Showing 27001 words to 30000 words out of 48162 words
Chapter 10 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah
sai shina Abba ya fara kuka
Ganin abun nasu ya koma hadda yada kai a cewar Dady, ta ?a?a zasu tsaya a gaban iyalansu suna kuka, to su mata da suka fisu rauni sai su yi mai kenan ?
Dady ya ?an daga murya yace dan Allah ya isa haka Hussain ka zama jarumi mana , ta Ni dana je na gansa daga nesa fah ,a ranar dana je bincike akan Muhammad har Hassan din sai danaga ni , ko ince gani gashi amma haka na ha?ura ban nuna inada ala?a dashi ba , zaka tuna ranar
watanni biyar baya , zaka shiga gida bayan kun dawo daga cin kasusuwar Garin Magarya , ka ta yar da wayar ka garin shigar da mashine dinka cikin gida na ?auka na baka
Cak Baba ya tsayar da kukan yana kallon Dady , tabbas ya tuna lokacin da yake magana akai kuma sai Yanzu ya kalli Dadyn da kyau,
Jinjina masa kai Dady yayi yace '' eh nine a ranar sai da naji kamar kar na barka acan , in dauko in taho da kai dan anfi bu?atarsa ka anan ,
Ku buba kuga idan mu muna maza muna kuka to ita , wacce tafimu shiga damuwar faruwar hakan mi zata yi ,
Ya fa?a yana nuna musu inda Hajiya take zaune tun dazu , sai yanzu suka lura da yanayin zaman ta tun dazu
Inna da tafi kusa da ita tace Hansatu ki ?aga kanki kiga , yau gamu ga Hassan zaune a waje ?aya , har yana magana da bakinsa
Allah Sarki ashe rai kan ga rai .
Shiru taji kamar ba da Hajiyar take magana ba, sai ta kai hannun ta tana ?ago da fuskar Hajiyar ,
Luuuu taga taga ta sulale akan carpet kamar matacciya
Kafin kowa ya iso wajan tuni Hassan ya ?araso yana jijjigata da kiran sunan ta , yana kuka yana fa?in karki mini haka dan Allah , ki tashi kiga na dawo gareku , idan kika yi haka kamar Ni ka?ai kika yiwa dan Allah kimun afuwa wallahi ban barku da gangan ba , nima bansan lokacin dana bar gidan a lokacin ba , Please dan Allah ki tashi Mamana, Baba ya fa?a kamar wani zararre
Kutsawa tayo ta tsakanin mutanan wajan ta isa wajan da Hajiya take kwonce kanta akan cunyar Baba da yake ta faman sabbatu ,
Dayawan mutanan falon suna kuka, sai manya dake a tsaitsaye suna kallon ikon Allah, da tambayar juna abinda ya sameta har ta fa?i
Kusa da Hajiya ta matsa tana tana ?ara hannun ta a sautin hancin ta , da sauri ta ?ora kanta a kan ?irjin ta dan sauraron bugun zuciyar ta ,
Yaya Muhammad ai suma tayi, ta fada tana kallon sashen da yayan nata yake , yace 'l to kiyi wani wani abu mana, sai kace ba aikin kiba ya fa?a adan fusace
Tuni tashiga taitayin ta , ganin kamar ya kufula da ita,
tace sister dan Allah kibani ruwa mai sanyi tana kallon Maryam take Maganar, kafin Maryam tayi wani yun?uri har yaya Safwane ya ?auko ruwan har tuntu?e yake ,
Muhammad sai da yaji dama shi yaje ya dauko ruwan , dan a tunanin sa ko Safwane din yayi ne dan ya burge Matar sa
Ruwan ta yayyafa mata a jikin ta amma shiru bata farfa?o ba , sai Abubakar sakataren Abba yace ko zamu kai ta asibiti ne , kar abun yayi nisa
Bata basa amsa ba sai hannun ta data ?ora da kan cikin Hajiya ta shiga danna daidai kusan ?irjinta
Dannawa na uku sai ga nunfashi sama sama ya biyo baya .
