Showing 165001 words to 168000 words out of 261814 words

Chapter 56 - AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE.txt

MAMUGEE   

07 Jul 2024

59018

Kiransa cikin sa'a ya tashi kuwa Nan suka fara magana bayan ta gaidasa.

Har suka Isa wayar sukeyi sai da zata shiga exam sukai sallama bayan ya mata adduoi sosai,

Babbah ta kira Shima Amma har lokacin Bai tashiba Dan haka ta shiga exam dinta kawai.

Acan gida ma Hafiz na gamawa dayake shi ya gama nasa karatun na 2yrs ne yayi tini ya fara aiki da babban matsayin dana Ameenatou dinne yake Kai kafin ta gama duk da matsayi daya zasu hau a kamfanin.

Tareda Arfat ya fita zuwa office sbd yau ba Wani aiki ne dashi sosaiba,

Suna fita Dadah ma ta koma bangarensu har lokacin Babbah Bai tashiba Dan haka a dining din palonsu ake jere masa nasa abincin Dan Daman can su basa joining Jamaar gidan cin abinci a table musamman idan Omar Yana gari.

*****Karfe biyu ta dawo gida ta tarar da kowa Yana jiranta cikin farin ciki da murnan gamawanta suka fara murna suna tayata murna sosai,

Mum Nur ce ta rungumeta tana cewa

"Congrats my girl"

"Thank you Mum Nur"

Didi ma rungumeta tayi cikin farin ciki Da Jin dadi kafin Fatmah ma datake gida ta miqa hannu ta tayata murna fuska a sake.

Daidai lokacin ne Hafiz da Arfat suka dawo fa gudu yayo gurinta yana nuna mata abinda yake hannunta ta dagasa daqyar sbd yanada nauyi tana kallan Yaya Hafiz Dayake kallanta Yana cewa

"Finally Lady AM budurwan Babbah ta gama karatu, congrats Lady Jden"

Dariya tayi sbd a yanzu duk lokacinda aka ambaceta da sunan budurwan Babbah farin cikine ya ke rufeta sbd haryanxu duk yanda ta samu sauyin da wayewan ita dai dince budurwan Babbah da haryanxu yake jinta kaman yar jaririya Baya ganin girmanta duk da lafiyayyan jikan data dire masa.

"Yaya Hafiz thank you,Amma ka Tina alkawarinmu right??

Dariya yayi Yana wucewa hanyar dakinsa Dake gefensa shi Daya Yana cewa

"Ban manta ba"

Yana wucewa Kai tsaye palon Babbah ta nufa daidai Yana fitowa zai tafi makarantar tata da kansa su dawo tare sbd farin cikinsa Baya misaltuwa kaman yanda Omar yake can farin cikinsa a bayyane na ganin wannan Rana.

Hannu Babbah ya miqa mata daidai lokacinda suka Hade a tsakiyar palon fuskansa a washe da farin ciki yayi Wani irin haske Shima ya sauya sosai Hutu ya ratsesa daidai gwargwado.

"Budurwata ayau ta zama mace itama ta tashi daga yarinya yar makaranta ko?"

Dariya tayi tana kama hannunsa cikin nata tace

"Babbah ai kullum ni baby ce a gabanka,
Thank you."

Dadah data qaraso ciki itama zaunawa tayi tana kallan yanda Ameenatou din ke narkewa a gabansuĀ  kaman dai koyaushe yanda suka Saba abunsu tafara sakawa karatun da rayuwarta albarka harma da Arfat da babusa a zancen.

Bata Wani zauna sosai ba ta miqe ta fita ta haye Samanta inda dakinta Dana ARFAT ne kadai a saman sai Palo wadatacce sai kofar da zata sadar da ita zuwa palon Dad dinta.

Dayan bangaren saman shine na Uncle Ahmed da matarsa aunt Didi sai dakin Fatmah itama a saman,Hafiz Kuma bangarensa daban.

