Showing 198001 words to 201000 words out of 261814 words

Chapter 67 - AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE.txt

MAMUGEE   

07 Jul 2024

59034

shirya.

James ne ya budewa Dad Omar din da sauri Cikin nutsuwa Yana matsawa gefe Dan basa Damar fitowa.

Kofar gidan suka nufa James na rigansu isa ya buga kofar me shegen Kuka Yana sake Kiran sunanta.

Jin shiru ya Saka uncle kallan James shima James din da sauri ya sake miqa hannu xai sake bugawa aka Bude kofar.

Sanye take da doguwar rigar atampar data Dan wanke sbd yaji Dan haske alaman wankewan tsufa.

Kallansu takeyi da Idanuwanta Cikin Dan girmamawa ta gaidasu tana musu barka da zuwa kafin ta tsayar da Idanuwanta kan James daya taho mata dazu ya tambayar dunsnta.

James dinne ya sanar mata baqi ne gurinta zuka taho.

Kasa dagowa tayi ta kallesu sbd kwarjinin Dad Omar tace

"Ok Bismillh ku shigo"

Dayake basuda lokacin batawa maganar suke baqace da suka sunyi San haka Ciki suka wuce Mai tsaye zuwa palon gidan dayake kaman office dinta sbd teaching takeyi yanzu sai Kuma Wani local asibiti da ko wuta Babu tana zuwa Aiki duk Dan tasamu abin dogaro da Kai.

Zama sukai Babu qyama ko tsayawa kallan yanayin gidan
James kuwa a waje y tsaya Bai shigo ba sbd tsaro.

Sake gaidasu tayi Cikin wata girmamawan kafin ta Dan dago kadan ta Kalli Dad Omar dayake mata kama da fuskan Babynta da Babu ranakun da Bata kewa da hawayen rashinta Dan tayi yawo asibitinsu nemanta bayan warkewanta Amma karshe MD sakawa yayi securities suka hanata shiga asibitin ma gaba daya haka ta hakura ta tattara ta dawo gida sbd bazata iya hada Ido da JAMAAL ba daya bar mata amanar Ameeenatou din ba tace ta rasa Ameeenatou Dan haka ta hakura da zaman Lagos sbd kadai kunyar haduwanta da Jamaal ta gwammaci zaman abeokuta dadi da qunci da wuya Amma rubutacen alkwarine a zuciyarta duk ranar data ga Ameeenatou zata Nema Jamaal da kanta ta sanar dashi komai daya faru.

Uncle Ahmed ne ya Bude Baki zaiyi magana Dad Omar ya dakatar dashi sbd da kansa yakeson magana da ita Baki da Baki.

"Ms Ashley Adrian Abdulra'uf right???

"Yes Sir" ta fada tana Jin jikinta na sanyi haka kawai.

"Ms Ashley ba tareda Bata lokaci ba Kai tsaye sunana Omar jden Seelah nine na mahaifin daya haifi AMEEENATOU OMAR.....

da Wani irin sauri sister Ashley ta dago ta kallesa Idanuwanta na sauyawa take tareda cikowa da Wasu irin hawayen dasuka Sakata rufe Idanuwanta da tafin hannuwanta.

Tsantsan kaunar datakewa Ameeenatou ya hango a Idanuwanta da yanayinta daga fadar sunan Ameeenatou din.

Jin yayi jikinsa yayi sanyi Amma dole ya Yi hakan.
Kallanta y sake Yi yace

"Daga ranar data shiga asibitinku da hannunki nakeson sani,
Sannan shin kinsan da akwai Ciki a tareda ita lokacinda Kuka rabu???

Hawayen datake riqewa ne suka gangaro mata sbd Babu ranar da Bata hawayen rashin nata Cikin ba da fatan na Ameeenatou dinta Yana Nan.

Dagowa tayi bayan ta share hawayenta ta sauke ajiyan zuciya tace

"sorry sir ko zan iya tabbatarda Kai dad din Ameeenatou ne??