Saida kowa ya sauke ajiyar zuciyar samuwar nunfashin, ba ya kamar Baba da yake jin yafi kowa shiga damuwa
Murya suka ji ?asa ?asa tana cewa Hassan dama kana raye
Juyawa suka shiga yi dan ganin ta inda sautin muryar yake fitowa , *Humaira* da take kusa da ita tace ai ga wacce take Maganar, dan ita batasan Hajiya bata magana ba , shima Baba bai jima da saniba sai bayan Muhammad ya auri Maryam.
Kai alhamdulillah cewar kawushe da wata ranar da zata riske mu ta farin ciki irin haka ,
Hansai ke ce kike magana da bakin ki
Da taimakon Mama ta tashi ta zauna tace Eh Ni ce kawu alhamdulillah yau Allah ya hukunta kowa zaiji sautin murya ta , Alhamdulillah bi ni'imatihi wakafa bihi ni'imah
Hajiya ta kara da cewa , yau rana ce ta da bazan ta?a mantawa da ita ba , a yau kaso saba'in na damuwa ta ya ragu
Tsoho na kusa da kawu yace '' Allah mai iko wannan fa Hansai na ce , wallahi ita ce
Kawai sai ya fara share hawaye
.............RAF RAF RAF
Sukaji ana tafi daga kofar shigowar falon.
Sanye yake da kayan sojoji a jikin sa, yayi kyau masha Allah sai wata jaka irin tasu daya rataya a ?ayar kafa?ar sa
Kyakkyawan saurayi dan kimanin shekara ashirin da takwas.
Hararar sa yaya Safwan yayi yace '' shine zaka shigowa mutane falo ba sallama kamar a gidan arna ,ko nan barikin sojoji ne nan aka gaya maka
?ar dariya yayi yana cewa '' Assalamu alaikum
Da amine wa'alaikum Salam kowa ya amsa
Ya ?araso ciki yana ?o?arin cire takalman ?afarsa
Sai da ya tsugunna a gaban iyayensu ya shiga gaishe da su cikin girmamawa.
Yan'uwansa maza ya kalla ya fara basu hannu suna misabiha, sai da yazo kan yaya Yace ai nayi sallama yaya Ustaz , tun lokacin shigowar su Baba nake a tsaye awajan, kusan a tare ma muka shigo
Sai dai ba wanda ya kula da tsayuwa ta a wajan.
Matse masa hannu da ?arfi Safwan yayi, ?ar ?ara yasa yana cewa yaya dan Allah kayi ha?uri, irin wannan matsa ko a atisaye ba'amini irin taba , yaya Muhammad dan Allah ka ceceni.
Dariya aka sa duka falon, ganin ta?arar da yake yi gatoto dashi sai tsalle yake wai acece shi, kuma badan bazai iya ?ocewa daga ri?on da aka masa ba a'a, kawai shi dama haka yake idan yana waje dole a dara
Shine Sarkin tsokana nawan family , har Dady bai bariba wajan tsokana da sha?iyan ci, ba ya kamar Abba daya mai dashi abokin wasan sa .
Tasowa Muhammad yayi yana dariyar data ?ara fito da asalin kyauwon sa , ya iso yana ri?e kunne yace '' ayi mana afuwa babban yaya tuba muka
Safwan da dama haushin Muhammad din yake ji, ganin yana shirin katse masa mafarkin sa sai ya ?ara matse hannun *Ridwan*, ?ara ya kuma yi a karo na biyu.
