Showing 174001 words to 177000 words out of 261814 words

Chapter 59 - AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE.txt

MAMUGEE   

07 Jul 2024

59031

takai Saida ta Dena communicating da kowa sbd cimma manufa har suka gama sai gashi Cikin Tarin turawan qasashe daban daban itace ta zama gwarzuwa Akai programs din da zaayi na kammalawansu aka gama ta dawo da mamakin wanda Idanuwanta suka ganar mata a gurin program din Amma Kuma tasan hakan bamai taba yiyuwa bane ganin Haroon gareta Amma Kuma tinawa da kamannin Jamaal ya sakata Tinanin yanzu akwai  wanda yake da komai n kamannin Haroon dinta.

A daren a matiqar gajiye take Dan haka hutawa tayi tsawon kwana biyu kafin tayi Shirin tafiya gida ta Siya ticket din France Kai tsaye.

Da daddare jirginta zai tashi Dan haka  ta fita ta Dan yiwa Arfat dinta shopping sama sama sbd Babu m abinda yake buqata sbd Babu ranar da Kila Hafiz baya Siya masa abubuwa harda na shirme.

Kayan Yara ta Siya sosai tana dawowa sallah tayi ta sake wanka ta shirya tana gamawa Ariana na isowa lodge din da mota ta dauketa sai airport.

Ko awa daya bataiba a airport jirginta ya tashi tabar Madrid.

Ko data isa France safiya tayi Hafiz ne yazo daukanta tareda Arfat wanda Yana hango mommansa da Wani irin gudun gaske ya kwace daga Hafiz ya nufeta yana ambatar sunanta farin cikinsa Mai tsananin gaske Yana bayyanuwa sbd Bai taba dadewa haka batareda mommnsa ba.

Itama ware hannuwanta tayi Cikin tsananin farin Cikin da take Idanuwanta suka ciko da hawaye tana cewa

"My blue eyed champ,mommas love, honey I missed you like crazy,ohh my love......."

Daukansa tayi tayi sama dashi duk da nauyinsa tana dariya Shima dariyan yakeyi.

Hafiz daya iso gurinsu Cikin farin Cikin ganinta Shima barka da sauka yayi mata Yana kallan yar ramar datai Amma ta qara haske sosai yace

"Yau akwai turancin France a bakin babbah da Dad jden idan yaga yar budurwansa ta rame haka"

Dariya tayi Suna yin gaba tana cewa

"Allah sarki babbahna duk kun rikita masa yar budurwansa"

Dariya yayi Shima Suna isa mota ya Bude aka Saka komai nata ya Bude mata ta shige ya karbi Arfat dinsa ya Bude masa baya ya sakasa tareda Saka masa seatbelt ya rufe kofan kafin ya zagaya ya shiga lafiyayyan motar ya tayar suka bar airport din aguje.

Idan akwai abinda yafi hawan jini to siddeeq Yana cikinsa sbd mutuwan tsaye yayi na ganin babyn a tsakiyar Hafiz da AM Kuma Yana kiranta mommah idan kunnuwansa sunji masa daidai kenan.

Innalillahi wainna ilaihi rajiun""

Wannan babyn waye ne ya haifesa a kaf familyn jden shine abinda yake tsananin son sani kafin isawar da Jamaal wannan sakon da zai iya tarwatse komai,
Tukuna ma Ina aka samu jinin bature a fmlyn??
Kodai Cikin familyn asalin jdens dinne Omar jden ya dauko...

Numfashi ya sauke daqyar dole Yana buqatan sanin komai kafin barinsu AM din kasar kaman yanda JAMAAL yafa masa.

Su kuwa Kai tsaye gida suka nufa Suna isa Aunt Didi ce tafara farin Cikin ganinta sbd zata fita ne tana bakin motarta suka shigo.

Rungumeta tayi tana mata sannu da zuwa itama Cikin farin Cikin ta rungumeta tana Dan bayyanarda shagwabanta.

Wata lafiyayyan Ferrari ta Gani a harabar gidan Amma Bata damu da tambayar ba sbd tinanin ko Dad dinta ne ya siyo sabuwan motan kokuma ta Hafiz ce.

