Showing 30001 words to 33000 words out of 48162 words

Chapter 11 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah

10 Jul 2024

3357

yana ?o?arin ?wace sitiyarin motar da wannan bawan Allah ya ke tu?awa, da har Baffan yace yabari zasu nemi abun hawa , sai yace ai ba zai yiyu ba, kawai su shiga ya kaisu, duka a cikin motar suke wannan dramar.


Ganin yana shirin sawa suyi accident yasa Alhaji Issiyaku ya ja burki ya tsayar da Motar.
Fitowa yayi ya jingina da jikin Motar shima Baffa ya fito, daga ?arshe daya ga sun barshi shi ka?ai shima sai ya fito yana rarraba ido, ko zai gane inda yake a Yanzu ,
Alhaji Issiyaku yace wa Baffa '' amma dan Allah idan bazaka damuba zan tambaye ka ,
Yace '' karka damu ina jinka,
Yace '' dan Allah ko dama yaronka yanada ciwon hauka ne , naji yanata wasu maganganun da bansan inda suka nufaba, bansani ba ko kai kana fahimtar a bunda yake nufi, ya ?arasa maganar yana tsare Baffa da ido danjin amsar da zai bashi .
Baffa yace Wallahi a'a Lafiyar sa qlau kawai inaga ya dan bugune akansa sanadin haka wata ?ila ya tuna wani abu na daga Rayuwar sa ,
Gyara tsayuwa yayi yace '' Kamar yaya a yadda naga kun taho a tare kai dashi, inma ?anka ne ko kuma sirikin ka , ko wani makusancinka , dan Allah ko zan iya sanin wani abu daga Rayuwar ku, wallahi zuciya ta tashiga wani kokwonto.
Baffah yace Wallahi Labarin da tsawo kaga bazai yiyu mu tsaya a hanya muna zance ba gashi da alama ba zai iya jurewa ba , ya kalli inda Tijjani yake yace zai
Saidai idan zaka bimu muje gida, ga shi kuma dare tana shirin yi, komawa suka yi cikin Motar har Tijjani daya zama kamar wani zararre sai dube dube yake, har suka isa ?ofar gidan Baffa lokacin har anyi Sallah magriba , basu zauna ba sai da suka gabatar da sallah , kafin aka shimfida musu tabarma a tsakar gida inda Baffa ya umarci da Umaima ta fito da yara nan suka fito suka zauna a ?ayar tabarmar da Muhammad ya shinfida daga gefe ?aya
Zama sukayi suna sauraron Baffa .


Sashen da Tijjani yake ya kalla yace abubuwa dayawa sun faru , amma Kafin kaji komai inaso insan ko kai waye , Asalin ka da kuma cikakken sunan ka ,
Shuru yayi kamar ba dashi a ke magana ba .

Gyara zama Alhaji Issiyaku yayi yace '' muna jinka dan Allah kayi magana duk na za?u inji kace wani abu dan inga ta inda hasashe na zai tabbata .
Kamar ba zai yi magana ba sai kuma Yace '' suna Hassan Gambo, mu uku mahaifin mu ya haifa tare da mahaifiyar mu m
Nan ya shiga basu labarin rayuwar su da yadda aka akashe mahaifin su yana kuka kamar wani ?aramin yaro.


Sosai Alhaji Issiyaku ya ?ore shi da ido yana kallon shi yace yadai tabbata kai dan gidan mai gidana ne , tun lokacin dana ganka nake tuna a inda nasan fuskar ka , Alhaji Gambo mutunen kirki ne
Har yanzu ina ci daga arzikin sa , dan ni nake kula da sashen kasuwancin su na nan Garin miryyah gaba ?aya , ankashe shi har a cikin gidan shi , kuma har yanzu Banji ance an kama shi ?an nasa wanda da sa hannun sa aka yi aika aikar .

Umaima da su Muhammad suna zaune suna ji sai dai su Humaira ba lallai su gane inda zancen ya nufa ba, Muhammad kam tunda suka fara magana yake kallon bakin kowannan su , kuma tuni ya copie duk maganganun su a cikin kwakwalwar sa, dayake yayi wayo sosai yanzu haka yana aji biyu a secondary , kuma yana ?o?ari sosai .


