Showing 93001 words to 96000 words out of 261814 words

Chapter 32 - AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE.txt

MAMUGEE   

07 Jul 2024

59023

bane.

Tsaro da kulawa me tsananin gaske tareda Wani irin taka tsantsan sister Ashley keyi da AMEENATOU din tin daga ranar da Dr Adams yabar asibitin hakama barin Dr Adams asibitin shine ya dawo dawo da wannan girmamammen nauyin na AMEENATOU a kanta sbd komai ya lalace ne daga wannan lokacin zuwa yanxu dan haka sosai take kulawa da ko cup din daya shafi shan ruwanta bata wasa dashi,
Hatta iskan da Ameenatou take shaka a dakinta kiyayewa akeyi sbd kudin da ake Bata na Hakan gigita suke Neman yi da kuntar mata da kai.

Kasan dakin data dauke kafafunta Ameenatou din ta sake kalla tana Dan juyar da Kai ahankali sbd son ganin ruwan dataji sanyinsu ya ratsa har cikin kanta sedai Bata ga komaiba Dan haka ta sake zuro kafarta Daya ahankali ta sake dorawa a qasan ta sake Jin Wani sanyin ya sake ratsata me tsanani Dan haka ta sake dauke kafan da sauri tana sake kallan kasan da kyau sedai wannan Karan a hankali cikin sautin muryanta me taushi cikin sanyi tace,

"Ruwa?
Ina ruwan?
Bangansa ba"

Bude kofar dakin me tsananin karfi da kaurin gaske sbd tsaro Akai ta dago idanuwanta da sauri ta zubawa kofar tana ganin sister Ashley ta sake murmushin Daya Saka sister Ashley din sauke ajiyan zuciya sbd ba qaramin sanyin kyan Ameenatou take Gani ba hakama juyewan kwakwanta daban yake Dana sauran patients nasu Dan ita komai nata sanyi da rashin hayaniya ne dashi Wanda ita datake kulawa da ita take kallan Hakan a matsayin Kila Daman can miskila ce Kokuma gata ne yayi mat yawa yasaka batada hayaniya.

Wani murmushin me kyau Ameenatou ta sake saukewa tana dawo da kallanta kasan tana cewa

"Kafan Ameenatou ya shiga cikin ruwa" ta qarasa fada tana nuna kasan dakin da hannunta Daya har lokacin idanuwanta na qasan hakama fuskanta daukeda kyakkyawar murmushin nata me sanyi.

Qarasowa sister Ashley tayi tana kallan kasan tana Dan sake fuska da kulawa da murmushi sbd fahimtar saukowa tazo yi taji sanyi sosai shiyasa gashi Sam Sam Ameenatou din batason sanyi ko kadan shiyasa kusan koyaushe sanye take da kaya masu nauyi da rufe jiki akan uniform dinta har gwara idan tana dakinta ne takan cire mata tabarta da iya uniform din.

A farko kusan kayan da ake kawowa sbd Ameenatoun Babu Wanda bame kauri da rufe jikinba shiyasa kusan itama Ameenatou din ta Saba da kayan batason sanyi ko kadan,
Hakama socks ma kusan basa rubuta da kafafunta musamman da dare idan zata kwanta baa taba mantawa baa Saka mata ba,

Ta bangaren rayuwarta a asibitin babu Wani kusanci ko maamalantar datake shiga tsakaninta da kowa bayan sister Ashley da likitocinsu,
Kaman yanda dokar take zuwa daga Sir siddeeq Wanda shine kadai Wanda sister Ashley ta sani family din Ameenatou din Babu Wanda ya yadda dashi na a bari ya samu kusanci ko shakuwa da ita tin daga ma'aikatan asibitin har nurses da sauran patients,
Ita kadai yake buqatan rayuwarta a cikin gurin batareda kusancin kowa ko wata muamalan ba Dan hakane ya Saka sister Ashley ta yafe ranakun hutunta koyaushe tana asibitin dare da Rana sbd Ameenatoun wadda duk yanda suka samu shakuwa da kauna tana kulawa da ita bakin Rai bakin fama Amma duk yanda taso sanin komai akan Ameenatou din Bata samu sanin komaiba Abu Daya kadai ta sani a bakin Ameenatou din shine Babbah da Haroon datake fada wasu lokutan a cikin yanayin ciwonta tamafi fadansu a cikin baccinta Amma bayansu Babu sunan wani data tana kamawa,

