Showing 36001 words to 39000 words out of 48162 words

Chapter 13 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah

10 Jul 2024

3349

cikin su ya ya matso kusa da Ridwan dan ya cire masa takunkumin da aka rufe musu baki dashi .


'' Ka dakata '' suka ji murya kamar daga sama , tabbas wannan muryar Mk ce duk da bai ta?a jinta a zahiri ba , saidai yasan ta farin sani , ko in ce ya yardace ta a kwakwalwar sa .
Cikin sauri suka juya fuskokin su inda suke jin kamar daganan sautin ya fito, mutum ne zaune akan wata hamshaqiyar kujerar da take juyawa , ya bayansu kawai suke iya hangowa .
Ridwan da yaki ma?ura wajan danne zuciyarsa yayi ?ofa, fuskarsa cike da alhinin rashin samun dama a yanzu da bashida ita , dasai yaga mai rabashi da wannan Mk din , inama shine Kawu Adam ko kuma wani na tare da shi , ko ma dai wanene yau sai sunga ?arshen sa.


Kuyi da kujerar yayi ya fuskancesu , baban mutum wanda a?alla zai haura shekara sittin ko saba'in a Duniya, yau da Alhaji yana a raye da sai su ce zasu yi kusan sa'annan juna dashi , farar ?asumbar data kewaye fuskar shi ya fara ja da hannun sa yana murmushi kafin yace '' barka zuwa sashen wannan gida nawa mai ?unbin Tarihi samarin gidan Abba da Dady '' .
cikin razana suka kalleahi su duka ko zasu karasa fahimtar manufar zancen sa , Abdul wahid da Hausa bata gama zaunawa ba sai rarraba ido yake , basu idasa tamtamar abunda kunnuwan su suka ji musu ba suka ji ya kuma yace '' kanan Mamaki matu?a gaya , kana tunanin kafini wayo kawai ?'' , '' amma kod yake ka fini wayon dan duk tsawon lokacin nan ban gano kaba sai a yanzu shigowa ta wurin nan , gaskiya kayi ?o?ari sosai dan Matashi , saidai ina mai farin cikin sanar dakai cewa su wannan Hussainin na bogi da ka kawo a matsayin sune bazasu bar nan ba har sai ranar da na kama asalin wayan'can , Bama su kadai ba , ku duka ba wanda zai bar nan na har 'abada , koda na kama su , zan ta taraku anan ina azabtar daku , Kamar yadda na fara tun farko , kasan miye asalin sunan wannan waje , ko ince gida , to nan ne Gidan zubda Jinin duk wanda ya ce zai ka mani cikas a rayuwa , amma Saboda halarci da zaman tare yasa na haramta zubda Jinin Ahalin Gambo a gidan nan , sai dai alkawarin azabar wa har ?arshen Rayuwa .



Allah ba zai baka wannan damar ba , wacce ya baka ta farko itace rabon ka '' suka ji magana daga bakin ?ofar shigowa wajan , dan dama ba wani rufe wa suka yiba .
Cikin razana Mk ya tashi tsaye yana nuna su da yatsa yace '' ta ina kuka shigo nan , waya baku izinin shigawo ?'' ya ?arasa maganar kamar wanda wani abunsa mai muhimmanci arayuwa yake son ku?uce masa .


Ta kowa da?i da Abba suka fara yi har cikin tsakiyar wajan kafin Dady yace '' dama ba kana neman muba, to shine muka kawo kanmu '' yayi maganar yana kallon sashen da su Muhammad suke yacigaba da cewa '' kunyi Mamaki ko , ta yadda har muka san fitowar ku , kuma muka biyo bayan ku .
Cikin tsananin mamaki Muhammad da yake ?o?arin kunce ma Safwan hannu yace '' Ai Dady kun fuce tinanin mai tunani , Ni so nayi kawai da kubar mu mu karasa aikin da kuka fara ''.
Ridwan '' yace Abba dama wannan shine oncle Adam din daya har giza mana , farin cikin ku '' yana kallon Mk da idon shi ya gama raina fata yake, har yanzu tunani yake ta yadda suka iya ?erare securitys din da suka kewaye wajan nan yake , kusan shekaru da dama yake she?e ayar sa anan , kuma bai ta?a samun matsala ba , hasali ma ba wanda ya ta?a shigowa har cikin nan , idan ba wanda rayuwarsa tazo ?arshe ba , sai kuma wani ran daya kasa salwantar wa na tsayin lokaci , yake ajiye dashi kamar wani Kayan wanki .


