Showing 204001 words to 207000 words out of 261814 words

Chapter 69 - AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE.txt

MAMUGEE   

07 Jul 2024

59011

tana Bata barka da zuwa jdens family.

Godiya tayi tana miqa mata hannu.

Sama Dad Omar da uncle Ahmed Kai tsaye kowa bangarenda ya nufa sbd a matiqar gajiye suke kansu ma a cike yake da gajiyar tashe tashen hankalin da suka shiga Dan haka a yanzu da matsalar ya zama sun rufeta sun Kuma riqe wadda take shadar a hannunsu Hutu kawai suke buqata.


Sarrah ce datake kitchen tana aikin breakfast din Arfat ta fito ta iso palon tana musu sannu da zuwa Cikin girmamawa tana karban jakar hannun sister Ashley cikeda girmamawa tayi sama dashi kaman yanda Ameeenatou ta buqata.

Suma saman suka nufa hannunta na Cikin na Ashley sbd kuzarinta Bai gama dawowa ba.

Ashley ma jikinta Babu kuzarin sbd tsoron Allah da mamakin duniyar data samu kanta ayau aciki,

Tsari da asalin zubarwa da muhalli dukiya take Gani ayau,
Bata taba shiga ko ganin zahiran gidan dayake da girma da luxuries koina ba sai ayau din,

A waya ko hotina or tv take ganin mansions Dan haka sai yau Taga asalin mansion wanda daga lokacinda suka shigo anguwar ma tasan ta baro Muna Lagos ta shigo Lagos me aji,
Suna shigowa mansion din kuwa tasan ta shigo duniyar masu abin duniya uwa uba tinda suka shigo taji gashin jikinta na tashi sbd mamaki da ganin inda ake nufin anan yanzu zatai rayuwa.

A sama kuwa lafiyayyan palon Ameeenatou ne sai bedrooms dinta Dana Arfat sai Wani daban daya iya su ne a saman Dan haka Kai tsaye ta Saka Sarrah takai kayan Ashley dakin wanda komai dayake cikinsa na musamman ne sbd duk abinda yake samanta na musamman dinne.

Lafiyayyan bedroom ne hade da makeken toilet me Fadi da walwala wanda Shima komai a Ciki sedai kayan amfaninta ne kadai Babu Suma Sarrah na ajiye handbag din sister Ashley din a Cikin wardrobe ta juya taje store na kayan kamshi da ire iren hakan ta dauko mata toiletries kaya guda ta taho Dama dasu ta shiga toilet ta jere mata su.

Su brushes, toothpaste,hand wash, mouth wash, towels kusan 6 pieces Manya da qananu 4 sai Kuma sabulun wanka dasu shavers duk ta jere mata su ta sake wanke toilet din ta fito ta sake gyara dakin ta kunna ac da humidifier ta fice.

Numfashi sister Ashley ta sauke tana sake kallan dakin jikinta na sake sanyaya kafin daqyar ta miqe ta nufi toilet Dan wanka sbd jikinta har Wani nauyi ya mata sbd kwamacalar asibitin da suka baro din.

Kafin ta fito wanka dayar me aikin ta kawo mata dogayen rigunan Abayas masu kyau da tsada guda uku da sabbin undies da suke cikin bags dinsu ko tag baa cureba aka ajiye mata sai turarukan Da Suma na Ameeenatou ne aka dauko mata guda biyu masu shegiyar tsada aka ajiye mata gaban mirror tareda dai da duk abinda aka San zatai amfani dashi kafin a huta ayi mata shipping komai.

Suna gana ajiye mata komai suka fice tareda ja mata dakin wanda ya sauki sanyin ac da qamshi me sanyin gaske.


Ameeenatou ma wankan tayi ta fito ta shirya Cikin kaya marasa nauyi na bacci ma ta haye gadonta take bacci yayi gaba da ita me karfi sbd Cikin magani da alluran da aka saka a Cikin ruwan da aka Saka mata asibiti akwai maganin bacci me Dan karfi.

Gidan ma gaban daya daman basa fitowa da wuri Dan haka tsit kakeji

Itama Sarrah tana bawa ARFAT abincin safensa ta gyara dakinsa tareda Yi masa wanka ta shiryasa ta tareda maidasa bacci takaisa dakin mommansa ta ta kwantar gefenta ta fice tareda rufe dakin.

