Showing 9001 words to 12000 words out of 48162 words
sai kuma ta fasa ,yaji aranta tana so taga mahaifinta adaidai wannan lokacin, kuma tasan a irin wannan lokacin indai yana gida to zaka' samesa a jardin ne
Kai caye ta nufi hanyar da zata Kai ta jardin din
I sarta yayi daidai da da wayar da Abbanta da oncle dinta Oncle dinta Almustapha suke yi
Abba yace yaya Ni abun ya fara bani tsoro kasan yanzu mi suka rubuto min a sakon danake gaya maka
I sarta wajan yayi daidai a wayar da abbanta da oncle Almustapha suke yi
Abba yace yaya Ni abun ya fara bani tsoro kasan yanzu mu suka rubuto min a sakon danake gaya maka
Ka daina ?ata lokacin ka wajan yin bincike,shekara da shekaru kana abu daya amma bakwa gajiya ,to zanyi maka warning na ?arshe karka sake yunkurin cewa za kayi wani bincike,insan ba haka ba zaka tonowa kanka abunda bazaka iya dauka ba
?asa aranka ka'ida ganin Hassan har abada,ka cire ran zaka sake ganin shi arayuwa
Idan ba hakaba zaka sha mamaki
Wannan shine sa?o na ?arshe daya shigo waya na
Yaya ina jin tsoro sosai ,yayimun Bara zanar idan ban fasaba komai zai iya samun yarinya ta,
Bansan ya akayi suka san kowa nawaba '' dan nisawa D.P.O yayi kafin yace Hussain ka ga zargin a ya tabbata kenan,cewa Adam ne yake turo da sakonnin ,kuma yana bibiyar rayuwar mu ,yasan duk wani motsi namu
Amma yaya taya kake tunanin Adam ne ''zai iya kasancewa shine ko wani na tare da shi,ka lura ba'a turo maka da sa?o sai lokacin da kayi wani yunkuri akan zakaci gaba da bincike game da mutuwar Abba
Ban Gaya maka wani abu ba ,da naso sai na gama ha?a duk wani abun daya kamata kafin kasani
Tun ranar farko da aka turo maka da sa?o ,kana turamin sa?on nasa akamin bincike akan number da ma mallakain ta
Saidai an gano cewa daga waje sa?on yake shigowa,duk da boyayyiyar number ce ,amma yaron dana saka yamin aikin sai da ya gano sunan da mamallakin number yake amfani da shi , *MK* sunan da yayi rijistar dashi kenan a qasar da yake
Sunan MK Barister ya yasa ke maimaita wa yace
To yaya ai sunan Adam baya kamanceceniya ko yanayi da wannan sunan ''''shine abunda ya daure mun kai nima ,amma kar ka damu ka kwontar da hankalinka tunda har suka yarda muka fara musayar magana da su toh wata rana zasu kawo mana kansu har inda muke
To shikenan yaya ,amma ina ganin mizai hana mu aurar da Maryam,kaga zamufi samun kwanciyar hankalin ?ara sa abunda yamana saura
Barister kana ganin idan muka yi haka ba mu tauye taba ,nakega kamar yayi gaggawa mu yi mata aure yanzu,kadai sake tinani
duka da duka na Maryam din take
Yaya ka fahimceni yanzufa sun kusan rufa ashirin ita da Ru?ayya,so kaga babu zancen ?an?anta anan
Idansu a kanta yake ayanzu ,idan muka gusar da ita daga gabanmu kaga shikenan
Ganin ya nace yasa yace masa shikenan na fahimcekan,amma maganar karatun ta fah
Eh zata ci gaba da zuwa agidan ta bisa Amin cewar mijinta
To shikenan zuwa gobe sai ka turo min ita gida zamuyi magana''' to Nagode yaya Allah ?ara girma, insha Allah gobe zaku ganta
nagode a gaida gida
Ka kashe kiran daga nan zan daga wani kira ya shigowa'' da to ya amsa yana katse kiran daga ?angaren shi
Mi?ewa yayi dan shiga cikin gida ganin magriba tana gaba towa
Ajiyar zuciya ya ji kamar ana kuka a bayan shi, juyawar da zaiyi sai ganinta yayi a tsaye kamar an dasa ta , kallon ta yayi cikin second 5 ya gama karantar yanayin ta ,s
Da alama dai taki wayar da suka gama yi yanzu kenan
Isa yayi inda take tsaye ya kama hannun ta yace ya kuma kika tsaya anan umma na,dayake shima haka yake gaya mata kamar yadda oncle dinta yake gaya mata ,kasan cewar ta mai sunan mamansu
Abba dama dadyn ka ba rasuwa yayi ba kashesa aka yi??