Komai na Ameenatou da Arfat a gidan ya banbanta Dana kowa duk da na kowa dinma duniya ce me zaman kanta Dan kuwa kaf gidan baka gane waye Asalin 'dan me gidan waye bare,

Rayuwar Hutu da daula kawai sukeyi da wayewa da zallan ilimi sbd ko Babbah yanzu yana shiga mutane ba laifi sbd tini yayi abokin hira Wani dattijo Dan boko dayake zaune kasar da yayansa da matarsa yayi retire tini zaune yake a gida Yana hutawa Kuma me kudi sosai Amma kasancewan baida matsala ba ruwansa sosai yake buqatan Abokin hira da tattauna tsufa da lokaci tini suka dinke da Babbah dayake a kusa suke Dan Hakan kusan koyaushe suna tare kodai anan gidan can bangaren hutawar Omar ko a gidan shi Alh Al'ameen din.


Bedroom dinta ta Isa Kai tsaye Arfat Yana biye da ita Yana rigimar a cire masa kayansa damunsa sukeyi.

Tana shiga bedroom din qamshin turarenta na Rasasi Daya kama dakin da sanyin AC suka buso mata lumshe idanuwanta farare tana qarasawa ciki ta ajiye wayarta dake hannunta sbd handbag dinta tana shigowa sarrah ta karba ta hawo sama da ita.

Kayan jikinta ta zare ta janyo bathrobe ta wanka ta Saka jikinta gajera fararen dogaye cinyoyinta Dan bayyane ta nufo inda Arfat yake zaune a couch Yana Shan smoothie Daya shigo dashi Yana Sha Yana rigima.

Zaunawa tayi gefensa tana cewa

"My blue eyed champ zaqin ya Isa haka zo Mommah tai Maka wanka.,

Karban abinda yake hannunsa tayi ta ajiye kan table tareda zaran tissue ta goge masa bakinsa tana kallan fuskansa cikeda tsananin so da kauna tareda tinani da burinta Daya da a duniya takeson cimmasa fiyeda komai akan 'danta,

Lokuta da dama ARFAT Yana mata yanayi da Haroon Wanda tinanin hakan kadai Sai Yana bata tsoro da fargaban idan b ciwonta ne ke Neman dawowa ba sbd Babu ta yanda zaayi 'danta yayi kama da Wanda bayama duniyar,
Ta bangaren Daya kuma tsoro da mamakinta shine ta yanda babynta yazo a bature tamkar ba itace ta haifesa ba Kuma Tako ina bata hada jini da turawaba,
Kakanninta na asalin Jadens Kuma da ake fada basu hada jini ba bare tace daga can ta debo jini haihuwar baturen baby.

Babban burinta a dunuya yanzu shine idan ta tsayu a Kan kujeranta datake Kai yanzu shine neman sister Ashley da Hafiz ya tabbatar mata da ita ce kadai zata iya sanin waye uban cikin sbd a yanda bincikensa yazo itakadaice tasan yanda Ameenatou tayi rayuwa a asibitin tin daga ranar data shiga har ranar da suka rabu babu abinda ba itace take kulawa dashi ba na Ameenatou.

Basa Nigeria Amma duk wani bincikensu akan Neman sister Ashley Hafiz Yana gudanar dashi daga Nan din batareda sanin kowa ba daga shi sai Ameenatou din,

Bata San kamannin sister Ashley ba a idanuwanta Amma yanda take samun bayanan da ake samowa da yanda Suke fada mata yanda taso ta ko bayan dawowanta hannunsu batada abin fada sai sunanta ya saka takejin kaunarta da tsananin son ganinta da son sanin waye uban 'danta sanyin idanuwansu.

Sarrah ce ta shigo dakin dauke da Madara me dumi da aka gama hadawa AM din Dan kaidanta ne Shan Madara me dumi kafin cin abinci.

Acikin glass jug ne da cup akan tray ta ajiye kan table tana sake mata barka da dawowa tana kallan Arfat Dake Kiran sunanta Yana dariya.

"Thank you sarrah
Ki Jira nayi masa wanka kafin na fito kuje dakinsa ki shiryasa Shirin bacci sbd zamuyi bacci kafin yamma kaina yana Dan ciwo.

