Showing 15001 words to 18000 words out of 48162 words

Chapter 6 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah

10 Jul 2024

3355

gidan ,dan dama tunda taga Momy cikin damuwa ta Matsa mata da tambaya sai da ta fa?a mata ,kuma tana ji lokacin da Momy take wayar
''ke dan Allah kiyi mana shuru waye ya ce miki Hussaini ya mutu,kuma ma ko mutuwa yayi ai ba kururuwar kuka zamuyi masaba,ki tashi mu tafi kawai

Wata number Dady ya a
kuma kira yace kaje kanfani dauko kawu yanzu ku zo dashi gidan Hussaini, zaman ujula ne ka hanzar ta ''to yallabai

Mu huce ofishi akoy abunda zanyi ya fadi kamar bashi yayi maganar ba duk kanshi yadau zafi, yama rasa abin yi
Suna isa ya sauka ya fara takawa cikin takunsa na zaratan maza,duk da ya fara girimta amma har yanzu yana bada gudunmawa sosai ta hanyoyi dadama ,gaisuwa ake miga masa ta ko ina ana sara masa , direct ofishin sa ya fice ya zauna ya cike wata takar da kafin ya bi wata hanya ya fa?a wani ofishin

Cikin girmamawa ya shiga mika tasa gaisuwar ta ban girma zuwa ga shugaban yan'sanda na wannan jahar''amsawa yayi shima cikin girmamawa dan baya raina na qasa dashi ko ya yake yace'' sannu Almustapha ashe accident din da akayi na yau ya shafi ahalinka,sako ya same ni cewa kace abar bar duk wani abinci ke akan accident din ,nasan bazaka yi abunda bai dace ba shi isa nace abarshi,to ya masu jikin fatan suna samun sau?i

To alhamdulillah za'ace yallabai shi direban bai samu wani rauni dayawa ba ,amma shi Hussaini din sai ahankali''cikin razana yace kana nufin dama Barister Hussain ne ya yi ha?arin ?
Eh shine cewar Dady yanzu haka nazo neman izinin a jiye aiki ne na wani lokaci,zan fita dashi waje ko Allah zai sa a dace ,ya fadi yana dora takardar ajiye aiki daya rubuta
Ba wani ?ata lokaci ya sama hannu tare da fatan sannun lafiyar dan'uwansa kuma aminsa

Yana tafiya yana bada umarnin a shirya masa tafiya zuwa Indiya gobe_gobe ,ko ba jirgin da zai tashi gobe to a tana dar masa mai zaman kansa ,zai biya ko nawane shidai burinsa shine samun lafiyar amininsa tramsfer yayi na magudan kudade dan komai yazo masa da sauki ,daya ke dama abokin cinikin su ne na danan aka shiga shirya masa tafiya ,dama suna da copie na passford nashi

Kai tsaye gidan Abba suka nufa lokacin har ?arfe sha biyun rana yayi,sun iske su Momy sun dade da iso wa tambayar duniya babu wacce inna bata mata ba akan ta fa?a musu mi yake faruwa ta ganta afujajan gashi duk tayi kuka ,amma Momy ta?i tayi magana ahaka su kawu suka shigo shida sakataren Abba ,wanda shine Dady yace ma yaje ya dauko kawun daga kamfani

A falo ya same su duka a zazzau ne suna jiran zuwan shi ,harda hajiya wacce ta da?e da sadda?arwa cewa wata jarabawar ce take shirin ta risketa,tana adu'ar Allah ya bata ikon cinye ta ko wace iri ce

Zama yayi ya gaishe dasu ,kawu yace'' Almustapha nasami kiran gaggawa daga gare ka, kuma dana zo sai iske ashe bani kadai kasa akira ba Allah dai yasa lafiya kawu ya ?arashe Maganar cikin jimami
'' eh kawu an daura aure kamar yadda na gaya muku har munkai ta gidan ta, lafiya muka rabu dashi ,ahanyar su ta komawa gida shida direba suka yi accident ,yanzu haka suna babba asibiti