Maganar Abba ce ta maidoshi cikin tunanin daya fa?a yana yace '' A'a yarona wannan ba shi bane Adam , ma dade ina tantamar ba Adam bane ba , a yanzu ba sai anjima ba , shi da bakin sa zai fa?a mana inda Adam din yake , munafiki mai cin dudduniyar wanda ya yarda da shi, bazan ta?a manta wannan bakar Fuskar taka ba , a lokacin da aka kashe mana mahaifi , awannan lokacin ka bacce wa ganina ,ko ka?an tunani da kuma bincikena bai ta?a kawo mini kai a raiba , da tun a waccan lokacin na gama da babinka a Rayuwa '' .


Cikin rashin fahimta Dady '' yace wai dama kasan shine ?'' , '' eh ai kaima kasan shi saidai ba lalle ka gane shi ba , zaka iya tuna ranar da kawu yazo daga ?auye ya nemi alfarmar a bamu Gawar baba ayi masa sutura?'' , '' eh na tuna lokacin '' Dady ya fa?a yana ?ara ?ure fuskar Mk da gumi ya gama jikawa , wai ko zai tuna inda yasan fuskar .


Abba yace '' wannan shine *Alhaji Munir Kabiru* , wanda da alfarmar sa kuka yadda kuka bamu Gawar dan a suturtata '' ya shammacemu dayawa , dama ashe kaine Mk , ma'ana Munir Kabiru ko , to yayi yanzu ina Adam yake kuma dalilin ka na tarwatsa mana ahali har haka ?'' Abba ya tambaye sa cikin ?acin ran daya zama sabo a yanzu daya ke gaban mutumin daya hana musu jin dadin rayuwa .
Basu akankara ba ya tako ya rike wuyan Abdul wahid , ya kara masa ?aramar bindiga a kansa , ihun da Abdul ya saka shiya ankarar dasu da zancen da suke , da baya da baya ya fara yi dashi , cikin fasashshiyar muryar shi yace '' eh nine nan Munir , kuma nine na kashe mahaifin ku , sai akayi yaya , bayan haka na kuma sace Hassan , kuma na killace dan'uwan ku a wurin da bana tunanin zai fito na har abada , nine nan nayi komai , kuma bazan dakata ba har sai na idasa '' yayi Maganar wuyan Abdul a hannun sa .
Ba zato suka ga Muhammad ya ciro bindiga a bayan wuyan rigar shi , ya saita daidai hannun Mk ya sake masa harbi, ?ara ya saka lokacin dayaji harbi biyu Lokaci guda , lokacin da Muhammad ya harba shi a hannun , shi kuma Ridwan a ?afa ya harbeshi , nan yayi ?asa yana kururuwar neman agajin gaggawa dan rayawu baya san abinda zai taba lafiyar jikin sa ,
Muhammad yace '' naga kanaso ka bata mana lokaci ne , shi wannan daka ri?e ai baya ?aya daga cikin mu , shi miye nasa a ciki kawai fa mata yagani yace yana so , kuma dan kar taga Rago zata aura shi yasa ya biyo mu , ko ba haka ba '' ya ?arasa Maganar yana kallon Abdul da yake ta matse matsen cinya wai kar suga fitsarin daya dade da kufce masa tun lokacin daya jishi a hannun mala'ikan mutuwa ,a cewar sa , dan Lokacin da Mk ya kama masa wuya sai ta fara nanata kalmar shahada yana mamaki , da Nazarin ya akayi duk zaman sa.
A duniyar bai ta?a tambaya ko lokacin da yake zuwa islamiya ta ina ake zare rai ba , shidai na nashi cire ran ta wuya aka fara .

Safwan dan dariya har sai da ya zube a ?asa yana ri?e ciki , cikin dariyar data kasa barin bakinsa yace , koba komai idan kana waje bazaka bari ba?in ciki da damuwa su samu gurbin zama a cikin Zuciyar mutum , kana Banu nisha?i My ?anina , Allah ya kaimu ranar bikin nan , dan Ni tuni na dade da baka Ru?ayya '' .
Su duka sai da suka yi dariya ganin sha?iyancin da Safwan din yake ma Abdul wahid .

Dady daya lura da yawan jinin da yake zuba a jikin Mk ya karasa inda bindigar ta gangara daya jefar da ita lokacin daya ji bullet , dan tissu yasa ya dauka ya sai ta wajaje biyu sa yayi harbi cikin ?orewa , maidata yayi kusa da inda Mk din yake kwance ya juya ya kalli Abba yayi masa sigina da ido alamar komai daidai .


Ba ?ata lokaci Abba ya daga waya ya kira wata number '' yace zaku iya shigowa ''
Hasken Camera ya isar musu susan da suwaye Abba yayi wa jagora da su shigo.