Toilet ta jasa suka shiga wanda yake a fadade kaman ba toilet ba sbd tsari da tsafta tareda qamshin dayakeyi,

Komai na amfaninta su toiletries nata na musamman ne gasunan a jere,

Shower gels da toothpaste, mouth wash da face wash da towels na amfaninta duka a tsare suke designers da ordernsu akeyi ana ganin sun kusa qarewa Ke ciresu a jera mata wasu masu aikinta kenan kuma kusan komai na amfaninta Dana Arfat hakan ne ake masu basa qarewa har karshe ake siyo wasu a dauke waincan a jere sabbin.

Da Asalin original bismd akewa ARFAT amfani Dan haka akwai set dinsu a dakinta da toilet dinta Kuma akwai a dakinsa da toilet dinsa Dan haka shi tafara yiwa wanka ta miqowa Sarrah shi daqyar daure da qaramin towel dinsa a jikinsa suka nufi dakinsa dan a shiryasa.

Wanka Tayo a natse tareda alwala ta fito tana qamshin Rosella shower gel daureda towel blue sbd gurin wankan Arfat ta jiqa bathrobe din data shiga da ita.

Gaban mirror ta zauna tana goge jikinta ahankali tareda kallan fatar jikinta Dake wani irin daukan idon haske da lafiyayyun gyara datake samu na luxury life.

Oil na original Neutrogena ta shafa a jikinta na tareda bodyplash masu sanyi ta miqe ta nufi closet ta saka black laced undies kafin ta Saka Doguwan Rigan AnnaBrom black data fitar da kyanta sosai duk da bame adon komai bace sedai kudin kadai zai iya ciyar da wani gidan n sati biyu.

Veil me kauri ta nada akanta tayi sallan dhuhur tana idarwa Sarrah ta shigo da Arfat a jikinta yayi bacci ta kalli bakinsa da yayi pink alaman yasha Wani abin bayan wankan datai masa Dan haka Sarrah data kwantar dashi Saida ta goge bakinsa da tissue kafin AM din ta gyara masa kwanciyarsa cikin kayansa ba bacci ta hau gefensa ta kwanta bayan Tasha madaranta sosai.

Sarrah ce ta kashe musu hasken dakin tareda rufewa ta sauka Babu me sake Hawa saman sai sun farka sbd kada a tadasu wannan shine kaidan gidan.
#MAMUH#
#AM JDEN
#THE SEELAHS
#JAMAAL MAM SEELAH


*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
101

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products šŸ‘‡

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

***********
Bacci sosai tayi ita da Arfat sai yamma ta tashi,

Sallah tafara yi kafin ta sake wanka ta sauya kaya zuwa boot cut jeans Blue da milk turtleneck top da suka zauna daidai jikinta siraran cinyotinta suka fito tsaf a cikin jeans din ta zauna dakin bata fito ba ta kunna laptop tana duba ayyukan dake jiranta da Bata duba ba.

Tana cikin aikin Arfat ya tashi nasa baccin ya sauko gadon Yana cewa

"Mommah Arfat zaije toilet"

Dago fararen idanuwanta tayi ta kallesa cikin tsananin kauna tareda yin gefe da laptop din ta miqe tsaye ta ka)wo9ma hannunsa suka shiga toilet yayi fitsarin ta sake masa wanka ta fito dashi tareda daga wayarta ta kira sarrah ta hawo sama ta miqa mata shi taje ta sake shiryasa cikin kaya masu dan nauyi navy blue saiĀ a lokacin suka sauko qasa tana gaba tana waya sarrah na biye da ita dauke da Arfat da zaa bawa Abinci.

Mum Nur ce kadai a palon qasa zaune tana waya Aunt Didi tana kitchen tareda Dadah da Bata iya zama ba aiki suna Taya chiefs din Dake musu abinci Aiki.

Mum Nur ce ta karba Arfat din ta zaunar dashi akan qafafunta tana kissing gashinsa me tsayi tana magana da Ameenatou akan Graduation dinner dinsu da zaayi daren gobe da kuma tafiyar da zatai Miami Gurin Dad dinta su qarasa abinda yakaisa itada hafiz su dawo tare.

