Showing 24001 words to 27000 words out of 48162 words

Chapter 9 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah

10 Jul 2024

3354

, kodai tayi error number ne
Kiran ta katse ta kuma kira number, again wayar ta guma daukan kuwwa
Ya Ubangiji ta fa?a a bayyane
Kenan dama shine yake kiran ta dayi mata message?
To Amma ya akayi ba fuskar sa ba ake gani idan taje waccan gidan
Haba shi isa a kullum indai har zata je wajan wancan sai taji ?anshin turaren sa,
Dayawan lokuta sai taga kamar yanayin su daya ,tsawan su ?aya , yana yin tafiya sa da tsayuwar sa a waje sak Muhammad.

Akwai lokacin da taga irin motar sa a nesa ka?an da ?ofar waccan gidan da take zuwa, amma a lokacin batasa komai aranta ba,
Koma ranar da sukayi wayar ?arshe dashi, taji muryar kamar na wani makusancinta, ashe Muryar shi taji,to idan shine ya akayi yake canja fuska ?
Tayi wa kanta tambaya, koma dai ba shibane to yana da ala?a da waccan mutumin,
komai yazo ?arshe wallahi a yau sai ta tona masa asiri a gaban su Dady, dan susan dawa suka ha?ata zama ,
Dole ya amsa tarin tambayoyin ta agaban kowa, bazata bari ru?anin Da yake sakata ya kashe ta da ranta ba.


Takowa yake cikin tafiyar sa mai ?aukan hankalin mai kallo, a da kafin ya fara caza mata kai idan yana tafiya birgeta yake, amma yanzu sai taji kamar zuciyar ta yake takawa tafiyar nan da yake yi ,
?arasowa yayi yana daukan wayarsa yace ''sorry na barki kina ta jira , naga kin dau wankan zuwa ganin Abba, shine nima na ce Bara nadan yi wanka nima tunda Abban ba nake daya bane
ya fa?a a sigar zolala yana yin gaba ya nufi Hanyar fita daga falon


Binsa tayi da ido tayi mutuwar zaune, to da Abba bana ita ka?ai bane na ita dawa ye
, Anya kuwa?
Bara dai su isa gidan yau za'a yi ta ta ?are
Fita tayi ta iske shi dan har la'asar ta gabato

Tunda ta fito yake ?are mata kallo, tarin damuwa ya hanga akan fuskarta , shi sa yaso tun jiya ta gane wani abun, shine dalilin da yasa har ya ?ir?iri kiran wayar sa da Tata wayar , ko zata an?ara da number
Amma sai yaga bata lura ba
Yanzu ma da gangan ya kirata ,kuma ya bata damar da zata iya kiransa duk dan ta gane dashi take magana.

Bai so zata tafi wajan Abban ta da ?acin rai a tare da ita ba, yaso su tafi tana farin ciki
Amma hakan bai samuba , yasan zai yi wuya ya iya sauke ta kafin su iso gidan Dady

Zagayawa tayi tashiga gaban motar Ba tare da tace dashi komai ba ,zuwa yayi ya ?ude gete kafin ya dawo ya fita da motar
Sai da ya rufe gidan ya dawo yaja motar suka bar layin.


Hanyar da zata kaishi waccan gidan da suke ha?uwa yayi, tana kallon sa har yayi parking a ?ofar gidan Fita yayi daga motar yace ta jira shi , ita da Mamaki ya sa?arar da ita a zaune sai bata ce komai ba,
Har ya shiga na tsayin mintuna biyar ya fito yana yarfe ruwa akan fuskarshi alamar kadai yayi al'wala, ko kuma ya wanke fuska, '' to kenan da mutane a gidan ta fa?a a ?asan zuciyar ta, tunda a zuwan su bataga sanda ya bu?e gida ba, kawai shiga yayi
Kuma yanzu ma daya fito bai rufe gidan ba
Wannan shine dalilin da yasa tace kawai da akwai mutane a gidan



Tafiya suke irin ta kurame ba mai yiwa ?an uwansa magana, kowa da abunda ya ke sa?awa a ransa, musamman Maryam kanta yafi na kowa ?aukan zafi
Daidai ?ofar gidan Dady ya shiga danna odar motar
Nan danan aka bu?e musu ?ofa dan ko su securitys din gidan sun san yau za suyi ta samun ba?i , tunda mai gayya mai aiki ya dawo.