Salati da sallalami ne suka cika falon ,inna da Ru?ayya sai kuka suke
Kawu yace'' ba kuka ya kuyi ba kuyi masa adu'a Allah ya tashi kafa?un sa

Nan Dady ya fa?a musu abinda ya tsara na fitar da zai yi da Abba qasar waje yace'' na ajiye aikina na lokacin da dan'uwana zai sami lafiya, inaso ku ha?u a waje guda ,ma'ana ku zauna anan,ita Maryam ku barta a can inda take ko waya banaso waninku yayi da ita,gudun kar a sami matsala,zanyi magana da mijinta shi zai san yadda zai gaya mata ta fahimta
Maganar kasuwanci kuwa ga kawu zai kula da komai , sakataren Abba ya kalla yace a ajiye duk wani casa_casen da kasan tana jogaran ta ka basu uzurin rashin lafiya
Insha Allah zan kira *Safwane* ya dawo gida karatun nan ya isa hakan nan ,shi zai kula da harakar cikin gida kafin dawowar mu ,nasan a ka?an zamuyi wata da shida kafin su bamu sallama dan har shekara anayi acan indai sukaga jiki ya?i sau?i

Masha Allah _allh ya bashi lafiya ya tashi kafa?un sa, insha Allah zaka sami komai fiye da yadda baka tunani ,za muyi iya bakin ?o?arin mu

Da dare Dady ya kira Muhammad lokacin ya dawo daga sallah isha'i kenan ,yake gaya masa duk abunda ya faru , cikin tashin hankali yace'' innalillahi yanzu ya jikin nashi
Dady ya ce ka kwontar da hankalinka.
Muhammad zuwa gobe insha Allah zan fita dashi Indiya so zanbar aikin da muka fara a hannun ka ,dan Allah ka kulamin da komai kafin dawowar mu na ajiye aikina koda mun dawo sai naga karshen miya gun cen kafin na koma bakin aiki
Cikin sanyi murya Muhammad yace to Dady insha Allah zan kula ,amma baka tunanin accident din kirkiran shi aka yi ''eh dama shiryayan abune da suka shirya ,kuma insha Allah a wannan karon bazan barsuba ,nidai inga tashin Hussain din kawai shine

Kwonce akan kujera 3 siter tun safe da su Abba suka kawo ta ba abinda yake tashin ta anan sai sallah,da azaune take yanzu kuma akwonce shiyasa bai ganta ba har lokacin, da yake wayar yace '' ka kar ka bari Maryam ta ji abunda ya faru kawai kace mata munyi tafiya Ni da abban ta ,kuma ma zan kirata da zaran mun sauka ''to shikenan Dady ma gode Allah ya ?ara girma ya ba Abba lafiya mai ?orewa
Da amine Dady ya amsa
katse kiran yana zama akan kujerar dake bayansa ,sai yaji ya zauna akan ?afar mutum
Juyawar da zai yi sai ganinta yayi akwonce tana ta kuka mara sauti

?asa yayi da guiwoyin kusa da fuskar ta yasa hannu ya shafo hawayen da suke zubowa akan fuskarta yace'' kuka kuwa , to minene na kukan Please dan Allah ki tashi muyi magana
Bamusu tashi yace miye dalilin kukan ki Please
Miyasa mi Abba na, shine tambayar data fito daga bakin ta, sannin taji wayar dayayi yasa ya ?i ?oye mata komai ,ya fa?a mata duk yadda suka yi da Dady

Kuka take sosai yana rarrashin ta ,tare da mata maganganu masu da?i wanda zai sa ta ji sanyi aranta
Tunawa da yayi cewa basu ci komai ba ayinin yau daga shi har ita yasa yace mata ina zuwa
Kicthing yana nufaa dan sama musu abinda zasu ci

Washe gari jirgin su Dady ya daga zuwa Indiya
Cikin nasarar Ubangiji suka sami tarba daga mahukuntan asibitin abunka da manya nanda nan aka shiga ba Abba agajin gaggawa


