Showing 18001 words to 21000 words out of 48162 words

Chapter 7 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah

10 Jul 2024

3359

sanye da manyan kaya riga ?ar ciki da gari ,harda hula
Shuru tayi tana ?arema photon kallo, yaushe Abba ya fara saka manyan kaya haka,itadai a iya saninta dashi baya saka manyan kaya sai ?anana
Haka kullum suke sha da Dady akan ya bar saka ?ananan kaya ,yanzu fa ya girma ,tunda har yayi wa ?a aure (yana nufi Anty Ramatou da take aure a Niamey)

Kallon kayan take ko zata tuna yaushe ta ta?a ganin sa da su, babu taba kanta amsa
Detail din photon ta duba dan ganin yaushe aka ?auke shi , 2ga november 2010

Dogon nazari tashiga yi,idan ta akan photon idan bata mantaba a 2010 tana aji hudu na primary ,kuma awannan shekarar Abba ya tafi ?arin karatu qasar France to yaushe ya dauki photon kenan .
?ara janyowa tayk dan ta kalleshi da kyau ta tantance ,ya akayi kuma anan yayi dan duhu ,sannan kamar taga wushirya abakin sa ,bayan itadai bata ganta abakin Abbn ta , yanayin wajan da akayi photon kadai ya isa ayar tambaya,koma dai minene zata ci gaba da bincike,dole tasan koshi waye ,tariga da tasan misaya ya shigo rayuwarsu ,dan ya idasa aikin da uwayan gidan sa suka fara

Wayarta fara goda alamar batery
Yayi qasa,cireta tayi daga jikin computar tana juyata a hannun
yanzu mi ya kamata nayi ,ta ina zan fara shi wancan dan mulkin yace zai yi 2week a tafiyar da yayi , kuma kafin ya dawo in nemo ma'anar *Mk* da *GZJ*
Gashi yanzu wannan al'amarin ya Kunno mata kai ,wanda shi yama fi tada mata da hankali
Ta ?a?a zata zauna gida daya da mutumin dayake farawtar rayuwarta da ta iyayen ta ,gaskiya abun da kamar wuya

Bubbuga ?ofar da akeyi shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin data lula
Ki bu?e ?ofar mana Maryam,kina jina ''ya fa?i yana ?ara buga ?ofar a karo na biyu

Duba agogon wayar tayi taga ?arfe ukun dare har da rabi ya kusa ,zaro ido tayi waje tana mamakin yadda dare yaja har haka bata saniba,
Takawa tayi ta isa bakin ?ofar,da kamar baza ta bu?e ba sai kuma tayi shahadar bu?ewa
Shiga yayi tsakiyar dakin ,ita kuma tana a bakin kofa a tsaye ,ganin computer a bakin gado yasa ya juya da sauri yana kallon ta yace''wai badai baki kwonta ba haryanzu,! karfe nawa kuwa ??
Inda_inda ta fara tana ?oye wayar tashi a bayan hannun ta ,dan batasan ya amsa yanzu har sai ta gama daukan abunda take bu?ata
?arasawa yayi wajan computer Tata ya tsaya,da gudu tazo ta rufe dan batasan yaga ta copie masa komai na wayar satda tayi

?ar dariya yayi yace'' to nida ban ma iyaba ,mine na boyewa nida ban iya computer ba
Bani wayana, kuma dan Allah kibari ki kwonta ,koma miye kwa yi shi gobe
Ni nayi tunanin tun ?azu kin kwonta ,dan ni najima dayin bacci yanzu ma juyawa nazo yi naga bakwa nan sai natu dama baki kwonta tare dani ba, yau ?ar rigima ce ya fa?i yana kwonta wa a gadon
Daukan computer tayi ta kashe ta maida wajan ajiyar ta ,ta shiga toilet ta ?auro al'wala, Sallar nafila tashiga yi ,har kusan asuba ,ta yi wuturi sannan ta zauna tana adu'ar Allah ya shiga tsakanin ta da miyagun nan ya musu maganinsu ,a haka har aka kira sallar asuba
Juyawa tayi ta kalli inda yake kwonce sai taga ya motsa ,tashi yayi ya shirya ya fice masallaci ,ita kuma ta maida sallar asuba kafin ta haye gado, dan wani irin bacci take ji,bata jima da kwontawa ba bacci mai nauyi yayi gaba da ita