A farfajiyar gidan suka gamu da su Dady sun fito zasu tafi masallacin ?ofar gidan dan gabatar da sallar la'asar


Da gudu ta fito daga Motar ta nufi inda su Dady suke sai da tayi kamar zata rungume Dady irin yadda suke masa ada idan yadawo daga doguwar tafiya, sai kuma ta tsaya cak, komai ta tuna oho, '' cikin farin ciki take gaishe da Dady tana le?en ta inda zata ga Abban ta, Dady yace '' ai Hussainin yana cikin gida na ce yayi Sallar sa a ciki tunda bai gama warware wa ba , masha Allah Mamana anya ma kinyi missing namu kuwa ??

Cikin jin kunya ta sadda kanta a ?asa tana wasa da yatsun hannunta, idan ta fahimci Maganar Dady yana nufin kamar ta canja kenan, aure ya ?ar?eta , to ina wani jin da?i a zama da mutumin da rashin sanin data masa yafi sanin data masa yawa

A'da tana tunanin tasan san tasan duk wani abun dayake so da wanda baya so, ashe bata ma fara ?aukan darasi a class din sanin koshi waye ba , hum kawai ta fa?a '' ki fice cikin gida , kai kuma Muhammad sai mu huce masallaci koh Dady ya fada yana kallon Muhammad daya da?e da iso wa inda suke,
duka ta?arar da tayi nason ta rungume Dady duk akan idanun sa aka yi, ''
Da toh ta amsa ta nufi hanyar shiga falo ba tare da ta lura da yaya Safwane da yake Mata kallon kura taga Nama ba

Dama haka Maryam ta girma, shifa ya bari ne su Dady su huta kafin ya tanbayi inda aka kai masa mata a cewar sa
Sai gashi yanzu ya ganta da wani gardi a tare da ita
To waye shi kuma miyasa yaga sunzo tare da ita ?
Dama a gidan su take komai ?
shi bai ma ta?a ganin gay din ba sai yau
Kuma wallahi har kama yaga suna yi
, To waye shi ?
Ya tambayi kansa
Jin an tayar da sallah yasa yabar dogon tunanin ya nufi masallaci da tarin tambayoyi a bakin sa, da kuma alwashin yaga abar ?aunan sa bazai bari ta kubce masa ba
Zaune suke a falo, duk wani wanda daya ke cikin falon yayi shuru, ana sauraron adu'ar da kawu yasa yaya Safwane ya bu?e musu zaman da ita

Masha Allah kowa ya nutsu yana saurara, wasun su suna amsawa da amine , bayan ya ida kowa ya shafa hannun sa akan fuskar sa


Dan hadisi ne daga mazon Allah S.A.W yana cewa '''' idan zaku ra?i Allah madaukakin sarki, to ku riskeshi da tafikan hannun ku, karda ku ro?eshe da bayan hannun ku , sannan kar ku ajiye hannayan ku , har sai kun shafa a fuskokin ku , domin Allah yana sanya albarka a cikin su .


Bayan gama duk wannan, kawu yayi gyaran murya yace '' masha Allah cikin hukuncin Ubangiji gashi Su Almustapha sun dawo, da nasarar da ba sai na fa?a muku ba kowa yana gani da idanun sa ,ga Hussaini nan zaune a tare damu
Bayan babu wanda bai tsire rai dashi ba, alhamdulillah.


