Showing 45001 words to 48000 words out of 48162 words

Chapter 16 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah

10 Jul 2024

3351

kafin ?aurin Aure ba , shiga dole yaje zinder kawai dan yaganta, a yadda take bashi Satar Amsar yadda tayi kyau yasan shi idan ya ganta sai Gyaran Allah idan bai yi Hauka ba, sai da Mamma tayi masa jan ido kafin ya shiga Tunanin sa , ya maida Hankali wajan shirye-shiryen Aure gadan_gada.


Saura sati biyu aure Anty Ramatu tazo da shirin idan an gama Aure ta biya da Amaryar su, tasha ta?ara a wajan Abdul akan ta kula masa da Mafarkin sa a cewar sa, shifa Ru?ayya Rayuwar sace , ko a Lokcin da yake kan sira?in Mk mai wuyar Tsallaka wa , sai ya tuni da ita sai goma kafin ya tuna da sauran so ?aya.


*Yaune Ranar*
Yaune Ranar da aka daura Aure kusan Shida tare da shaidu da kuma wakilai, an bada Sadaki gwargwadon iko da ?arfi, da Farko aka ?aura Auren *Baffa* da *Inna* *lami* , bisa neman yardar su, kawu ya ha?a wannan aikin.


Sai aka ?aura na *Oncle Adam* da *Fassuma* , ?ar Aiki ce a nan Gidan Dady, tana da kusan Shekara Arba'in amma batayi Auren fari ba, tana fama da lalurar Aljanu, tun Iyayenta suna nema mata Magani har suka gaji suka barwa Allah, suka nema mata Aikatau takeyi, kusan shekara goma kenan take Aiki a Gidan Dady, kuma ba Laifi sun yaba da Hankalin ta, Momy ce ta bawa Dady wannan Shawarar, ya Kar?a kuma ya baya da Tunanin ta , shiyasa har kullum yake ?ara Godewa Allah daya bashi Mace tagari a Matsayin uwar Yaransa.
Safwan yayi mata magani, kuma cikin ikon Allah sai sa warke har ta amsa da bakinta ta amince da auren Adam din.


Sai *Abba* da *Batoolah* yar Jarida, Allah ya ha?a abunsa, tun Lokacin da tazo neman ?arin haske a wajan Abba dangane da labarin da take so ta fitar na Mk, sukayi Musayar Number ita da Abba, abu yayi ?arfi har akayi zancen Aure.


Sai *Safwan* da *Humaira* , *Ridwan* da *Hafsat* , *Abdul wahid* da *Ru?ayya* .


Masha Allah haka aka ?aura Auren nan cikin Farin cikin, Kawu shine Uba kuma Kakan Angoye .


Tun Lokacin da labari ya iso cikin Gida cewa an Daura aure, wani zazza?i ya rufe Maryam, kai kace yau itama aka ?aura nata Auren, bayan ta kusan rufe Shekara da Igiyar Aure a kanta.
Shima gogan yana cikin jama'a suna ta gaisawa ana musu Barka, sai ji yake gabansa yana Fa?uwa, Maryam ta fa?o masa arai, a ?an kwanakin nan Tunanin ta yake faman ya hanashi sukuni, yayi nisa sosai cikin Soyayyar Yarinyar, amma ita yaga alamar sam baya gabanta, ?ar Soyayyar tasa ma daya fara gani a ?wayar idanunta a wancan Lokacin , yanzu sam ta hanashi damar da zai kalleta ma, bare har ya gane inda allon sa ya kwana.
Sulalewa yayi ya fice daga wajan batare da su Safwan sun saniba, dan sunanan da abokan su anata faman yi musu sha?iyancin sun zama Angoye, Ridwan baki har kunne, yau shima ya zama Magidanci, Abba kam abunsa a ransa, ba wanda zai iya misalta halin Farin cikin da Zuciyarsa take ciki, a yadda yake jin soyayyar Batoolah tafi gaban ya kwatanta ta a bainar Nasi, yasan ita ka?ai zai nuna ma irin salon tasa Soyayyar, dan har ga Allah bayan Rasuwar Juwairiyya bai ta?a ganin wata Macen da ta tafi da Imanin sa irin Batoolah.


