Showing 42001 words to 45000 words out of 48162 words
Chapter 15 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah
suturtashi , ashe shi kansa ne yake yiwa Sutura, da yake Allah ba Azzalumin Sarki bane ai Yanzu gashi an kama shi '' , Dady ya dora da gaya musu da yadda aka yi har suka ga Adam, lalurar idanun daya samesa da komai.
Abba ya kalli Adam da yake kallon su Dishi dishi yace '' Adam ka fitar damu daga duhun Hanya, ka saka mu a Sar?a??en tunanin da muka rasa taya akayi ya zama babu sa Hannun ka a cikin kashe Alhaji da aka yi, bayan kaine ka bu?e musu ?ofa suka shigo, ya aka yi har ya killace ka , a Gidan kasar da muka sameka a ciki?'' Abba ya yiwa Adam wa'yannan Tambayoyi a Jajjere.
Cikin sanyin jiki ya kalli kowa na falon, yaga duka Idawansu akan shi suke, kowa yana jiran yaji mi zai ce, ?an Nisawa yayi kafin yace '' a lokacin da muka zana Jarabawar shiga secondary nida ?an'uwa na , har ga Allah naji zafin rashin Nasarar da banyiba, Alhali su su Hussain sun cinye da Manyan maki , na Fusata ainun, naje har Ofishi nayiwa director rashin kunya, a wannan lokacin ne ya ?ata mini takardu, ina ji da ?uruciya da rashin kunya a lokacin, ban fa?awa kowa yadda muka yi da principal,
Har muka ?auro Garin Miryyah, ?an'uwana suna sona sosai, amma Ni sam bana kulasu, kuma badan bana sansu ba A'a, ina sansu fiye da kima, sai dai aka samu Matsala, Mo?obcin mu Alhaji Munir ya sami Nasarar Rabani da kowa nawa , sara ne aka yi akan ga?a,wata rana da Safe muka sami Matsala da Hussaini akan brush da makilin, kuma fa nasa ne , kawai a Ranar na tashi da rashin jin Magana, tun Asuba naji raina yana ?aci, hana muka yi ta fa?a akan abinda na da?e da Sanin tabbas ba nawa bane , Hassan yayi yayi ya raba , amma ya kasa , sai yaje ya kira Alhaji, tare suka shigo da Hajiya suka rabamu, Fa?a yayi mana tare da ?o??aran kashe akan kar su sake ganin irin hakan na faruwa a cakaninmu!
fitowa suka yi suna zaune a falo suna jajen na zame musu ?arfen ?afa, akan kunnena mahaifiyata take cewa wai ko dan shi aka yanka wa Tunkiya a cikin su ne shiyasa baya ji?'' , wallahi da munsan haka ne ai da mun jira har sai an sami Ragon shima a yanka masa .
Alhaji yace '' karki Jahilci lamarin nan Hansatu, Mutun nawa ne ake yankawa Tunkiya kuma su zama mutanan kirki, nidai kawai Adam shine Jarabawata, ina Ro?on Allah ya bani ikon cinye wannan Jarabawar mai wahalar Gaske , dan wallahi ina jin tsoron abunda zai biyo bayan wannan rashin jin na Adam'',har na wuce su a Falon basu Gan niba.
A haka na baro Gida da ?uncin zuciyar abinda naji iyaye na suna fa?a, kenan ya tabbata tun muna tsumman goyo suka bambanta Ni da ?an'uwana.
A wannan lokacin Alhaji Munir ya iso inda nake zaune akan dakalin Bayin Gidan mu, Hannun sa ri?e da wata kolba ,ya shafa kwalli a idanun sa, abunda ban ta?a gani ba tun Zuwan mu wajan.
