Showing 39001 words to 42000 words out of 48162 words
Chapter 14 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah
yayi Hanzarin ciro ?ar ?aramar Bindigar dake jikin ?ugunshi ya kalli Abba yace '' ka jirani anan Bara na shiga '' , cikin gaggawa ya kutsa kai cikin Gidan ?asan , tashin hankalin Dady ya kusa ya zarta na Muhammad, ya jima yana aikin Dan sanda, amma bai ta?a Gamuwa da da irin wannan Abubuwan ba sai yaunzu , ?ashishiwan mutane yake gani agaban sa , innalillahi duka wannan aikin mutum ?aya ne, yake wannan ta'asar?, kuma a cikin ?asar sa , a ?asar tasa ma a Jaharsa , Gaskiya awannan ga?ar yaga Kasawar su , da suka kasa Gano da wannan Mutumin na Tsayin Shekaru.
?araso yi har Tsakiyar Dakin dayake ta wani irin ?arnin jini daya gama kamaw ya Tsaya a cikin sa, Dube dube ya shiga yi dan Ganin ta inda zai ga Muhammad, amma bai ganshi ba , daya ke bai kalli ?asan gaban sa ba , kiran sunan Muhammad ya shiga yi yana wawwaigawa , nan shima yaji an ri?e masa ?afa , Cikin dakiya da jarumta irin na Mazan fama ya cije yana dubawa dan ganin Abunda ya ri?e masa ?afa, saita bindigar sa yayi yana kallon ?asa, wani Tsohon Mutum ya gani Fuskar sa duk Gashi ya baibaiye, ba Gyara, ga duk Furfura ta ko ina , nan take wani Tsoron ya kuma kama Dady, tunawa da yayi har Yanzu baiga Muhammad ba , yasa ya dake ya ?ara wa wannan Halittar Bindigar a kansa yace '' ka sakar mani ?afata, waye kai , Mutum ko Aljan, kuma ina Yarona daya Shigo Yanzu, ka fa?a Mani ko na Harbeka yanzu!'' Dady ya jero masa Tambayoyi a Jajjere .
Saka masa ?afar yayi ya tashi Zaune jin ba Muryar Mugunsa ba ce , cikin Dasashshiyar
Muryar sa Wanda ta Da?e ba'ayi Magana da itaba Yace '' Sorry ai nayi Tunanin Munir dinne,
Mugu Munafuki, a yau nayi Alwashin idan ya Shigo wajan nan ko ni ko shi , Please Kafa?a mini kai waye , ko kai ma ya kawo ka nan ne dan ya Rufe Babun Rayuwar ka?''.
Zuwa wannan Lokaci tuni Dady ya kunna Fitilar wayar shi, ya ?ure fuskar Mutumin da ido yana so ya Gas?ata
Zuciyar sa data da?e da sa?a masa cewa wannan Adam ne , dan ya ida Tabbatar wa yace '' kafin na baka Amsa inaso insan Inda yarona yake '' , nuna Masa inda Muhammad yake kwance a ?asa yayi yace '' ga dai wani can daya Shigo na ri?e masa ?afa , nayi Tunanin Mk ne , to inaga yaji Thoro ne sai ya suma , zan zuba masa Ruwa ne naji Shigowar ka'' , ai Dady bai gama jin Abuda yake fa?a ba yayi kan Muhammad yana ta taka ?ashishuwan mutane da ?afarsa, dayake yana sanye da Takalmin sa Ha?e da Iniforme na Yan'sanda, Tun da zasu fito da Abba ya saka su , suka biya ta Ofishi yakoma bakin Aiki.
?arawa yayi yana Jijjiga Muhammad da iya ?arfin sa, yana kiran Sunan sa cikin Tashin Hankalin rashin tashin Muhammad din, Mutumin nan ne ya tashi ya nufi wani Bangare , ?ar tafiya ka?an ya shige wata ?ar kwanah , can ya fito da wani dan kwano a hannun sa ya tunkaro inda su Dady suke .