Koda ya shigo cikin Gidan sai yayi tsaye, yama rasa wane ?angare da zai je ya sameta, gashi duk Mutane ne takota ina , kutsa kai yayi Sashen Baba, ya kuwa yi Sa'a yau ?an'matan anan suke, ?angaren Momy yau Akwai Manyan ba?i, Matan Manyan Mutane daga Mabanbantan ?angarori, ga kuma ba?i kusan Mutun uku daga Niamey wanda suka zo ?aukan Amarya, jirgi guda Ambassador Aliyu ya ?auki shatar sa dan kowawa Auta Matarsa har Gida, a cewar sa karta wahala, yanzun haka lokaci kawai ake jira su wuce da ?arfe shida na yamma.


Allah Sarki Ru?ayya Mutanen Niamey, nikam Maman Abdallah nace bazanje rakiya ba, saboda kar nayi missing tarewar Mrs Muhammad.


Kansa a ?asa kamar Munafuki haka ya Shigo cikin Falon, tarin ?awayen su ne na Makaranta, ga kuma ?awayen su Humaira da akaje har Jalmari aka dauko su a gaban Iyayensu da Zummar sai an gama biki kafin a Maidasu cikin Aminci.
Woow wata ?awar su Maryam ta Makaranta mai suna Firdausi ta fa?a lokacin da taga Shigowar Muhammad, sanye yake cikin blue din Shaddar da suka yi Anko su duka Matasan, yayin ba Iyayensu suka yi kalar Maroon, kawu da Baffa kalar orange gare su, kuma duka Dady ne da wannan Aikin.


Tsaye yayi ya rugume Hannayan sa biyu a ?irjinsa yana kallon Maryam da tun shigowar sa Falon idanun sa da ita suka fara tozali, shine ya Nutsu a guri ?aya yana kallon ta , ?ishirwa ta samu Ruwan sha.
Wannan woow din da Fidy ta fa?a ita ta ankarar dasu da wanzuwar da a wajan, har Maryam sai da ta ?aga kanta, dan tun ?azu zuciyarta da hancinta suke yaudarar ta akan ?amshin turaren sa take ji, ashe kuwa haka ne zuciyarta batayi ?arya ba , taji Maha?in ta yana gab da ita.


Hafsat ce ta taso tazo kusa dashi tace '' yaya Muhammad kana neman wani abu ne?'', '' Hararar ta yayi yace har ai ma kin Tanbaya akan mi nake nema Bayan duka Muhammad din ne anan ''
Rufe baki Hafsat tayi da kunyar da yayan nata yake so ya bata, kenan idan har ta fahimta ita Maryam din ce Muhammad, shi kuma Muhammad shine Maryam, ikon rabbi itafa a kullum ganin tasu Soyayyar take kamar wasa, dan tasan wacce za'a zuba a wajan wa'yannan miskilan guda biyu zasu sha kallo, su kam sun cinye tasu a baka .


'' Zaki kirawo mini ita ko gulmar zaki tsaya tayi da sa ido ?'' cewar Muhammad.
'' Zan kirata yaya Ango, ka shiga wancan ?akin ba kowa sai nayi Wa Amarya iso ko ?'' ta ?arasa maganar da Sha?iyanci a ciki.
?ofa yayi ya fara takawa zuwa ?akin data nuna masa, yana ayyanawa a ransa Rashin aure da bai yi da wuri ba, duk shi ya jamasa har ?annansa suke Ganin kansu ?aya dashi, tunda gashi zasu tare a Gidajan aure Ranar daya a yau, shiga yayi ya zauna bakin Gadon da yake ?akin yana jiran Hajiyar sa.


Koda Ru?ayya ta fa?a mata yaya Muhammad yana karanta sai tayi kamar bataji ba, daidai lokacin Anty Ramatu ta Shigo ?akin da wata roba mai murfi a Hannun ta, asali Anty Yani ce zata kawo musu sauran Tsumin Agallashe da ta ha?a musu, sai ta sami kira daga maigidan ta da shima ya sami Halartar ?aurin Auren, shine yanzu zasu wuce daga an ida sallhr la'asar , shine zasuyi ban kwana kafin itama bayan kwana biyu tabi bayan abunta.
?arasowa tayi inda suke a zazzaune su da ?awayen su, wasu sai Shegantaka suke musu wai daga yau sun zama Manyan suma , Ru?ayya tace '' Anty Ramatu wai yaya Muhammad yana kiran ta, na fa?a mata, kuma ta ganshi da idanunta, amma ta?i zuwa'',
Nan anty Ramatu tasha toka ta kalli Maryam tace '' tashi kije kar na ?ata miki '' , sumi-sumi ta mi?e ta nufi ?akin, dan bataga alamar wasa ba , haka Ramatu take wani Lokacin ba wasa, ko wanda ya fita a Shekaru tana masa ?warjini wani lokacin.