Gadan gadan ya nufi Fuskata da wannan kwalbar, sai naji gabana yana Fa?uwa haka kawai, hannu nasa na kadas kwalbar ta fa?i ?asa da nufin kare Hanci na daga jin wani Mahaukacin warin da yake Fitowa daga cikin ta , amma ina n Makara, dan tuni najishi har ?wa?walwa na, Kaina ya shiga Juyawa kamar zai cire, tun daga wannan Ranar ya zama bana ganin kan kowa da gashi idan ba na Mk ba, ya Rabani da kowa nawa, duk wasu kalan kaya maye shi yake sa ya bani, ya Gargade Ni akan kar na yarda a gane da wata Alaqa a Tsakanin mu ,Mk ya koya mini neman Mata tun bansan kaina ba, shi yake bani Manyan Ku?a?e na ri?e a Hanuna, nan na ?ara ganin Gazawar Mahaifina, ganin irin Gatan da Mk yake nuna mini sai na bashi Babban Matsayi, bana ji , bana gani, komai nawa Mk, sai nayi sati ban zo gidan muba, ina can Gidan da Mk ya Mallaka Mani a Matsayin Gidan Daba ta , a wannan Lokacin har Yara gareni sunfi Goma wanda suke take mini baya a Harakar Sara Suka, kuma duk da daurin Gindin Alhaji Munir.
Ranar da muka biyo wani Mutum bisa Umarnin Mk , ashe suna tare da Alhaji na sun dawo daga Masallaci, wannan Fa?uwa da yayi , na yun?ura zanyi kanshi Mk ya Girgiza mini kai Alamar kar na soma, ina ji ina Ganin Magaifina a ?asa Sumamme amma na kasa bashi taimako, Sai Umarni na bawa yarana akan su kaishi Asibiti, kuma su fa?awa Iyalansa.
Rayuwa tana tafiya, lokaci yana ?ara Shu?ewa, a haka Mk ya sani wani aikin da nafi wata guda ina Shawarar yinshi, wayo yayi mini akan wata kwangilar Gina wata kasuwa ya cikewa takardu, kuma bayada yawan Ku?a?en da aka ?u?ata wajan Mallakar wannan Kwangilar, sai ya nema wajan Alhaji rance, Alhaji yace bazai bashi ku?i sama da Miliyan daya ba,saboda yasan halin Jagwal irin tasa .
To shine yake so mu shiga Gidan mu sato ku?in alhajin, in yaso bayan kammala ginin kasuwar idan aka sami riba sai mu maidawa Alhaji ku?in da da kaso mai yawa daga cikin Ribar, duk da bana cikin hayyacina sai da naji bazan iya wannan kasadar ba, sai yayi mini Barazana da Rayuwar duka Ahalina yace zai ?one gidan mu, nasanshi ba sanin wasa ba, zai iya aikata fiye da haka ma, sai na yarda da Maganar shi ta farko akan muje mu sato ku?in.
A Ranar da su Hassan suka dawo daga Makaranta a Daren Ranar komai ya faru, haka muka tsara in Shigo Gidan dan in musu Jagora, shine nazo tun a Farkon dare,na zauna a Tsakiyar Dangina, naci Abinci tare da su, nayiwa Mahaifina kallon ?arshen da bansan shi nayi masa ba , na kalli ?an'uwa kallon Allah yasa da rabon Ganawa, duk bansan za'ayi haka ba'' Maganar da yake ce ta Sar?e masa a baki ya kasa ?arasa ta, kuka yake yi kamar wani ?aramin Yaro,
Kowa na falon yayi Shuru Yana sauraron labarin da yake badawa, ya cigaba da cewa '' na bu?e musu gida da niyyar satar ku?i, ashe shi mugun da abinda ya tsara daban bayan wannan, lokacin da muka shiga ?akin Alhaji ya gama Sallar nafila kenan yana na?e abin Sallah, ?otsam sai ganin mu yayi akansa, ba ?ata lokaci muka ?auke duka ku?a?en da a suke cikin kwabar da yake Ajiyar ku?i, mu duka Fuskokin mu a rufe suke, ba mai gane mu, Ashe MK yayi shirin Tarwatsa mini Rayuwa, sunyi da ?ayan Yarona akan ya bu?e mini Fuska a gaban Mahaifina, ban ankara ba na kusa dani ya Janye mini ?an kwallen dana rufe Fuska ta dashi, Hankalin Alhaji ya tashi ainun, shi da Farko da suka ?auki ku?in bai wani damuba, a Tunanin sa Allah daya basa , shi zai kuma lunka masa , ta yiyu Allah ya Hukunta tun azal sai ?arayin sunci abinci daga arzikin sa, sai suka yi Gaggawar neman sa ta hanyar Haramun, shi haka yasa a ransa, sai bayan ganin Fuskar ?ansa a cikin jerin wa'?anda yake Tunanin sun ?ata, har yake nema musu shiriya a Matsayin sa na Cikakken Musulmi, ashe shi ya?in a cikin Gidan sa yake, bai san lokacin da ya Fa?i akan Gwiwoyin sa ba yana kuka yana Godewa Ubangiji, dan fa?in Allah Ma?aukaki yana cewa (Idan kuka Gode mini, sai ma ?ara muku, idan kuka Kafurce mini, to Lallai Azaba ta mai Tsanani ce ).