Dayawa daga cikin ku basusan abinda ya faru ba , nan ya fara basu labari tun daga Barazanar da aka yiwa Abba akan Rayuwar Maryam, da yadda suka shirya suka yi mata aure, da kuma accident din da Abba yayi duka sai da ya maida yadda akayi har zuwa yau da suke zaune ?onsu da ?or?otar su,
yace to ayau gasu sun dawo sai muyi adu'ar Allah ya kiyaye gaba ya sa qarshen wahalar mu kenan.


Da Amine suka amsa dukkan su , kafin Dady ya ce muna godiya sosai kawu Allah ya ?ara girma da nisan kwana mai anfani, tabbas komai ya faru a lokacin da muke Nan har ma da Bama nan , abubuwan da suka faru duka sun faru ne sanadiyyar wani aiki da muke yi nida dan'uwana na thayin shekaru .

Nan Dady ya ?oshe komai ya fa?a musu tun daga dawowar su Hussaini daga makaranta har kashe Alhaji da ?atan Hassan, lalurar Hajiya na rashin magana da inda ya samu asali


Tsit falon yayi bakajin komai sai shashekar kukan Hajiya, yau an tuna mata da komai, ganin abun take kamar yanzu yake faruwa

Ru?ayya da juriyar ta ya gaza tun tana jurewa yanzu har ta kasa ,
Rarrafawa tayi kusa da Hajiya ta rungume ta suna kuka abunsu, inna ce mai basu ha?uri, itama kuma kawai jurewa take, da kawai ci irin nasu na tsaffin da ,kuma macece mai tawakkali da tawadi'u tun da can .


Anty Ramatou bata ta?a jin wannan lokacin ba duk rayuwar ta sai yau ,sai take jin abun kamar al'mara

Yaya Safwane ya shiga doguwar suma a zaune tun lokacin da kawu yake cewa wai sun yi wa Maryam aure bai sake ko motsi ba, da ala'ma duk wani jawabin daya biyo bayan maganan kawu Bai san suna yiba

Sauran iyayen nasu kowa yasan da wannan labari,dan haka basu wani girgiza ba ,
Abdul wahid ya kalli ya kalli Muhammad dayake kusa dashi yace '' brother dama a dagaske ana haka ba sai a flim ba ??
Muhammad da bazaka iya gane yanayin saba ,
Cikin dasashshiyar muryan shi yace gashi kuwa anyi kana ji, na rantse da Allah da ace a wancan lokacin aka yini da anga abun Mamaki.

''' Ai kam a yanzu ma sai anyi abun mamakin agaban idon kowa da kowa cewar Maryam da take ?o?arin tashi tsaye cikin matu?ar ?acin
Dady a yau ba sai gobe ba ya kamata kusan dawa kuka ha?a, wannan shima da kuke Ganin shi mugune kuma mai muguwar aniya
Ya zo ya nuna muku fuskar shi ta Muhammad, kuka ?auki yarda kuka bashi, harda ?aukan ?arku da kuke tunanin sama mata Garkuwa kuka bashi , bayan bai nuna muku asalin fuskarshi ba
Shi ba abun yarda bane , nayi tinanin daukan fansar abunda aka yiwa ahalina , ina cikin tunanin ta ina zan fara sai na sami wani sa?o ............


Nan ta fara basu labari tun daga ranar da aka akaita gidan sa da yadda ya ke wasa da hankalin ta a matsayin mutum biyu
Daya gashinan ku tambaye shi waye shi, kuma mi ya shigo da shi cikin rayuwar mu tabbas kai ba alkhairi bane kamar yadda iyaye na suka baka yarda har suka yi tsammani za'a samu alkhairi daga gare ka , kayi magana mana kayi magana ta fa?a lokacin data isa inda yake ya kama wuyan Rigar sa ,
ai ji kake tasssssssssssssssssssss


To fah yadai tabbata cewa Muhammad ne da fuska biyu ????
Mizaki ce ???



Yau fah anyi faro masha Allah duka dangi sun taru banda yaya *Ridwane* soja ba?????¡á?, soja mazan fama kana ina ana yi banda kai??