Koda ta shiga sai ta tsaya daga bakin ?ofar Shigowa, kanta a ?asa, tasowa yayi ya fara takowa inda take a tsayen, hannu yasa ya ?ago Fuskar ta wadda ta gaji da ?ara kyau akan wacce take dashi , yace '' kusan sati biyu, ko ?an ganin da nake miki daga nesa ban samu ba, kowa a cikin mu yana ?an rage Lokaci da tasa abar ?aunar Amma Ni sam banida wannan damar, Maryam kina bawa zuciyar Muhammad wahala, yanzun haka ina cikin Mutane na kasa ha?ura, tunanin ki ya hana ni Sukuni '' tayi Maganar cikin Marairaicewa.
Fa?awa jikin sa tayi tasa masa kuka, ita kanta Bazata iya fa?in ko kukan miye ba, amma ta bawa zuciyarta amsar na farin ciki ne.


?arfe shida daidai jirgin su Ru?ayya ya ?aga zuwa Niamey, tare da rakiya Mutum biyu, idan aka ha?a da anty Ramatu uku , da dangin Ango wanda suka zo ?aurin Aure haka suka isa , a daren Ranar akai Amarya ?akin ta, wanda anan kusa da su Ramatu suke, Ambassador Aliyu yayi wannan aikin tun lokacin da Autan ya fidda Matar Aure, ya sayi wani fili anan jikin gidan Abdurrahaman din shine aka yi masa nasa ?angaren, da wani tsararren gida Pappa ya bashi, amma ya?i yace yafi san kusa da yayan sa.


A ?aya

A ?ayan ?angaren suma sauran Amaren Wuraren ?arfe taran dare aka mai?asu ?akunan su, tare da fatan Allah ya bada zaman lafiya.


*Bayan wasu Shekaru*



'' Anty Anty Maryam wai kina ina ne? '' , '' gani tanan miye ake mini kiran mafarauta cewar Hajiya Maryam da ta fito daga kicthing Hannunta rike da dan tiren da ta zagaye shi da kayan marmari, cikakkiyar mace mai kyau da diri, yar kwalisa kuma darinar ado, wani uban Maroon less ne a Jikinta da yaji dinki, ya zauna da ajikin kamar a jikin aka yi dinki, fuskarta ba kwalliya, amma kana ganin ta kasan tana cikin kwanciyar hankali.
Munira ?ar gidan Ammi Batoolah Matar Abba da yanzu ta zama Budurwa ?ar Kimanin Shekara goma sha shida tace '' kai Anty dama wai yaya Amir ne , sai kuma tayi shuru '' , '' dama mi fa?i ina jinki , ko wani laifin kika yi masa ya hukunta ki kamar yadda yake yiwa Mutane, koda yake shi basai anyi masa wani abu ne yake cin zalin Mutane ba ko? Idan ban mantaba haka kika fa?a mini '' , cikin zaro ido waje kamar wacce tayi ?arya tace '' kai Anty Ni yaushe na fa?a, kawai fa dama yace yana Sona ne kuma har yace zai fa?awa su Abby '' tayi Maganar tana rufe Fuskar ta alamar jin kunya .
'' ?ar nema, da ban yi miki haka ba , da har zuwa yanzu kinanan kina ja mini rai baki fa?a mini ba '' cewar maryam da farin cikin maganar ya gama rufe ta .
Suna tsaka da haka sukaji Shigowar ?an Makaranta sun dawo, bayan sunyi sallama suka shigo falon, da gudu *Nana* tazo ta zagaye ?afafuwan Umman tasu tana cewa '' yau nice farko '' ji sukayi an ?aga ta sama yana juyi da ita kafin ya sauke ta yace '' kece farkon ganin ummah bayan dawowar ku, Ni kuma nine Farkon ?aukar ki kafin Umman taki '' Muhammad ya fa?a yana lakatan Hancin Nana, a shekarun tarewar su Allah ya albarkacesu da yara har hu?u, *Adam* shine babba, sai *Ismael* shine na biyu, *Anas* daga shi sai *Nana* *Juwairiyya* , wacce taci sunan Mahaifiyar Maryam din, sai suke kiranta da *Nana* .
Kama Hannun Nana Munira tayi tace '' my ?awa zo mu tafi na cire miki wannan Iniforme din'' , suma su Anas nasu Dukin suka nufa yayin da shi Smol Adam ya ?arasa nashi ?akin dayake shi nasa ?an n daban.