Ashley ma Jin shiru yasa itama bayan fitowa wanka ta shirya a daya daga cikin kayan da aka ajiye mata ta nemi guri a bakin gadon ta zauna daga Nan ta zame ta kwanta itama tana son tintsawa Amma Kuma tinane tinane ya hanata sbd batasan inda rayuwa zatayi da ita ba Kuma yanzu data samu kanta a Cikin wainda take kauna suke kaunarta sbd Jamaal kaman yanda ta fada a gurinsa zata zauna Amma idan Ameeenatou tace ita takeso yanda take son hakan zatai.

A tsakanin Jamaal da Ameeenatou tasan kowa daman xaice shine zai zabeta,
Duka tana tsananin sonsu sbd Allah daya Saka mata hakan ko Dan Jamaal dinne suka tallafi rayuwarta data mijinta Amma kaunar datakewa Ameeenatou jinta takeyi kaman jininsu ne daya,
Kaunace take mata kaman Babynta Dan haka kaunarce ta Saka takewa Jamaal kaunar data wuce misali sbd irin Azababben son dayakewa Ameeenatou tana Gani a Idanuwansa duk da bakinsa Bai furta hakanba Dan haka Bata Jin zata iya barin Ameeenatou tayi kuskuren rabuwa dashi sbd JAMAAL zai yadda ya rungumi balai Amma bazai taba sakinta ba kaman yanda ya fada mata a jiyan ko su Dad dinta su yadda kokuma su Sha bakin mamakin dazai tada hawan jinin kowa masu sabo da masu tsoho.

Daga karshe dai itama baccin ne ya Dan dauketa Dan haka Koda Sarrah ta jero mata lafiyayyan breakfast a qaton tray ta shigo dakin Taga tayi bacci fita tayi ta koma dashi tana rufe dakin a tsanake sbd kada ta tadata baccin.

Hafiz ma ciwon Kai Mai tsananin gaske da cunkushewan Kai Dana zuciya ne ya sakasa wanka kawai ya Kwanta Yana rufe Idanuwansa da sukai jajir sbd zuciyarsa Dake shiga tinani kala kala musamman azababbiyar so daya fahimta a Cikin zancen Jamaal na yiwa Am,

JAMAAL irin mutanen da idan Suna yiwa Abu mugun so me karfi basa buqatan Bude Baki su fada sbd kallo daya ya wadatar ka gane Dan haka yasan Jamaal ba lallai ya Bude Baki ya fadawa su Dad gaskia ba sedai zasu tabbatarda da hakan idan Basu aminta da aurensaba,

Sannan duka wannan tashin hankalin shine tayaya zaa boyewa Jamaal Arfat dansa ne?
Hakan zai iya yiyuwa kuwa har abada?
A baya tashin hankali da duka baqin Cikinsu shine anwa Ameeenatou fyade an mata Cikin to Kuma yanzu sun Gano ba hakan bane,
Mijinta ne halak dinta yayi Cikin Kuma family ma ne me zai Hana a fito a fadan idan yaso a taru a boyewa wanda zaa boyewa din.

Numfashi ya sauke Idanuwansa na nauyi sbd ciwon Kai,.

Shi dai a nasa bangaren idan Ameeenatou ta karbi Jamaal to tabbas zai tsaya ganin ta samu Jamaal din kaman yanda idan ma ta rufe Ido zatabi babbah da Dad dinta to tabbas bazai bari tayi Nisan da zatai Dana saniba ko baqin Ciki,
Tin farko shi Mai tsananin son Mai sonta da gaskia ne shiyasa ya kaunaci Haroon da qarfinsa Dan haka zaici gaba da kaunar Jamaal da tsaya masa Dan bazai taba ganin illar wanda yayiwa Ameeenatou abinda Babu wanda zai mata a duniya tinda basa Nan,ya tsaya mata ya Bata cikakkiyar gata da kariya a lokacinda Bata tareda kowa nata kowama Bai San inda takeba,Dan haka shi Hafiz idan har akwai a duniya wanda zaiwa 'yar uwarsa hakan ya Bata kariyar da sune yakamata su Bata Basu Bata ba basama Nan to baida wanda ya fi masa a gurin zama cikakken cancantar Matarsa da 'dansa.

Da wannan tinanin ciwon kansa ya tsananta ya rintse Idanuwansa Yana son yin baccin da kansa zai sake din bayan ya rage qarfin AC din dakinsa.


****Su JAMAAL ma Koda suka isa gida Jamaal jikinsa yakeji sosai Dan haka Kai tsaye Mum tafara dubasa hankalinta na tashi siddeeq na mata bayanin abinda ya faru itama take taji zuciyarta ta karaya sedai Kuma bayan ta gama duba Jamaal din ta basa magani Wani wahalallen bacci ya daukesa ta zauna tafara tinanin wasu abubuwan da Omar ke gujewa wanda itama tana guje musu din sbd shedancin Mam karshe ne.