Maryam fah ta dau zafi dayawa mi kuke tunanin zai faru ???


?????? Nafa ji kamar an yi mari to wa aka mara ne ?????¡â????¡á??????¡â??????¡â????¡á?



...........Kayi magana mana ta fada lokacin data isa inda yake ta kama wuyan rigarsa,

Ai ji kake tasss Abba ya wanke mata fuska da mari, a fusace yace '' mara kunyar banza, agaban mu kike nuna mana Mijin ki bai kai ki girmama shi ba, dama ana ?agawa Namiji murya ne, bare harki kama kwolar rigarsa , makamancin hakan idan nasake gani wallahi sai kinga yadda zan yi da ke .


Dafe ?unci tayi kwalla kafin wata ta sauka wata ta gangoro
Kawu ya kalli Abba yace '' Hussaini dawo ka zauna, ai she komai yanada dalilin sa, kuma mu munsan irin tarbiyyar da muka bata, haka kurum ba zatayi haka ba
Ga dukkan alamu da akwai abinda ta sani wanda mu bamusan shi ba ,a labarin da ta bayar naji tace yana ya mata wasa da hankali, wajan nuna mata zasu dau fansa tare , kaga anan dole musan asalin ko shi waye


Juyawa kawu yayi ya kalli mutane falon Daya bayan daya ,
Babu wanda yaji da?in marin da Abba yayiwa Maryam dan kowa tausayinta yake a matsayin ta na marainiyar da ta rasa mahaifiya tun a shekarun yarinta.


Yaya Safwane sai da ya ri?e kunci lokacin da Abba yayi marin, ita aka mara amma shi yaji zafin a ?asan zuciyar sa

Muhammad yana ankare da shi sai yaji dama a ?ara mata marin kamar uku haka, ko zai yi sanadiyar ?ugewar zuciyar Safwane din


Kawu yace'' Kuma bayan haka inaso daga yanzu Maryam ta zauna anan har sai komai ya dai-dai ta kafin muga ko da yuyuwar komawarta cikin Rayuwar sa, dan bazai yuyu su koma a tare ba, duba da abunda ta aikata a yanzu fatan kun fahimceni ,


Dady ne aya kar?i maganar da cewa '' mun fahimta kawu insha Allah za'ayi Kamar yadda ka ce
Amma ban yarda na bashi auren ?arinyata ba sai da nasan koshi waye , kawai na bari ne har lokaci yayi ta yadda zai bayyana ya fa?a da kansa

Lokacin da na nemi a cikin yaran aiki na wani ya min bincike akan number da aka yiwa Hussaini message tun a matakin farko , sai aka ha?ani dashi a matsayin wanda zai mini aikin, a daren ranar da nabashi aikin , a daren ban kwonta ba sai nada naje har ?ofar gidan iyayen shi
A ranar nayi farin ciki mara misaltawa , idan ba haka ba ta ?a?a zan yarda in ?auki auren ?a in baiwa wanda bansan ko na ina bane a'a, nasan komai na rayuwar ka, asalin sunan ka, da inda kayi karatu duk nasani , zaka sha mamaki idan na ce maka har aikin ka nasa, ya fa?a yana kallon sashen da Muhammad yake.



Cikin tsananin Mamaki yake kallon Dady , jin abunda ya fa?a , shi a tunanin shi akan Tsarin sa komai yake tafiya ashe ba haka bane, idan shi a hanya ya kwana to Dady a can ya kwana , tabbas Dady akwai haza?a ,
A kurkusa baiga wanda ya ta?a yi masa wayo akan wayonsa ba sai Dady , gaskiya ya jinjina masa

Shuru yayi yana nazari Abba yace '' kayi magana Muhammad muna jinka , duk da Ni bansan komai waye ba amma nasan ya'ya ba zai barmu zama da wanda zai cutar damuba , zuciyata tana bugawa da sauri sauri , kayi magana kuma ka tabbatar ka fa?i abinda nake tinani a cikin zuciya na , sa?anin hakan za'a samu matsala
Dan bansan yanda zanyi controling zuciya na ba, ya ?arasa maganar yana dafe sautin zuciyarsa.