Bayan wata hudu

Abba yana samun sauki sosai ,ya da?e da farfadowa har ya fara magana , kuma suna waya da su Momy lokaci_lokaci ,har Maryam ma sunyi magana da ita kusan sau biyu
Yace kwontar da hankalinta yana samun sauki , tafiya ce dai har yanzu bai faraba saboda jiki ba ?ori

Kawu yana kula da kowane bangare tare da tallafin sakataren Abba
Yaya *Safwane* bai sami dawowa ba saboda jara bawar ?arshe da suka yi A ?arshen watan daya wuce ,yanzu haka yasa ranar dawowa next week,amma bai wani sami amsar kirki daga Dady ba saboda yana fushi dashi na rashin dawowar da bai yiba lokacin daya ne meshi

Tausayi ,kyautatawa,da kuma tausayin junansu ne ya shiga tsakanin Muhammad da Maryam ,suna zaune lafiya sun fahimci juna ta yadda har tasan abubuwan dayafi so da kuma wanda baya so ,ta karanceshi sosai,ta karanci halayyar shi da kuma abunda yafi ?orewa akai har ta ?udura aranta cewa zata yi anfani da wayon sa,kwazon sa ,da kuma kasancewar sa na miji wajan daukar wa abban ta fansa akan makiyan sa
Wannan alqawarin tane kafin dawowar su Dady take so ta ha?a komai na binciken ta game da aikin da su abban suka fara na tsayin shekaru da kuma musabbabin accident din da mahaifinta yayi wanda yayi sana diyyar barinshi qasar na tsawon lokaci

Wannan shine asalin labarinta da abunda ya kunsa

??
Dawowa cikin asalin labari
Tunda ta fara karan ta littafin yake abakin kofa a tsaye kuma yana ji har inda ta tsaya ,ta ?ora da tunanin abunda ya faru bayan bata littafin da Abba yayi ,yadda akayi auren su da yadda suke zaune ayanzu..................




Tsab ?a?a_?ara_?a?a masu karatu mi kuka fahimta a labarin nan ????


Shin kin gane inda labarin ya nufa kuwa?????

Mi zakice game da labarin Maryam da kuma asalin ta!!!!


Shin mizai faru nan gaba ,mun dai dawo cikin asalin labari

Yanzu ma aka fara
Please idan kun karanta inga comments ????


?

Ta kowa ya fara yi daga inda yake a tsaye ya iso bakin gadon da take zaune kallon shi take tun daga ?afafuwan sa har takai idanun ta kan fuskarsa, ?ureshi tayi da ido sosai abunda bata ta?a bayi tun zamansa da ita,kallon sa take kamar wacce ta ke so ta tuna wani abun
Tsak tunanin ta ya zatsaya zuciyar ta tashiga harbawa da sauri_dasauri sai yanzu ta tuna a inda ta ta?ajin wannan kalmar *Mk* idan har bata tuna akai wannan kalmar a labarin data ida tunawa ayanzu ,to idan haka ne minene alaqar yaya Muhammad da wannan kalmar da har taji yana waya akan ta
Anya kuwa ba yaudarar iyayen ta yayi ba ,shima yana cikin azzaluman can

Tayi nisa sosai cikin tunani har batasan sanda ya zauna a kusa da ita ba ya hauda kansa bisan kafadarta yace ''daga tuna baya kuma sai ki shiga dogon tunani har haka ,kiyi ha?uri insha Allah Abba zai sami cikakkiyar lafiya,zai dawo ya ci gaba da rayuwa cikin farin ciki kamar kowa
Shuru tayi masa kamar batanan, ko tabatan nan daya yi sai taji duk bataso ba , sa?anin da, da suka fara fahimtar juna ta yadda hatta bacci yanzu a ?aki ?aya suke yi,ya lura da hakan sai ya tashi ya nufi toilet , al'wala ya ?auro ya fito yana goge fuskarsa da tafin hannayan sa ya ga tana nan a inda yabarta ,fita yayi ya rufe kofar falo ya kashe haske ya dawo dakin
zama yayi a inda ya tashi yace dan Allah ki tashi ki kwonta hakanan
banaso in ganki cikin damuwa Allah kuwa ya fa?i yana lan?oshe kai alamar taji tausayin shi
Basarwa tayi da fa?in yau ko kunyi magana da su Dady kuwa ,da ''eh ya amsa ta ,yace ko kina so kuyi magana dasu ne, cikin hanzari tace dan Allah baka Ni nayi magana dasu kaji nan ta shiga ro?on shi