Tinawa tayi da bayanin siddeeq akan Kada ta yadda da kowa da wuri akan lamarin Ameeenatou idan ba shi kadai ba ko ogan gaba daya wato Jamaal.

Uncle Ahmed ne ya Ciro wayarsa daga  aljihunsa ya Nemo videon labaran da akaita yadawa na ranarda jden ya bayyanawa duniya yarsa Ameeenatou na gefensa riqe da hannunsa ya ajiye gaban sister Ashley din batareda yace komai ba .

Fuskan Ameeenatou ta zubawa Idanuwanta tana Jin zuciyarta da jikinta na tsananin mutuwa sbd da alama Ameeenatou dinta ta warke ba kuma lallai ta Tina da ita ba.

"Uhummm??? Dad Omar ya fada alaman idan ta Gani Suna jiran bayanin komai dalla dallah.

Ajiyan zuciya sister Ashley ta sake saukewa jikinta na tsananin sanyi ta Bude Baki tafara zayyano musu komai a tsare daga ranar farko har zuwa ranar rabuwarsu Bata boye komaiba hatta yanda rashin hankalin ya sakata sakawa ya sadu da ita akan dole sbd baida zabin daya wuce hakan tareda dararrakun daya ringa batawa na kulawa da ita idan batada lafiya tareda yanda ya tare asibitin gaba daya rayuwarsa sbd Ameeenatou Bata rage komaiba ta zube musu bayanin komai a gabansu tareda tabbacin baisan da Ameeenatou nada ciki ba ita kadai ce ta sani sai doctors uku wainda duka basa qasar sun tafiyarsu wasu qasashen kaman yanda ta samu labari.

Wani zazzafan numfashi suka sake a tare jikin kowannensu Yana sanyi da tsananin tashin hankali abinda daga Ameeenatou din harsu Ashely din sukai going thru da Kuma yanda Jamaal ya ajiye komai nasa y tare Nigeria a asibitin sbd Rai daya.

Dad Omar daya kasa cewa komai sbd zuciyarsa data riqe ta Dena bugawa sosai.

Dagowa yayi ya Kalli Ashley da Idanuwansa da suka sauya xuwa ja ya Ciro Wani blank cheque da Kuma wanda aka rubutawa wasu mahaukatan kudin da ko a lissafi Bata taba lissafowa kanta su ba ya ajiye a gabanta tareda kallanta yace

"Ki dauki wanna ki qara da blank din ki saka numbobin kudin da kuke ganin zai isheki har tsawon lokacinda zaki Gina kanki ki zama me abin kanki kema,
Zan baki gidan zama a duk qasar da kikeso a fadin duniya ki zaba da kanki,
Zan Gina Miki asibitin kanki kiyi Aiki a Cikinta,
Duka wannan amtsayin godiyata daga kauna da kulawan da kikaiwa AM da Kuma kariya danakeson ki Bata a yanzu ita da abinda ta Haifa ta hanyar nesa da rayuwar duk wanda ya sanki a families dinmu duka har jdens har SEELAHs,

Magana ta Kai tsaye inason ki bacewa duniyar JAMAAL SEELAH kwata kwata har abada kokuma lokacinda na buqaci ki dawo,
Bazaki taba barin JAMAAL yasan ind kike ba bare ki bari ya ganki sbd idan har kinason bawa Ameeenatou da abinda ta Haifa tsaro to karki taba barin JAMAAL ko Wani daga ahalinsa yasan Ameeenatou ta taba samun Ciki daga wannan auren,
Ki shirya zanji da komai zaa turaki wata qasar."

Ashley kasa motsawa tayi sbd tsananin mamaki da tsoro da suka rufeta lokaci daya sbd bata taba tinanin Jin hakan ba,
Me hakan ke nufi??
Cikin Ameeenatou na Nan kenan harta haifesa,
Hakan na nufin kenan Jamaal haryanzu Bai San da Cikin bane?