Ruwane a kwanon ya shiga yayyafa ma masa, Ajiyar zuciya ya sauke yana bu?e idanunsa a hankali yana kiran sunan Baba '' , Dady yace '' gani a kusa dakai Muhammad fatan kana Lafiya ?'' , '' Dady kaga abunda nagani kuwa , ?ashishiwan mutane nake gani har yanzu a idanuna, dama Akwai irin wannan Gidan a ?asar nan , kuma ace mutum dan Adam ne yake wannan ta'asar duka , Dady ina Duniya zata kaimu '' Muhammad ya ?arasa Maganar Hawaye suna bin gefen Fuskar shi .
Dady yace '' ka tashi Muhammad ai harda Mutum mai rai a wajan, shine ya kama maka ?afa daka Shigo '' ya fa?a yana nuna masa Dattijon da yake tsaye yana kallon su .
Daidai da shigowar Abba wajan , dan ya gaji da jiran Fitowar su.
Nuna shi Abba yake yi da Yatsa yana ambaton sunan Adam , cikin Firgici Muhammad da yake kwance ya mike tsaye Dady bakin sa ya?i Rufuwa yace '' dama tun ?azu nake kokwonto ko shine Adam , ashe dai shi?in ne , Allah mai iko ''.
Sadda Kansa ?asa yayi yana mai ha?e mai jin Kunyar Abba, dan komai zai fa?a bazai iya fidda kansa daga zargin da kowa yake masa akan Rasuwar Mahaifin nasu, ?asa da Muryar sa yayi kansa a ?asa yace '' ina Mamana ?'' , nasan bazan Tambaya da Hassan ba, dan agaban sa aka masa illar da ba lallai yayi rai ba , yana kallo aka jefar masa ?an'uwaa Dajin uban giji, a lokacin Bashida Damar da zai kare koda shi kansa ne ,bare ya kare ajalinsa, yana kallo aka kashe masa mahaifi har lahira, bazai ta?a yafewa Mk , dazai sami dama sai ya ?aye masa Fatar jikin sa da ransa.
Abba ya kalleshi kallon tsana yace '' ai dama saidai ka Tanbaya da Hajiyar kawai, itama a lokacin dakuka aikata Mummunan Aikin ku nasan Allah ne bai Hukunta Lokacin ta yayi ba ,da har ita zaku ha?a ku kashe Saboda cikar wani Buri naku na daban.
Adam idan har ya Tabbata kaine ka kashe mana Mahaifi da Hannun ka , to wallahi sai kaga irin Hukuncin da zan Daure ka dashi.
Kuka yake Sosai har kafar sa ta gaza Daukan Gangar jikin sa , yayi ?asa yana kuka mai Tsuma rai.
Gyaran Murya Dady yayi yace '' duka wannan ba Maganar nan bace, kamata yayi mu tafi gida sai mu zauna ayi zance na fahimta'' , '' Wallahi wannan Mugun bazai bimu Gida ba , salon ya kuma ga yadda zai cutar damu a karo na ba adadi'' Abba yayi magana cikin mugun ?acin rai.
Cikin kuka Adam yace '' ka mini adalci Hussaini, nasan Ni mai laifi ne , amma ku Saurare ni na Fa?a muku uzuri na dan Allah '' ya fa?a cikin kuka yana hade Hannayan sa biyu a guri daya alamar ro?o.
Nan Abba yaji Jikinsa yayi sanyi sosai, dan abunda kaga yasa Adam kuka to mai ?arfi ne, mutun ne mai ?ye?asashishiyar Zuciya tun suna Yara , bazai tuna abunda ya ta?a sa Adam kuka tun suna yara ba .
Dady ya kalle cikin Tausaya wa yace '' kufice muje dan Allah , insha Allah ai komai yazo ?arshe'', tunda har Allah ya bamu ikon kama shi MK din a wannan ga?ar.
Cak ya Tsayar da kukan da yake yi , jin abunda Dady Dady yake cewa wai sun kama Mk , amma abun da Mamaki sosai , bai ta?a tunanin a irin wayon sa zai bari a kamasa ba, sai dai Allah baya bacci, gashi ya kawo masa Danginsa har inda yake Batare da yasha wahalar naman suba.
Gyada masa kai Muhammad yayi yace '' haka ne tabbas a yau mun kama Mk , yanzu haka yana Hannun mu , da rabon zamu ganka nema har muka Shigo nan'' .
