku da kusan rabi tayi wallahi na ?agu inga Abbana
Maryam dake zaune bisa hannun kujera ta fa?a tana kallon agogon wayar hannun ta
Kira tagani har guda biyu daga garesa,
Abun mamaki yau sam bataji fa?uwar gaban ganin kiransa ba


Bin bayan kiran tayi kuma tanada tabbacin kiran zai fita tunda da number sane,
?aran waya take ji kamar abayan ta, juyawa tayi dan ganin ko wani kiran ne daban ya shigo wayar yaya Muhammad, dan tun zaman ta anan ta ankara da wayar sa da ke ajiye a saman kujerar daya tashi
Tab-dijan number ta tagani tana yawo akan screen din wayar da sunan *Sayyada ta*
Fa?uwar gaban da batayi taba ?azu, sai da ta biya bashin ta a yanzu

Innalillahi wa inna ilaihi raji'une , dama yaya Muhammad ne yake sauya mata kamanni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login