Showing 12001 words to 15000 words out of 48162 words
wajan fidda miji
Wane ne zai yarda batare da wani dalili ba yayi aure ba tare da sanin iyayansa kinga ai ba dama
Kedai ki tayamu da adu'a Allah yasa dai-dai muka aikata ya kuma bamu galaba akansu a wannan karon''' dan nisawa tayi tace to Allah ya shiga al'amarin ''yace amine
Duba agogon hannun sa yayi yaga ?arfe tara da rabi na dare
Wayan shi ya ciro daga al'jihunsa ya kira shugaban securitys din gidan yace a sami mutun biyu zasu fita da yara yanzu'' da to ya amsa yana sara masa kamar yana gaban sa
Sauke wayar yayi daga kunnan sa ya kalli Ru?ayya yace ki tashi kuje can gidan ,ki taya ta ta dauko duk wani abu datasan mai muhimmanci ne agareta
Insha Allah kafin safiya komai ya kankama
Ba musu suka tashi, daki suka nufa suka sanyo hijaban su.
Koda suka fito har daya daga cikin securityn gidan ya tada mota, ?aya kuma ya bu?e musu murfin motan,suna shiga ya rufe ya zagaya wajan mai zaman banza ,motar suka ja sai gidan Abba a daren nan
Bayan fitarsu Dady ya kuma tura wani kiran,ba jimawa aka amsa da sallama ''barka da dare ya'ya, ya ya gida ya iyali.
Barka dai ,gida alhamdulillah ''to masha Allah,ashe da yamma ka shigo bana nan '' eh ai naje mun yi magana da Hajiya ne ,dawo wana daga wajan kawu kenan kusan magriba ,na fada masa komai da ake ciki,naso mu taho tare da shi dan ya halarci daurin auren ,amma sai yace gobe akoy taron ma'aikata da zasu yi acan kanfani kuma ?arfe bakwai taron zai fara,so ba damuwa duk yadda muka yi yana goyan bayan mu ,tunda yasan baza muyi abunda zai cutar da ita ba ,yadan nisa kafin yaci gaba da cewa na tura yaran nan suje su dauko duk wani abun da ita Maryam din zata bu?ata nan kusa ''eh ai naji shigowar su yanzu,to suyi gaggawa su yi su dawo ,bana san a samu matsala,koda yake na hada su da securits guda biyu.
Insha Allah ba zasu dau lokaci ba zaka gansu,na gode sosai yaya Allah ya bar zumunci ya mana jagora, ''da amine Dady ya amsa yace ka shigo da wuri ina ayi komai a ?an?qnin lokaci''
Insha Allah , Allah ya nuna mana asubar lafiya ''amine Dady yace yana katse kiran,ganin wani kiran ya shigo a dayan wayan nashi.
Da a sallama ya amsa kiran da fara'a akan fuskar shi,bai da an miyasa yaron yake masa kwarjini ba,Adan lokacin da suka hadu dashi,ya gano kyawawan halayen shi sunfi a ,qirga ,yana kamun kai , nutsuwa, da a kuma girmama babba.
Basu jima da ha?uwa ba ,lokacin da ya nemi da ,daya daga cikin yaran aikin shi ya masa bincike akan wannan nomber da akayi wa Barister sako ,sai yake ce masa ya gaza amma akoy wanda yana tunanin zai iya ,kuma ba sai da computer ba ,da waya yakan iya datsar ko wace irin na'ura,yana fi?ira a harakar yanar gizo gizo''' bai yi sanya ba yace ya ha?a shi da shi ''bako ?ata lokaci washe garin ranar ya kamasa shi har ofis din shi
Baiyi jayayya ba ya kar?i aikin,kuma cikin ?ananan lokaci ya samowa D.P.o duk wani bayanin da yake bu?ata
Ko a jiya da safe ya same har ofis ya kai masa wasu yin information daya samu akan aikin da ya bashi''ya lura yana cikin damuwa sai faman tunani yake yi ''ya tambaye shi miye damuwar ko da wani abun zai iya yi akai.