Kallon Hassan Baffa yayi yace lokacin dana sameka a daji da alama yadda kai akayi , nan ya bashi Labarin duk abunda ya faru, har Auren sa da Umaima da yaran da suka haifa ga kuma wani cikin a jikin ta .

Mamaki sosai Hassan yake dajin wannan labari mai kama da almara wai shine ya rayu a wani waje na daban , kuma yayi aure harda ?a?a , Allah mai iko ?adirun alaa man yasha'u,
Kallon yaran yake da kuma matar sa , sai yaji ?aunar su mai tsanani ta kamasu, ya ?ude hannun sa yana musu alamar su zo inda yake , da gudu su Humaira da Hafsat suka shige jikin Baban nasu , shima Muhammad kusa dashi yazo yana share ?ar ?wallar data taru masa a ido na tausayin mahaifin nasu itama Mama kukan take jin labarin mijinta a bun alfaharin ta , Hassan ya kai a soshi ta kowane ?angare , kallon ta yake yana yabawa da kyawun ta .

Alhaji Issiyaku yace dan ya tuna koshi waye ba shi yake nufin zai koma cikin ahalin sa yanzu ba a'a ,
Yanzu Hussaini yana zinder da zama yajima da barin miryyah har mahaifiyar ku ashekarar dayayi Aure,
Cikin Murmushin farin ciki yace '' ashe dan uwana yayi aure , Allah mai iko,
Eh yayi aure harma yana da yarinya daya bazata huce sa'ar su wannan ba ya nuna su Humaira ,saidai iyalin nasa ta rasuwa yanzu shekara hudu kenan ,
Nan ya bashi Labarin dan abinda ya sani dan gane da ahalin gidan Alhaji Gambo mai mutuwa.

Tun daga wannan ranar alhaji Issiyaku yake kula da rayuwar su bamya nawa Baba jari ya fara harkar kasuwancinm yana bin kasuwannin ?auyuka ,

To a wannan lokacin aka haifi mai sunan Gambo suna kisan sa da Amir, sai mai bin bayansa Usmanu sai kuma yan biyu Hassana da Hussaina sune ?anana.


Alhaji yaci gaba da kula da karatun Muhammad har yakai matakin lycee .
Zuwa wannan lokacin ya gama neman su inda su Abba suke , da taimakon Alhaji Issiyakun.


Baffah ya gama basu labarin yadda aka yi ya ha?u da Hassan har suka zauna tsakanin jika da kaka ,
Kabbara kawai Inna lami take tana tuna lokacin da mutanen ?yauyan su suke yiwa Hansai gorin rashin dangi, a yau ga mahaifin Hansai agaban ta gaskiya taji dadin wannan al'amarin, a bayyane take Maganar kowa yana jinta
Tanayi tana marma?e kamar tana gaban mutanen ?auyan.


Can Muhammad ya nisa yace ''
Lokacin danaji Labarin rayuwar mahaifina nashiga tsananin damuwa da tashin hankali, amma a lokacin babu Abinda zan iya yi saboda ?arancin shekaru na, na dage ina ta karatu tu?uru dan cikar wani muradi nawa.


A shekarar da ya fara University a nan Garin Zinder, a lokacin ya fara neman dangin Bana, ba wani wuya sa samu dan a yanzu ko a ina ansa Abba.


Na shiga gidan Abba a lokuta mabanbanta, a macayin ?an aike , dan gyaran pampo, dadai sauran su, tun a lokacin danaga Maryam naji ina santa har cikin raina , so bana dan uwantaka ba a'a,
so irin na aure burina a kullum bai huce in mallae ta a matsayin matar aure na ba ,
Kuma har iyaye na sun san da haka ,dan bana ?oye musu abu ko ya yake , shekaru biyar kenan dana fara bibiyar Maryam da duk wani shige da fice nata , sau kusan uku ina kare harin da ake kai mata batare da ita kanta ta saniba.