Bayan barinsu wajan Muhammad ya kara matsowa kusa da ita yace '' shine aka mini wayo akan za'a kawo mini kayan lambu ko ?'' , mi?a masa tiren da yake Hannun tace '' eh ai ba wayo nayi maka ba , baga shiba, na ?auko zan shige nasami kiran gaggawa daga Munira kasan mi take fa?a mini kuwa?'' , '' a'a sai kin fa?a '' ya fadi tare da ajiye tiren kayan Marmarin a kan kujera mafi kusa da su , ya matso daf da ita ya kara kunnansa a sautin bakinta, ya lumshe Idanun sa yace '' ina jinki '' , cin kasa ?asa da Murya tace '' Oga Amir yaga ?anwata Munira yana so saboda haka , daga yanzu kuna bina a hankali kar na hanaku eheeeeeeee '' tayi Maganar da Muryar da ni kaina sai danayi da gaske na ita jin abunda take fa?a, tsak ya dauke ta ya nufi ?akin sa da Ita, haka na dage ?afarsa ?afata haka muke tafiya, ban lura an kawo bakin matsayar shiga ?akin oga Muhammad ba, sai da naji ya maido muni ?ofa akan koshina, ji kake gum Goshina ya amsa, falon na dawo ina murz wurin dan kar yayi mini kunburi ina tsaka da haka na tuna baya da labarin da ban baku ba , ba bayan tarewar su .
Nan na shiga tunani , bayan tarewar Aure shida, na Mutum goma sha biyu da aka daura, abubuwa dayawa sun faru ciki har da Rasuwar kawu da Baffa, kusan a shekara ?aya suka Rasu yanzu shekara shida kenan.


Inna lami ana nan a na shan tsufa, dan ma nasu tsufan na Imani ne , tunda har Yanzu tana gane mutane amma ba sosai ba .
Tana ibadar ta daidai gorgodo, da yake dama ba wani d'yawa ne da danginta acan kanyar, yawan ci Duk Sun rasu sai iyalan su , sai ta cigaba da rayuwar ta tare da su Hajiya da Yanzu take Rayuwa cikin jin dadi da jimami, a Yau jin dadinta ?aya ne tana tare da zuri'arta a gu ?aya, cikin Aminci , gata ga jikoki, ga ?iyan jikokn ta, Allah mai iko a da ta fidda rai da rayuwa kamar haka cikin yawan jama'a har haka, ashe da abunda Allah ya Hukunta, taso Alhaji yana raye yaga Yawan zuri'arsa , tasan da sai ya fita farin ciki.


Masha Allah a shekarun nan a cikin kowane Gida Allah ya albarkacesu da samun ?aruwa samun ?a?a, Ammi Batoolah Matar Abba tana da yara uku bayan guda biyun da tazo dasu Munira wacce yanzu Amir mai bima su Humaira ya ke so yayi wuf da ita, sai kuma ?anenta, ta haifi *Almustapha* , *Zuhrah* sai kuma ?aramin *Sagir*.


A Gidan Oncle Adam kuwa yara biyar gareshi, da yake fassuman tana Rirritsan haihuwa ne, Haihuwar ta ta Farko ?an'biyu ta haifa *Hassan* da *Hussaini* , sai Gambon su mai sunan Baffa wato *Idriss* , ta hu?u *Fadeela* , sai kuma *Yusrah* ita ce ?arama.


Yaya Safwan da Humaira an zama iyaye yaransu uku , ta farko Macece mai sunan Maman su Muhammad wato *Umaima*, sai **Ramlat** sai karamin su *Saifullah*.