Sanin sister Ashley sir siddeeq ba shine Asalin Wanda yake tsaya akan Duk abinda ya shafi Ameenatou ba ubangidansa ne Kokuma tace ogansa ne sedai ta rasa sanin waye to?
Waye shi?
A Ina yake?
Meyasa Bata Taba ganinsa ba sedai siddeeq?
Meyasa Dr Adams duk girmansa da matsayinsa Saida ya kusa aran hauka lokacinda aka ciresa daga asibitin dagama kasar gaba Daya Rana tsaka sbd kawai Ameenatoun yayi rejecting sauyinsa wadda ya basa matsala babba,
Meyasa Dr Adams zaiyi risking Career dinsa me tsananin girma ta shekaru akan Ameenatou?
Wacece ita?
Sbd waye Shima Dr Adams din yayi Hakan?
Menene dalilin Daya Saka sabbin likitocinsu da aka kawo suka Fi Maida hankali akan Ameenatou din Suma har Saida suka tabbatarda haukarta tafi wadda aka kawota da ita Dan yanzu komai nata ya juye kaman baby haka take shiyasa a yanzu komai nata yake a sanyi kaman yanda sanyi babu hayaniya babu abinda ta sani daga sister Ashley sai siddeeq dayake zuwa dubata kusan kullum shima har lokacin batasan waye shi a gurinta ba amma dai akwai shakuwa da kauna data shiga tsakanin sabuwan alaqarsa da ita wanda a yanzu shima duk duniya itace kadai abinda yakejin zai iya bada rayuwarsa dan bata kulawa da kariya sbd matsayinta a gurin Ubangidansa kuma mutumin dayafi so da kauna fiyeda komai nasa da kowa a rayuwarsa ta yanzu,.


***Bayan barin JEEY SEELAH qasar komai ya faru ba Ayanda kowa yaso ba sai yanda ubangiji yaso,

Yanda kake tsari daban da yanda ubangiji yake tsaro Maka,

Mam seelah rashin Haroon ya tabasa fiyeda yanda ya tsammata Dan kuwa Bai taba sanin mahimmancinsa ba sai yanzu da bayanan Dan kuwa a yanzu tamkar uban da Bai da 'da ko Daya a duniya yake,
Bai taba sanin kaunar dayakewa Jamaal girmanta yakewa Haroon dinsa ba sai yanzu Daya rasashi,

A yanzu baida 'dan da zai ganawa azabar yayi fadan Kuma yayi masa yanda yakeso,

Duk yanda yake nuna jarumta da dauriya tareda komawa kan harkokinsu gadan gadan Dan nuna jarumta a cikin zuciyarsa raunine da gurbi me girman gaske da Babu me iya cike masa shi harda qari idan ba JAMAAL SEELAH ba Amma yasan wannan Wani mafarki ne da bazai taba samun cikewansa ba,
Buri NE da bazai taba cika ba Kila a garesa na samun JAMAAL dinsa yanda yakeso matiqar ba zubarda makaman yaqinsa zaiyiba ya tuba ya dawo hanya Hakan ne kadai zai Saka zafin kan JAMAAL sauka ya karbesa a matsayin Uba Wanda shikuma Bai debo wainnan shekarun da kashe kashenba Dan ya tuba a gaban Dan Da shine ya haifesa batareda ya samu abinda yakesoba,
Duk rayukan da suka dauka sun tafi a banza,
A daidai yanzu zai iya cewa Bai damu da rayukan da suka mutu ba akan duka wannan burin nasu dasuke dauke dashi tin Ashalawa,
Tin daga mutuwar su kasim da jamilu har izuwa ta Abdul din Babbah zai iya cewa ya barsu a banza Amma a yanzu da Haroon dinsa ya rasu a wannan fadan bazai taba saurarawa ba sedai ayi kowa ya rasa Amma bazai iya barin OMAR JADEN SEELAH da dukiyar da gurin fadanta ya rasa 'dansa jininsa ba kwalli Daya da duk duniyar Nan shi kadai ne yake tsananin sonsa tin daga jini da zuciya.