Sarrah kitchen ta nufa tafara aikin hado abinda Arfat zai ci.

Sunanan zaune Hafiz ya shigo dashi suka qarasa firan Yana yi Yana amsa waya hakama firan duka a lafiyayyam turanci suke yinta sbd Mum Nur din Bata fiya hausaba hakama Suma kusan Hakan ya jima da shigarsu harsun Saba.


Da daddare gabaki dayansu a dining din main palon gidan sukai dinner suna gamawa kowa ya wuce dakinsa Hafiz kuwa fita yayi Dan Baya dawowa sai kusan 12 na dare.

Washe gari Bata fita koina ba tana bangarensu Dadah acan tayi zamanta sai yamma masu mata Shirin fitan da zatai dinner party din suka iso aka hau dasu har sama a dakin Arfat.

Sai data gama duk abinda zatai da wayoyinta kafin ta sake wanka ta fito sanye da bathrobe fara qal a jikinta fatanta Yana sake daukan ido ta zauna suka fara shiryata.

9 suka fito tana sanyeda doguwar fit padded Rualler maroon data kwanta ta zauna jikinta daidai sai veil da aka daura mata a kai ya lafe hade da gashinta.

Simple diamond necklace ne a wuyanta da earrings suna shining a hankali sai wayarta kawai ko jaka Bata dauka ba hakama makeup dinta simple and nude ne Babu wani hayaniya.

Hafiz ma cikin simple Armani's suit blue ya shirya ya fito daure da a

Mum Nur da aunt Didi ma duka sun fito a shirye kaman halfcst dasu Babu Wanda ba sarkan diamond ne a wuyansa ba sai Fatmah ce ta fito karshe sanyeda Riga da wandon Balmain na mata da wedges suka fice.

Arfat gurin dadah aka barsa Dan tini yayi bacci hakama Sam baa fitan dare dashi sbd kiyaye lafiyansa daga sanyi wannan dokan Dad Omar ne sbd idan ma Yana gida Arfat Baya zama gurin kowa sai gurinsa sbd shine Asalin Buddy dinsa kaman yanda yake fada.


Sai dare sosai suka dawo anyi dinner anyi komai
Washe gari Kuma Akai graduation din gabaki Daya aka watse.

Kwananta biyu tana Hutu Bata fita koina ba saida tai sati tukuna tafara fita office hankali kwance.

Fara fitanta office ya Saka ta fara zama busy Dan haka Bata Wani zama gida sosai sai dare take samun time din Champ dinta Amma da safe sai ta ajiyesa school take wucewa office din.

Girma ake Bata sosai sbd sanin matsayinta,
Hatta daga Nigeria ma sosai take samun calls daga wasu manyan Ma'aikatansu Dan gaitada da son samun shiga,

Wasu Kuma da yawa manya masu taka nera da dollar yanda sukeso sun fara nuna shaawan Sonta Amma Kuma sanin waye Omar Jden da yanda turai ta ratsashi bazai iya aurawa yarsa dattijo ba,

Wasu Kuma masu shigowan matasa ne masu dollar da nera lafiyayya Amma Kuma duba da yanayin rayiwanta da itama Sam Babu alaman namiji na gabanta Sam ya Saka suke fakewa da zama abokan business kawai.

Babbah da Dadah ne tareda Arfat da mum Nur suka tafi Umrah ita Kuma da Hafiz suka wuce Miami sbd Dad dinta dayake Jiransu acan akan sabbin shares Daya Siya da sunanta suna baqatanta Dan signing nasu shares din Dan haka ita da Hafiz suka tafin sbd komai Daya danganceta shine yake hannunsa.


