Showing 3001 words to 6000 words out of 48162 words
ya kama ya dam'qa a hannun Gambo yace ku tafi Allah ya muku albarka,harsun ?an fara tafiya sukaji yace yaro nace kai na inane ?kanyar waziri yace suka cigaba da tafiya ahaka har suka iso garin su Gambo suka sauka a dan dakin sa daya,wanda yaci alwashin insha Allah a gobe sai ya kewaye gidan koda da karan dawa ne
Ahaka sukaci gaba da rayuwa ko wannan su ya rungumi dan' uwansa,kuma suka rungumi ?addarar su da tazo musu a haka
Ahaka har sukayi kusan shekara goma kafin aka haifi yin'ukun
Bayan shekara Bakwai su Husaini, Hassan da kuma Adam sun fara girma har sun fara karatu a 'qaramar makarantar primary da ke garin sedai an sami matsala dan Adam ya kasance daban a cikinsu mugune na gaske
Gashi bayajin magana ko kadan, dan ya fiddo wa mutun jini ba wani abu bane..........
A yanzu arayuwar su basuda mastala, rashi da babu kam tini suka fuce babinsu dan tin lokacin haihuwar su Hassan bayan suna suka tattara dan abinda suka samu nadaga albarkar yaran ya
Ya fara kasuwar Kayan kwali,ya ko fara a Sa'a da a?an table yake jera kayan amma yanzu babban shago gareshi
Akon a tashi asarar me rai yau su Hussaini suka rubuta jarabawar karshe a makaranta wacce da sakamakon tane mutum zai iya shiga College
Kuma a cikin wannan shekarar ne Malam Gambo ya ida ginin gidanshi a can cikin garin miryyah,ya gama komai tarewa kawai ta rage musu, shima fitowar sakamakon jarabawar yaran kawai suke jira, kuma ma an ce nanda kwana biyar zata fito
Yau ne ranar,babban allon rubutu na katako naga an kafa takaddu a jikin,dan?azun ?alibai kowa so yake ya duba ko zaiga sunansa
Awannan lukacin ne Adam ya zare jikinsa ya fice awajan ganin baiga sunan saba,yasan sarai munafuncin wannan directeur dinne(shugaban makaranta) Har ofishin sa yaje yayi masa futsara dai-dai da farashin daya saya,ran shugaban makaranta ya ?aci tini ya 'qudura aransa cewa ai se idan yana karatun ne zai kema manya iskanci ko, insha Allah shida makaranta sai dai iyayen sa su biya masa privete
Ahaka suka koma gida bawanda ya san mi Adam yayiwa darector ,suka shiga tattaran kayan ?aura dan komawa sabon gidansu, suka bar garinsu na gado
Shekaru sunja abubuwa dayawa sunfaro
ciki harda fasa karatun da Adam yayi,ba makarantar boko , kuma islamiyar ma yanzu baya zuwa a cewarsa yanzu ya girma,ko a da'can basan zuwa yake ba,bare yanzu da yake da shekaru kusan goma sha tara aduniya,har suna ya sak¨¦ Wa kansa a madadin Adam din da mahaifinsa yayi masa Yanka dashi,Yanzu *kwaro*ake ce masa,shifa yanzu gani yake daidai yake da kowa,dama baya shiga harkar yin'uwan,tini yakeda abokan da suka maye masa gurbin danginsa ciki kuma harda iyayen sa,dan sai yayi kusan sati basuganshiba
Tin abun baya damun Alhaji Gambo da hajiya habsatou
Har yakai ya fara tada musu da hankali,da badan a gida a ka haifesuba wlh da sunce sauya musu shi akayi a asibiti, a yanzu shikadai ne damuwar su, Alhaji Gambo ya zama me hali daidai gwargwado yanada dukiya mai tarin yawa duka a harkar kayan kwalin daya fara da ita Allah ya sanya wa kasuwancinsa albarka
tabbas Ubangiji Mai iko ne,shike fidda mai rai daga jikin matacce,ya fidda matacce daga jikin rayayyaye
Adam shine jarabawar su a yanzu
Haka rayuwa taci gaba da tafiya sanu sanu Adam ya zama ?an tada zaune tsaye, ya fan?are bayajin Maganar kowa
Yin ?ananun kayan mayan nan babu wanda baya sha,Adam tin kafin yakai haka ya fara kule kulan mata,matan ma baya kula masu shigar mutunci bare har ace za ai zance cikin mutunta wa
