Showing 6001 words to 9000 words out of 48162 words
nuni da hannu da ya kira Hassan su dauke shi akaishi asibiti
Tana magana amma ba'aji tsananin tashin hankali , da gudu yagito ya nufi masallaci dan kiran Hassan a tunaninsa yana can ko ya xaya azkar ne
Har can yaje amma ba Hassan daya tabayi wanda suke zaune irin masu zama har sai gari yayi haske a masallaci ko sunga hassan suka ce ayau basu ganshi ba ,kuma ba ?abi'arsa bace fita ba sanarwa
Juyowa yayi ya dawo
gida a?ofar gida ya gamu da baba me gadi,wanda yaga fitowar sa kamar ba ya cikin hayyacinsa sa ,shine ya biyo baya yaga ko lafiya
Yauwa baba dan Allah muje ja kamamun Abba za'a kaishi asibiti bayada lafiya bai karasa
maganar ba tini baba me gadin har yakai kofar falon tare suka shiga har ?akin alhajin
suna shiga Hajiya ta muna musu drowar da Alhaji yake ajiyar ku?i wayam ba komai
ga kuma wayar Hassan a yashe a qasa da wani abunda samari suke daurawa a hannu wanda ko ajiya da dare yana sannn Hassan din
To kenan Hassan ya shigo dakunan komai ya fadi a fice duk yana rasa ta ina zai fara
Baba kamamun mutafi lokaci yana tafiya
ko da baba mai gadi ya ta?a jikin Abba sai ya fashe da kuka yace yaro saidai muyi ha?uri Alhaji ya riga mu gidan gaskiya
Hussain bai san sanda ya zube akan guiwoyin shiba , Hajiya ko jingina tayi da bango ji,jiri yana daukan ta
tun shigowarta dakin tagane Alhaji baya nunfashi amma tayi tunanin ko sama ne yayi
Baba cikin kuka yace ba fa'ida zaman mu a haka muyi gaggawar sanar da hukuma idan kunban izini sai naje nagaya musu
Dakai kawai Hussaini ya iya bashi amsa,baba yana fita daganan sai police station
Hussaini ya tsaya da zancen yana kuka mai cin rai dan tambayar da aka yiwa Hajiya ce ganin ta?iyin magana sai shi ya amsa ta
Cikin jimami jami'in yace a labarin da ka bani naji kace ku duka kunanan har wanda yaba gidanma shima yazo a jiyan hakane da eheeeee gabashi amsa
Jami'in yace waye shi
Dan ukun mune sunansa Adam amma baya tare damu ayanzu sai lokaci bayan lokaci yake zuwa
A ina yake da zama ,ko yana aiki a wani garine
A'a baya aiki kuma bansan inda yake zama ba Har ya buda baki da niyyar sake yi masa wata tambayar sai kuma ya fasa
Shikenan Ni yanzu zantafi,zan iya dawowa da kowane lokaci akoy jami'ai guda uku zasu zauna tare daku agidan nan
Bashi ga, sannan kuma Ba fita daga har sai nagama bincike na
Ya idasa maganar yana mi?ewa tsaye yace nabarku lafiya............
Har yatafi sai kuma ya dawo yace kace muna sunan dan'uwanka
Adam ya sake fada masa akaro na biyu ,yazama dole shima bincike ya biyo takanshi yana fadin haka yayi ficewar shi ya bar su a zaune kamar gumaka................