A yau
Adam ya sake yarda da Girman Ubangiji sai iko da kuwa da komai , mai yin komai a Lokacin daya so , Alhamdulillahi alaa Kulli Halin.
Dady yace '' mu Tafi Lokaci yana ?ara ?urewa Barister ! '' ya fa?a yana kallon Abba.
Fitowa suka yi daga Gidan ?asan suna nufi Hanyar fita , Adan yace '' ina zuwa '' ya fa?a tare da komawa cikin gidan ?asan da Sassarfa, kowa a cikin su saida tayi Mamaki da yake irin wannan Tafiyar yana nuna ?arfi kamar wani Matashi mai ji da ?urujiya da Jini a Jika.
Can Tsawon mintuna biyar ya fito ?auke da ?aton bahu a Hannun sa , Tarbar sa Muhammad yayi da nufin a amsa sai yace ya bari bazai iyaba, ?ar Dariya Dady yayi yace Adam kar ka maida mini Yaro baya , da Jami'in Tsaron al'umma kake Magana'', Cikin jinjina Adam ya mi?a ma Muhammad Bahun yana ?are Fuskar shi da tafin Hannayan sa Biyu, ji yayi idanun sa sun kasa Daukan Hasken Ranar da yayi Shekaru bai Ganta ba.
Sosai yaso jurewa amma ya kasa, ji yake kamar idanunsa zasu fa?i ?asa tsabar zafi , Dady ya lura da Hakan sai ya kama Hannunsa, wani irin tauri yaji kamar ya kama Dutse, ?ara ri?e Hannun yayi sosai ganin yana layi kamar zai fa?i, Dady yace '' Hussaini ina Ganin fa kamar yana da Matsalar Idanun , kafafa yanda yake kare idon shi da hannu'' , Murmushi Adam yayi idon shi a rufe Kamar Makaho yace '' yana ?aya daga Dalilin da yasa na kasa Komawa Gida na tsayin Shekaru , Mk ya Mk ya Kasheni da raina, shekaru Goma baya sai da nayi Ko?arin dana fito daga Gidan nan, amma rashin idon yasa na koma , Sanadiyyar zaman da nake yi cikin Duhun ?asa , yasa Idanuna suka kasa Daukan Hasken Rana ,a ranar nayi kuka kamar zan mutu, badan nasan Hukuncin wanda ya kashe Kansa ba, da tuni na bar wannan Duniyar '' ya ?arasa Maganar da karyayyiyar Zuciyar sa da ta gama zama ta Salihan Mutane tun Ranar da aka Rabashi da kowa nashi.
Abba yace '' kar ka damu insha Allah kamai zai zo da sau?i da yardar ubangiji '' , shima kama ?ayan hannun nasa yayi suka saka sa a Tsakiya , Muhammad yana gaba da Bahun da Adam ya bashi ya ri?e, Motar da su Dady suka zo da ita acan dan nesa ka?an da wajan yakai ya kasa , Lokacin su Abba suka iso , bu?e musu ?ofa yayi , Dady da Adam suka shiga Gidan baya, shi kuma Abba ya zaune a kusa da Mazaunin Direba, juyawa Muhammad yayi , ya hangi mafi munin Gidan daya ta?a gani a rayuwar sa ta Gidan Duniya, har zai shiga Motar sai kuma ya fasa , yaji idan bai ?arasa Aikin sa Kamar yadda ya tsara to bazai samu Nutsuwar Zuciya ba, dan takawa yayi ka?an ya Matsa daga jikin Motar, jakarsa ya sauke daga kafa?ar sa ya fito da tanadin da ya yi wa wannan lokaci da kuma wannan Gidan, batare da Neman Shawarar su Dady ba yayi Kukan Kura ya wulla wa Gidan wani abu da shi yasan ko miye , ai ji kake Buuuum , ila hirin Gurin ya Tarwatse sai tashi haya?i da ?ura a Wajan, Mamakin sa bai bar su Dady ba sai da suka ga ta kuma jefa wani a karo na biyu, ai kuwa har ya fi na Farko tashi, dan har Wajan da suke sai da ?ura da kuma haya?in suka iso gare su , shi kanshi mai Gayya mai Aikin saida ya kare Fuskar shi da Hannayen sa , su Abba da yake a cikin Mota suke sun ?an samu Ragowa.