Tun da ya dawo daga masallaci ya sata agaba yake kallon ta ,komai nata yayi masa , kwazo ta,jarumtar ta ,da kuma jajircewar ta suna matukar birgeshi

Masha Allah tanada ilimi ya fa?a a bayyane
Komai datayi a dakin yana kallon ta ,tun daga shigowar ta dakin da binciken da tayi masa a waya ,har copie datayi na komai na wayar sa yana sane ,kuma shi ya bata damar yin hakan ,daga kai yayi ya kalli wata ?ar ?aramar Camera daya hada a jikin kan gadon ta ,yayi murmushi yace kina ?o?ari *Maryama* na tabbas zakiyi nasara a rayuwa ,naga kanki yadau caji
Zan sawwa?a maki neman ma'anar kalmomin,kamar yadda kika ce dama awaje kika ji kuma awajena zaki samu ma'anar
To zaki samu insha Allah

A bayyane yake maganar sa,da murmushin daya kasa barin fuskarsa ya je kusa da kanta yayi kissing nata akan goshinta ya furta ''kinada kyau *yan'matan Muhammad*
Bata ma san yana yi ba haka ya gaji da surutu sa ya yi gaba , har zai fita kuma ya dawo da baya ya isa wajan dayaga ta maida laptop din ,ya fito da ita
Budewa yayi ya fara sarrafata kamar yana wasan yara

Nida kaina MAman Abdallah sai dana yi mamakin yadda yake yawo da hannun sa akan computar

Mamaki bai ?are ba sai da naga yayi nisa cikin rubuta wasu jawa bai, dayake da sauri yake rubutun kafin na karanta layin farko tuni har ya gama ya rufe computer ya mai da ita mahallin ta ,
Kamar ba'a ta?a ba
Nace tofah muje da sauran kallo kenan , dan yanzu ma aka fara

Bayan kwana hu?u rayuwa dai suke yi ba wuya ba da?i Maryam bata kuma bin takan komai ba,dan tun ranar data kwana a zaunan nan take fama da zazzabi kuma shidai wanda take tinanin makashinta ne shiyake jinyar ta
Haka zatayi ta masa shago?a ,shiko yana biye mata ,a cewar ta koda kashetan zai yi sha?uwar da take tsakanin su zai sa yayi mata sassauci
Al hali bata sani ba, daga ita harshi kowanan su yana famar kokawwa da zuciyarsa akan soyayyar junan su ne

Shikam gogan ya da?e da sanin yana santa tun shekaru biyar da suka wuce ''Ita kam tanajin yanayi da kuma shau?i yana kamata a wasu lokutan, musamman cikin kwanaki hudun nan da batada lafiya ,amma daga ta tuna cewa yana da ala'qa da wayan'da suka kashe mata kaka,sace mata kawun ta da kuma sanadiyyar accident din da mahaifinta yayi,sai taji duk duniya babu mai munin halin irinsa

Rana ta shida

Yau sosai ta tashi da ?arfi a jikin ta ,ta warware sosai dan har abun karin safe ta ha?a musu
Cikin nishadi ya fita daga gidan kusan ?arfe goma
Bayan ta tattare komai takai kicthing ta wanke ta maida komai wajan da ake ajiyeshi sai ta koma falo ta zauna ,dama kafin ya fita yace kar ta ?ora komai da rana ,zai biyo musu da wani abun,ko ?azun ma da tayi dan yana bacci ta fara aikin sai dayaji kanshi ya cika masa hanci ,yana zuwa ya iske har ta kusa gama ha?awa ,amma sai da yayi mata ra'kin miyasa zata fara aiki bayan batada lafiya
Tana zaune a falon tana aikin tunani ta zabura ta mi?e kamar an nitsineta sauri_sauri gudu_gudu da ?arasa dakin ta,tunawa tayi da aikin data fara kafin ta ?onta jinya
Laptop dita ta dauko ta jona a caji
har zata gusa sai kuma taga idan tace ta barta har ta dauki caji ,ta ?ata lokaci kawai sai ta zauna ta ?uba ta fara dubawa