Su Hussaini suna University a zinder inda acan suke da zama sai Lokaci zuwa lokaci idan sun sami sarari,sukan ?an le?o gida na kwana biyu zuwa uku
Shi Hassan yana karantar kasuwanci ne,a cewarsa tunda mahaifinsu bai yi karatun zamani ba yake gudanar da kasuwanci,to shi zai yi karatun ta wannan fannin dan ya taimakawa mahaifinsa
Shiko Hussaini shari'a yake karanta a yanzu haka saura shekara uku ya gama,ya fito a cikakken lauya
Wannan shine burin su,kuma sun sami goyon bayan iyayen su,suna basu gudummawa da aljihunsu da kuma tunaninsu na manya na abinda zai anfanesu
Ba?in cikin Adam da abinda ya za?arwa kansa a rayuwa,da yadda yake so ta ?arfi sai ya ?atawa mahaifinsa suna a gari, wannan damuwar Alhaji yasawa ransa wacce tayi silar kamuwarsa da ciwon zuciya,adalilin Adam ya kamu da hawan jini mai ctanani,har likitan da yake dubashi idan ciwon ya tashi gareshi
A wata ranar juma'a Alhaji ya dawo daga masallaci shida ma ?obcin sa suna tafiya a gafa, dan a?a ?dar sa baya shiga mota inda har masallaci zai ze
Sallahr farillah,juma'a kai har sallahr idi da ?afa yake zuwa,a cewarsa yafi lada
Suna cikin tafiya ne suka ga wani babban mutun magiganciyanq gudu ga wasu matasa sun biyo shi kowanne da makami a hannunsa,daya daga cikin sune yayi kukan kura ya dam?oshi ji kake yum sun fadi qasa
Marin sa ya shiga yi ya ?akautawa yana cewa kai dan ubanka ogan namune zaka tserewa eyeee
Nagode wa Allah ?aramin oga bai bada umarnin a kareba,da wallahi da wannan addar tawa zan rahama biyu,shege wuya ya mari?in lema Tashi muje ko na ?allaka anan
Duk wannan abunda ake yi a gaban idon su Alhaji a kayi,
Ku bada hanya ga ?aramin oga nan yana zuwa,wata murya suka ji tana bada umarni , juyawa su Alhaji sukayi dan gani wane wannan uban ibilisan da bai maida rai a bakin komai ba,har ake cewa dan bai bada umarnin ayi sara ba,to daya bada kenan zasu iya kashe mutun ko
Innalillahi Ubangiji ka shiryar damu ka shiryi zuri'armu
Ai bai idasa adu'ar daya dauko ba ganin ?aramin ogan da suke magana
Ya sulale a ,qasa sumamme.........
Yau kwana shida kenan da aka kontar da Alhaji a asibiti yana jinya kuma alhamdulillah ya na samun sauki
Tin lokacin daya fadi bai sake sanin inda kansa yake ba se da yayi kusan kwana hudu kafin ya farfa?o,ko yanzu ma ba magana yake ba saidai yayi ta kallon mutane
Su Hassan da tun ranar da abun yafaru suka nemi excuse a makaranta su da mahaifiyarsu duke jinyarsa
Adam kan ba labarin sa tin ranar daya bada umarnin akai alhajin asibiti dan ya lura dashi tinda ya doso wajan ya hangoshi har lokacin daya fa?i ya gani kuma ya tabbatar da mahaifin nasa ne lokacin da yaransa suke cewa wlh baban oga ne
Dayake dama sunsanshi, kawai dai bashi da darajar da za'a gaida shi ne koda an hadu a hanya shiyasa shi bai wani san suba amma su sunsanshi
Umarni kawai ya basu da sukai shi asibiti,kuma suje su gayawa iyalansa cewa yana asibiti niko maman Abdallah nace to kodai shi ba dansa bane dayake cewa agayawa ahalinsa ohoo
Jiki yayi sau?i har an sallamesu daga asibiti tare da musu gargadi cewa inhar basu kiyaye abunda zai ke ?ata ran alhaji ba to lallai wata rana abun bazai yi kyau ba
Dan ko ayanzu idan ya tuna wai dan daya haifa da cikinsa ,shine shagaban yan'daba sai yaji kamar zuciyarsa zata faso ?irjinsa,haka zai yi ta istiqfari yana nema masa shiriyar Ubangiji
Bazai yi masa baki ba dan baisan inda zai kai shi ba
,Dama ya lafiyar kura bare tayi hauka
Abangaran Hajiya kuwa,hakuri ta sawa ranta, amma badan bata jin wuya ba, ita juriya kawai ta fishi, tabar abun aranta kasancewarta mace me ha?uri da kawaici