Idan har JAMAAL bai San da Cikin Ameeenatou ba kenan haryanzu baisan inda Ameeenatou din take ba,

Damarta ce tazo mata har gida ta cikawa Kanta alkwarin Neman Jamaal a duk ranar data samu Ameeenatou ko me??

To Amma Kuma da gaske Ameeenatou din d abinda t Haifa Suna Cikin hadari??

Meyasa Dad dinta bayason Jamaal ya sani??

A saninta har abada Jamaal bazai taba  iya cutatar da ko wanda yakeson Ameeenatou ba bare Ameeenatou bare Kuma harda abinda ta Haifa da sunansa.

Cakewa kanta taji yayi tareda mata nauyi sbd tashin hankalin lokaci daya da duka maganganun da bakon lamarin da aka taho mata dashi suka sakata.

Ja Idanuwanta sukai take sbd sarawa da kanta ya fara.

Kallan Dad Omar din ta Dan dago tayi sedai kafin tai magana uncle Ahmed ya Bude Baki yace

"Wannan zabi ne Mai tattareda ingantacciyar rayuwar dake jiranki Kuma take jiran Ameeenatou da 'danta sbd tafiyarki itace kwanciyar komai.

Cikin rashin fahimta ta sake kallansa tana sauraron bayanin dayake sake mata akan tafiyarta shine maslahan komai.

Shiru tayi Idanuwanta na sake yin ja da wannan tinanin sbd zata iya komai Dan bawa Ameeenatou da Babynta kafiya kaman yanda Kuka zata iya komai Dan ganin ta samu ganin Jamaal a duk inda yake a yanzu wanda idan har tanason zuwa inda JAMAAL yake ta sanar dashi komai to tabbas tana buqatan amsar kudin Dad din da amfani dasu.
###MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
118

*_HONEY DROPS_*
Albishir! Albishir! Albishirrrr!!!

Kin gaji da wula’kancin miji, ke ke nan kullum hantara da kyara , an hana miki rawar gaban hantsi a gidan aurenki, shin ko baki San gabad’aya dadin aure ba?. Hajiyata idan kina da kyau ki ‘kara da wanka, ke ke nan kullum babu wani sauyin dandano kullum zuwa kike wajen oga yadda kike, haba mana ba darajarki ba ne, mace ai ‘yar gyara ce, a d’in ga yi ana cleansing ana kuma spicing other room affairs. Sannan a gyara boobs d’in nan su cika su yi ma sha Allah a bar barinsu kamar guga, yanzu mace figure 8 bata burgeki ki ga ko ina ma sha Allah ga na Oyoyoo ga na bye bye, kina da HONEYDROPS me ya kai ki shaawar wata bayan kema tsaf zaki koma haka. To gyara ki ji ni da kyau HONEYDROPS wannan shahararren kamfanin na Aphrodisiac ma’ana kayan mata sun shirya tsaf don kawo muku zafafan kayan gyara wanda zaki mallake oga tsaf tsananin dadinki da niimarki, kayanmu aiki suke kamar yankan wu’ka kuma babu boka ba Malam, tsananin sanin makamar aiki ne kawai. Kayanmu na saka oga kyautar dole, muna soyayya da kulawar dole, suna birkita lissafin kishiya don dole ta ha’kura ta zama borar coz yan ajin HONEYDROPS a kullum sune Mowa, Muna…Muna… Muna…Muna fitattun kayan da ba su da na biyu kamar su