Da har ya so ya biye masa, amma tuna wani abun yasa ya fa?a masa cewa miji yake so ya samawa ?arsa ,da kuma yadda ya kamata mijin ya kasance''ba tare da wani dogon tunani ba yace,ni idan har kun yarda da ni za ku iya bani auren,koda na wucin gadi ne ,insha Allah zaku same Ni kamar yadda kuke so''' ?ureshi yayi da ido dan ya gano gaskiyar abinda ke ransa,amma sai yaron yayi ma sa kworjini,ya ji yana iya bashi auren ,amma bayan yasan koshi waye
Kallon shi Dady yayi yace waye kai,su waye iyayanka ''nan ya fa?a masa cikkaken sunansa da kuma asalin sa''can Dady ya linfasa yace shi kenan zan ne meka bayan nayi tinani''da to ya amsa kafin ya bar wajan da tarin tunanin nuka a ranshi
Wannan shine asalin ha?uwar su da yaran
?aga kiran Dady yayi cikin dattako da sallama abakinsa'' cikin girmamawa ya fara gaishe da shi yana sosa ?eya kamar yana gaban shi,yace dama sai kuma yayi shuru ''' Dady yace ina jinka .
Dama nace bara na kira naji ku shuru ne '' eh dama ina famar kiran kane yanzun kayi kira fa?in Dady
Cikin jin kunya yace ah '' Dady yaci gaba da magani yace ai kasan gida ko '' da eh ya amsa''yace to ku iso da wuri insha Allah bayan Sallar asubahi za'a daura auren sai ku huce
Na gama shirya komai har gidan da zaku zauna na tanada ,nidai ka ri?emun ?ata da amana,kaga dai yadda komai yake tafiya.
Insha Allah zaku same ni mai ri?on amana da al'qawari,Kuma zakuyi farin ciki bisa ga yardar da ku kayida ni ''allh yasa sai zuwa asubar insha Allah ''to alla ya bamu alkairin sa
Dady ya amsa da amine yana mai katse kiran
Momy da tun dazu ta zuba masa ido tana kallon shi tace Kuma Yanzu dady ,dayake haka itama take kiranshi da shi , kuma Yanzu daga andaura Aur¨¦n zasu tafi tare da ita?'' yace eh ai n'a gama tsara Duk abunda ya dace ace nayi a matsayina n'a uba ,ya rage saura naki ne ki yi mata n'a nasiha a matsayin ki 'a uwa agare ta,basan kin san komai daya kamata ace ta sani ,idan Sun dawo sai kuzauna dabita ''to allh ya taimaka ya sa ayi a sa'a ''ya amsa da amine
Shiyasa har kullum take kara shiga ranshi ,bata ta?q yi masa musu ko da wasa,komai ya fa?a angama,a haka suke rayuwar su ,kuma yana alfari da 'ita a koda yaushe
Abangaran su Maryam kuwa suna isa gidan Abba suka fito suka nufi cikin gida,yau harda Abba a falon suka yarda shi yana waya ,koda suka gaishe shi ma hannu kawai ya daga musu lokacin suna magana da Dady
Hajiya da fitowar kenan Daga dakinta da tsarbi a hannun ta tana lazumi, suka gamu da a ita ahanyar da zata kaisu ?akin ta,suka gaishe ta ta daga musu kai tana murmushi tare da yiwa Ru?ayya nuni da hannu tana tambayar ta mutan gida''tace lafiyar su qlau
Dakin inna suka nufa ta gama sallah kenan itama tana nanna?e hijabinta ta ajiye shi, cikin zolaye tace haba shiyasa nakejin kanshi ya cikan hanci,kice amarya ce da shigo gidan
Kai inna wallahi kedai wata ra na sai ahankali,ai yanzu ba lokacin wasa bane,kuma ma aimu ba abokan wasanki bane ,ta fa?a cikin shagoba'''
inna tace ?ar nema sai yau kika san cewa Ni ba kakarki bace uwa ce ,sau nawa ake fada muku amma sai kuce ai kakani sunyi ?aramci ,dole ana rage yawan uwaye suna koma wa kakanni
Ru?ayya tace to shikenan dai kuma daga yanzu ki zaman ki a matsayin uwa kawai ,abar kakan can nan ,dan Bama yanayin wasa ayanzu