Idan tace zata sa damuwa arai to za'ayi bawan, ba ,qanin,
Alhaji ba lafiya to itama inta nuna damuwa ,su Hussaini ya zasu yi kenan
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya , al'amurra sun fara daidaita, Alhaji ya fara fita kasuwa suma su Hassan sun da?e da komawa makaranta dan suna daf_da gama karatu har anfara shirye-shiryen yaye ?alibai na wannan shekara kuma suna daga cikin wandaza'a yayen
A daidai wannan lokacin kuma Adam ya ,qara ,qarfi a harkar daba , yanzu Bama ya ala,qanta kansa da wannan ahalin kuma suma basa nemansa
YAU NE RANAR
yau ne ranar da gomnatin jaha ko ince ta ,qasa baki daya tashirya bikin yaye dalibai,wanda sukayi karatu ta bangarori mabanbanta
Anyi taro inda manyan masu ilimi na , qasa sun halarci taron,anyi ta bada kyaututtukan ban girma ga ?alibai masu ,qazo da haza,qa
Iyayen yara kowa yazo dan taya dansa murnar cikar barinsa,a ciki harda Alhaji Gambo da Hajiya Habsatu
Sun dawo gida tare da nasar da suka samu na hada digiri (Degree) a bangaren da kowannan su ya karanta
Bayan sallahr isha'i suna zaune su duka a falo suna ba iyayan su labarin makaranta sai ji sukayi an turo ?ofar ,da alama shigowa za'ayi
Hankalin su ya raja'a wajan ganin ko waye haka zai shigo ba neman izini, yan'aiki dai babu wacce take kaiwa magariba,dokar me gidan ne bayaso yan'aiki suna yin dare,daga maraice tayi suke komawa gida sai kuma gobe da safe sudawo
Ida bu?e ?ofar akayi, wazasu gani..................
Idasa bu?e kofar aka yi wazasu gani ,Adam ne ya shigo sanye cikin cikin qananan kaya,wando 3quater da riga amles, silifas ne a Qafar sa,yasa Safar hannu a hannayansa
ya daura layu a dantsan sa kamar wani dan fawa,kan nan nasa yasha kitso Arab,kai kace kan wata matar ne,
Duk ya dafe,yayi ba?i sigari ta ?oneshi,bazaka ganshi ka ce dan'ukun su Hassan ne sunfi shi haske,amma ya fisu bu?ewa
Babu annuri da has?en musulunci ko kadan akan fuskarsa,
Sallama yayi
ya Q'arasa ya zauna a daya daga cikin kujerun falon,da fasashshiyar Muryar sa yace sannunku da gida
Kusan atare suka amsa da mamaki a fuskokinsu,Hajiya rabon ta data ganshi da idonta kusan watanni uku kenan
suko yan'uwan zasu iya cewa anfi shekara rabonsu dashi,dan ko lokacin da sukayi jinyar mahaifinsu basu ganshi ba duk da shine silar kwonciyar nasa
Maganar sa ce ta dawo da kowanan su daga tinanin da yake,yace nasamu labarin kun dawo,kun gama makaranta, shine nazo in muku sannu da zuwa
Kamar a mafarki sukaji wannan magana tasa
Cikin farin cikin daya kasa boyuwa afuskarsa Alhaji yake yiwa Allah godiya a bayyane
Ganin kamar addu'ar dayake yawan yine kullum se yanzu Ubangiji ya amsa,yau gashi da duka iyalansa azaune waje daya
Ga Adam dinsa yazo cikin danginsa ya zauna har yana musu fatan alkhairi,kai gaskiya wannan abun murna ne
Alhaji ya kalli Hajiya cikin farinci yace Hajiya a tuna baya,ki bamu abinci muci yau gani ga yarana uku da ubangiji ya albarkaceni dasu
Shi dai gogan bai ce koma ba sai wayarsa daya fiddo yana dubawa jin ?aran shigowar sa?o
Suko su Hassan sai murmushi suke ganin mahaifinsu cikin walwalar data da?e da bari
rayuwarsa,
Su dama basu ?ishi ba,kuma suna sanshi,mugun halin sane basaso, alhajin su yanajin Adam a ransa shiyasa yafi kowa shiga damuwa akan lamarin sa
Share hawayan idonta Hajiya tayi tana me hamdala a cikin ranta, abincin ta zuba musu,su duka a baban tire har ita suna ci suna fira
Mafi yawan firar sune suke yinta a tsakaninsu jefi-jefi Adam din yakan dan saka baki ........