A yanzu da AMEENATOU OMAR JEEDEN SEELAH din ta zama Daya daga cikin ahalinsa ko Omar naso ko Jamaal naso ko basa so aikin gama ya Riga ya gama dama me girma tazo hannunsa da Babu Me kwance masa Dan kuwa Babu Wanda zai raba wannan auren da aka daura batareda ya rabasa da duniya ba ko waye,

Baisan lokacinda JAMAAL ya daura auren da ita ba sai da aka daura suka sani Amma Kam ya sani ko shi Daya aure tan bai Isa ya saketa ba wannan insha Allah alkawarinsa ne da Babu me daga masa shi.
#MAMUH#
#WAR#SEELAHS#JDENS
#AMEENATOU JEDEN SEELAH
#JEEY SEELAH
#HOTLOVE
#ROMANCE
#CRAZY IN LOVE
#ZAFIN KAI


*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_AMEENATOU_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar



59
A ranar da JEEY yabar qasar BB da Daddy lameenu sukaji kaman sun fita daga mummunan balain da basusan Yaya zasu siffantashi ba Dan kuwa dukkaninsu a rikice Kuma a tsorace da fargaba suke akan zai iya tsananta bincike akan ciwo da mutuwar Dan uwansa Amma ba sanin nasa ne babban balai da masifar ba idan Mam yaji ko ya sani Babu Wanda yasan ta inda mutuwarsu zata bullo daga hannunsa ba a cikin ruwan sanyi da qwarewan da ko su da kansu bazasusan kashesu yakeyi ba da duk hanyar dayaso Dan Mam seelah idan ya tashi koda ta iskan da kake shaqa ne zai iya kasheka Kota suturan sakawanka ne kuwa Dan haka kullum Daddy lameenu a ajiqe yake cikin fargaba da rashin nutsuwa Amma Shima kwata kwata a bayyane ya boye batareda Mam din ya gane fargabansaba Koda wasa.

BB kuwa da dukkanin yaransa JEEY ne abin tsoro da tashin hankalinsu Dan haka rayuwarsu a rikice take har Saida suka ji yabar qasan suka shaqa numfashin Jin dadi da Kwanciyar hankali.


Shiru komai yayi na tsawon lokaci kwanaki,
Kowa ya dakatar da komai na buri da qudurinsa sbd samun nutsuwa da dawowa daidai Dan kuwa kusan kowa a lokutan da suka gabata an shiga tashe tashen hankali da firgici harma da masifu daban daban Dan haka kowa ya lafe ya bari ya dawo daidai ya samu nutsuwa,

Su BB ma Hutu suka tafi Dan samun caja Kai da hutun zuciyar tashin hankalin da suka shiga na tafiyar JEEY,

Ta bangaren Mam ma dakatar da komai yayi Yana buqatan Hutu tukuna hankalinsa kwance kafin daga baya ya tashi tsaye a komai,

Ta bangaren su Babbah kuwa Babu wani sauki ko ci gaban da ake samu daga yanayi nasu.


****A Poland kuwa Dr Aleena jikinta yayi tsananin da isan JEEY hankalinsa yayi mummunan tashin da zafinsa yake neman qarasa zafafa kansa da zucuyarsa dan kuwa a yanxu mum dinsa itace abu ta karshe da bazausi rasawaba ko wani babban abin ya sameta dan haka take komai da kowa ya fice daga kansa bayan ganin samun lafiyan mum dinsa dan haka komai nasa ya dakata ya dauke wuta hatta siddeeq da duk wani me nema ko buqatan jinsa daga Nigeria dif suka jisa babu ko labarinsa.