Ciki sukayo Arfat har lokacin Yana maqale da ita a hannunta babbah bayanan shi da dadah Dan haka Kai tsaye palon Dad dinta ta nufa da Arfat a hannunta Hafiz na gefenta suka shigo palon.

Dad dagowa yayi fuskansa cikeda farin Ciki ya kalleta Yana ware mata hannuwansa ta taho har Arfat din suka shige jininsa sai alokacin ta lura d JAMAAL SEELAH dayake zaune tareda Dad din batareda y dago ya kalletaba waya yake amsawa a Cikin wata irin nutsuwa da kamewan data sakata dauke nata Idanuwan daga kansa
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
106

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

*****************
Dauke kallanta tayi daga kansa tana kokarin Hana kanta sake kallan inda yake zaune a natse Cikin yar basarwa tace masa sannu da zuwa tana tashi daga jikin Dad dinta sbd qamshinsa daya Hana numfashinta shaqan kowacce iska sai shi.

Arfat dayake jikinta Shima sauka yayi tareda Hawa jikin Dad Omar sai a Lokacin yaga JAMAAL din Cikin yarinta yace

"Grandpa Ashe kanada friend but he is younger.

AM kasa zaman tayi sbd qamshin ruda kanta yakeyi Dan haka ta miqe ta fice tana cewa zata ta huta.

Tana fita Arfat ya sauka daga jikin Dad Omar ya taho gaban Jamaal din ya tsaya Yana kallansa kafin yace

"Bakaga Mommah na ba? you didnt say hello to her."

Dago fararen Idanuwansa Jamaal yayi tareda saukesu akan Arfat din ya zuba masa su Yana masa Wani irin kallan tsaf sbd fuskan Mum dinsa dayake Gani Kai tsaye a fuskan yaron...

Denq jin abinda siddeeq yake fada yayi a wayar ya ajiye wayan gefensa batareda ya kasheba sbd mamakin dayake Neman kashesa,

Idanuwansa da hancinsa da komai na yaron irin na Mum dinsa ne take yaji zuciyarsa ta Dan tsaya daga bugawa ya miqawa yaron hannunsa Ya Bude baki a natse Cikin sanyi yace

"Heyy champ,wats up,wats your name??

Dariya Arfat yayi wadda ta sake kashe Jamaal da Sabon mamaki sbd dariyan ma sake hada kamannin yaron da mum dinsa yayi ya kama hannunsa daya miqo masa.

Arfat yace

"My name is Arfat jden,or you can just call me Mommah's Champ,
I m everyone's champ in this mansion"

Murmushi Dad Omar yayi Yana Dan son taqaita zancen sbd kada ya Fadi waye Mommah dinsa Dan haka yace

"Ok my champ,zo kaje gurin AM baka gama Yi mata sannu da zuwa ba karka damu Uncle Jamaal Seelah"

Gyada Kai Arfat din yayi sbd daman ba Wani rabar mutane ake barin yanayi ba kokuma su mutanen su rabesa shiyasa ya Saba baya Wani son zuwa gurin baqi Shima Amma this Uncle is handsome and classy,likes him" haka ya fadawa Mommah dinsa lokacinda ya isa dakinta.

JAMAAL kuwa har Arfat ya fice Idanuwansa na akansa hakama take zuciyarsa ta shiga Wani irin nannauyan yanayi akansa sai Kuma gashi a yanda ya fahimta kwata kwata dad Omar bayason yaron ya tsaya baisan meyasa hakan ba.

Maganarsu suka ci gaba da Yi Amma zuciyar JAMAAL tana kan tinanin Ina suka samu baby fmlyn sbd Dad Omar din dai da kansa ya wuce haihuwa,
Uncle Ahmed ma hakan ne sbd kusan ya manyanta sosai Shima,
To Kuma bare su dadah da Babbah,and Hafiz ma baiyi aure ba bare Lady AM din Mansion din da babu ranar da ko kallan banza Wani zai mata da aurensa akanta bare.