*I 'm bag* shine sa?on da ta fara gani ta email din ta
Da sauri ta duba ko wancan *Mk* ne ,dan taji ranar yace wa yaya Muhammad zai shigo soon
Can sai kuma ta tuna to ai ba ita aka yiwawancan sakon ba ,wanda kuma nata ne
Shiga tayi sai taga yaya *Safwan* ne ,batasan lokacin da murmushi ya su?uce mata ba tace '' manya mutanen misrah Allah yayi sai yanzu za'a dawo gida ,kai amma naji da?i wallahi

Shuru tayi da maganar da take yi tunawa da tayi da yanayin da suke ciki ,su Dady basa qasar,su Momy suna kulle ,to kulle zata ce dan sau daya tayi magana da Ru?ayya duk zaman nan shima a wayar shi ta amsa ta kira ,kuma basufi mintuna biyu ba ya amshe wayar ,anan ne ma Ru?ayyan take gaya mata suna nan gidan Dady duka harsu Hajiya da inna ,dan bin umarnin dadyn daya ce su ha?u waje guda
Ganin kamar gidan Dady yafi securitys kawu yace'' su zauna acan


*Gidan Dady*


Yau Yaya safwane ya dawo,tun lokacin da jirginsu ya sauka yake cikin shau?i da farin ciki ya dawo qasar sa ta haihuwa
Rabon shi da nan tun Shekara shida baya, lokacin dayaje qasar Gana rasuwar Ammin shi,uwar ri?on shi
Bai girma a ga ban su,Dady ba,
Asama'u ?anwar Dady wacce suke uba ?aya,ita ta dauke shi tun yana shekara bakwai a duniya
Kasancewar ita bata ta?a haihuwa ba,kuma bata sami matsala daga mai gidan taba,dan da yardar sa ko ince tare suka nemi a basu Safwane din
Basu jima da kar?ar saba aiki ya maida mijin Asama'u gasar sa ta gado wato qasar gana ,shine suka tafi dashi can
Acan yayi karatun sa har matakin digree a fannin islamique medecine
Lokacin da suke tunanin ya gama karatu,ya fara aiki suyi masa aure , a lokacin yayi zancen zuwa misrah dan ci gaba da karatunshi
Yasha wahala sosai kafin suka yarda ,ba ya kamar Dady ydanshi dama can baiso ya karanci islamique medecine donba ,a cewar sa namiji ya nemi aiki irin na maza kamar soja,dan sanda ,dan jarida..... dadai sauran su aikin zaune na mata ne a fa?ar sa

Saidai su Abbi da yake haka yake kiran uban ri?on nasa da Abba suka masa tsaye kafin Dady ya yarda ya tafi misrah
Shekaran shi daya da tafiya sa?on rasuwar Ammin shi ya riskeshi,lafiyan ta qlau ta kwonta da safe aka tashi ta rasu
Anan Gana suka ha?u dasu Dady, Abba Momy Hajiya harda inna sai da aka tafi da ita
Agida aka bar Maryam da Ru?ayya lokacin ba'ayiwa Anty Ramatou aure ba ,sai ita Maryam ta dawo gidan Dady da zama har suka dawo abayan anyi sadakar bakwai
Tare da su Abba ya biyo su suka dawo Nijar , awannan lokacin yaga ajiyar sa da kuma tanadin da yayiwa Rayuwar sa ,yasa aranshi cewa ba zai rasa ba zai samu ,kuma yasan kowa na ahalinsu zai yi farin ciki da hakan
Shi yasa yabar abun aransa har sai lokaci yayi,sannan ya bayyana ya fasa abunda ke ransa kowa ya sani