Ya kalli sashen da Maryam din take yace '' idan zaki tuna wani lokaci motarki ta tsaya abakin hanyar ki ta dawowa gida Daga makaranta, wani mutum yazo ya yazo y
Da rufaffiyar fuska ya duba miki motar ta tashi , to nine a wannan rana nasha matukar wahala a hannun wasu mutane wanda na lura suna farauta Rayuwar ki , tun daga nan na fara binciken sa kai dan gane da dangina, nan na gano binciken da su Dady da Abba suke yi , na kuma nemo na kuma kama biyu daga cikin wa'yannan da suke bibiyar rayuwar ki.


Saida na azabtar da su sosai kafin suka bani bayanin cewa ogansu suke yiwa aiki, kuma suma oda kawai yake basu , basu san koda fuskarshi, tashi hankali na ya ?aru jin abunda saka ce na tambaye ya akayi suke yiwa Wanda basu saniba aiki, sai suke fa?amun cewa shine yake kiran su yanada number kowannan su, idan ya fa?a musu aikin da zasu masa in sun gama ya biya su ta hanyar tramsfer, Wayoyinsu na kar?a na shiga bincika wa amma ban samu wani abunda ?ara mini haske ba .


Lokacin da Dady ya nemi da daya daga cikin yaran aikin sa yayi masa bincike akan wata number , sai na antayo a matsayin wanda zai yi aikin , dayake ina musu kutse a wayoyinsu daga shi har Abba , duk da sun dauki matakan kariya dan gudun irin hakan, amma sai da nayi Nasarar ha?a wayoyinsu da nawa , a lokacin danaga sa?on sai nagane marubucin sa?on dayane dana wayar wayanca mutanen dana kama .


Sosai na shiga bincike akan ma'abucin rubuto da wannan sa?on, har nayi Nasarar gano shi da asalin number shi da kuma ?asar dayake , duk Bayan tafiyar su Dady India , bisa jagorancin Alhaji Issiyaku na dawo da iyayena nan kusa dani a yan watannin nan Saboda tsaro, suna zaune a wani madaidaicin gidan da baka ta?a tunanin akwai dayan mutane har haka acikin saba.


Nan nafara kutsa kaina awajan wannan mutumin da ya tarwatsa farin cikin ahalina ,da bai wani kula niba, daga baya sai ya fara yarda muna dan magana dashi amma ba yawa , dan bai fiya doguwar magana ba , saboda bai yarda da kanshi ba , da ala'mu wani babba ne a ?asar nan, yana yi da magana da kuma izzar sa koda awajan magana ne , ina tunanin shine Oncle Adam din mu wanda ya fita Zakka a wannan family namu.


Nasami kusanci dashi ta yadda har ya yarda zai bani aiki , bayan na tambaye sa da kwana uku, duka abunnan da ake saidai shi ya kirani, amma Ni koda nakirasa baya fita ,
Ya bani aiki akan alhalin marigayi Alhaji Gambo mai kayan kwali, kan in hado masa kan Dady da kuma Abba, zai biyani ko nawa nake so, ya turo mini Bayanan su da inda zan same su , na amshi aikin da hannu bibbiyu, ganin nasarar da take tun karomu yasa na kasa fa?awa kowa wannan maganar na ?ara ?aimi wajan ganin komai yazo mana da sau?i, na daukar wa Dady alkawarin zan kula masa da komai , kuma zan cigaba da bincike har su dawo, nayi mamakin yardar da Dady ya ?auka ya bani , ashe shuka b
Nakeyi a idon ma?arwa, yasan Komai game da rayuwa ta, gaskiya ina jinjina ma Dady sosai da zuciya da kuma ?onjin sa yake bamu gudummawa batare da mukan mu mun sani ba, madallah da uba nagari agaremu baki daya , ya da?a na kallon mutanen falon da murmushi akan fuskarshi.