Infection flusher big 5k, small 3k
Breast firming sabaya 4k
Breast enlargement and hips sabaya 4k
Echoes of forever 3k
Her royal highness 2500
Milky vjay cake 3500
Ever bond 3k
Eternal flame 2k
Love nectar 2k
Cleanser pro 2500
Endless seduction 1500
Intensive love 1500
Swan 3k
Mowa’s secret 4k
Sugar queen 7k
Cloud9 4k
Sweet16 tightening gel 4k da sauransu. Muna da gumba kala-kala, tsumi kala-kala, muna dahuwar kaza, nama, tantabara, Ciccibi da sauransu. Muna da branches a garin Sokoto da Kano, sannan muna aike ko wani gari kowacce ‘kasa cikin amincin Allah, muna maraba da masu siyan daidai ko sari.
Za a iya tuntubarmu ta lambobi kamar haka
08167888934 ko
07026039714.
Ki yi ‘ko’karin ki tuntubemu don tabbas kukan damuwarki ta qare. Zaki iya tuntubarmu ta Instagram link dinmu kamar haka
https://www.instagram.com/honeydrops013?igsh=MW5saThrY3N0Z2Zjag%3D%3D&utm_source=qr

***********
Uncle Ahmed ne yayi amfani da maganganunsa masu kaifi da cikakkiyar manufa ya daure Ashley tsaf dasu ta rasa zabi bayan amincewa da buqatansu a zahirance Dan haka take aka zube mata cheques din kudin tareda karban passport dinta da komai Dan hada mata komai na tafiya a Cikin qanqanin lokaci da Kuma sakawa James ya samar mata gida a Abuja a gobe zata bar gidan ta koma Abuja kafin a kammala komai na tafiyarta.

Zuciyar Dad Omar sanyi tayi yaji kaman nauyin dayake kanta ya sauka Dan haka Suna shiga mota Saida ya sauke ajiyan zuciya me dumi tareda zare glass dinsa Yana rintse Idanuwansa Cikin Jin nutsuwa.

Tada motar uncle Ahmed yayi ya figeta suka bar gurin tareda kama hanyar barin garin.

Daidai titin ficewa daga abeokuta Suna wucewa da gudu motar su Jamaal na shigowa abeokuta din da gudun Suma.

Saida sukai Nisa siddeeq ya sake kallan motar da bar abeokutan ta mirror kaman yanda Jamaal ma yaga motar bayan wucewarta wadda babu wanda a cikinsu Bai San motar gidan JDENS ce sedai yanayin dayake cikeda zuciyarsa Bai barsa ya tsaya sake kallan motar ba sbd Jin yakeyi kaman Yana hanyar karban wata jarabawan ce sbd ganin Ashley tamkar Wani dadadden burin dayakeson cikawa ne sbd son dayakewa AM Bai cikaba idan Babu Ashley a tareda su sbd itace ta takawa sonsa rawar ganin daya samu kansa a cikinsa bayan bayajin akwai macen da zata iya shiga Ina fadeela ta shiga harma ta wuce sbd a yanda ya rasa fadeela ya kusan zaucewa sbd tabar duniyar gabaki daya, ita wannan ba duniyar ta bari ba hannunsa ta bari Amma inda zaucewa yayi da yafi masa akan halinda ya shiga sbd seda yakai allura yakewa kansa da kansa ya samu Idanuwansa su rufe yaji sassaucin abinda yake ji,har Dan iska ya zama yayi yawon clubs Koda zai Dena Jin abinda yakejin sedai ganin mata ma cinawa zuciyarsa wuta yakeyi dole ya zabi janyewa daga mutane gabaki daya ya kebe kansa a Wani gidansa daya saya a California can Cikin woods Babu mutane shi kadai ko siddeeq da Mum dinsa dole kyalesa sedai suke kawo masa ziyara sedai siddeeq dole Shima ya tattara ya dawo California din shida Mum a Cikin gari har tsawon shekara daya haka sukai wannan zaman kafin da daqyar da addua da roko suka samu ya fito yafara dawowa JAMAAL dinsa.

Dan haka tayaya zai bari Ashley da itace kadai ce ma a bangarensa yakejin tana yiwa AM so da kaunar da Babu sirki,
Duk mewa am wannan son bazai taba barin ya bar hannunsa.

Suma akwai wanda yake jiransu shi suka dauka suka wuce gidan Kai tsaye ya kaisu har kofar gidan,

Suna parking JAMAAL ya rintse Idanuwansa ahankali zuciyarsa sanyi me nutsuwa hakama siddeeq ajiyan zuciya ya sauke a bayyane Suna fatan Allah yasa Ashley dinsu ce da suke Nema ba wata ba.