Sauke Glass din da yake gefen sa Dady yayi yace Yarona sannu da ?o?ari, wannan ai kana ne cika Aiki , ina Jinjina, yanzu sai ka zo mu Tafi ko ?'' Dady ya ?asara Maganar yana Jinjina Al'amarin Muhammad din , Gaskiya yarone hazi?i mai komai cikin shirin da kuma Tsari, baya wasa da Dama ko ya'ya yasame ta .
Shigowa Motar yayi yana Huci Kamar Wani kumurci , ya tashi Motar suka fara tafiya , Adamda yanzu ya ?an fara gani amma ba sosai ba yace '' amma ya aka yi sa rushe Gidan yarona?'' , juya kan Motar Muhammad yayi ya saita ta kan hanya kafin yace '' ina Ba?in cikin na wannan Gidan da zummar har sai bincike da Hukuncin Magabata ya isko shi , daga Hakan ya kasance to Kamar mun kashe Maciji ne bamu sare kansa ba , nan gaba Ka?an wani zai zo ya dora daga Inda ya Tsaya, Zuciya ta Bazata iya Daukan Hakan ba , shine nayi Maganin kar ayi Hakan '' yayi Maganar ciki ?acin rai kamar tana gaban wanda zai cigaba da Aika aika a wannan Gidan bayan Shu?ewar Labarin Mk a Doron ?asa .
Abba yace '' yaya ina muka nufa daga nan? '' ya yiwa Dady tanbaya.
'' da nayi Tinanin Direct mu huce Gida , ganin yayanin da Adam yake na rashin Gyaran Jikin Shi , bai kama mu tafi dashi Gida a haka ba , inaga muje Salon kawai , bayan an Gyara masa jikin sai mu wuce '' cewar Dady da yake kallon Adam da yanayin jikin sa, bashi Dau?a ko ?aya, kuma baya tsami, matsalar sa daya wannan Gashin da ya kusan rufe masa duka Jikin sa .
A ?ofar wani Salon Muhammad yayi parking na Mota , shida Abba suka zauna a cikin suna jiran Dady da oncle da suka jima da shiga , kusan yanzu sai zancen fitowar suma .
Tsaf suka fito Dady ne a gaba yana janye da Hannun adam, anyi masa Aski sosai aka Gyara masa Fuskar , da alamu har wanka yayi , tunda ba kayan daya shiga dasu bane a jikin sa , Gyaran Farce , kunne Babu inda ba'a wanke a jinkin saba, kuma duk Dady ne yasa ayi Hakan .
Masha Allah ya kuwa fito a Adam dinsa , sai dai wancan Adam din saurayina mai ji da ?uruciya da shegantaka, shi koma wannan wani sabon Adam ne mai cike da Tsantsenin Duniya da Miyagun Ayyukan da ake aikawa a cikin ta .
?arasowar kisan Motar yai daidai da fara ringin din da wayar Dady tayi , dubawa yayi yaga sunan Baba ne , sai da ya sa Adam a motar kafin ta daga kiran lokacin shima yana daidaita mazan sa a cikin motar , ta cikin wayar Baba yace '' ?an uwa dayake haka yake kiran Dady tun dawowar su , kawai yaushe zaku dawo ne , tun ?azu mukaga isowar yaran nan , Gashi har Hu?u tana faman Rufuwa baku dawoba'' , '' lafiya qlau wallahi, gamunan a Hanya tare da ?arin farin ciki ?an'uwa'' fa?in Dady yana Magana yana kallon Adam.
Cikin mintuna talatin suka iso Gidan Dady, su Baba sun fito zasu shiga Masallaci dan gabatar da sallar la'asar, san bai lura da wanda yake bayan motar a kusa da Dady ba, ya idasa shigewa Masallaci, a Ban?akin ?an'aiki suka yi al'wala su dukan su , Dady yana ri?e da Hannu Adam suka nufi masallaci dan Gabatar da sallah , da kuma Ramuwar ta Azahar da basuyi akan Lokacin taba.