Dady yace yanzu aiki ya zama ya kowa da kowa Muhammad, tunda munyi a boyen mu biyu kadai bamu sami nasara ba , to Yanzu zamu ha?a ?arfi da ?arfe wajan ganin bayan ma?iyan mu, gani ya nuna kansa da yatsa, ga Hussaini, Hassan, Safwane,
ga kai ''ya nuna Muhammad, ga Ridwan ga sauran iyayen mu maza , ga matan da kowa yanada ilimin da Ai bamu gudummawa da kuma shawarar yadda zamu ya?e su a wannan ga?ar.


Kowa ba falon yayi shuru yayin da yaran cikin su suka da?e dayin bacci, kowa yana yaba namijin ?o?arin da su Dady da Abba suka yi, Safwan yayi shuru yana Mamakin ?wa?walwa irin ta Muhammad, ta ?a?a ya ha?a duk wannan da karatu da kuma lokacin aiki gaskiya ya jinjina masa ,dole ne ko ba yanzu ba Maryam ta so shi, dan yanada kolitin da duk wata mace zataso tayi rayuwa a tare dashiba, ya gama tunanin kawai zai ha?ura ya nemi wata, tun da ita Maryam din na rabon sa bace tun da can,
Kallon sashen da Muhammad yake yace '' ka bamu labari amma bamuji kace ga aikin da kake a halin yanzu ba ,
Kallon sa Muhammad yayi ya kashe masa ido daya kafin yace'' wannan sirri nane Brother kawai ka manta.


Duk akan idanun Dady saidai bai ce musu komai, yayi murmushi ganin sha?iyan cin
Da Muhammad yayi wa Safwan din ,
yace '' nayi magana amma banji kunce komai ba, ya kalli sashen da su kawu suke zaune sai yaga daga shi har Baffan sai gyangyadi suke abunka da tsohon rai, dariya Abba yayi shima sai yanzu ya kula yace'' gaskiya dare yayi ku tashi kowa ya tafi ya kwonta zuwa gobe sai mu ?arasa maganar
Yaci gaba da cewa nasan gidan nan zai ishemu mu duka mu zauna, dan Ni dan'uwana ginin mace hu?u yayi yayi maganar yana kallon Momy .


Dariya sukayi su duka har yaransu Momy tace '' kaidai Hussain bazaka girma ba Allah kuwa , to ai Dady ya girma inashi ina wani aure a Bayan nan , kuma shima yasan daga ni ba ?ari , dariya suka kuma yi su duka , kawu da dariyar su tayi sanadiyar tashin shi daga barcin daya fara yace'' kunji ko mukam a bamu wajan bacci idan ba so kuke ku fa?o daga kujerar nan ba, dariya Safwan yayi
yace '' kace gagin bacci gareka aboka to ku tashi kowa akaishi masaukin sa.


Cikin mintinan da basu fi goma sha biyar ba suka kwontar da duk mutanen gidan ya rage daga Dady,Abba, Safwan, Muhammad da kuma Ridwan,
Sabon miteeng suka soma akan al'amarin Ridwan yace'' Abba Ni aganina KUBAN izini inkai Maganar wurin ogan mu kunga abun sai ya zo mana da sau?i, kafin Dady yayi magana Muhammad yace '' babu amfanin yin hakan, na gama komai ayanzu haka ya bani tabbacin biyu ga wata november zai shigo qasar nan , na bashi tabbacin zai tarda komai ya kammala dangane da aikin daya bani kuma yaji da?i dan yace ma zuwa gobe zai aikomin da address din inda zamu ha?u dashi.


Abba yace '' to ai yau ashirin da biyar ga december kunga kenan saura kwana shida ya shigo kamar yadda yace ,
Safwan yace '' eh hakane to ai sai muyi amfani da zuwan nasa mu ai watar da ?udurin mu ko ?