Tasan Yana tsananin son duk Wani abinda zai fito daga jininsa musamman a yanzu da Jamaal kadai garesa Dan haka zai kaunace Arfat fiyeda yanda suke tsammani sbd jininsa ne 'dan Jamaal dinsa Amma Kuma hakan bazai Hana yayi amfani da Arfat din ba sbd ko yayansa daya Haifa Yayi amfani dasu Dan haka Arfat ne ma daidai amfaninsa sbd shine key na juya rayuwar Omar da dukiyarsa yanda yakeso Dan hakan ne itama take tsoro da shakkar saninsa Dan haka a qasan ranta ta fahimci Omar ta Kuma San yayi hakan ne sbd kauna da kulawansa ga Jamaal din tinda ai ba zai boye masa har abada.


Sai safe guraren 10 da Rabi Jamaal ya sauko har lokacin jikinsa da fuskansa ba walwala ko kadan sai kamewa.

Ganin hakan Mum ta zauna dashi da Siddeeq ta musu nasiha da bayani a tsare akan abinda ta fahimta ya Saka Omar din yin hakan Dan haka kada suji komai wata kaunar tana Saka ka batawa masoyanka indai zaka Basu kariya ko musu abinda zai amfanesu a gaba.

Jamaal kaman yanda tsarin rayuwarsa a duk tsananin lamari Yana kebe kansa Dan ya hadiye komai sbd fuskantar lamari a natse a nasa tsarin Dan haka Koda ya tashin bayajin komai bayan tsayuwarsa a maganarsa ta farko,
Babu saki a aurensa kaman yanda shi maganar Arfat kaman a rubuce yake ai karban dansa kawai dai bayason disrespecting Dad Omar ne zai barsa ya cike time din daya dibar musu su sauko din idan ba hakan ba zai bada mamaki sbd zai taho da Dad din nasa a gaban Dad Omar ya fadawa Dad dinsa Arfat dansa ne jinin SEELAHs
Bayan ya fada hakan Kuma ya karba dansa zai ajiyesa a gidansa yaga idan Dad dinsa zai tabasa Dan ya nuna musu Babu 'dansa ko matarsa a Cikin abinda aka fara Kuma ake kan Yi yanzu,
Duk wanda ya sakosu a Ciki a Lokacin ne zai dawo musu da Jeey dinsa.

Siddeeq dayaga yanayin Jamaal din take ya shirya musu tafiyarsu daya kamata su tafi Amma ya dakatar sbd abubuwan dasuka faru Amma ayanzu da kan Jamaal yake buqatan sake warwarewa gwara su tafi din sbd akwai Mahimmancin zuwan Jamaal din da kansa Dan haka Shirin tafiyar kawai yayi a daren yau zasu wuce.

Shi kansa Jamaal yayi Naam da tafiyan kawai sbd zai bawa gidan Dad Omar din Hutu na kwana biyu.

Mum dinsa ma kwanciya hankalinta yayi da hakan da kanta ta kaisu har airport tareda driver suka dawo.


A gidan jdens kuwa sai 11 kowa ya fara fitowa.

Ameeenatou ce ta fito ta karshe tareda Arfat dayek biye da ita Yana tsallen surutun special Aunt dinsa datace masa zata nuna masa.

Dakin Ashley suka nufa tayi knocking ahankali tareda budewa ta shiga daidai Ashley din ta gama waya da Siddeeq ya sanar da ita sunyi tafiya.

Zubawa Arfat Idanuwa Ashely tayi tanajin jikinta gabaki daya na sakewa da ganin Jinin Jamaal dayake bayyane a tattareda babyn gabanta.
#MAMUH#*_Arewabooks@Mamuhgee_*
121

*_HONEY DROPS_*
Albishir! Albishir! Albishirrrr!!!

Kin gaji da wula’kancin miji, ke ke nan kullum hantara da kyara , an hana miki rawar gaban hantsi a gidan aurenki, shin ko baki San gabad’aya dadin aure ba?. Hajiyata idan kina da kyau ki ‘kara da wanka, ke ke nan kullum babu wani sauyin dandano kullum zuwa kike wajen oga yadda kike, haba mana ba darajarki ba ne, mace ai ‘yar gyara ce, a d’in ga yi ana cleansing ana kuma spicing other room affairs. Sannan a gyara boobs d’in nan su cika su yi ma sha Allah a bar barinsu kamar guga, yanzu mace figure 8 bata burgeki ki ga ko ina ma sha Allah ga na Oyoyoo ga na bye bye, kina da HONEYDROPS me ya kai ki shaawar wata bayan kema tsaf zaki koma haka. To gyara ki ji ni da kyau HONEYDROPS wannan shahararren kamfanin na Aphrodisiac ma’ana kayan mata sun shirya tsaf don kawo muku zafafan kayan gyara wanda zaki mallake oga tsaf tsananin dadinki da niimarki, kayanmu aiki suke kamar yankan wu’ka kuma babu boka ba Malam, tsananin sanin makamar aiki ne kawai. Kayanmu na saka oga kyautar dole, muna soyayya da kulawar dole, suna birkita lissafin kishiya don dole ta ha’kura ta zama borar coz yan ajin HONEYDROPS a kullum sune Mowa, Muna…Muna… Muna…Muna fitattun kayan da ba su da na biyu kamar su