Kuka yake iya ?arfin sa, Ganin ba?in cikin da nine Sanadiyar shigar Mahaifina a cikin sa , sai na kasa jurewa, Tsalle ?aya nayi na ganni a gaban Mk, bai Tantance ba nima na janye kariyar Fuskar sa,
A Razane Alhaji yake kallon Babban Amininsa Kuma Ma?obcin sa, daidai da buga ?ofar ?akin Alhaji da Hassan yake yi, nida kaina ban Ankara da Lokacin da Mk ya harbi Abba a gefen cikin sa, daidai da Shigowar Hassan ?akin, ?ayan Yarona mai Suna Laminu ya bugi Hassan a kai a Sandar da take Hannun sa, cikin Tsananin Tashin Hankalin nake kallon su a kwankonce ga jini yana ta tuba daga jikin Alhaji, nayi akan shi da gudu na , amma sai naji kaina yana juyawa, take Idanuna suka Rufe,ban sake sanin inda kaina yake ba, sai a cikin wannan Gidan ?asar da kuka fito dani a Yanzu'' Adam ya ?arasa Maganar yana share Hawayen Fuskar shi, ya cigaba da cewa '' a Shekararun Farko Mk yana kai mini kayan abinci, Shinkafa, mai, da kuma Magi, Gas kusan Biyar ya ajiye, sai yayi kusan watanni Hudu, Biyar, wata rana har fin haka ma yakan yi batare da na saka shi a Idona ba, Akwai Rijiya a cikin wajen,
Haka yake kawo Mutane wajan ya barsu da ransu, amma basa fuce kwanaki uku suke Mutuwa, haka Mutum zai kunbura har ya fashe, ya bushe ya zama ?ashi, sai daga baya na gane a she kafin ya kawo Mutun wannan Wajan sai yasa anyi masa Allurar Mutuwa, lokacin da nasan da hakan sai na cika da Mamakin ya aka yi Ni ya ajiye Ni na Tsayin Shekaru bai kashe niba, har ma yake bani Abinci, buda kaina nake bawa kaina Amsar saboda ?acewar basira ya ajiye ni batare da ya kashe niba.
Da Hannaye na na shiga ?an?arar ?asa, da wani dan ?arfen dana samesa anan tun zuwa na, na fidda ?ar kwana na yi Dakin sa har Yanzu Mk bai san da wanzuwar saba, a cikin nake Rayuwa, duk Mutumin da aka kawo ya Mutu nan yake nake cire Manyan kayan Jikin sa, daga Ranar sun zama nawa, a wannan batun dana baka duk tarkacen Mutane ne, kama daga Biro, kuda?e,walet, photonan Mamatan dadai sauran su, daya wansu sun Rubuta wasi?u a matsayin wasiyya, kuma ninsuke bawa, nakanyi iya bakin ?o?ari na wajan ganin suna Rayuwa amma ina kwana uku yayi yawa daga ankawo mutun sai ya zama babu.
Wata Rana da Mk ya yau da gobe ina sassa?ar ?asa da ?udurin barin wajan ko ta halin ?a?a, nayi Nasarar faso Hanya har waje bayan wannan Ginin, gani ga hanyar Gonakin mutanan garin da bansan sunan saba, saidai mai ?
Idanuna basa ganin komai sa Duhu, Murna da sai na koma ciki, bana gani ta ?a?a zan koma gidan idan na dawo gida wace Hujja gareni wacce zan kare kaina da ita, kawai sai na koma ciki, haka duk dare nake fitowa ta wannan Hanyar, ba laifi ina ?an gani idan da dare ne, har cikin ?auyan nake shiga ina sha'a nina, haka za suyi ta yi mini kallon rashin sani, da irin Ku?a?en jikin mutane da nake samu nake siyan abubuwan bu?ata, da da ruwan Rijiya kawai nake wanka a ?ar bayin da adda kwai a Wajan, na fara wanka da sabulu
A haka naci Baga da rayuwa, daga Magariba tayi nake fitowa nida ina koma sai kusan Asubahi, shima dan kar na wayi Gari na kasa gane Hanyar Komawa cikin wajan, wannan lalurar idanun data sameni ita ta hanani dawowa gareku duk da nasami Hanyar da zan iya guduwar'' Adam ya ?arasa Maganar cikin alhinin Taskun Rayuwar daya shiga .