Kawu yace '' tuzurun abokina sai ka kashe dan mutane ne ?
ka saka masa hannu kumu tashi muyi al'wala dan ana ta kiran sallar magariba , bayan mun Dawo daga salla zamu zauna muji magana daga bakin kowannan mu
Tashi suka suka shiga yin al'wala a toilet din dake falon ,
Suma matan haka suka shige dakuna bisa jagorancin mutanan gidan
Humaira da Hafsat abokiyar tagoytakar ta, ?akin su Ru?ayya suka shiga tare da Maryam
Gambo mai sunan Alhaji suna kiransa da Amir, da mai bi masa Usmane sun tafi masallaci tare dasu Dady
Sai yan biyu Hassana da Hussaina sune ?anana suna tare da Momy, tun zuwan su gidan suka ma?ale mata a jiki, dama basuda sar?afa
Koda suka fito daga masallaci Abubakar yayi musu sallama yace zuwa gobe insha Allah zai shigo , Allah ya huce gajiya,
Sosai ya taya Abba murnar samuwar lafiyar sa , data mahaifiyar sa da kuma dawowar dan'uwansa cikin rayuwar sa
'' godiya Abba yayi masa kafin shi Abubakar din ya huce ,
Tun tashin su yan'aiki suka shiga
Jere tarin kalolin abincin da suka shirya, suna da azanci sosai , tunda suka ga da ba?i a gidan suka shiga shirya abinci ,kuma mai yawa suka yi , shiyasa kowa na gidan yake jin da?in zama dasu ,har sun zama kamar ?an gida , ta yadda indai ba ba?i to basa bari sai an bau odar abin da zasu girka , kawai sai dai su zaba da kansu suyi
Kuma masha Allah suna fidda su kunya, komai yawan jama'ar da suka tara .
Saida suka ci abinci kafin kawu ya kalli Baba yace '' Hassan muna sauraron ka ka fa?a mana dalilin ka na barin gida , adaidai lokacin da bai kamata ace ka gusa ba .
Cikin tsananin tashin hankali na tuna baya Hassan ya fara bayani kamar haka ,
'' a daren ranar da muka dawo daga makaranta daren komai ya faru , Adam yazo gidan , cikin farin ciki muka zauna dashi tsawan awa uku kafin yace zai tafi , babu wanda yaji da?i lokacin da yake fa?in zai tafiyar sa , amma haka ya fita ya barmu da tsananin kewar rashin zama damu da bayayi, duk da miyagun halayen sa , hakan baisa mun ?i saba , kawai halinsa ne Bama so
Lokacin da Hajiya ta ce muje mu kwanta nisa, bamu jima da shiga dakiba Hussaini yayi bacci, nima inaso inyi baccin Amma ya?i zuwa sai juyi nake akan gado, can nace bari inyi sallar nafila ko zan samu nutsuwar zuciya,
Dan wata damuwa naji tana tasomun kamar wani abun firgici zai riskeni, idan na tuna maganganun Abban kunya yayi a ?azu sai inji hankali na ya ?ara tashi .
Al'wala nayi na fara sallar nafila, ina yi ina adu'ar Allah ya sassauta min wannan danuwar danaji rana shirin rabani da walwala na,
Har ?arfe ukun dare ido na biyu ina karatun Alkur'ani mai girma , sai naji nunfashi na yana ?o?arin dauke kamar wanda iskan danake shaqa tayi Mani ka?an
Kur'anin na maida wajan ajiye sa ya zo wajan window dakin mu , na yaye labulen dan samawa kaina iskar sha?a, ko zanji nunfashi na ya daidaita.
Bu?awar dazan yi yayi daidai da Adam ya bu?e ?ofar gida wasu mutane guda hu?u suna shigowa da san?a ,
Mamaki ne ya kamani ganin shi kanshi Adam din a cikin gidan , bayan tun ?arfe goman dare yayi mana sallama akan ya tafiyar sa .
Mamaki da kuma tsoro basu gama kamaniba sai dana ga ?aya daga cikin mutanen ri?e da bindiga daya kuma yana ri?e da ?atuwar sanda suka nufo hanyar da zata sadasu da ?ofar falo bisa jagorancin Adam.
Da sauri na sake labulen na dawo ina tashin Hussain, ada bashida nauyin bacci, dan shi yake tashina a mafi yawan lokuta, haka nayita tashin sa amma kamar ya mutu , ko motsi bayayi,
Fitilar wayana na kunna na fito daga ?akin mu na nufi falo .