***************
Black Lamborghini ce tayi parking a haraban asibitin ALEENA BOZEMAN,

Bude kofan motar Akai tareda fitowa gabaki Dayansa cikin nutsuwansa da kamewansa data rabasa da kusan Rabin abokan Aikinsa a yanzu sbd komai nasa ya sauya daga Dr JEEY din da suka sani Dan yanzu kamewansa da rashin sakewansa da mutane ya wuce tinaninsu,

Kwata kwata Baya maamalantar mutane sosai sbd bayason hayaniya ko yawan surutu,

Ya Dena aikin asibiti kwata kwata sai dace kawai ake samun damansa idan case ya zama babba yaxo ya duba musu sbd Bayama zama guri daya,

Yawon qasashe kawai yakeyi yanzu sai business dinsa Daya bunqasa fiyeda na iyayensa a yanzu Amma Sam ba shine akan business dinba ma siddeeq ne akan komai,

JAMAAL SEELAH ayanzu Wani JAMAAL dinne daban ba Wanda suka saniba,

Mum dinsa ta warke kaman Bata taba ciwo ba ganin tana kwance zata rasa 'danta Daya Dan haka ta dage da dauriya da fighting da rokon Allah
Allah ya tayar da ita ta warke fes Abinta ta fara taro danta daga damuwan da zata iya kashe mata shi sbd tasan idan zai rasa ransa ahakan bazai taba fadan abinda yake ransaba,
Siddeeq ne ya sanar da ita komai Dan haka itama saita Hana kanta damuwa akan yawon tafiye tafiyansa kasashe bayason zaman gurin Daya Koda Hakan zai sake masa zuciya.


Ya samu sauyin rayuwa Dana kamanni sbd irin hasken Daya qara na asalin baturensa da wani lafiyayyan gashin fuska Daya Tara me tsananin laushi da kyau Daya qara masa sosai kaman bazaka iya dauke idanuwanka daga kansa ba,

Komai nasa ya sauya tin daga kan,
Halaye,yanayin gudanar da rayuwa,
Sake budewa sosai a jikinsa Sbd geamin da nutsatsiyar Hutu da daulan rayuwan Asalin luxury life dayake cikinta na komai Daya sake zaunuwa a rayuwansa.

Dukkanin wannan sauyin Abu Daya ne Bai sauya ba daga zuciya da rayuwarsa Wanda yake zaune boye cikin ransa shine Neman Ameenatou da Neman Ashly da Bai denaba Kuma bayajin Hakan zai tsayu har sai ranarda yayi ido biyu da dayansu.

A Baya Yana communicating da Ahmed akan lafiyan Dad Omar da tana hannunsa Amma daga lokacinda ta bata daga asibitin Kuma lokacin ne ya samu tabbacin samun lafiyan Dad Omar din Bai taba barin sun sake magana ba sbd radadin dayake Ji a zuciyarsa na bacewanta a hannunsa batareda ya sadata da mahaifinta ba.

Qarin abinda ya Saka Dad Omar a nasa bangaren Baya samunsa shine yanayin rayuwan Hutu da yawon dayakeyi ya Saka idan ba siddeeq da mum dinsa ba to duk Wanda ya nemesa Baya samunsa Saiya bi ta hanyarsu,

Ko Dad dinsa Saiya nema siddeeq ko mum din yake samun Daman magana dashi sai idan shine yaso ya nemesa da kansa.


Ash Ralph Lauren Riga da wando da loewe jacket,
Wayarsa ce kadai a hannunsa ya nufo cikin asibitin duk inda ya wuce sai qamshinsa ya sauya iskan gurin da qamshin Paco Rabanne dinsa Da shine abinda kadai Bai sauyaba daga sauyin dayawa komai na rayuwarsa.

Doctors din Dake jiran isowansa ne bayan request da suka ringa turawa na buqatan zuwansa tin last month sai yanzu ya samu Daman sauka Poland din Dan haka fitowa sukai gabaki dayansu Dan tarbansa da masa barka da zuwa suka dunguma zuwa ciki Asalin office din mahaifiyarsa dayake ba Wani zama zaiyiba a qasar yanada tafiya Miami a satin dan haka Kai tsaye baya buqatan Bata time zai duba musu cases din a kwanaki kadan yabar qasar.
#MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
102

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login