'' Ikon Allah sai kallo, mu muna Tunanin mun shiga u?ubar Rayuwa ashe kai kama fimu shiga Tashin Hankalin, mu duk Rintsi mun Rayu tare wuri ?aya, kuma ta wani fannin munyi Rayuwar ?anci da jin Da?i tunda har munyi Aure mun Hayayyafa, ka duba yadda kayi taka Rayuwar, banban cin ka da Matacce shine Nunfashi, mamaye Mamaki da ka Rayu, warin Gawa bai kasheka kaba, duk akan Rashin jin Magana na yarinta, Adam bakaji tun muna Yara, ka maida MUGUNTA Halinka, ba yaran wajeba ko mu da muke ?an'wa ka bakajin sha'yin ka mana Mugunta, ka fiddowa Mutum Jini a Jiki a Gunka ba wani abu bane, sai gashi kai wani Bare yazo har Gida yayi maka MUGUNTA nafi muni a Rayuwa, Tabbas Annabi yayi Gaskiya da yace ( *Abinda kayi, shi za'ayi maka)* kai har nunka maka yayi '' Baba yake Maganar ?unar rai .
kukan Hajiya ne ya karra?e Falon cikin Tausayawa tace '' na yafe maka Adam, na yafe maka, ba shakka kaga Rayuwa, yayin da nake nan ina fama da Lalurar rashin Magana, kai kuma kana Can kana fama da rashin Idanu, Ubangiji ya ha?amu yayi mana Rahama ya Ji?an Mahaifin ku, yayi masa Rahama ya bi masa kadun Rayuwar sa da aka ?auka ba tare da laifin komai ba'' kuka take sosai yayin Maganar.
A guje Adam ya tashi ya nufi inda yake jin sautin Muryar yana fita, dan tun ?azu Baisan da wanzuwar ta agunba, dan ba shi sosai yake ganin suba duk da a ?an Ragowar haske a Falon.
Rungumar ta yayi ya saka kuka kamar wani ?aramin yaro, bazai iya tuna rabon shi da yajishi a jikin Mahaifiyar tasu ba , tun bai kai ashirin ba ya Nisanta Kansa da ita, ko nace aka Nisanta shi da kowa nashi .
Duk wani mai Ruwan Hawaye a kusa a Falon nan sai da ya zubda su, hannu Hajiya tasa tana shafar kansa da shima ya fara farin Furfura, sai dai tashi ta wuya ce, tunda ga ?an'uwan sa nan koda za'a samu a Jikin su ba sosai ba, Soyayyar Uwa da ?anta sai Allah, sai taji duk wani abunda Zuciyar ta ta ?ulle ta ?orawa Adam ?in ta sauke shi, kaso Ashirin daga Damuwar ta ya kuma Raguwa, yan sai kaso Goma na Rashin uban ?a?anta, shi kuma ya riga da ya ku?uce mata na har Abada.
Kawu ne yayi Gyaran Murya yace '' to Alhamdulillah, Godia ta Tabbata ga Ubangiji, Allah shi ya Hukunta hakan sai ya Faru tun Azal, sai mu Godewa Allah daya ta?aita abun a iya haka, Allah ya bawa Magabatan mu ikon Hukunta wannan ?asurgumin mai Laifin, a yanzu abinda ya kamata shine akai Adam Asibiti dan Aduba Lafiyar sa, kafin muga abunda za'ayi nan gaba'', '' A'a ai ba sai an kaishi Asibiti ba , Ni nan zan ha?a masa magani da yardar Allah zai sami lafiya'' cewar Safwan.
'' Masha Allah, Shikenan sai ka ha?a masan kawai ashe Munada Docton Gargajiya a Gidan '' cewar Baffa.
Cikin Mako ?aya su Dady suka ha?a su wasu Bayanai da Hujjujin da zasu Gurfanar da Mk a gaban Kuliya, Abba shi zai Jagorancin Shari'yar a Matsayin Lauya.