Boyayyan numfashi ya sauke tareda gyara zamansa Yana cire zancen a ransa tukuna.

Ya Dade a gidan sai guraren lunch ya tafiyansa duk da Dad din yaso ya tsaya yayi lunch tareda su Amma hakan Bai samu ba sbd akwai inda zai tafin ana jiransa.

Dadah da babbah basa Nan ne sbd zuwansa gidan babbah ya fice sbd Baya kaunar ganin duk Wani jinin Mam seelah da lameenu Seelah,
Yasan Jamaal baida laifin iyayensu Amma bazai iya kallansa ba sbd zai tsanesa ne kaman yanda yake Jin tsanar su mam a Cikin jininsa sbd yanada tabbacin ko fyaden da akaiwa AM daga garesu ne ya fito sbd hakanne ma yasa yake qara Jin bazai taba kaunar duk Wani jininsu ba har abada Kuma bazai taba aminta ko muamalantarsu ba.

Jamaal ma fahimtar hakan ya Saka bazaiyi saurin sanar da aurensa akanta ba sbd tashin hankali ne kawai zaayi akan wannan bayason wannan yanason fushi da bacin Rai ya Saka a yanzu hukuncin da daga baya kowa zaiyi Dana sani Dan haka a yanzu daya fahimci har ita AM din zafin Kai zata basa Babu abinda yake buqata fiyeda komai sama daya Nemo Ashley sbd a zancen Dad Ashley ce a ran Am ita kadai take tinawa a lokacinda tayi hauka sbd da ita a bakinta su babbah suka daukota hakama har ranar da zata dawo daidai Saida tayita ambatar Ashley da Haroon.

To idan har Ashley ce a ran AM Yana buqatan fara samun Ashley din kafin Ameeenatoun sbd itace kadai zata tinatar da ita komai akansa batareda anyi hayaniya da tashin hankalin da babbah yakeson ayi ba idan har zaiji maganar Jinin Mam seelah ne ko yanzu mijin 'yarsa.

A dakinta kuwa tini tayi wanka Sarrah ta sake gyara dakinta da duk da batanan kullum sai an gyarasa a kaida Dan hakan ne komai yake fes fes da kamshi da sanyin Aircon kaman tana Nan.

Fatmah ce kadai Basu gaisaba tinda ta dawo Saida ta sauko tana qamshi sanyeda Ted Baker sweatset farare na mata da suka mata kyau sosai iri daya Da Arfat wanda shima nasa White dinne Sarrah ta masa wanka ta Sako masa.

Zuba mata idanuwa Fatmah tayi tin data doso palon koyaushe kyanta kaman qaruwa yakeyi,a yanzu zata iya cewa bayan rape da 'dan gaban fatiha da AM din ta Haifa to Babu Wani Abu data rasa a rayuwanta sai kuma mijin aure Dan kuwa ko zata hakura da komai akan AM bazata iya dannewa ba tana kallo ta Dad Omar ya hadata da Wani Billionaire ta aura ba abarta Dan zata iya fadawa duniya AM jden nada 'dan rape data Haifa mara uba.

Ita ma kyakkyawa ce Kuma fara hakama Babu abinda ta rasa sbd Dad Omar baya wasa da sake mata kudin duk abinda takeso a rayuwanta Amma damuwanta finta da AM din tayi a komai.

Fatmah dince a Palo zaune tareda Mum Nur da Hafiz dan haka kowa da tsananin kauna da kulawa yake kallanta tareda farin Cikin kasancewanta a cikinsu Amma Fatmah Kuma radadi ne me qunar zuciya take kallanta dashi har AM din ta iso
Ita tafara kalla Cikin sakewa ba damuwan komai tace

"Fatmah barka da gida,dazu bamu gaisaba Koda na dawo kaman bakya Nan ma ko?

Numfashi ta sake a boye tareda Dan sake fuska kadan tana cewa

"Eh,Ina Nan Amma Ina daki Ina bacci ne,
Barka da dawowa,ya Madrid?