Mrs Ridwan uwar ?an uku Hafsat ita tace sai ta kuma yin ?an ukun Alhaji Gambo mai Kayan kwali, yara uku ta haifa kuwa duka maza, kuzo kuga murna wajan Familyn nan a wannan Ranar, sai dai Operation aka yi mata, dan kusan kwana da yini tayi tana makuda amma shiru, sai da aka mata Cs aka ciro su, masha Allah ranar suna yara suka ci sunan *Abubakar, Umar da Usman*, saboda wahalar da tasha hakan yasa ta ?auki dogon hutu, yanzun haka shekarar su tara amma shiru tayi kwance da kaya .


Su Ru?ayya ?an Niamey Matar Abdul wahid Sarakuwar Mataimakin Shugaban kasa a Yanzu, bayan auren su Ru?ayya Pappa a jiye takarar shugaban kasa sai yazo a mataki na Biyu aka bashi Mataimakin sa, yaran Ru?ayya biyu na farko *Bashir* suna kiransa da Alfah , sai *zainab* mai sunan Momy suna kiran ta da Ummita.


Anty Ramatu ta kuma haihuwar yara biyu bayan Nasir , *Faisal* da *Abdul Fatah* su Ihsan kam an girma.


Gidan Baba ba'a kuma samun wasu yaran ba , sai ma ?watsan Amir da Momy tayi musu, yaza ?an Gidan Momy da Dady, yanzun haka shine babba a Matasan Family kuma shike Hukunta duk wani mai laifi matukar ya girme shi, gashi da san girma kamar ?urji, ba yauba yake cewa shifa bazai bari ya tsofe a gida kamar yaya Safwan ba, yanzun haka yana shirin yayi wuf da yarinyar mutane tunda har ya fara bude mata a binda yake Ransa game da soyayyar ta .


A daidai nan na dawo daga duniyar Tunanin dana lula na labarin baya da ban baku ba.
Zaune kawai nake ina jiran inga lokacin da Hajja Maryama da Alhaji Muhammadu zasu fito.
Can naji fitiwarsu suna Dariya, juyawar da zanyi sai naga Maryam tana Gyara wa Muhammad wuyan Rigar sa Jallabi dayasa zai tafi masallaci tace '' yaya Muhammad muna barar Adu'a '' , da Murmushin farin ciki da ya kasa akan Fuskar shi yace '' insha Allah Matar Muhammad '' ya fa?a yana kashe mata ido ?aya alamar tasan sauran zancan.
Rufe Fuskar ta tayi wai taji kunyar kiran ta da yayi da sunan , gaba yayi yana ?ar Dariya, yasan in ya biye mata sai ya rasa sallar jam'i. ?ofar ?akin Smol Adam yayi , kafin yayi gaba, dama haka yake musu, daga ya buga ?ofar Adam din, shi sauran aikin nasa ne, shi zai tiso ?eyar ?annensa har Masallacin sake cikin jerin gonon Gidajen nasu.
Dakinta ta nufa dan kintsa kanta a kan lokaci, kar Magariba ta ku?uce mata, dama ance ita sallhr Magariba kurciya ce, baka tantan cewa take fice wa , idan ta fice kuma saidai kayi Ramuwar ta .
Ganin an shareni yasa na Fusata ainun, na totse Biron a ?asa, na yaga Takardar, na ?aga da Babbar Murya nace ( *Tamat bi Hamdullah* )



????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
*Toh Masoya gamu a ?arshen littafin nan namu mai suna* ????
*MUGUNTA FITSARIN FAKO*%%
*Masha Allah , abunda muka Fa?a daidai Allah ya* *bamu Lada, wanda muka yi Kuskure* **Allah ya Gafarta mana.*
*Duk wanda yaga littafin yayi* *daidai da Rayuwar sa to akasi aka* *samu*..

**Wannan* *shine littafina* *na Farko, anyi* *ta samun* *typing error a* *cikin ,* *dama wasu kurakurai* *dadama, duk* *da Littafin Free, kunyi* *Ha?uri sosai* , *akan jinkirin* *da* *ake samu na yi muku* *update kullum, ina Godiya Sosai* .
* Kuma Kuna Comments* *bai laifi , a wannan* *ga?ar ma ina godiya irin* *sosai* *din nan* .
*Basai da* *wane da* *wane ba* , *dukkan Ku ga* *naku* ??????????????

*Ina Godiya Sosai* *Fans* ??

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login