Dady yayi ajiyar zuciya yace Allah dai yasa ba Adam bane wannan *Mk* zango samun nutsuwa idan ya kasance ba shi bane , wlh banajin da?i ace akan daya daga cikin dangin mu muke wannan zaman.
Abba yace '' niko zanyi Farin ciki idan har ya kasance shine, wallahi da sai anyi Shari'a da kuma mafi munin hukunci akansa.
Muhammad '' yace ai nariga dana tsara Komai tunkafin ya aiko mini da address din Ni na da?e da samowa, G.Z.J shine asalin gidan da yake duk wasu miyagun laifukan shi acan , nasha wuya kafin na sami bayanai akan wannan gidan , hankali ya tashi lokacin dana gama gane Ma'anar kalmar G.Z.j ashe hakan yana nufin Gidan.Zubda.Jini, naje har wajan cikin cikin Sar?a?iyar Duwatsu , acan cikin wani ?auye da ake kira Rigar ?aure anan ne suke da wannan gidan , naje har wajan amma haka na dawo dan babu wata hanyar da zaka gane akwai wani gida a wajan dan duka wajan a mamaye yake da itatuwa da Sassar?un Duwatsu , ba yadda zamuyi muyi Nasarar Shiga Wajan sai dai idan shi ya Mana Jagora Wajan isa har inda yake.
Mu jira zuwa nan da kwana shidan ina mai Tabbatar muku a Wannan karon sai sun shiga Hannu dan ha?an ba naku bane Dady namu ne a yanzu , ku kungama naku insha Allah a wannan karon namu ne .


Abba yace '' ba shakka kayi ?o?ari sosai Muhammad ka Mana Bazata, Allah ya Muku Albarka , ya ya bamu nasara ya Dawwamar da Farin cikin a rayuwar mu da ta iyalan mu,


Amine ya Rabbal izzati gaskiya naji da?in yadda na riskeku, da iyalan namu baki daya , Husaini da iyalinka ta Rasu sai kawai ka?iyin Aure , ai ba'a haka da kayi wani Auren ai yanzu dana isko yan' dagoy dagoy koh ? '' cewar Baba da yake kallon sashen da Abba yake .


Dady yace ai insha Allah daga wannan Matsalan ya fice zai fito da wata in masa aure, idan kuma bai Fiddoba, to nida kaina zan fito masa da ita , dama akwai wacce na da?e ina Tunanin ha?a shi da ita kawai Hankali ne bai kwanta ba .


Kusan a zaune suka kwana Suda ?a'?ansu Maza suna ta fira da tsara yadda zasu aiwatar da komai a tsare.



Washe Gari
Washe gari
Haka suka tashi cikin farin ciki, kasancewar su a waje daya
Kawu Yayi musu sallama akan zai koma gida, nan Baffah yace bazai bar shi a gidan Yara ba, har gida safwan da Muhammad suka kaisu, akan hanyarsu ta dawowa gida suna tafiya suna fira , nan safwan yake cewa '' nayi mamaki lokacin da kace shekara biyar Kenan daka fara San Maryam, ni n'a fara santa Santa tun tana yarinya, saidai ban fada ba , ita kanta ban taba gaya mata ba, Ashe Kaine mai rabon " 6a karasa maganar Yana kallon bangaren dama Dan Kar Muhammad din ya lura da yanayin canzawar fuskar shi.



Tsayar da motar Muhammad Yayi lokacin da ya gangara bakin titi, ya juyo ya Kalli safwan da idanun sa daya gama canza kala yace " yaya safwan muyi mqgana ta fahimta dakai, wallahi inada tsananin kishin abinda nake si, KO yanzu danaji ka anbacin sunan ta wallahi sai danaji kamar zan mutu,
Bazan iya jurar hakan musamman daga gareka , na dade da lura kana San Maryam Amma yanzu Allah ya Riga da ya Nuna nine mai rabon, so Dan Allah kayi hakuri kq nemi wata ,
Idan ma a gidan ne kake so ka samu ai ga wasu kannan Namu nan ba sai ka zaba tsananin Humaira da Hafsat ba , Dan Allah kayi hakuri idan har maganar Danayi ta Bata maka rai , kawai sa kasa controling Kaina ne shi yasa " ya karasa maganar Yana kokarin tayar da motar .
Safwan ya kalle shi yace '' ka jira ai bamu gama magana ba , tsayar da tada Motar yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login