To waye ya kasheshi??
Kuma Abba waye Adam din danaji kuna magana akanshi??
Minene alaqan ka da shi??
Suwaye suke maka barazana da rayuwa na Abba???
Tun ina ?aram idan na tambaye ka ina Hassan din sai kace yayi tafiya zai dawo very_soong ,ashe ba haka bane ,naji kana cewa ance maka bazai dawo gare ka ba har abada, Abba minene gaskiyar zance anan Please inaso in sani dan Allah,ta ?arasa maganar muryar ta yana rawa kamar zatayi kuka
Sakin hannunta Abba yayi ya juya ya koma da baya zuwa inda ya tashi
Wayar shi ya dauko tare da wannan littafin da ya ajiye akan table , ya dawo inda take a tsayen da murmushi akan fuskarshi yace duka wannan tambayoyin Ni zan amsa su,ki ce yau kin zama lauya,to ga wannan ya dan?a mata littafin a hanunta yace ki sami lokaci ki karanta wannan,zaki sami duka amsoshin tambayoyin ki a nan
Hannun daya dam?a mata littafin ta tabi
Da kallo kafin tace amma Abba ........kafin ta ?arasa fa?in abunda yake abakinta ya katse ta,ta hanyar kiranta da asalin sunanta,kibar wannan zancen Please zuwa gobe kije gidan yaya yana san ganin ki
Yana gama fa?in haka ya tura wayar shi a al'jihunsa ,ya ra?a ta gefen ta ya fice abunsa
Ya barta da tarin tambayoyi abakinta
Ita da ya barta tayi masa koda tambaye daya ne ,taji ance za'a aurar,kuma idan kunnan ta yaji sosai kamar ita akace za'ayiwa aure
To akan mi, zuciyar ta ta antayo mata wannan tambayar,saboda ya tseratar da ke daga sharrin wa'yannan da suke masa barazana da rayuwar ki akan aikinsa
Wata zuciyar ta bata amsa
Ahankali tasa hannun ta ta share kwallar data Dubo mata akan fuskarta ta tausayin mahaifin nata tace Allah ya kare mun kai abbana , insha Allah zan kasance mai yi maka biyayya akan duk abunda ka zartar akaina matu?ar bai sa?a wa Ubangiji bata fa?a a bayyane
Juyawa tayi ta fara tafiya jin an fara kiraye_kirayen sallar magriba
Tana tafiya tana tunanin ko dawa za'a ha?ata oho
Ita dai tasan batada saurayi,tun bata kai haka ba samari suke jerin gwano wajan ne man soyayyar ta ,amma bata sauraron su , karatun ta kawai take
Kullum suna shan fa?a da Ru?ayya akan kula samari,sabanin ita Ru?ayyan da tun suna aji uku na secondary take soyayya da wani mai suna *sadeek* kuma har yanzu suna a tare
Isowarta ?ofar falon yayi daidai da ?arasa tinanin da take,tura ?ofar tayi da sallama a bakinta
Babu kowa a falon ,koda ta shiga ?akin ta wayar ta da littafin da Abba ya bata ta ajiye a bakin gado ta fa?a toilet,wanka tayo tare da ?auro al'wala ,ta fito daure da tawel ajikina ta ,da wani ?arami tana goge sumar kanta da shi
Drower ta nufa ta dauko wata doguwar riga mara yauni ta saka, masha Allah tayi kyau sosai duk da ba wani ado tayiba
Hijab ta sa tanufi inda aka tanada dan yin Sallah..............