Fitowa ta yayi daidai da shigar su ciki ?akin Abban mu da gudu
Na ?araso wajan
Amma kafin in ?araso har sun sakawa dakin key
Kofar na shiga bugawa da iya ?arfina , bansan mi suke yi aciki ba , sai da nasamu nasarar balle ?ofar ?akin.
Bana yayi shuru yana share hawayen fuskar shi , kafin yaciga da cewa '' balle ?ofar danayi yayi daidai da harbin Alhaji a ciki da wannan mai bindigar yayi ,
Kukan kura nayi na nufi inda yake amma ban ?arasaba , bankuna sanin inda kaina yake ba, Baba yana magana yana kuka yace '' sun kashe mana abban mu, abun bq?in ciki bisa jagorancin ?an uwanmu wanda muka fito ciki guda dashi , nayi ba?in cikin da nima basu ha?a da niba , da nasamu sassaucin ra?a?in da zuciya na take min har gobe , idan banga Adam a gaba na ba an yanke masa hukumci daidai da abinda ya aikata ba
To bazan samu nutsuwar zuciya ba ,
Allah ya ji?anka Abba yayi maka Rahama yasa aljanunah ta kasance masauki agare ka ,
Da amine su kawu suka amsa, amma baya gamsu duk mutanen falon kuka suke jin yadda aka kashe kakan masu har lahira kuma ace dan cikin sa yayi haka , abundam daciwo sosai.
Tsoho na kusa da kawu yayi gyaran murya yace '' da farko dai zan fara da neman afuwar yarinyata kuma , Hansai ina mai baki ha?uri dan Allah ki yafewa babanki laifukan shi agare ki , nasan Ni mai laifi ne ko awajan Allah , amma har ga Allah bansan nayiba .
Sai a lokacin take kare masa kallo da kyau tace '' Baffa dama kaine ta ta fa?a tana nuna mahaifin nata da yatsa,
Kowa ya cika da mamaki jin ta kira Baffa da mahaifin ta,ciki kuwa harda Hassan da iyalansa
Bai ta?a ba tunanin Baffan kakan sa bane ba , shidai yasan ya kar?esa kuma ya zauna dashi iya wuya.
Jinjina kai tsoho Baffa yayi yace eh tabbas ita ?a tace kuma abun sona da ?auna ta , banida abin da nake so kamar Hansai lokacin tana yarinya, bayan rasuwar mahaifiyarta sai komai ya canza, bana jin soyayyar yarinyar ko ka?an araina, kuma duka makircin matata Laure ne, sai bayan na aura wa Gambo Hansai da kusan shekaru kafin nasake tunawa da ita , gashi na manta sunan garinsu daya fa?a mini,
Haka nayi ta adu'ar Allah ya sake ha?ani da ita kodan in nemi yafiyar wofintar da rayuwar ta danayi, amma shuru ban gan taba , ko labarin ta babu .
Haka nake gaura cikin daji can cikin gonakin sai inyi sati acan da komai na bu?ata na, bana so in shigo cikin mutane dan komai baya mini da?i.
Wata rana da sanyin safiya ina zagaye acan gaba ?a gonakin mu , sai na hangi wani abu kamar mutun , cikin tsoro na ?arasa wajan , ai kuwa dai mutum ne. A kwance .
Kyakkyawa dashi sai dai da alama ya mutu, da har zan zan gudu bin barshi sai kuma na dawo , na tsire wannan tsoron daga raina , zuciyar tausayi, taimako da kuma imani ta shige ni , naji zan iya taimakon sa, koda ace a mace yake to zan tsaya har sai anyi masa sutura irin na kuwane cikekken musulmi, dan kana ganin shi kasan musulmi ne har da ?ugon sallah a goshin sa.
Hannu nakai na ta?a ?irjin sa sai naji kamar yana nunfashi ,da sauri na ?aga rufar sa na duba yanayin fitar nunfashin sa ga kuma ma?ogaron shi yana motsi tabbacin yana da rai .