maryam dai tana jinsu ta lumshe ida nunta tun shigowar su dakin ta jingina da bango tana sauraron su ,bu?e ido tayi tace karfa dare ya ?ara yi kinga goma ta rufa mu hanzarta
Ficewa suka yi daga ?akin sunaji inna tana fa?in to maryam sai wani lokacin insha Allah zamu kai miki ziyara
Dakinta suka nufa ,da taimakon Ru?ayya ta ha?a kayanta da duk wani abun da zata nema mai muhimmanci,ciki harda wannan littafin da Abba ya bata jiya da yamma
Akoti biyu suka janyo da sai ?ar ?aramar jakar hannu'
Afalon suka iske duk mutanen gidan nan,gidan nan abba da inna suka ?ara bata shawarar wari kafin ya kira wani daga cikin yan aiki ya fitar musu da kayan wajan mota,har abakin motar inna da Hajiya suka rakasu , Ru?ayya ta fara shiga , Maryam zata shiga taji an ri?e hannun ta juyowa tayi dan ganin ko waye
Hajiya ce sai kawai ta fa?a a jikin ta ta fashe da kuka ,dama can jurewa take ,amma tun ?azu take so tayi kuka ko zata sami sassauci a zuciyarta''' bubbiga bayan take yi ahankali, sun kusa minti uku a haka sai da Abba yaji shuru basu shigo ba ya. Leko dan ganin abinda ya zaida su ,sai ya gansu ahaka '''karaso wa ya yi ya raba tsakanin su ya tura Maryam a mota ya rufe yana daga musu hannu mati?in motar yaja suka fice daga gidan
asuba ta gari
?arfe biyar da mintuna talatin aka daura auren Muhammad Haruna da Maryam Hussaini,akan sadaki dubu hamsin a masallacin ?ofar gidan Dady Almustapha
Abba shine al'walin ango sai Dady ya zama al'walin amarya tarin jama'ar da suka zo sallahr asuba ta wannan ranar sun shaida daurin auren
Masha Allah Dady ya tanadi komai na al'ada irinsu horo da dabino da dai sauransu
Awajan bada sabaki har Muhammad ya ciro daga al'jihunsa zai bada ,sai Abba ya riga shi bada wa,haka kawai yaji hakan yazo ma sa a rai
Cikin gida
Masha Allah ,muna godiya dga Allah daya sa hakan ya faru cikin amincewar sa ,ba wani ?ata lokaci za'ayi ba
Bangaren da Muhammad yake zaune ya kalla yace Muhammad ''dago da kansa yayi ya kalli Dady ''dady yaci gaba da fadin wannan shine asalin mahaifin Maryam ya nuna masa Abba, wannan kuma itace uwarta a yanzu ,dan mahaifiyar ta ta da?e da rasuwa,ni kuma ya'yan mamata, sauran kuma duk zaka sansu daga baya insha Allah
Magana ta biyu anan shine na baku gidana na *jaune cadre* a can zaku zauna nasa an zuba komai na bu?ata aciki ,saboda haka yanzu zaku tashi muje tun kafin gari ya gama waye wa
Dady ya fara tashi sai kuma Abba,kafin su duka suka tashi ,kayanta aka fiddo aka saka a mota kafin aka raba su daga jikin juna ita da Ru?ayya ,tun ?azu suke kuka sun ?i suyi shuru
Mota biyu suka yi,Dady, Abba da Muhammad a ?aya,dai kuma Momy da Ru?ayya da Maryam a dayar
Su su Abba Muhammad ya jasu,su kaisu Momy direba ya ye tu?asu,ahaka har suka isa gidan da zasu zauna amatsayin ma'aurata
Cikin dan lokaci suka dai-dai ta komai suka musu sallama da fatan alkhairi tare da ?ara jaddada musu muhimmanci ri?on amana ,da kuma illar karya alqawari
Har ?ofar gida Muhammad ya rakasu yana musu godiya da yabawa da ?aramci irin nasu
Su Dady da suka shiga mota ?aya ,yace direba yaje ya sauke Abba a gida
Anan suka rarraba kowa ya kama hanyar gida cikin nutsuwar zuciya .