Kafin la'asar gida ya cika da yan zaman makoki har yan kauyen su Alhaji sun iso bisa jagorancin ?anin mahaifinsa
Su sai bayan isowarsu ne suke jin cewa harda Hassan shima ba'a ganshiba
Sun shiga tashin hankali ainun musamman kawu yafi kowa shiga tashin hankali yayi kukan rashin Alhaji ?an zumunshi wanda ya dauke shi kamar shiya haifeshi
Gambo yayi masa komai a rayuwa ,ya kula dashi ainun
Ashekara goma ma bai sayi abincin da zai ci a gidan saba
Zai iya cewa tunda Allah yayi Gambo bu?i ya ke ci daga arzikin shi ,har hajji yaje ya sauke farko kuma duk shi ya biya masa,ko ana sauran sati kafin abunnan ya faru sai da yaziyar cesu kuma yayi musu alkhairi mai tarin yawa
Allah dai yaji?anka ya maka rahama,ya toni asirin wanda suka yi masa wannan aiki
Shi ko Hassan Allah ya bayyana mana shi cikin aminci
Da Amine suka amsa su duka kafin kawu ya cigaba da magana bai kamata ayi ta ajiyar mamaci ba dasunan sai angama bincike ba , Hussaini ya kalla yace kayi magana dasu ,Alhaji dan Allah ku shiga maganar nan abamu shi muyi masa sutura in yaso komai ya biyo baya
Ya ?arasa maganar yana kallon Alhaji munir magaucin Alhaji
wanda tare suka je masallaci a wancan ranar
Cikin hanzari yace to ba damuwa kawu insha Allah zamuyi magana dasu amma ba lallai su bamushi ayau ba sai dai zuwa gobe
Ko goben nema sai ayi kaga ai zaifi ko kawu yafadi cikin jimami da ?ara jin Tsoron duniya,na rashin sanin ?arshen ka da inda ajali zai riskeka
Gashi dai shi ya zauna da kowa lafiya amma ga yanda ?arshen shi yazama ,
Washe gari da safe akayi jana'izar Alhaji bisa amincewar hukuma,da har sun?i yarda amma ganin kawu da Alhaji munir sun nace yasa suka yarda ,bayan sun cike takardu aka basu shi, amma hakan bashi zai hana su cigaba da binciken su ba
Rayuwa kenan ba wanda yasan mizai faru gobe sai Allah ,kwana biyu_uku da suka wuce Alhaji yana raye _cikin_ iyalansa, amma yanzu gashi ya rasu suturar da za'ayi masa ma saida aka nemi alfarma
Bayan kwana bakwai,anyi adu'ar bakwai gida taro ya watse ,ya rage daga kawu , Hajiya, Hussaini,sai ina lami da akace ta zauna da Hajiya,sai kuma masu aiki
Har wannan lokacin ba Hassan ba labarin sa
Zaune suke a falo su duka DSP Almustapha ne yake musu ?arin bayani game da inda binciken su yakai
Gyara zaman sa yayi kafin yace gaskiyar magana ni bansan ta ina zan fara ba ,abun duka ya zo mana abai bai, anga wayar Hassan a dakin Alhaji hakan ya bada tabbacin yaje dakin kenan, kuma ga abun hannun shi shima
Ya fiddo su daga aljihun shi ya ajiye saman table din da yake gabansa ,yace basubar wata kafar da bincike zai gano suba,ko harbin da aka yiwa Alhaji bai zauna a jikin sa ba ,ta sharan cikinsa yabi kuma sun dauke bulet din bare ya zama shaida wajan kamasu
Ba shakka sun ?ore a harkar
Gashi ba c.c.t.v Camera a gidan nan ,zaku sha mamaki idan nace muku ta ?ofa suka shigo gidan nan , bakwai dirowa sukayi ba
atare su duka suka kalle shi suna masu neman ?arin bayani
Ci gaba yayi magana yace bakunce a ranar Adam yazo gidan nan ba to bai bar gidan ba har saida suka aiwatar da aikin su.
Cikin tsananin tashin hankali ,firgici da razana Hussaini ya dangi kai yana kallon shi yace kana nufin dasa hannun Adam ake nan
Wai miyasa zaka ce shine'''''mi Abba yayi masa dazai sa hannu wajan kashe shi ,kuma idan har shine to ina Hassan ko shime shi ya sace shi. Magana yake kamar zararre yana yi yana kuka" maganar D.S.P ce ta katse sa daga kukan dayake yace tabbas dasa hannun sa ,babu inda bamu duba agari nan ba amma babu shi mun kama wasu daga cikin tawagar su saidai ba wani abinda muka samu dan gane da binciken mu
so tunda abun yakasance daga gida ?arakar ta samu '''' Ni zan jingine kes din nan
Muyi hakuri Allah ya ji?an Alhaji ya masa rahama yayi gaggawar bayyana Hassan a duk inda yake''da amine suka amsa su duka harda hajiya da take ta kuka
Yau abun ya zame mata sabo,gashi abunda ta da?e tana zargi azuciyarta ya tabbata" dan data haifa da cikin ta shina dasa hannun sa a mutuwar mijinta uban iyalanta kuka take sosai inna lami tana data baki
Kawu ne yayi gyaran murya yace shikenan Allah ya ji?anshi ya masa rahama.......Allah bayanan Hassan cikin gaggawa ya kareshi aduk inda yake
Bamu san manufarsu tayin hakaba,amma koma minene Allah ya fisu
D.S.P yace hakane Ni zan tafi ''juyawa yayi inda Hussaini yake zaune yace mika karanta naji ance ranar da kuka dawo daga ```makaranta``` a daren abun nan ya faru
?aga kanshi yayi daya ke mai azabar ciwo yace Shari'a nakaranta good kasameni wani lokacin,ya kamata ka fara aiki baza'a rasa yadda za'ayi ba
Da to Hussaini ya amsa, kawu yana masa godiya kafin ya fice
Ahaka rayuwa ta ci gaba da tafiya dasa hannun D.S.P Almustapha Hussaini ya fara aiki tare da wata ?ungiyar kare hakkin mata dake zaman kanta amatsayin lauyan ?ungiyar
Ba laifi yana samun nasara kuma yana ganin haske a aikin
Abangaran kasuwancin mahaifinsu kuwa amsa wakilan a duka shagunan sa kuma suna kula kamar yadda ya kamata, Hussaini ya kanje ran gadi lokaci yan Lokaci
Shekaru sun ja komai yana tafiya daidai lokaci da kuma yanayin rayuwa , Hussaini yayi suna da kuma ?aukaka ''kasancewar sa mutun mai gaskiya da kuma jajircewa,?aifi ?aya ne idan yace zai yi to zai yi ne Idan kuma Yace a'a to ba mai sauya wannan ~maganar ta zauna
Manya_manyan lauyayi suna jin sha'yin Shari'a ta hadasu dashi dan sunsan ba sau?i
Yanada kyakkyawar ala?a da kowa,bashida hayaniyadama can Hassan ya fishi yawan magana "sun zama abokan juna shida Almustapha duk da ya girme shi amma ba wata tazara mai yawa bace ,shi yanada mata guda daya mai suna zainab da yaransu uku ,sai kuma ?anwarshi da take zaune tare dasu mai suna Juwairiyya .......