?aukan shi nayi a kafada ta na nufi gonata dashi, bansha wata wahala ba ya farfa?o , alhamdulliah kawai nake cewa , a yau nima nayi aikin cetar rai, dan Allah nayi kuma nasan zai bani lada, adu'a nake Allah yasa ladan wannan
Aikin dana yi ya zama kankarar zunubai na ne .
masha Allah ya fada yana kallon yaron yace '' yaro ya sunan ka , kuma ina ne Garin ku , dan da gani kai ba na nan Garin bane ,
Budar bakin sa sai yace bai sani ba
Cikin mamaki na sake tambayar sunan Garin su nan ma yace bai saniba ,
A takaice dai wannan saurayin bai san komai nasaba , hasali shi kanshi bai san ko shi waye shiba .
Na zauna sosai nayi nazari , zan ri?e shi a waje na kuma zan dinga yawo dashi duk inda zani, a haka wata rana zai ha?u da wanda yasani , nan nace masa sunan sa Tijjani , ya daga kai alamar haka ne , nan na lura kamar ya mance komai nasa ne sai abinda na ?orawa akai , insha Allah zan ri?eka da amana daga nan har in ha?u da wani naka , na ?aukar wa kaina alkawari .
Tun daga wannan ranar Tijjani yake wajena, ko ince ya zama ?an gidana , mutane duk wanda ya tambaye ne daga ina na samo sa sai ince. Jika nane na wajan Hansai, ashe da gaske jikan nawane ,
Lokacina da banba Hansai ba , shina ba wa danta Hassan, na zauna dashi daidai gorgodon halina .
A kakar wannan shekarar da za'a yiwa yan'mata da samarin ?auyan mu aure , nima na ha?a harda Tijjani , ganin da alama shi yama girmi samarin a shekaru ,
Mu kuma Bama barin yara suyi irin wannan girman ba tare da mun aurar da suba , sai na ha?a shi aure da ?ar ma?oncin mu mai mutuwa malam mu'azu, sunan yarinyar Umaima, ya fa?i yana kallon inda Mama take zaune yace '' yarinyar kirki ce bata Musa ba ta ?arbi Tijjani a matsayin abokin rayuwar ta .
A haka rayuwa taci gaba da tafiya shekara biyu da aure aka haifi Muhammad sai kuma haihuwar ta daga har kusan shekara takwas kafin aka haifi yan' biyu mata , wanda suka ci suna, Humaira da Hafsat mai sunan Hansai, haka kawai naji ya kamata ayi mata takwara
Har a wannan lokacin Tijjani bai tuna da ko shi waye ba , kuma , babu inda bana zuwa dashi
Ko Allah zai sa ya ha?u da wani nasa , amma shuru,
A shekarar da za'a haifi Gambo ?an biyu Wato Amir a wata rana mundawo daga gona nida Tijjani zamu tsallaka Hanyar mu ta komawa gida, akan babban titin daya rabe cakaninmu da gonakin mu,
Bisa tsautsayi wata mota ta buge Tijjani ,
Mai motar daya buge shi ya kaimu asibitin miryyah , yana tsaye a kanmu har aka masa traitement , dan baiji wani ciwo ba .
Ganin Irin kallon da yake mana nida wanda ya ka?e sa yasa nace masa '' Tijjani lafiya kuwa , wannan wanda ya ka?e ka ne , kuma mutanen kirki ne , dan dayawa idan hakan ta faru sai wanda yayi laifin ya tsere, musamman damu abun ya faru damu a bayan gari , dan haka ina mai tayashi bamu ha?uri, muyi ha?uri Allah kiyaye gaba.
Kallona kawai yake baya ko ?iftawa, ya kalleni ya kalli wannan mutumin,
Can yace wai wane zance kuke yi ne , suwaye ku mi ya kawo ku gidan mu, miyasa kuka kashe mana abban mu, ina Adam din yake wallahi bazan barkuba , yana magana