Cikin nisha?i duke komai har kusan ?arfe goman dare,Adam ya tashi da niyar tafiya kallon sa sukayi har suna ha?a baki wajan fadin ina kuma zaka
Kallon su yayi da yanayi da bazasu iya fassara shiba yace zan wuce sai wani lokaci fara takawa yayi har yakai bakin ?ofa ya juyo ya sake kollon su daya bayan daya kafin ya kuma cewa sai wani lokaci
Rufe ?ofar da yayi ,yayi daidai da a jiyar zuciyar kowanne su,babu wanda ya iya cewa komai, jiki a sayyaye su Hassan suka tashi zasu fice dakinsu
Alhaji ne yace kuyi ha?uri da dan'uwanku,kuzama masu juriya da iya tsayawa kai duk rintsi ,ku kula da mahaifiyar ku
Batada kowa sai Ni ,na dora yaunin kula da ita a kanku,dan Allah ku kula da junanku,
Hajiya ce tace wai mikake cewa ne haka ,sai kace wanda yake barin wasiyya,dan Allah ka bari,kana taryarmun da hankali wallahi
Juyawa tayi tace musu kuje ku kwonta Allah tashe mu lafiya
Da amine suka amsa suna barin falon jiki a sanyayye
Hajiya ta isa kusan kujerar da mijin nata yake ta kama hannun sa
tace abban Adam dan Allah ka kwontar da hankalinka kagafa bakada Lafiya,kuma kaji abinda likita yace inhar baka rage damuwa ba
?ara dan?e hannun nata yayi sosai a nashi yace Allah ya miki albarka habsatu, Allah ya zama gata agareki,tabbas kedin mace tagari ce,kin zauna dani alokacin da banida komai ,kinbani farin ciki,kika haifa min yara har uku,
Naso ace nasadaki da dangin ki a karo na biyu amma inaji araina kamar hakan bazai yuyuba ,dan Allah ki gafarceni ya ?arasa maganar Muryar shi tana karkarwa kamar zai yi kuka
Fa'?awa jikinsa tayi ta sa masa kuka yana cewa ka daina ban Allah ka bari , Allah maganganun ka suna bani tsoro,shuru yayi ya barta tana ta kuka ta saida tayi san ranta yana dan bubbuga bayanta har tayi shiru tana ajiyar zuciya
?agata yayi daga jikin sa yace to nabari,yanzu ki tashi kije ki kwonta ,zamu yi sabkon zuwa asibiti dan banajin da?in jikina,da to ta amsa amma badan ranta yaso ba ,bata masa musu akan komai,haka ta mi?e ta nufi dakinta,shima nashi ?akin ya fuce tare da fatan Allah ya tashemu lafiya
Washe gari
Antashi da mummunan labari agari cewa a gidan Alhaji Gambo an................