Tasan koda ta goda kira da Tata wayar baya fita ma bare ayi zancen ya shiga kuma duk aikin Dady ne yasa Muhammad ya rufe mata kofar sadarwar dayake tsaninsu gudun kar abi giddigin number ta har asan inda take ,kuma batasan da anyi haka ba ita a tunanin ta ko sha'anin network ne

Ganin magiyar ta?i ?arewa ya ya manta wayar a falo tace ta dauko sai tayi kiran
Cikin jin da?i ta tashi tana murna jin zatayi magana da Abban ta , cikin duhun falon ta shiga laluben wayar shi akan kujerar daya zauna ?azu a dawowar shi ,tsaraf taji an ri?e hannunta
Ihu ta ?urma tana kiran yaya Muhammad, ke yi shuru da a Allah nine fah ya fa?i yana haska fuskarshi da hasken screen din wayar shi , ajiyar zuciya ta sauke tace'' wallahi kanan tsoro kaida na bari a ?aki yaqa qa zanyi tunanin kaine

Janyo ta yayi ya y
Zaunar da ita kusa dashi cikin dariyar tsokana yace kedai kawai ki e matsoraciya ce Sayyadar tawa ''eh din nidai ka bani na kiransu dan Allah,ta fa?i kamar zatayi kuka

Mi?a mata wayar yayi ,tace to ai baka fidda mun security ba ,yace'' ki fidda da kanki
Ganin yanaso ya jamata rai ne kawai yasa ta ajiye masa wayarshi akan cinyarshi
Bata kai ga dauke hannun taba ya ha?a da hannun da wayar ya ri?e yace '' karkiyi fushi Please baya miki kyau
Ai sunan ki ne securityn ki saka kigani zai bude
Daukan wayar tayi ta rubuta sunan ta a jikin *Maryam* nan take wayar ta bu?e mamaki bai bartaba sai da taga photon ta a saman screen din wayar,ita da kanta bazata iya tuna yaushe tayi photon ba ,gashidai ya nuna kamar a makaranta akayi photon

Mikike tunani ne matar Muhammad ,kunya ta rufe ta jin sunan daya kirata dashi sai tayi sauri ta shiga contact ta fara neman number Dady
Kira ta tura tana jiran tsammani ,
Sallamar Dady taji cikin nutsuwa ta amsa ta fara gaida shi da tambayar ya me jiki
''Dasau?i cewar Dady ,amma yanzu yana bacci ya yanayin maza a ba?on waje Dady ya tambaye ta ,tace alhamdulillah ''yace kiyi ha?uri ki zauna agidanki insha Allah wata rana za kiyi alfahari da wannan abun, kedai ki kasance mai biyayya ,gaya muka Miki kuma zakiyi alfahari da hakan watarana
Cikin sanyin murya ta amsa da''to Dady insha Allah zaku same ni fiye da yadda kuke tunani
Masha Allah _allah ya albarkaci rayuwar ku ,kafin tace wani abu tuni ya yanke wayar
Danjin tayi tana razari mamaki take ,sau kusan uku kenan suke waya dasu dadyn kuma bai ta?a tsayawa yaga karshen maganar suba sai ya katse kiran ,bai ta?a cewa ta bashi Muhammad ?inba ,kuma shima bai ta?a kiran Dady agabanta ba
Koda wasa basa yarda suyi waya agabanta ,to miyasa ?
Miye dalilin da yasa yake nuna kamar yasan komai na rayuwar ta ,ita dai tasan basuda wata alaqa dashi hasali ma ita sai da aka daura aurenta dashi ta sanshi
To waima waye shi , miye tsakanin su da Dady da har suka dauki yarda suka bashi,harda damqa masa amanar ?arsu
Ita fah tama fara zargin sa ,tabbas yasan wani abu na rayuwar su ita da iyayenta ina hakaba ya akayi taji kalmomin nan ranar yana waya
Dole a gurinsa zata sami amsar kalmomin tunda dama agunsa ta jisu
Wayar ta danna dan ta fita daga cikin jadawalin kira kafin ta basa
Idanun ta suka sauka akan kiran daya shigo wayar na ?arshe kafin kiran Dady
Sunan ta maimaita ta kuma ?ara maimaitawa idan har idanun ta sun nuna mata daidi to *MK* taga an rubuta
Turqashi mi kenan, ta kisa abubuwa sunfi goma acikin ranta
Innalillahi kawai take fa?i a cikin zuciyar ta tabbas su Dady sun kara makasa indai har ya tabbata da wancan *MK*na cikin binciken su dashi yaya Muhammad yake waya