Tun ranar da Muhammad ya fadawa su Dady duk wani shirin sa da yadda yake tafiyar da komai cikin tsari , kwanaki shida Kafin dawowar Mk kamar yadda yace , tun a wannan lokacin Dady ya sanya idon sa akan kowa na gidan , na'urar bin diddigi a kowace motar da take gidan , duk wani daki yana da Camera da yake iya ganin duk wani abunda yake faruwa aciki da wajan gidan , ko lokacin da Muhammad yake fa?awa Safwan komai da safe duka yana ji , har shigowar su Ridwan da Abdul duk akan Idanun sa , lokacin da suka fito suna kokarin barin gidan asace , ya fito basu ganshi ba , ya jefa na'urar bi diddigi a bayan jakar baya da Muhammad ya rataya , ba tare da sun saniba , to shine har suka biyo bayan su , Dady ya fa?a wa su Abba da Babba komai har yanayin aikin Muhammad din yake yisai da ya fa?a musu ,dan kar suga yana anfani da makami suyi masa wata fassara ta daban , dan shi tun lokacin da yayi bincike akan Rayuwar Muhammad din ya gane cewa Jami'in sirri ne .
Idasa shigowa suke ,sai daukan photo suke ba ?a?a?aw tawa , sauran jami'an da suka zo tare da Dady suka shigo da wa'yannan Mutanen da Mk ya jibge a waje a matsayin masu bashi kariya , ?arfe takwas daidai Dady ya biya ta ofishi ya koma bakin aiki , ya kuma ha?a rundunar da zasu rakashi ya?i a matakin ?arshe , tare da Abba suka tafi , yayin da suka bar Baba ya kula da Gida , kira daya Dady yayi gidan Rediyo Television Anfani ya sanar dasu Akwai labari , su riskesu a hanya , to shine suka zo dan daukar wannan hamshaqin Labarin da suka samu jira daga mai girma D.P.O.
Haka suka gama su wace daya ana ta ?aukan photon Mk da mabiya bayan sa , Dady yana musu bayani suna rubuta wa , masu yin video suna yi masu yin tambaya suna yi .
wata mata wacce zatakai shekara talatin da biyar , Dagani ita ke jagorantar su tace '' yallabai da alama wannan abun daya faru ba shi ne na farko ba , nasan akwai labari , ina neman alfarmar sanin minene asalin yadda abinnan ya faru tundaga farko pls koda daga baya ne '' tayi maganar tana kallon Abba da tunda ta fara magana ya kafe ta da ido yana kallon ta , adu'a yake yi cikin ransa Allah yasa ba matar aure bace , idan har ya tabbata batada aure to shikan ya sami matar da zai aura a karan farko tun bayan rasuwar matarshi Juwairiyya.

'' Yallabai Barister ana maka magana '' cewar Dady yana masa kallon na harbo jirgin.
Abba ya dan sosai ?eyarsa kafin yace '' bakida damuwa Madam ?ofa a bude take a Kowane lokacin '' , harda su Safwan saida suka masa dariya dan suma sun gane Abban nasu ya fa?a anan , Allah dai yasa rabon sa ce .
Dady ya juya ya kalli yaransa yace '' ku tattara su mu tafi , Akwai sauran aiki dan har yanzu bamu kama dayan abokin aikin nasa ba , kuma bai mana wani bayani akan ko yanan tare dashi ko a'a , saboda haka abashi agajin gaggawa ya sami sau?i ta Yadda zai iya bu?e baki yayi mana bayani '' , duka aka fara fita dasu ana saka su a mota , wasu sun masu karaya , wasu sun suma , wasunsu ma dai da alama kamar ba nunfashi a tare dasu , dan dayawan su sun so guduwa , lokacin da ake artabon , anyi gogormaya kafin suka samu suka kama su su duka , kusa da motar Mk Abba ya tafi ya tsaya yana ?are mata kallo , babbar mota ce da yanzu yaga ana yayinta a kasar America , kuma shine shi har ya Mallake ta , suna sai sufi shekara biyu suna anfani da samfurin mota kafin a fara tallar ta anan , amma sai gashi shi atare dasu yake fara yayin mota , can kuma sai yace zai iya kam dan a yanzu shine Number daya a yan kasuwa da masu ku?in ?asar nan , shike juya duk sauran jagororin sa suke jagoran tarmu , dan akowane kamfanin dayake kasar nan yadana hannun jari a ciki , ko a kamfanin su na kayan kwali yana da kasu goma sha biyar a shiyar kamfanin , a hakan ma dan shi Hussainin ya?i yarda ne da sai ya saye kanfanin da yawo da dabara , sai dai bada sunan MK yake aiki ba , da asalin sunansa take yi , shiyasa a wancan lokacin basu gane shiba , kuma harda rashin sawa arai cewa bazai iya musu MUGUNTA ba , dan bazai iya tuna rabon shi da Ganin shi ido da ido , komai sai dai wakilin sa Iliyas yake masa .