Kusan awansu daya a hanya,saboda gosulo da adda koy a cikin gari kasancewar yau ranar Litinin ne,ranar aiki wacce ko nasara yana tsoran ta.,ga ma'aikata ga yan 'makaranta garin sai ya dauki haya niya tunda safe
Shigowar su gidan yayi daidai da kururuwar neman agajin gaggawan da wayar Dady ke yi bai tsaya ya dakga kiran ba sai da ya isa falo ,ya zauna akan kujera
Ya duba wayar yaga da sabuwar number aka kirashi,har zai bi kiran,wani sabon kiran ya shigo a karo na biyu
Ha ka kawai Dady yaji gaban shi ya fa?i ,amma ya dake da gada ya kara wayar a kunne ai bai idasa sallamar da ya fara ba jin abun da ake gaya masa wayar ta fa?i a qasa tji kake rassssssssssss
wayar Dady yayi daidai da isowar Momy wajan''tace subahanallah Dady lafiya ''innalillahi wa'inna ilaihi raji'una kawai yake fa?i,kafin daga bisani ya tashi tsaye
tashin hankali ya bayyana akan fuskarshi,dayar wayarshi ya laluba ya Tura a aljihu yafara tafiya zai bar falon cikin hanzari
Momy ta kasa hakuri da yanayin da ta ga yashiga daga dawowar su gidan,ta Kuma cewa dan allh ka fa?a mun miyake faruwa ne ,bai kamata ka fita a yanayin da kake ba
Juyawa yayi ya fuskance ta yace Hussaini ne suka yi accident a hanyarsu ta komawa gida ,Yanzu haka suna nationale hospitale ( babban asibiti )
Ai batasan lokacin da ta zauna ba tana jaddada kalmar shahada
Yana fita s¨¦curity suka shiga Sara masa ,kamar ba yanzu y
Ba jimawa suka gaishe Shiba
Motar da zai shiga ya nufa,nan danan Aka bu?e mai ?ofa ya shiga ,aka tayar ,sai bayan sun fito daga gidan har sun fara barin unguwar da suke kafin yace babbar asibitin gari zamu
Nan direban ya juya akalar motar shi zuwa inda aka umarce shi
?aran wayar Dady ya cika motar amma bai ?aga ba ,kuma ba'a fasa kiran ba har sai da dayan security na zaune a kujerar me zaman banza ya juyo dan ganin miya hana me gidan nasu daga kiran sai yaga ba alamar sawa a tattare dashi ,sai yayi shuru
Haka wayar ta gaji da neman agaji har me kiran ya ha?ura
Gudu suke sosai dan haka mintunan kadan ya kawo su asibitin
Tun kafin su shiga sukaga taron jama'ar gari wanda akayi akan idanun su ,dayawan su wajan aiki zasu ,wasun suma dalibai ne , amma saboda kar ayi basu sai da suka zo har asibitin
Abun a tsakiyar hanya ya faru dayake akoy yawan mutane awajan nan danan aka sanar da jami'an tsaro,yanzu haka suna can suna ta faman awne awnan awajan, Danganin minene mu sababbin faruwar accident din
Direban bai wani sami rauni sosai ba,har an masa traitement na ciwukan daya ji a ?afa da kuma ?oshin shi
Abba kam yana koma tun da aka kasu a ambulance likitoci su ka karbe shi ,da aka shigar dashi wani daki haryanzu ba wanda ya ?ara fito, suna can suna faman ceto rayuwar sa, daya daga cikin yan sanda ne yake yiwa Dady bayani cikin girmamawa