Sallaman Abiola Siddeeq yayi akan ya jirasu bakin layin zasu taho idan sun gama.

Siddeeq dinne ya fara Bude motar ya fito hakama Jamaal Bai jira Abiola Dake kokarin Bude masa ya Buden ba ya fito.

Sister Ashley Dake zaune inda su Dad Omar suka barta ta zubawa cheques din dasuka bar mata gabanta Idanuwanta sunyi jajir kukane tayi Mai tsananin Ciwo da radadin gaske sbd Bata taba dauka tsananin kaunar datakewa Ameeenatou ba zata zama ta abinda zaa biyata da kudi ace tabar qasarta sbd hakan,

A yanda take Jin Ameeenatou kaman ita jininta ce,
Kaunar Ameeenatou da Jamaal a jininta suke sbd bazata taba iya yin abinda zai cutatar dasu ba Amma Kuma a yanzu an dorata akan zabin cutatar da daya tabar daya...

Idan har ta zabi tafiya Dan bawa Ameeenatou da Babynta kariya to tabbas ta cutatar da Jamaal wanda tasan a duk inda yake nemanta yakeyi,
Hakama idan ta zabi zaman zata Saka Ameeenatou da baby hadari.

Wani Sabon kukan Mai ratsa zuciya mara sauti ta sake sbd rayuwarta gabaki daya ta hargitse ta juye ta koma abar tausayi,
Bata kowa Bata komai,
Iyayensu sun rasu daga mamarsu har baban,yayyunta kuwa kowa ba baya abeokuta din kowa da inda yake rayuwarsa Babu ruwan Wani da Wani Dan kusan shekaru biyu kenan ma ko dayansu Bata sake Gani ba a wayar ma basa kiranta sbd addininsu da ba daya ba Dan haryanzu taqi riddah ta koma christian din dasuke mata barazanan idan Bata komaba ma kasheta zasuyi Dan gwara su San Bata Raye.

Batasan Ina zata Saka rayuwarta ba gashi yanzu qasar akeson ta bari ta bacewa kowa taje rayuwa a inda batada kowa batasan komaiba.

Tafin hannuwanta ta rufe fuskanta dasu lokacinda Wani sabon Kuka Mai radadi ya taho mata tana Jin inama itama ta mutu tabi Abdulra'uf da duka sun huta da wannan rashin madafar.

Buga kofar gidan Akai ta dago jajayen Idanuwanta da har suka fara kumbura sbd itama fara ce sosai sbd asalinsu Igbos ne.

Kasa motsawa tayi ta rintse Idanuwanta hawayenta na sake qaruwa.

Siddeeq daya kasa hakuri sake buga kofar yayi tareda shigowa sbd kofar a Bude take ya Bude bakinsa muryansa a natse yace

"Hello"

Dago jajayen Idanuwanta tayi Cikin farban data shigeta me karfi ta Kalli kofar tsakar gidan daga Dan sitting room din datake zaune zuciyarta Cikin tashin hankali ta furta "SIDDEEQ"

JAMAAL ne daya Sako Kai a bayansa qamshinsa ya bayyana a tsakar gidan Dan qarami wanda ya sakata miqewa tsaye qafafunta na rawa sbd muryan Siddeeq da kunnuwanta suka dauko mata da Kuma qamshin da tafi kowa sanin Kona waye sbd shine a jikin Ameeenatou dinta a Koda yaushe tabaro gurinsa.

Takowa tayi a hankali qafafunta na rawa kaman yanda zuciyarta ke rawa ta nufo kofar palon ta miqe hannu ta dauke labulen take numfashinta ya kusa daukewa tayi baya ahankali tareda dauke wuta sbd shock da Wani irin farin da sanyi sbd ganinsu Dan batasan ta yanda zata bar qasar ba batareda taga Jamaal ba zuciyarta takasa nutsuwa da yin hakan ko kadan sbd Jamaal ne nata a kaf ahalin Ameeenatou ita Jamaal tasani shi takeso shi take bi.