"Fine Alhmdllh" ta fada tana isa gurin Mum Nur tana zaunawa gefenta tareda Dan shagwabewa tana cewa

"Mum amaryan Dad"

Dariya Mum din tayi tana cewa

"Rabb ya shirya AM"

Kafin su qara wata magana su dadah sun dawo Dan haka Bata tsaya komaiba ta miqe ta fice zuwa bangarensu tana iso babbah daya matsu yaga yarsa Shima tini ya kamo hanyar nasu bangaren a kofan palonsa suka hade tana ganinsa Idanuwanta suka ciko da kwalla tana rungumesa shi da dadah lokaci daya atare hawayen na saukowa tace

"Nayi kewanku babbah,
Dadah bazan iya sake dadewa Wani gurin ba tareda ku ba,wlh nayi kewanku."

Kaman baby haka ta ringa musu hawaye Saida aka suka zauna Suna aikin rarrashinta babbah kaman zai fasa kukan Shima haka ya ringa rarrashinta yanajin radadin kewanta da yai Shima sbd a rayuwarsu idan ba da tsautsayin daya rabasu ba Shima sbd Baya hayyacinsa kwance Cikin Ciwo itama bata hayyacinta Basu taba rayuwa ba juna ba sai wannan karan.

Hafiz ne daya shigo yaga yanda su babban suke rarrashinta kaman yarinya qarama irin yanda suka Saba mata tin tana yarinya ya Saka shi hade fuska Yana cewa

"Meye hakan to??
Ke wai bazakiwa kanki fada bane kisan kin girma qatuwa Dake kin zauna kina hawaye ana rarrashinki."

Harara babbah ya dago ya watsa masa kafin yace

"Meye naka a Ciki malam,inace mune masu rarrashin ba Kai ba ko?
Karna sake Jin kalman qatuwa a bakinka Ina tayi Wani girman data wuce rarrashi daga iyayenta tinda ba duniya ta haifeba,
Ko ta tsufa Kai indai Ina Raye saina rarrashi abata."

Dadah dai Batama ce komaiba tissue ta Zara tana gogewa AM din fuska tana cewa

"Kinga Arfat Nan Yana kallanki Yana dariya da mamakin mommansa na Kuka ana share mata hawaye Dena ya isa hakan tinda gashi ai kin dawo din."

Sai a lokacin ta dago ta harari Yaya Hafiz din kafin ta Kalli Arfat dayake mamaki da dariya yace

"Kaka Babbah Mommah na Kuka kana share mata hawaye kaida Granny dadah haka takeyi tin tana baby Irina itama??
Gashinan Uncle ya fada."

Dariya Hafiz ya sake shida Arfat din lokaci daya Yana cewa

"Haka mommanka take koyaushe rigima, shagwaba,Kuka,tayita sakawa su dadah na sakani aikinta fa."

"Really uncle??

"Yes Son,haka mommanka take,hmmm Nasha wuyanta,
See her face now ko kunya gatanan haryanzu budurwan Babbah"

Dariya Arfat yayi Yana sauraron kuruciyan mommansa wadda ta tashi tana kokarin bin Hafiz din dadah ta riqeta tana cewa

"Kyalesa haka yakeso ki tashi ki nunawa Arfat din abinda yake fada masa Dan haka karki bisu kyalesa"

Babbah Janta yayi har dining inda kafin fitarsu aka jere mata abincin da dadah ta girka musamman sbd ita kawai.

Zaunawa tayi tana ajiye tissue din datake share fuskanta dashi tana kallan Jerin abincin Dake dining din.

Wainna ta Gani taji Wani Dadi na mamaye ta,ta mayar da idonta kan Samosas da Kuma Nigerian JollofRice datake zuba qamshin Nikakken daman dayake cikinta da spices na gargajiya.

Kasa tsayawa kallan sauran abincin tayi tafara Bude plate da daukan cutlery dadah na fara zuba mata.

Rice din tafara ci baifi spoon hudu ba ta ajiye taci wainan dayayi haske sosai ya gasu yayi Saqa kaman Suna Nigeria ne.