Har suka ida sallhr Baba bai kula da Adam sai akan har sun shigo Tsakiyar Farfajiyar Gidan suna ?o?arin shiga falo, nan Baba yayi tozali da Fuskar babban Makiyin shi wanda bazai ta?a manta Ranar dayaga a gaban idon sa aka kashe Mahaifinsu ba tare da yayi wani yun?urin hanawa ba , zai ta?a yafewa Adam ba , a kullum idan ya tuna shine silar Wargajewar ahalin su sai yaji idan da zai ga Adam zai iya kasheshi shima, basu Ankaraba suka ga Baba ya Dam?i wuyan Rigar oncle Adam, cikin tsananin ?acin rai yace '' Munafuki, Azzalumi, bakin wake mai ?ata komai kyaun Miya, Adam ka zalumcemu , ya ?ata mana sunan ahali da kuma nasaba, nayi Nadamar kasantuwar da jinina a jikin ka, wallahi nayi ba?in cikin tsaya kasance kaidin kana da ala?a dani, yanzun niya kawo ka nan , kazo ka ?arasa Tarwatsa dan Farin cikin da muka samu da dawo garemu , na tsawon shekaru muka rasa shi , dan Girman Allah kar ka shigo Rayuwar mu, yanzu muna da iyalai da yawa, bazasu iya jurar u?ubar ada mu muka jura ba, na ro?e ka kabar gidan nan dan Allah '' Baba ya ?arasa Maganar da sakin wuyan Rigar Adam yana kuka, shima Adam din kukan yake, duk da baya ganin ko waye agaban shi , ya tabbatar da ?ayan ?an'uwan nasa ne wato Hassan , tabbas yayi wa kansa Babban tabon da ba lallai ya goge ba har?arshen Rayuwa.
Daga bayan su suka ji ana cewa '' Suba hanallahi, Hassanu miye haka kuma , ai ko Ubangiji a kullum muna masa Laifi, kuma baya gazawa wajan yafe mana, shidin Gaffurur rahimu ne , da ba'a yafiya a Duniya da tuni Allah ya juyar da mu a kan Zunuban mu, amma sai Allah ya barmu da halayen mu, wasu yayi musu Rahama, wasu kuma ya azabtar dasu , tun anan Gidan Duniyar kowa yake fara Girbar abunda ya shuka'' kawu ya mike Magana cike da Garga?i, da kuma jan kunne.
Kowa yayi shuru suna sauraron shi , duk jikin su yayi sanyi, Musamman Baba .
Tsoho Baffa da suka shigo tare da Kawu yace '' mu shiga daga ciki mu zauna inaga ai zaifi ko?'', shiga suka yi cikin falon su duka suka Zauzzana a cikin Tsari , Ladabi, da kuma Girmama na Manya, su manya sune akan kujeru, yayin da matasa da sauran yaran suke a ?asa Mazan su da Mata, Abdul wahid haka yake yiwa Ru?ayya kallon ashe da rabon Ganawa , dan shi a ?azu da Mk ya ri?e masa wuya ya Sada?ar ya gama Rayuwa, yasa a rai Shikenan shida ya kuma ganin Ru?ayyar shi sai a Darussalam, ko a aljannah idan aka ha?a ?an'mata da Samarin Aljannah ta?i ya za?e ta a Matsayin Matar sa ta aljannah.
Suma sauran Samarin haka kuwa yake ma tasa Masoyiyar kallon ?auna , da shau?i kamar sunyi wuni uku basu gansu ba.
A wannan karon ma Ustaz Safwan ya bu?e musu taro da Adu'a, kafin Dady ya zayyane musu duka Nasarar da suka samu na kama Mk , juyawa yayi ya kalli kawu yace '' kawu wai kasan waye Mk kuwa ?'' , '' a'a sai ka fa?a Almustapha'' cewar kawu.
Dady yace '' Alhaji Munir Kabiru, wanda kuka tafi neman alfarmar a baku Gawar Alhaji kuyi mata Sutura a wancan Lokacin! '' , '' eh eh kam na tuna shi , Innalillahi wa'inna alaihi raji'un , yanzu dama shine ya kashe Gambo kuma ya dawo akayi zaman makoki da shi , harda saka baki wajan ganin an