..............Sallahr ta tayar cikin nutsuwa,bata tashi a wanjan ba sai data gabatar da sallahn isha'?
Bayan tayi azkar dinta kamar yadda ta Saba ta cire hijab din ta dauko wata ?ar hula ta saka a kanta
?arasawa tayi inda ta ajiye wayar ta abakin gado ta dauka ,har zata fice sai kuma ta dawo ta ?auki wanna littafin ta kai shi cikin inda take ajiye takardun ta masu anfani ta ajiye ta fice daga ?akin
Falo ta nufa Hajiya ce zaune a kan kujera tana kallon wa'azi a Manara tv ,sai inna dake cin abinci a kasan moket (carpet)
Kusa da Hajiya ta zauna daga ?asan ?afarta tana gaishe su cikin ?arkonci irin na kaka da jika
A hankali Hajiyar ta kai hannu ta shafi kanta tana murmushi,alama da kuma tabbacin yaji da?in ganin ta cikin ?oshin lafiya
kanta ta ?ora bisa cinyar hajiya tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa
Har ga Allah tana jin tausayin kanta amma tafi jin tausayin tsohuwar,ace saidai taji mi ake cewa ga baki amma babu halin yin magana
Ita dai tun tashin ta bata ta?a jin muryarta ba
Tasha tambayar inna ko dama can hajiyan haka take bata magana
Amma bata ta?a bata amsa ba
Tana cikin tunanin taji inna tana cewa kije ki zubo abinci kizo kici ,dan na lura kwana biyun nan bakwa san cin abinci ''''da to ta amsa tare da mi?ewa ta nufi daining,abincin ta zubo amma ba wani mai yawa ba ,ta dawo kusa da inna ta far cin abincin
Fira suke da inna jefi_jefi ,Hajiya tana daga gefe tana sauraron su saidai ta murmusa baki yayi nisan zango......
Anan take fa?a musu gobe daga wajan aiki zata fice gidan Dady,dayake haka suke kiran D.p.o Almustapha ,shiko Barister su ce masa Abba
Eh ai Hussainin bai jima da barin nanba ,ya gaya mana duk abunda ake ciki, Allah dai ya basu sa'a a wannan karon ,ya kuma bamu rinjaye akansu'''lomar ?arshe da ta dauko ta ri?e a hannu ba tare da tasa abaki ba tace inna su waye kike magana akai ta jefa wa inna tambaya
Inna da dama ta gama cin nata abincin ta mi?e tsaye tana gyara daurin zanin ta ,tana tuna su?utar bakin datayi tace
To ?ar jarida , wallahi kedai Maryam kar Allah ya ha?a mutun dake a dakin tambaya,dan sai ya rasa abin fa?a,haba mutun sai tambaya
?ar dariya tayi tana saka sauran lomar abakinta da murmushi akan fuskarta tace ,kai inna daga miki tambaya guda dayaduk kinbi kin ru?e ,kuma ma ai baki bani amsa ba,ta fada tana hada kwanukan waje ?aya
Inna da tuni ta fara tafiya dan shige wa ?akin ta tace ai ke din ce wani sa'in kamar wanakiri agun tambaya
Haka ta idasa shigewa dakinta tana mitar Maryam ta cika yiwa mutun tambayoyi,kodan tana abinda take karanta oho
Dama Hajiya ta da?e ta shigewa,sai ya rage sai ita kadai a falon kicthing ta kai kwanukan ta ajiye ta dawo ta kashe tv da hasken falon ta shige nata ?akin itama
Washe gari
?arfe shida na yamma tabar gidan television ta nufi gidan Dady Mustapha,mintuna talatin suka Kai ta gidan
A parking space ta dai-daita tsayuwar motar ta ta fito ta nufi cikin gidan kai tsaye