To awannan zuwan ne ya ?udura aransa yazo kenan cikin danginsa tare da cikar burinsa na zama cikkaken Doctor na ha?a magungunan gargajiya,tare da fatan cikar dayan burin nasa na mallakar abunso abun kaunar sa wato Maryam
Tun da ya iso gidan take raba ido dan gani. Ta inda zai ganta ,tunda yaga su Hajiya da inna to tabbas yasan itama tana gidan ,amma shuru har dare bai ganta ba .ga shi bai sami fuskar tambayar Momy ba ,dan tana fushi dashi tunda ya?i bin Maganar Dady lokacin daya ce yadawo gida ana bukatar shi,wai sai ya bada wani uzurin sa na banza wai zasu fara jarabawa
Aganin ta sallah ne ka?ai idan yanayi bazai amsa kiran mahaifinsa ba ,shi yasa take fushi dashi kuma sai ta nuna masa kuskuran sa na bijirewa maganar mahaifinsa dayayi
Ko ?azu daya shigo samu inna da Ru?ayya suka tarbe sa sai Hajiya da take ta faman murmushin ganin babban jika.

?arfe takwas na dare ya titse Ru?ayya a falo yake tambayar ina Maryam ne ,shi tun yazo bai ganta ba ,gashi lokacin makaranta ne bare yace ko taje hutu wani wajan
A haka ya kwana cikin damuwar rashin ganin ta ,Baisan ya damu da ita har haka ba da bai yi wasa da al'amarin taba
Da safe haka ya gaida Momy amma ta?i amsawa,sai damuwarsa ta ?ara nunkuwa ,kusa da Hajiya ya je ya zauna yana gaishe ta ,nan take ta fa?a?a murmushin ta ,ta lura yana cikin damuwa tun dawowar sa
Tana so tayi masa bayani amma babu baki ,dan jiya tana ji lokacin da yake tambayar Ru?ayya inda Maryam take
Ta manta tabzahar ta ne a falo shine yazo dauka ,kuma har ta dauka basu luba da ita ba
Batun yau ba ta lura da yana san Maryam din tun lokacin rasuwar Asama'u,da ta iya rubutu da ta rubuta masa komai yadda zai fahimta
Suna wannan zaman na kurame kawu yayi sallama
Tun daga ?ofar falon ya fara zolayar Safwane daya taso ya tarbeshi,kawu yace'' ina yiwa tuzurun abokina sannu da zuwa ,yaushe a gari
yana ?ar dariya yace ''naji Ni tuzuru ne ,kai kuma mai ran ?arfe ko
Ka duba kaba tamanin baya kullum kamar dan shekara arba'in ,ka gani Ni kuma duka nawa nake duka yanzu nake talatin da shida fah inaga ma ban rufa ba
To ai ka kusan rufe arba'in babu auren fari
Ni naga ?o?arin iyayen naka da suka barka har yanzu ba aure
Mu lokacin da aka mana auren fari ko ashirin bamu rufa ba ,kawu ya fa?a yana faman zama akan kujera
Hajiya tana aikin da ta saba ganin kawu ya zaune a kujera sai ita ta sauka qasa , cikin girmamawa ta daga hannun ta alamar tana gaishe da shi,ya amsa cikin sakin fuska yana tambayar sauran mutanen gidan
Tashi Safwane yayi yace kawu bara nakira Momyn
Koda yake tana waya amma bai fahimci dawa take wayar ba sallama tayi da wacce suke wayar tana hararar shi tace '' miye haka qato da kai zaka shigo min ?aki ba neman izini
Shi maganar ta dariya ma ta bashi wai ?ato ai shi indai yana gabanta to yaro yake kallon kanshi