Ganin motar a bude take '' yace Yaya ko Za'a tafi da motar nan ne ?'' ya tambayi Dady , '' Dady yace '' eh ai dama da ita za'a je Bama ita kadai ba Komai nanan sai an fita dashi ,sudai nafiso so tafi in yaso mu sai mu ?arasa yan'dube dube ko Allah zai sa mu sami wani ciga ''.

Juyawa yayi ya umarce su da su tafi ya kalli jami'i Idriss yace ka kula da Komai , akaisu asibiti dukan su , ka tabbatar da tsaro a tare dasu , dan Bama so koda mutum ?aya ne ya ku?uce mana '' .
Cikin girmamawa ya amsa da '' to yallabai '' yana sara masa kamar yadda yake a ?a'idar aikin su , girmama na sama dakai koda kuwa ka girme sa ne .


Dady ya kalli su Muhammad da suke zaune suna fira abun su kamar suna falon Momy yace '' ku taso nan '' su duka suka mi?e sai Abdul daya kasa mi?ewa , sai yanzu kunyar su Dadyn take ?ara kamasa , kusa da su suka je , Abba yace '' yawwa kai Ridwan ya akayi ka yarda yaki harbi da bindigar ka , bayan ba oda aka baka ba , baka ganin za' sami matsala '' ? , '' A'a Abba na , ai banyi Komai ba sai da Sanin Ni na ku gafara ceni yanzu haka akwai madaukin da zasu iya ganin Komai daga inda suke '' ya nuna musu dan ma?allin rigar da yake jikin sa .


Cikin jinjina da yabawa Abba yace '' gaskiya na jinjina maka sosai yarona yanzu zaka ja wannan motar kai da Safwan da Abdul , ku kaita ofishin su yaya , kafin mu isa , in yaso shi Muhammad ya tsaya tare damu anan sai mu ?o e agida '' Abba yayi Maganar cikin bada umarni.

Cike da girmamawa suka amsa , Ridwan ne a mazaunin direba , sai Abdul wahid a kujerar mai zaman banza , yaya Safwan shine Alhaji na Bayan mota , da yake dama key din motar a jikin Mk ya bari abunka da manya , sai kawai ya tashi motar suka bar wajen.


Muhammad ya riga kowa lura da wani dan
Dakalinna siminti kamar kamar murfin ramin kota da ake yi , a kasan inda Ridwan ya janye motar , nuni yayiwa su Dady da wajan da alamar tambaya akan fuskar shi , Abba ya taka har wajan yana nazarin yanayi da yadda aka yi dakalin , anan dai bauta wani ban daki ba , bare yace ko ma'adanar kashi da Ruwan wanka ne .


Dady yace '' ai wannan yayi kama da gidan kasa ko , tunda dai ba ban?aki bane kamar yadda kake hasashe '' , '' komai minene yanzu zamu gani '' cewar Muhammad daya fara kokarin daga wannan dan dakalin da ?arfin sa na matasan da suke aikin ceto na ko a mutu ko ayi rai , dagashi yayi ya ajiye a gefe , sai ga wata ?ar ?ofa ta bayyana , zancen Dady yazo gidan kasa ne anan , ba tare da neman shawara ba Muhammad ya kutsa kai yana cewa '' Dady ku jirani anan ina zuwa .


Sannu sannu yake shiga ciki , har ga Allah bai shigo da tsoron Komai ba , amma Yanzu Ganin abubuwan da yake gani sun fara fuce yadda ?wa?walwar sa zai iya ?auka , ?orangol da ?ashishiwan mutane ne , wasu a jingine , wasu a kokkonce wasu kuma duk sun wawwatse , yana tafiya yana kuka ganin yadda aka wulakanta rayukan mutane dayawa har haka , shikam wannan Mk din wane irin mutum ne , anya ma yana Sallah kuwa , dan cikakken musulmi bazai aikata irin wannan ba .

Bai tsure da lamarin ba saidai yaji an dam?i ?afafuwan sa duka biyu an rike da dan karfi , ai baisan sanda ya ?ola kiran sunan Abbaaaaaaaaaaaaaaaaaaaa
Shine abinda ya fa?a kawai ya sulale a ?asa Sumamme, yau ga abunda ya ?agawa Muhammad Hankali har ya suma , lallai Abun Babbane.
Jin ?arar kiran da yake ma Abba ne yasa da Dady

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login