A hanya suka gamu da Dady zai tafi masallaci,har ?asa ta tsugunna tana gaida shi'''ya amsa cikin sakin fuska da farin cikin daya kasa ?oyuwa akan fuskar shi yace ki shiga ciki nizan huce masallaci
To Dady a dawo lafiya'''da amine Allah yasa ,ya amsa yana ficewa
ita kuma ta ?ara sa daga ciki
Babban falo ne daya gaji da kyau ba ?arya ,babu kowa aciki
Dayake dama ba wani yawa ne dasu a gidan ba
Yaya *Safwane* shine babba yana ?asar *misrah* yana karatun *islamique medecine* shine ustaz din gidan koma ince na family baki daya
Sai anty Rahama ita ko tana aure a *Niamey* da yaran ta biyu
yaya *Ridwane* shine na uku,
Soja ne yanzu haka yakai wata uku baya ?asar ,an turasu wani atisaye ?asar *Mali*
Gidan ya rage daga Dady sai Momy sai *Ra?ayya* wacce itace sa'ar Maryam kuma daga ita Allah bai sake basu wata haihuwar ba
A da can tana samu sai dai baya fuce wata uku zai ?are,daga baya ko batan watan ma ta daina
Momy zainab kenan,mace mai ha?uri da dattako
Da sanin ya kamata
Direct dakin Momy ta fice dan ta gaishe ta sai ta iske tana sallah
Fitowa tayi ta nufi dakin Ru?ayya
Fitowar ta kenan daga toilet ta yo al'wala sanyin Sallah taji sallamar Maryam''ai da gudu take ta fa?a a jikin ta tana mata oyoyooooooo
Ke dallah Malama Ni ki sakani wallahi sai kin karyani wata rana
Ru?ayya ta ?agata tana dariya tace kai sis wallh duk murnar ganinki ne fah
Eh daya ke mun shekara bamu ha?uba ba,ina ce duka ko shekaran jiya mun ha?u a makaranta ,kuma ko yau da safe sai da muka yi waya
Tana maganar tana mata hararar wasa''''Kama baki Ru?ayyan tayi tace bani nakar zoman ba Hajiya ,ni yanzu sallah zanyi bari idan na gama sai muci ga ba ko
Ta ?arasa maganar cikin sha?iyanci
Kwaji da shi tafada tana cire hijab din dayake jikin ta ta fa?a toilet
Wanka tayi,ta kintsa kanta dayake tana fashin sallah ne ,tsab ta shirya cikin kaya riga da wando na fakistane
Irin bur?umemen wando nan da riga iya guiwa,damata ta nada kayanta a gida haka itama Ra?ayyan tana da nata acan
?aramin mayafin kayan da ta yafa ajikinta,daidai da shigowar Momy ?akin
Cikin nutsuwa ta shiga gaishe da ita'''tana amsawa cikin farin cikin ganinta
Har kullum ta kalli Maryam sai Juwairiyya ta fa?o mata a rai,Allah Sarki rayuwa kenan
Maganar Ru?ayya ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin dara lula tace, Momy yau fah di?arki ba sau?i sai sorry,tana shigowa ?akin nan ta fara sauke mun ........bata ?arasa maganar da zatayi ba Momy ta kai mata ran?ashi akai ta ce to Sarauniyar kawo shaida, yaushe ma tazo gidan har zaki ishe ta da sharri
Narai_narai tayi da ido kamar zatayi kuka '''dariya take ?asa ?asa tana kallon Ru?ayya ta ?asan ido
Girgiza kai Momy tayi, tasan yanzu zata fara shari'a a gidan nan ,indai har suka gamu to haka suke kamar wasu yara
Yanzu dai kizo dadyn ku yana kiranku cewar Momy,tana kaiwa nan ta ta yi waje
Bushewa Maryam tayi da dariya harda ri?e ciki ,tayi tana kaikoyan muryan Ru?ayya lokacin da take kaima Momy gulmar ta