?arasawa yayi gabanta ya zu?e guiwoyin sa a qasa yana fa?in dan Allah Momy na ki daina fushi dani wallahi abin zai min nauyi dayawa pls ki barni da na Dady kadai ya isheni
Gashi itama waccen yarinyar tana bani damuwa ,har yanzu banganta,kuma bansan inda take ba ,har wancan gidan naje amma batanan
Momy yace''to naji ka sakar min ?afana in ka ida sakin layin,wace yarinya kake magana akai
Sai yanzu ya ankara da kato?arar da yayi ,sai ya far inda2 yana sosa ?eya yace
dama nashigo in ce miki kawu yazo yana falo
Ran?oshi ta kai masa ya goce yana dariyar farin ciki na Momy ta daina fushi dashi tace ''shine tun da ka shigo baka fadamun ba ka zauna kake mini surutu,tana magana tana ficewa daga ?akin
biyo biyanta yayi ,yanaji aranshi kaso arba'in da biyar ciki dari n'a damuwar sa ya ragu



*Jaune cadre* ( gidan Yaya mahammad )

Koda ta ga sa?on daga yaya Safwane ne sai ta kashe laptop ta dauki wayar ta
Kira biyu ta gani ,daram ?irjinta ya buga ganin number n ce ,to ya akayi ya kirani shida yace 2week zai yi,to ko har anyi mako biyu ne ta tambayi kanta
A'a wata zuciyar ta bata amsa ,saidai in wani abun ne na daban
Bazata manta ha?uwar su ta farko ba .

Tafiyar su Dady da kwana uku ,tana zaune duk abun duniya ya sha mata kai ,yaya Muhammad ya fita ,fitarshi ta farko tun bayan tarewar su
?arfe sha daya daidai na rana taga shigowar sako a wayar ta
Tayi mamaki dan tun da yazo gidan ta gagara yin kira ,ko message din ma idan tayi baya fita ,kuma ba rashin kati bane dan duk sati dady yake saka mata ita da Ru?ayya
Sa?on ta duba sai taga ba?owar number ce
*Assalamu alaikum,Ni ba?o ne ko in ce ba?owar fuskace agareki
Nasan kinsan *komai na rayuwar ki da ta iyayen ki ,Ni mai taimako ne agareki idan har kin yarda
Nima an cutar dani fiye da kema ,mu hada hannu da hannu mu ya?i ma?iyan mu
Komai zai kasance cikin sirri,idan na ce sirri ina nufin ko Muhammad kar ya san da wannan tafiyar,inhar kin amince to ki nemeni ta wannan layin kiyi shawara
Na barki lafiya

Wannan shine abinda sa?on ya kunsa,ta jima tana ?ara karanta sakon ?anta ?ara fahimtar ma'anar rubutun
Tabbas zatayi tunani kamar yadda yace ,tanaso
Ta dauki fansar ran kakanta,da ?atn kawunta ko ince sace kawun ta da akayi ,salwantar da farin cikin kakarta da kuma sanadin rashin lafiyar abban ta
Gaskiya idan tabar wayanda sukaeda alhakin wannan aikin to bata yiwa kanta adalci ba ,to ta ?a?a ,ta ina kike tunanin zaki fara daukan fansar
Wani sashi na zuciyar ta ya tambaye ta,''ta hanyar hada hannu da ba?uwar fuskar nan ka?ai zata samu cikar burin ta ,ta bawa kanta amsa

Mintuna talatin bayan katse kiran sai yaji shigowar sa?o *(na yarda ,miye zanyi* )
Ita kanta tayi mamaki da sakon ya fita , tunda layin ta ya daina aiki a tunanin ta matsalar network ne ,indai da wannan number ne zata iya kira kuma shima Ai kirata ,tun gashi sa?on ta ya fita yanzu,kuma tanada tabbacin yaje inda ya dace
Tun a ranar ya turo mata da address na inda zata same sa,tare da ?a'idojin aikin da zasu fara ,daga baya kuma ya ha?a da yi mata barazana da rayuwar mijinta Muhammad
Wannan shine asalin ha?uwar su da fara aiki atare da sukayi
Cire computer tayi daga caji ta dauki wayarta ta koma falo
A kujera ta zauna ta ?ora laptop din akan cinyarta ta fara dubawa.

Wayar ta da ta ajiye daga gefe ta fara kururuwar neman agaji,tana dubawa taga number ce kamar yadda tayi tsammani,daga kiran tayi ta kara wayar akunne yayinda ?ayan hannun ta yake yawo akan computar
*Na shigo jiya dare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login