Murmushin gefen baki yayi , ya danna dan madannin jikin agogon hannun sa kafin ya fara magana kamar haka

'' sunana Muhammad Tijjani Idriss Ni cikekken dan ?asar nan ne,an haifeni a wani ?auye ana kiran sa da Jalmari ,
nine babba a gidan mu, kuma inada ?annai guda shida , yanzu shekara talatin kenan a duniya


Muna zaune da iyayena awannan ?auyen har kwanan yau da muke zancen
Ban shigo Rayuwar ku dan in cutar dakuba,ko dan wata manufa ba a'a ,
Nashigo ne dan cikar burina da kuma muradin *Babana* abun alfahari na,


Daka tawa yayi ya daga kiran daya shigo wayar sa yace '' eh ku jira ganinan, fa?a yana kallon mutanen falon, '' yace ku gafarar ceni ina magana na tsaya, kamun izini in shigo da ba?i suna ?ofar gidan nan, sunada ala?a da wannan zaman

Kawu yace'' anyi maka izini kaje ka shigo dasu mudai muna fatan muji, kuma muga alkhairi ,
'' godiya yayiwa kawu kafin ya tashi ya bar falon

Har yanzu falon shuru bakajin komai sai saukar nunfashin ma'abota zama a cikin sa

Da sallama suka shigo abakunan su , bisa jagorancin Muhammad

Babban mutum ne a gaba da tawagar iyalansa a baya

Duka mutanen falon saida suka tashi tsaye , dan ganin mutumin daya shigo sak Abba


Nuna shi Abba yake da yatsa, bakinsa har rawa yake wajan furta Hassan kai nake gani ko ido na ne , dama kana a raye shine baka nememu ba, ka bar mu da ciwon rashin ganin ka juyawa yayi ya kalli Dady da yake zaune hankalin sa kwonce yace yaya ka tayani duba wa Hassan nake gani agaba na ,
Sai a lokacin Dady ya tashi tsaye ya kama kafa?arta Abba yace a iya sanina ka iya tarbar ba?i, to amma ya da haka , bazaka bar dan'uwana ya zauna ba duk ka wani jero masa tambaya kamar kana a kotu, ko an tona wajan aiki ne ??
Dady ya fa?a cikin zolaya

Kawu yace'' Bismillah ku ?araso mana
Baba ya kalli kawu yana ayyana abubuwa da yawa aransa wanda yake tunanin sun faru bayan bayana, shekaran da yawa, Allah ne ma ya nufa cewa zai sake ha?uwa da ahalin sa , da yasan sai adarussalam

?arasowa suka cikin tsakiyar falon masha Allah suna da yawa balaifi, ba dan falon irin mai girman nan bane da bazai dauke bangarorin guda biyu ba

Zama suka akan carpet dukan su ,
Sai kawu ya lura da wani tsoho a cikin su, wanda zasu yi sa'anni, sai dai kawu yafi shi ?ori ,
Zuwa yayi ya kama hannun sa ya isa dashi wajan da yake zaune , sai suka jera , tsohon yana tayiwa kawu kallon ?urullah , ji yake kamar ya sanshi


Momy ma zuwa tayi ta kama hannun wata mata, Dagani zasan itace mahaifiyar Muhammad tayi mata masauki akan kujera

Sai kuma wasu yan'mata gida biyu da zasu kai sa'annin su Ru?ayya, da alama kamar yan biyu ne , da ?annen su maza biyu da kuma mata biyu wanda aka yaye ba jimawa suma da da alama yan'biyun ne

Masha Allah zari'a ta samu daga Hassan din da aka fidda rai da ganinsa
Baba
yayi wajan Abba ya rungume shi yana kuka mai tsuma rai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login