Washe gari
Antashi da mummunan labari cewa yin'fashi sun shiga gida Alhaji Gambo
Wanda har sun yi sanadin rayuwar sa''''''wannan labari ya girgiza duk ilahirin garin miryyah gaba daya
Ba mutuwar alhajin bane tashin hankali ,tunda shi yanzu nashi ya ?are
Ba Kamar da aka nemi
Hassan a karasa,yan sanda sun iso gidan tin lokacin da labarin yakai garesu
Bincike ya biyo takan kowa a gidan ,,sunyi goje _goje da aune_aune inda aka kira ambilance aka ?auki gawar Alhaji dan Kaita mutuware
A cewar su sai bayan an gama bincike za'ayi sutura,jami'in da aka dorawa alhakin kula da kes dinne zaune yasa su Hajiya da Hussaini a agaba sai me gadi da kuma yan'aikin gidan guda biyu
Wanda isowarsu kenan
Ita dayar dayake ma'abociyar sauraron Radio ne taji a sanarwa, wacce ake yi bayan ida labarun safe na D.w Hausa''' dayar kuma ba tada labari sai bayan tazo ta isko mutane yan'ganin kof cike da ?ofar gidan
tambayoyi yake musu daya bayan daya kowa yana bashi amsa da abunda yasani
Ahaka har ya iso kan Hussaini wanda kallo daya zaka masa kasan yana cikin tashin hankalin daya kasa ?oyuwa akan fuskarshi
Yace niban san mizance ba abubuwa duk sun koncemin
Ajiya da dare ina tare da duka family na har wanda baya gidan a jiya saida yadawo,,,Amma yau gashi na rasa Abba na da dan'uwa ya karasa Maganar yana kukan da bai sami zarafin yinsa sai yanzu
Ha?uri ya bashi tare da tunatar da shi muhimmancin karbar ?addara a wanjan cikakken musulmi wanda yayi imanin cewa ba maiyi sai Allah kuma duk abunda yayi shine daidai
?angaren da Hajiya take ya kalla ya da?e yana nazarin yayinta kafin yace Hajiya kozan iya sanin abunda kika sani game da mutuwar mijin ki da kuma ?atan yaranki
Shuru tayi masa bata ce komai ba ,dama tun safe batayi magana ba
Haryanzu ta kasa yarda da abunda idanuwanta ya gani,hankalinta ya gaza dauka,dama a ajiya
da alhajin yake ta zantuttuka kenan wasiyya yake bar musu
Innalillahi wa inna ilaihi raji'rne, nan take ?o?olwarta tashiga tariyo mata abunda tagani da asubar yau wadda tazame mata ba?ar ranar acikin ranakunta na duniya da bazata taba mantawa da itaba.................
Da asubar tashin ta kenan tayi alwala harzata tayar da Sallah sai kuma ta fasa tunawa da tayi Alhaji ya ce mata bayanjin da?in jikin shi
Gashi baizo ya tada itaba har Lokacin sallah ya wuce Sanin ba halinsa bane ,yasa ta fasa tada sallahn ta wuce dakinshi
ko ajiyan bataso ta barshi shi kadai ba ,a santa su kwana tare kamar yadda suka saba
Amma sai yace mata taje ?akinta ta kwonta'''
Bata ta?a masa musu ba shi yasa a jiyan ma bata masana
Isowarta kofar dakin nasa daidai da ?are zacan zucin datake yi tura kofar dakin tayi da sallama a bakinta mi zata gani Alhaji ne kwance cikin jini yayi rubda ciki
Da gudu ta ?araso tana fadin Alhaji mi yasameka ciwon zuciyar ne yakai har kake zubda jini
Maganar datake yi ce ta katse lokacin da taga inda aka harbeshi a sharen cikin shi
Wani irin ?ara ta saki tana kiran sunan Allah
Cikin ficewar hayyaci,,,,, Hussaini da fitowansa kenan daga bayi yayo alwala shima yanzu ya tashi,bai san yau miya shiga kanshi ba yayi ta bacci har bai san anyi sallahn asubahi ba
Lokuta dadama shiyake tashin Hassan ,amma shine yau daya rigashi tashi bai tashe shiba yayi ficewarsa ko,,zai rama ne
Yana alwala yana mitar Hassan bai tashiba
Daidai fitowar sa yaji kamar ana kuka kuma indai kunnansa yaji daidai to Muryar mahaifiyarsu yake ji
Fitowa yayi daga dakin cikin gaggawa harya nufi dakin hajiyar tasu ,yaji kamar daga dakin Abba kukan yake fitowa
Dakin yanufa yana ta sa?e_sa?e arai kar aje ko wani laifin Hajiya tayima Abba ya kasa ha?ura duk da yasan ba halinsu bane
Tun suna yara baza'su iya tuna lokacin da suka ga suna koda musu ne bare har tai ga masa laifin dazai doke ta
Bubbuga ?ofar ya shiga yi,shuru ba'a amsa ba ?ara bugawa yayi da ?arfi amma ba amsa sai ?aran kukan daya ?aru,,,,,turawa yayi ya shiga ai dagudu ya qarasa in da Abba yake kwance tallafoshi yayi yana kiran Abba katashi mi yasameka
A rikice ya kalli Mahaifiyartasu yace umma mita sameshi cikin kuka ta nuna mishi cikin Alhaji wanda shi bai ma luraba
Arazane yace kamarfa harbinsa akayi gyada masa kai tayi,agigice ya tashi yana dube dube wai kozaiga wanda ya harbi baban nasu,cikin kuka take masa