Siddeeq ma ajiyan zuciya me karfin gaske ya sauke Idanuwansa na tsayuwa akan Ashley din datake tsayen bakin kofar hawayenta na tsananta gudu Kan fuskarta.

JAMAAL ma Idanuwansa take suka sauya ya zubawa Ashely din Idanuwansa sauyin rayuwarta da quncin datake Ciki a bayyane yake ta koma kaman wata tsohuwar mace sbd baqin Ciki da wahalan rayuwa.

Ahankali siddeeq ya Bude Baki Shima ya ambaci sunanta Cikin baqin Cikin ganin rayuwarta data matu Yana tinkaro palon.

JAMAAL ma Saida ya hadiye abinda yake ji kafin ya Tako ya nufo palon Shima suna shigowa ta kasa riqe kukanta ta fasa shi ahankali tana godewa Allah a Cikin zuciyarta daya kawo mata JAMAAL din a daidai wannan lokacin da batasan tayaya zata iya barin qasar ba saninsaba ta gaya masa Koda yabar Ameeenatou tana dauke d Cikin dasu Dr Ibrahim suka do zubarwa.

JAMAAL da Siddeeq dukkansu sunsan kukan ganinsu ne takeyi da samun sassaucin abinda yake zuciyarta na shekarun sedai Idanuwansu da suka sauka akan cheques din dayake ajiye a taburin robar Dake tsakiyar palon ya sakasu kurawa sunan dayake rubuce baro baro akan cheques din duka biyu Ido siddeeq ya dago ya Kalli JAMAAL Shikuwa Jamaal din Idanuwansa take suka sake sauyawa ya dago ya Kalli Ashley wadda itama cheques din ta kalla hawayenta suka sake gangarowa tana sauke ajiyan zuciya.

Silalewa tayi ta zauna tareda Ciro wayarta Dake inda ta tashi batareda ta iya Bude bakinta ba kawai ta kunna recording komai na maganarda su Dad Omar sukai da ita tin daga lokacinda ya sanar da ita shine mahaifin Ameeenatou ta Saka recording din sbd ajiyewa Jamaal din koman dadewa yaji da kunnansa.

Ahankali maganganun komai ke sauka kunnuwansu shi da Siddeeq tin daga farkon zancen har bayyanar Cikin Ameeenatou da yanda akaso ciresa da Kuma accident dinta da rasa nata babyn datai tin Bata haifesaba Cikin ya bare har zuwa offer din Dad Omar din kafin uncle Ahmed ya Dora da kaman threatening nata sukeyi akan hakan.

Dagowa tayi da jajayen Idanuwanta ta Kalli Jamaal sai alokacin ta iya Bude Baki Cikin rawar murya tace

"Bazan taba iya boye Maka Ameeenatou tabar asibitin tana dauke da cikinka a jikinta ba,.tayi Kuka tayi Ciwo tayi hauka duka akan rashinka daga karshe tin tana asibitin tafara warkewa sbd so da Dama takan zauna da hotonka a hannunta idan na bata a waya ta zuba Maka Ido
Akwai ranar data fadamun date na ranar data fara haduwa d Haroon a ranar nafara sanin tafara dawowa daidai sedai Wani lokacin ta Dan sake juyewa.

A karo na farko da Jamaal ya dago Idanuwansa da sukai Wani mummunan ja ya zubawa Ashely tinda ya sunkuyar da Kai akan abinda Dad Omar yayi masa zuciyarsa na breaking Cikin tsananin Ciwo da zafi me radadin gaske sbd Bai dauka zai taba samun hakan daga uban dayasan radadi da ciwon rabuwa da 'danka jininka gudan jininka,Jin date din Ashley din ta fada ya sakasa dagowa sbd

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login