Labari duk ya karra?e Gari ta Hanyar ?ar Jarida Batoolah, har Gida tazo ta sami Abba, bayan ya bata Izini da kuma Lokacin da zata samesa, ya bata Labari tun Farko, ta kuwa ji Da?i sosai, tare da masa Al?awarin taza tayashi ya?a wannan Abun a Duniya, dan ya zama Izina ga masu Hali irin na Mk, kuma zata ci gaba da Bibiyar su har ?arshen Shari'ar da za'ayi Ranar Litinin mai zuwa.
Batoolah yarinyar Macece ?ar Kimanin Shekara Talatin da Shida, Sa'ar Safwan ce, tana zaune da Mahaifiyar ta da Yaranta guda Biyu, Amir, da Murira, shekara hudu kenan da Rasuwar Mijinta, ya tafi neman Zinariya Djado, sai kiran su akayi akace ya rasu , toh dama tana aikin ta na Jarida, sai ta dawo Gidan su da zama ita da Yaranta, suke zaune a Unguwar Berlale.
Yau ne Ranar da aka yi Shari'a Tsakanin iyalan Gidan Alhaji Gambo mai kayan kwali, da Shugaban ?an kasuwar Jahar Damagaram Alhaji Munir Kabiru, Abba shine lauyan da yake kare ?angaran su, yayin da Mk ya kasa Samun Lauyan da zai kare shi, dan kowa yaga ta'asar daya ta?ka, wai dan ma 6an Jaridar basu ga wannan gidan ?asan ba a wancan Ranar da abun sai yafi yadda yake Yanzu Muni.
A Idon Duniya an yanke wa Mk Hukuncin Daurin Rai da Rai a gidan yari , a bayan fage Muhammad yasa aka masa Allurar Mutuwa Kamar yadda yake yiwaa Mutane, kwanan sa uku yace ga Garin ku, Gardawan Gidan yari da Bazasu wuce goda goma ba, aka basu shi akan su kaishi suyi masa Sutura, Oncle Adam da yanzu yake gani ras da Idanun sa , da Muhammad, Safwan, Ridwan, suka tare hanya suka yi fashin Gawar Mk, ba fashi na ?arfi da ?arfe ba , A'a saye Mutanan suka yi da Mahaukatan Ku?a?e, suka basu Gawar, suka koma a Matsayin sun Suturtashi.
Wani dan ?aramin Gidan ?asar da su Muhammad din ne suka gina shi acan Bayan Gari suka kai shi, a ciki suka saka shi suka rufe, basuyi wajan dan su dinga Ziyartar shiba, kawai dan ya zama ?worangwal shima Gangar Jikin sa ta shaida irin Azaba da U?ubar da yayi ta kasa Rayukan Jama'a a cikin sa.
?
_Bayan wata Biyar_
Anty Ramatu sun da?e da komawa Niamey, tuni Abdul wahid ya sanar da Pappa ya sami Matar Aure, yanzun haka sun dawo gida Nijar ?an fara Shirye-shiryen Auren ?an Auta.
Abba Hussain ya Gina Jerin Gwanon Gidajen da za'a iya kiransu da a Unguwa Guda, a Unguwar Tawalala yayi Ginin, daga su har Yaran su kowa da ?angaren sa, Baffa ma da nasa ?angaren, kawu ne ba yadda basuyi ba akan ya dawo nan ya?i, saboda sauran iyalansa.
an saka Ranar Auren Amare da Anko?an su, Masu Mata tuni suka tare da Matayan su kamar su Dady da Baba, su Abba ana shirin Angoncewa.
Saura wata Daya Aure ?anwar Momy tazo daga Diffa, da yake dama da su?in na can ne , ba ?ata Lokaci Anty Yani ta fara aikin Gyaran Amare baji ba gani, cikin Sati Biyu suka sauya kamanni, a kullum suna ma?ale da Angwoyan su ta waya, amma banda Maryam da har zuwa wannan Lokaci ta kasa sakin Jiki da Muhammad.
?angare ?aya Momy ta ware ta killace su, ba mai shiga, kuma suma ta hanasu Fitowa, daga su sai anty Yani a ?angaren.
Abdul wahid duk ya Burkice wa su Mamma a Niamey wai shi bazai iya Ha?uri bai ga Ru?ayyar shiba na Tsayin Lokaci