Suna zumunci sosai a tsakanin gidajan biyu sanadin haka soyayya mai ?arfi ta ?ullu tsakanin Hussaini da Juwairiyya dayake itama batada hayaniya sai tafiyarsu take tafiya dai-dai
Cikin ?an?anin lokaci iyaye suka shiga zancen akai komai akasa ranar aure
Bayan aure suka tare a ?erarran gidan daya gina a can cikin garin zinder ,dayake yanzu aikin shi yafi ?arfi acan
Babban gida ya gina musu mai ?angarori guda uku ?angare biyu iri daya komai nasu iri daya sak,sai kuma daya wanda bai isa kaisu girma ba ''shine na hajiyar su a biyun kuma daya nasane dayan kuma Hassan dinsa ya gina wa ,dan har yanzu bai fidda rai ba cewa dan'uwansa zai dawo gare shi
Hajiya bata tare ba sai bayan tare warsu da kusan wata biyu shima bada san ranta ba
Ita tafi sun ya barta can miryyah ita da inna lami data da?e da ?auro gidan gaba daya
ita agininta wace rayuwar jin da?i zatayi nan gaba bayan wacce take ciki ta ?uncin lalacewar ?anta,kashe mata miji da akayi ko kuma ?atan babban ?anta da har yanzu babu shi babu labarin shi wannan ?addara ce babba tafada wa ahalinta wacce ta tafi da farin cikin ta na ```har'abada```
Sai da yayi da gaske kafin ta yarda ta dawo gidan tare da inna lami
Shekara guda da tare warsu Juwairiyya ta haifi santaleliyar ?arta mai kama da mahaifinta haske kadai ta dauko na maman ta amma kana ganinta kaga Barister Hussaini Gambo
Ranar suna yarinya taci sunan *Maryam* bisa umarnin Hajiya Kasan cewar sunan mahaifiyar Juwairiyya ne kuma ta da?e da rasuwa shiyasa ma take zaune agidan ?a?anta a wancan lokacin
Sunyi farin ciki sosai da karar da aka musu nasa sunan mahaifiyar mai jirgin musamman ma ?a?anta D.S.p wanda a yanzu take da matsayin D.p.o na yan 'sanda
Masha Allah haka yarinya ta taso a cikin gata da cikakkiyar tarbiyya ta kowane bangare .............
Bayan shekara bakwai Juwairiyya ta *rasu akan guiwa,dama tunda ta sa samu cikin batada cikakkiyar lafiya
Ta tafi da cikin data kasa haifesa har an sata a dakin tiyater kafin akai ga fara mata aikin rai yayi halinsa
Allah Sarki rayuwa ta tafi ta bar mijinta da ?arta ?ar shekara bakwai
Barister yayi kukan rashin matar sa mai kyau da kyauwon hali ga girma mama na sama da ita,da faram_faram da mutane ''''''allh kenan baya barin wani dan wani yaje da?i
Nima Maman Abdallah sai da na masa ta'aziyar rasuwar matar shi kai har *_Sayyada Maryam_* sai da na mata gaisuwa rasuwar mahaifiyar``` ta ............................_ .