Can ta tsagaita ta daga gira daya sama tace ni din ta wasa ce aka gaya miki yarinya''' ?ofa Ru?ayya tayi tana ficewa a dakin ta nufi falo
Itama biyo bayan ta tana ?ar dariya kasa_kasa ,tasan yau akwai rigima tsakanin ta da ?ar'uwarta,?awarta kuma ?anwarta
A falo suka sami Dady da Momy azaune saman 3st
?ara gaishe da su suka yi suka suka zauna a ?asan carpet
Momy ta tambaye ta mutan gida''tace lafiyar su qlau
Kansu a ?asa suna jiran su ji miye dalilin kiran nasu'''baya kamar Maryam da tasan zaman nata ne
Gyaran murya Dady yayi kafin yace *maryam*
Da sauri ta dago da kanta jin yau Dady ya kirata da asalin sunanta
Mamaki bai barta ta amsa ba ,dan bazata iya tuna ranar da taji Dady ya kira ta da ainahin sunan taba''' *maryam* ya sake kiranta a karo na biyu
Sai taji bakinta yayi mata nauyi data amsa
Ta yi ?asa da kanta ,tasan yau koma mui Dady za ki fa?a mata to mai matu?ar muhimmanci ne '''ga nin ta kasa amsawa yasa yaci ga ba da cewa
akoy wani al'amari wanda ba lalle kun san da shiba ,mu da muke manya muka?ai mukasan dashi,kuma mu ka?ai muke fafutukar ganin mun shayo kan komai na tsayin lokaci
Amma abun yaci tura ta yadda har yakai ana mana Bara zana da iyalan mu akan aikin mu
A wannan ga?ar, ina so kibani hankalin ki da kyau Maryam a jiya an yi mana Bara zana da rayuwar ki akan wani aiki da muka farashi tun shekaru da dama
Muna samun nasara sosai a aikin kuma da ala'mu mun kusan samun galaba akan makiyan mu
Maryam hakan bazai faruba indai har kina a gaban mu, idanun su akan ki yake ayanzu
Dan hana faruwar wani abun na daban muka yanke wani hukuncin gaggawa akan ki
Zamuyi maki aure ne cikin ?an?anin lokaci, kuma zai kasance cikin sirri ta yadda ba wanda zai san inda kike ina ba muba
Da nayi tunanin ko na fidda ki daga garin,ko ?asar ma baki daya ,amma sai na tuna indai har zasu san shige da fitanki kina gaban mu
To ba inda zaki tafi basu bi ki ba
Saboda haka ki bamu hadin kai ,
A karon farko Ni nake naman alfarma a gareki
Share hawayen ta tayi tana ayyanawa aranta cewa babu abinda iyayen ta zasu nema a gunta indai tafi ?arfin sa basu samuba
Cikin dasashshiyar muryan ta tace Dady duk abunda kuka yanke akai na ya zauna ,koda bai yimin da?i ba
Wallahi na amince ,indai adu'a ana har kullum shine Allah ya kare munku ya baku nasara aduk wani abinda kuka saka a gabanku
Da amine suka amsa su duka harda Ru?ayya da take ta dirzan kuka jin rayuwar da ake so a aka ?ar'uwar ta mafi soyuwa aranta a ciki
Tana jin Maryam kamar uwa daya uba daya suka haifesu,sha?uwar da sukayi da ita koda anty Ramatou basuyi taba
Masha Allah haka ake so
Allah ya yi muku albarka
Koda yan'uwanku na kusa bance ku sanar da kowa wannan maganar ba fatan kun fahimta''
Da to insha Allah suka amsa
Momy da ruwa ya da?e da cinye ta sai yanzu tayi magana tace to amma Alhaji Banji ka ce ta fito da mijin ba ko shima ku zaku yi mata '' dan murmushi Dady yayi yace wata rana idan kika wani abun kamar yarinya zainab
Muda zamuyi mata auren sirri ai batada za?i