Infection flusher big 5k, small 3k
Breast firming sabaya 4k
Breast enlargement and hips sabaya 4k
Echoes of forever 3k
Her royal highness 2500
Milky vjay cake 3500
Ever bond 3k
Eternal flame 2k
Love nectar 2k
Cleanser pro 2500
Endless seduction 1500
Intensive love 1500
Swan 3k
Mowa’s secret 4k
Sugar queen 7k
Cloud9 4k
Sweet16 tightening gel 4k da sauransu. Muna da gumba kala-kala, tsumi kala-kala, muna dahuwar kaza, nama, tantabara, Ciccibi da sauransu. Muna da branches a garin Sokoto da Kano, sannan muna aike ko wani gari kowacce ‘kasa cikin amincin Allah, muna maraba da masu siyan daidai ko sari.
Za a iya tuntubarmu ta lambobi kamar haka
08167888934 ko
07026039714.
Ki yi ‘ko’karin ki tuntubemu don tabbas kukan damuwarki ta qare. Zaki iya tuntubarmu ta Instagram link dinmu kamar haka
https://www.instagram.com/honeydrops013?igsh=MW5saThrY3N0Z2Zjag%3D%3D&utm_source=qr



***********
Hawayen farin Ciki Mai tsanani ne ya ciko Idanuwanta tana kallan Arfat din fuskanta na bayyana hakan,

Takowa tayi tana nufosa Shima tsayawa yayi Yana kallanta da Blue Idanuwansa gefen momma dinsa.

Ameeenatou data sake fuska tana kallan Ashley gyada mata Kai tayi tana cewa

"NUHU ARFAT hs name"

Dawo da kallanta kan Arfat tayi Ciki kulawa da sakewan fuska sosai tana nuna masa Ashley tace

"Arfat,your special Aunt Ashley,
Say hello"

Sakin fuska yayi Yana kallan Ashley din ya maimaita sunan special Aunt Ashley da bakinsa kafin ta ware masa hannu ya tafi kuwa ta masa kyakkyawar runguma tana Maida hawayenta na farin Ciki sbd murnanta tai yawa,

Babynsu ne wannan na asibiti,.
Babynsu ne da suka Sha gwagwamarya akan samuwarsa da renonsa.

Wani kaunarsa itama taji ya mamayeta Dan haka ta dagosa tayi kissing hannunsa tana shafa fuskansa ta tambayesa Yaya yake
Ya amsa Yana kallanta Cikin sakin fuska.

Dagowa tayi ta kalli Ameeenatou Dake kallansu tana murmushi cikeda kauna da kulawa kafin ta Bude Baki tayiwa Ashley din barka da tashi.

Sarrah ce ta sake dawowa dakin dauke da lafiyayyan breakfast din Ashley din ta ajiye akan table tareda gaidasu cikeda girmamawa ta juya ta fice.

Tana ficewa zaunawa sukai anan sukai breakfast tare Arfat Yana jikin Ashley da kanta ta ringa feeding dinsa da kanta Suna magana da Ameeenatou din Cikin nutsuwa da kokarin sakewa da juna.

Saida suka gama suka sauko qasa Sarrah Kuma ta hau Dan tattara inda suka gama din.

Kai tsaye bangaren Dad suka fara zuwa suka gaidasa ta sake gaisawa da Mum Nur da Dad din harma da uncle Ahmed da Didi
Fatmah ma duka an gabatar musu da Ashley din daman a gurin breakfast Dad ya fadawa kowa matsayin Ashley a familyn daidai yake Dana kowa sbd inshallah ta zama tasu sune familynta ayanzu kaman yanda itama sune nata familyn a yanzu.

Babbah yayi mamakin hakan sedai Kuma Dad din ya sanar dashi sunyi magana da Ashley batasan waye uban Arfat ba Dan haka kawai kaman yanda suka rufe zancen basa tayarwa sunbarwa Allah.