'' Dady yace waye akan aiki ne a yanzu ''yace jami'i idriss yallabai'' cikin nazani Dady yace kayi magana dashi bana san aja Magana kan accident din nan ,ya rufe case din yanzun so kar inji zancen wani bincike ko nan gaba '' to yallabai ya amsa tare da barin wajan
Barinshi wajan kenan wani likita daga ya fito daga ?akin da aka sa Abba ,Dady ya tareshi da tambayar ya ake ciki,likitan yasan Dady sosai ,suna gamuwa a waje mabanbanta,cikin damuwa yace da Dady ya biyo shi ofis dinsa
Bayani ya mishi akan halin da Abba yake na mutuwa ko rayuwa
Hankalin Dady ya tashi ainun , ya rasa ina zai sa ranshi, Hussaini wani jigo ne na rayuwar shi idan ya rasa shi ko wani abu ya sa meshi ya zai yi
Kuma yasan sarai bazai huce sharrin su Adam ba
Kuma wallahi idan har wani abu ya sami dan'uwansa bazai barsu ba
Wannan shi ne last da yardar ubangiji a wannan karon sai ya ka ?arshen komai
Magana yake amma yaji shuru Dady ya lula duniyar tunani ,har sai da likitan ya dan buga table din dayake gaban sa ,kafin Dady ya dawo cikin tunanin sa ya'' yace dan allh zan iya fita dashi waje,inaso ya sami kulawa mai kyau,''mi zai hana tunda dai munyi ?o?ari nunfashisa ya dawo amma shi zai dauki lokaci kafin ya farka dan ya shiga doguwar suma sanadiyyar firgici da zuciyarsa tashi ga
To ba damuwa insha Allah zuwa gobe idan nasamu yadda nakeso sai mu fice
'' to wace qasa kake ganin zamu tafi ''yace inaga kuje India acan zakufi samun kulawa ,akoy wani abokina doctor ne a babban asibitin jinya a mumbai zan ha?aku dashi,insha zai sami sauki.
Yanzu zan iya ganin shi ''eh zaka iya dubashi amma saidai ta class dan bama san a maida mana aiki baya daga nan har kubar asibitin ''to ba damuwa yanzu bara naje dan Allah ka kula min dashi kafin in dawo ''ya amsa da to insha allah
Cikin hanzari ya fito ya nufi dakin ,Abba ya hango ta cikin glass an jona masa na'urar da zata taimaka masa wajan fidda nunfashi wato oxigene an kuma daura masa ruwa mai ha?e da allurai a hannunsa
Adu'ar samun sau?i Dady yayi masa kafin ya juya ya nufi inda akai parking motan daya zo da ita,shiga yayi suka mara masa baya
Gidan Abba suka nufa direct a hanya ya kira Momy da ta gaji da kukan ta ta ?oshi,bayan tayi ta kiran dadyn lokacin ya hanyar zuwa asibitin amma bai ?aga ba
Daga kiran tayi da sallama abakinta tana tambayarsa jikin Abba , Allah dai yasa bai ji ciwo ba''kina ji ko ki samu akai ku gidan Hussaini yanzu ,kar kibar Ru?ayya kuje da ita cewar Dady yana fa?in hakan ya kace wayar
?ara sautin kukan ta Ru?ayya tayi tana cewa shikenan Abba ya tafi ya bar mu,ita a tunanin ta ko abban ya rasu ne shi isa Dady yace suje can