Juyawa tayi ta kalli inda yake zaune sai taga kamar bayanan ,haska screen din wayar tayi taga dagaske baya nan ,sai tsoro ya kamata ,kar aje dama da abunda ya shirya kafin zuwan wannan ranar innalillahi,fmta fa?a a bayyane nan take wani ?arfin zuciya yazo mata taji yau sai taga ma?urar abunda yake ?oyewa da kuma gaskiyar koshi waye
Tashi tayi da wayar a hannun ta tana haskawa har takai dakin ta
Koda ta shiga baya dakin dama haka taso key tayi ?ofar taje wajan ajiyayyar kwantar ta,tabu?e gidab ?asa wanda shi murfin katako ne , sabanin saman duka murfin na glass ne
Janyowa tayi ta fito da computer ta dayake bata rabuwa da caji akoda yaushe
bakin gado ta dawo ta zauna ta jona wayar a computer ta shiga binciken sa kai.....................




Bincike sosai tashiga yi
Cikin jadawalin kira na Wannan sunan , kusan kira tara tagani kuma duka shigowa suka yi,,
Tabbas akoy lauje cikin na?i ,dubawa tayi ko zataga number ,amma sai taga boyayyiyar number ce ,shi isa kira bazai fita ba saidai ya shigo,kuma daga waje kiran yake shigowa

To miye ala'qarsu da me wannan sunan
Ya Ubangiji ka bu?a Mani ?wa?walwata ta yadda zan iya ?aukan wannan sar?ekken al'amarin
Ci gaba tayi da dubawa,cikin message ta dawo ,sai taga wani sabon sa?o da bai fi mintuna biyar da shigowa ba, hannun ta har karkarwa yake wajan dannawa dan ganin mi sa?on ya?umsa
*Biyu ga watan gobe nake saran zan shigo qasar, ina fatan zan tarda komai ya kammala* wannan shine sa?on da ta gani , nan take hankalin ta ya ?ara tashi ,dannawa tayi taga ko zai yi reply amma ya?i yi
Tabbas zargin ta ya tabbata yaya Muhammad yanada alaqa da binciken su Dady ,kuma shine ya zo yake musu zamba cikin aminci ?

Ya zama dole tasan koshi waye, Google ta fa?a dan nemo bayanai akansa da kuma rayuwar sa
*Muhammad Tijjani Idriss* shine asalin sunan sa , ta sami photos nashi dayawa a shafukan sada zumuntar data dudduba, yanada shekara talatin kenan a duniya,bayan wannan ta kasa samun wasu bayanan dangane da komai nasa,
Ya boye komai ,tabbas yanada dubara da kuma wayo sosai

Tunani tashigayi ,duk kanta ya kulle tama rasa mi zatayi Yanzu
Galerin wayar ta shiga ko zata samu wani abun , vid¨¦os ne da photos birjik ,nan ta fara dubawa daya bayan daya , acan ?asa taga wani photo kamar na Abban ta,janyo shi tayi da kyau taga tabbas wannan Abbanta ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login