Barister yayi kukan rashin Juwairiyya,har jinya sai da yayi
Bayan ya warke yaci gaba da zuwa aikinsa a bangare daya kuma rainon ?arsa
Dan ba yadda Hajiya bata ?otan taba akan Maryam ta dawo bangaren ta da zama ,amma yariyar ta kafe ita sai babanta ,koda ya barta a bangaren hajiyar haka za'ayi ta kuka ,komai dare sai an kira mata abbanta
Ko lokacin da maman ta take a raye tafi sha?uwa da mahaifinta, shiyasa ko yanzu kullum sana tare, sun sha?u sosai dan ko makaranta shiyake Kai ta kuma idan lokacin tashi yayi yaje ya dauko ta
Bata yarda da kowa sai shi,sai kuma oncle din ta Almustapha shima takan yarda dashi, watarana ma har gidan sa ake Kai ta_ ta yini ,daya ke
Akwai sa'ar ta a gidan mai suna Ru?ayya kuma makarantar su daya to watarana daga makarantar ake ficewa dasu gidansu Ru?ayyan
A bangaren kasuwancinsu kuwa sai dai ace alhamdulillah dan yanzu fa?in adadin dukiyar da suke da ita ?ata lokaci ne,an samu canje_canje da dama daga masu kula da dukiyar,su kuma canja salon kasuwancin zuwa ga fasahar zamani
Babban kamfani garesu na kayan kwali babu abinda basa sarrafawa indai har yakasance na kwali ne,bisa jagora kawu da kuma shawar_warin Barister adayawan lokuta idan kawu ya neme shi akan yazo ya duba wasu abubuwan daya kamata ace ya duba ,yakanji ?unci a ransa kuma sai ciwon rashin dan uwansa ya taso masa
,yasan da yana nan da shine zai kula da komai da suka mallaka tunda dama shi harakar kasuwanci ya karanta
Bayan wani lokaci
Maryam tanada shekara goma sha uku kenan a duniya ,kuma har awannan lokacin abban nata ya?i yayi aure
ba yadda ba'ayin dashi ba amma fir ya?iya ,a cewar sa mahaifiyar sa da kuma ?arda sa sun ishe shi rayuwa ayanzu .....
Aiki kawai ya maida wa hankali,aYan shekarun nan sau kusan biyu yaje waje ?arin karatu
Maryam ta tashi da burin zama cikakkiyar ?ar jarida , wannan shine birinta kuma shi take karanta
Tanada ?wa?walwa sosai ko a makaranta malamai sun santa,itadin ta dabance a bangaren maida hankali da kuma jajircewa, da kotanta abu kamar wata actress
Yanzu abbant a ya daina kai ta makaranta da kanshi ,ya sai mata mota ita da kanta take draiving kuma yanzu a bangaren Hajiya take da zama tun lokacin data fara girma ta dawo nan
Dama yanzu abbanta bai cika zama agida ba ayyaka sun Kunno masa kai,daga ita har Hajiya sun lura da hakan,da suka tambaye sai yace Musa wani aiki ne ya tashi mishi,da alamu aikin zai bashi wahalar gaske
kuma suma aikin ya shafe su, sudai tayashi da adu'a
Duk sai jikinsu yayi sanyi hankalinsu bai kwanta da aikin ba , amma haka suka masa fatan alkhairi.........
Yau asbar ranar hutuce
Zaune yake a jardin din gidan yana hutawa da ?aramin table a gaban shi wanda ya dora wayanshi akai,da kuma wani littafi irin me notes din nan ,ala'ama ya gama nazarin littafin ne ko kuma rubutu yayi a ciki ohoo
shidai a mafiya yawan lokutan hutu zaka ganshi da wannan littafin atare dashi
Wayar shi ce tashiga ?ara tana kururuwar neman agajin gaggawa,ahankali ya bu?e idon shi dayake a lumshe tundazun ya mai?a hannun sa ya dauko wayar yana duba screen din wayar dan ganin ko waye
Ajiyar zuciya ya sauke ganin sunan wanda yake ta kira tundazu amma shuru ba amsa,da har ya fara sa arai ko ba lafiya ba
Yayana shine sunan dayake yawo akan fuskar wayar ,kiran ya daga sanin dayayi ba wani a wajan sai shi kadai, yasa ya saka wayar a main-libre (handsfree ) ya ajiye ta akan table din dake gaban sa , sallamar da ma'abocin kiran yayi ne ya karrade wajan gaba-daya ,cikin yanayi na rashin walwala
Barister ya amsa mishi kafin yace yaya Mustapha ina ta kira baka daukaba Allah sa dai lafiya .......
Maryam yau yini tayi bata gidan ,duk da yakasan cewar yau ranar weekend ne
jiya daga makaranta aka turaso (stage) a gidan rediyo _televission anfani,zasu yi sati guda suna zuwa suna ganin yadda ake aikin jarida da kuma yadda ya kamata ace suna yi amatsayin su na masu koyan aikin
yau ko mota bata fita da ita ba, dayake ba wani nisa tsakaninsu da wajan shine ta tafi da ?afa,
Fitowar ta gidan kenan ta hangi motar abbanta a inda ta barta ,banbancin bai fita ba kenan ,amma tayi mamaki sosai tunda a yan kwanakin nan baya samun damar zama sam,har wata ?ar rama yayi saba da aikin dayasa agabansa har zata gota ta bi hanyar da zata sadata da falon Hajiya