Babbah yayi farin Cikin ganin Ashley sbd Yana kaunar duk me kaunar budurwansa musamman ita datai Wani irin zaman tsakani da Allah da ita.

A bangaren su babbah suka wuni Cikin kauna da kulawan dadah sai Rana bayan azahar Hafiz ya fito ya shigo palon su dadah sanye da guntayen kaya lafiyayyan fatar jikinsa na daukan Ido ya zauna cikinsu a tare sukai lunch dukkaninsu
Ashley na ganin kauna da kulawan dayake ta sakata hawaye tana hadiyewa sbd tsakani da Allah suke nuna mata kauna da kulawa.

Har dare suna bangaren su dadah sai da sukai dinner gaba daya gidan a tare dining room suka sake tattaunawa da Ashley Dan ta sake da kowa Dad Omar yace ta shirya washe gari akaita siyayyar abubuwan buqatanta.

Mum Nur ma haka ta sake Janta a jiki Cikin sakewa da magana hakama Didi
Su dadah kuwa already tafara Dan sakewan dasu a wuni daya.

Suna hayewa sama wanka kowannensu yayi tareda sallan ishai da Akai tini kafin Sarrah ta dauki ARFAT daga dakin Ashley takaisa dakinsa tai masa Shirin bacci ta dawo dashi dakin sbd Ashely tace abarsa ya kwana gurinta.

Ameeenatou tana gama Shirin bacci kwantarwa tayi duk da tanada aikin dataso dubawa a laptop Amma sai safe.


Washe gari AM Bataso zuwa office ba Amma akwai meeting da zasuyi dole tana buqatan halarta Dan haka Mum da Ashley dinne suka fita tareda driver a Cikin lafiyayyar motar data Saka Ashley sauke ajiyan zuciya.

Suna isa Mum Nur gurin hutarwa VIPs ta nufa ta zauna ta bawa Ashley card tace duk abinda idonta ya sauka Akai tana buqata ta dauka.

Siyayya sosai sukai wadda tayi yawan daya bawa Ashley tsoro sbd data Dan kwatanta ta dauka Mum shirme ta dauki siyayyar Dan haka da kanta ta tashi ta dibar mata asalin designers din gaske suka zubar da kudi suka dauki kaya wanda sedai motar gurin ce ta Kai musu kayan gida su daga Nan gurin siyan kayan native suka nufa anan ma wasu mahaukatan laces masu kudin gaske ta dibar mata da atampopi ready made din kwarai suka sake zubarda kudin kafin suka nufo gida.

Suna dawowa a gajiye Babu abinda sukai abinci suka zauna suka ci Koda Ashely ta isa dakinta tini Sarrah ta gama jere komai ta tsarasu hatta shoes da bags da Tarin uban undies din tini ta gyara komai ta jeresa.

Wanka tayi ta fito ta nufi dakin Arfat lokacin Sarrah na tareda shi tana tayasa wasa da books dinsa na drawing.

Yana ginin Ashley ya dawo gurinta suka dawo palon saman suka zauna kallan cartoon tana biyewa wasansa.


Sai yamma Ameeenatou ta dawo gida a gajiye tareda Hafiz da Fatmah wadda itama gabaki daya ta lafe sbd jiran inda tashin hankalin maganar data fada zata fara bullowa sbd tasan Jamaal bazai yadda da aurenba ayanzu a dayan tinaninta Kuma shirun dayayi ya fasa auren ne Shima yabarsa.

A jere motocinsu suka shigo Mansion din kowa yayi parking ya fito sukayo Ciki.

Samanta ta wuce Kai tsaye sbd gidan tsit su Dad tasan basa Nan Mum Nur Kuma tana samanta Didi Kuma tana kitchen ta sani.

Tana shigowa palonsu na saman Arfat Dake tsalle jikin Ashley da gudu ya sauko yayi gurinta Yana ambatar sunanta.

Cikin farin Ciki ta rumgumesa tana kissing gefen fuskansa tayi gurin Ashley tana mata magana.

Bata Wani zaunaba ta wuce daki Saida tayi wankan tai sallan laasar ta shirya ta fito Cikin skinny jeans da shirt me Fadi tazo ta zauna Sarrah ta kawo mata abinci anan ta zauna tanaci Suna magana fira da Ashley harta gama.


Cikin kwanaki kalilan Ashley ta Sabu da familyn duka ta sake a cikinsu ta koma yar gida sosai ake kaunarta ba banbanci ta zama yar gida hakama itama bata Wani son zaman banzan saukowa takeyi ta tafi kitchen tareda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login