Hafiz ma zama yayi bayan ya zaunar da Arfat a kujeran kusa dashi hadda babbah ma zaman yayi sbd suci gaba daya Dan sunyi missing hakan
Saida dadah ta gama zubawa kowa Shikuma Arfat ta zuba masa samosa daya da waina daya ta zuba masa Zuma a gefen wainan tareda zuba masa madaran mamansa da aka dafa mata ta sake masa mixing da Zuman a glass cup ta ajiye masa tana nuna masa yanda zaici wainan sbd baima taba ganinta ba,jollof din Kuma bata zuba masa ba da sauran abincin sbd kwata kwata baisan yaji ba Yanaci zai iya haukace musu sbd abincin sun Dan Yi yaji sbd a gargajiyance yau tayi abincin jamaar gidan ma kusan ba kowa yaci ba sbd Basu Wani iya cin yaji ba Amma uncle Ahmed da Dad Omar sunci wainan sosai sbd Babu wanda a cikinsu zai Tina yaushe yacita last,su Fatmah dasu Mum Nur Kam Basu ci ba har gwara Arry ya gwada ci Amma yajin yai masa yawa ya Saka Zuma yaci sosai da Zuman kaman yanda Aunt Didi itama taci sosai.
##MAMUH


*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
107

*_AISHA's COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu...
Join our group to see lot of our amazing products 👇

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

*************
Da daddare gurin Dad dinta da Mum Nur tayi dinner tareda su sbd haka take rabawa Dad dinta da su babbah kanta kowa tana tsananin sonsa tana kokarin basa time dinta da kulawanta yanda ya kamata sbd dukkaninsu ta rasa wanda ya fi sonta tsakanin Dad dinta da babbah.

Ko da suka gama dinner tin a Nan dining Arfat yayi bacci Dan haka Sarrah ta kira ta daukesa daga jikin Dad ta nufi sama dashi Dan masa wanka da Shirin bacci.

Itama bata Wani ci sosai ba sbd abincin Rana ya kama cikinsu sosai Dan haka itace ta fara tashi ta tafi har gefen Dad dinta inda yake zaune tai masa goodnight ta juya tayiwa Mum Nur hakama Uncle Ahmed kafin ta wuce tabar gurin sbd Didi batanan Fatmah ma Kuma haryanzu babu Wani shakuwa a tsakaninsu, da Arry ne ta Saba sosai har take wasa da shi sosai.

Tana zuwa daki toilet ta wuce tayi brush tareda wanke fuska da hannuwa ta fito tana goge fuskanta da towel ta sauya kaya zuwa kayan bacci masu kauri Riga da wando sbd tana wanka ne ta sauka dinner,

Face dinta ta zauna gaban mirror ta goge da cleanser din La Roche posay tana gamawa ta haye lafiyayyan gadonta tareda kashe wuta ta shige bargon da Arfat yake Ciki Yana baccinsa Cikin nutsuwa Yana fidda Wani sayayyan kamshi me dadi Dan baa masa wasa da qamshi ko kadan.

Addua tayi musu tareda shigewa jikin 'danta tana lumshe Idanuwanta.


Washe gari tin a gurin breakfast kowa na kan table Dad ya sanarda kowa yafara shirinsa sbd sati uku masu zuwa zasu tafi Nigeria din Dan haka kowa saiya fara tattara shirinsa da ayyukan gabansa.

Hakan shine ya Saka zuciyar AM shiga Wani irin sanyi da daci lokaci daya sbd abubuwa datake son ta isa Nigeria din tayi da kanta wanda ba komai bane Neman sister Ashley.

Hafiz ma hakan Yana daya daga Cikin burikansa na son komawa Nigeria Dan haka yaji dadin hakan sbd a yanzu basuda Wani fargaba ko shiga damuwan komawa Nigeria sbd sunyi tsayuwan da bazasu taba tabuwa ga kowa ba,

Shi kansa babbah daman hakan yake jira a koma Nigeria din su huta da Wani boye boye ko yawon gudun kowanne Jan wuyan.

Dadah kuwa tafi kowa ma farin Ciki Dan ita Kam daman koyaushe fatanta yaushe zasu Nigeria din.

Mum Nur ce ma ta Dan ji kaman bazata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login