Kasancewansa Daya daga cikin manyan kwararrun likitocinsu Kuma me asibitin kanta gabaki Daya hakama 'da Daya da suka sani na Dr Aleena din wadda take daya daga cikin shugabannin asibitin dama manyan ma'aikatan lafiyan da ake ji dasu ya Saka kusan case dinta ya dawo hannunsa Amma ba duka ba Dan Hakan bame yiyuwan bane sedai Kuma suna buqatansa Dan kwarewansa.

A duk yanda sukaso ceto ko Hana abubuwan tabbatuwa akan yanayinta Hakan Bai yiyuba sbd abinda Allah ya Riga ya kaddaro Dan haka ya sake shiga tashin hankali jikin mum din Dan kuwa kusan paralyze din duka suke gudu ya shigo ya shigo din sedai ba gaba Daya Rabin jikin bane daga qasa ne kafarta Daya yafara kamuwa Dan haka suka sake maida hankali sosai ba sauki da ganin samuwarta.

Ta bangaren Daya jininta kwata kwata yaqi sauka gata a kwance din Bata San waye akanta ba Amma a zuciyarta rashin danta kaman yaqi sakinta ko kadan su samu su shawo kan matsalar.

Acikin sati uku da yayi da dawowa Babu wani sauki da suka samu daga jikin mum dinsa ga bangare Daya rasuwar Haroon ba sakinsa tayiba Shima Wani tsananin radadi da kadaici tareda kewan Dan uwansa da mahaifiyarsa yakeji Dan haka gaba Daya rayuwarsa ta sake shiga Wani irin kadaici da miskilancin gaske Danma gabaki Daya ya Manta da auren Dayake kansa,
Ba auren kadai ba komaima ya ajiyesa gefe ya zabi mantawa dashi sbd zafin da kansa yake ci.

Siddeeq da shi kadai ne yake communicating dashi ta asibitinsu Bai taba yi masa maganar Ameenatou ba sbd ganin Halinda yake ciki Wanda Baya buqatan kowace irin sabuwar magana ko damuwa bayan wadda take gabansa dan haka Bai taba fada masa komaiba ya tsayu da kansa yana kulawa dasu Babbah shida umman fadila sai kuma AMEENATOU da kusan itace yafi bawa komai na kulawa da hankalinsa fiyeda tasa rayuwarma tareda tsayuwa tsayin daka Yana tabbatarda rayuwar luxury ake gudanar mata a cikin asibitin kuma hadda ganin JEEY ya manta da maganar auren gaba daya a yanzu ya sanyashi barin zancenta kwata kwata bai taba masa ba kafin nauyi da zafin zuciyarsa ya ragu.


*****Dr Adams dayake kulawa da Ameenatou fiyeda sauran patients dinsa duka hakama case dinta a hannunsa yake gaba Daya sbd Sanin Asalin matsalanta ita nata juyewan kan bana hauka bane daga alluran da JEEY yayi mata Wanda wata Daya kacal zatai ta saketa hakama yasan ba karamin mahimmanci ne da ita ba a gurin JEEY ba tinda ya zabi kawota anan ya ajiyeta dan kada kowa ya taba ta ga kuma wasu kudin gaske daya bayar a asibitin na tallafawa asibitin kawai duk da tsadan asibitin,

Wannan ne ya Saka ko file din Ameenatou Bai taba shiga hannun kowanne likita ba bare nurses bayanshi,
Babu Wanda yasan me file dinta ya kunsa sbd Babu wani bayanai sosai a file dinta bayan sunanta da sauran informations nata sai Dan taqaitaccen bayanin da Babu wani abin kamawa akan ciwonta,
Babban abin ma da kusan yake tsananin kiyayewa shine Babu kowane drugs datake Kai bayan na ciwon Kai saina yawan bacci da vitamins wannan ne ya Saka Sam Baya wasa da lamarinta Dan kada Wani likitan ya dorata akan wasu drugs ko alluran da zaa iya samun mummunan matsalan samar mata da ciwon haukan gaske.

Dr Adams da kansa ya Dora sister Ashley kulawa da Ameenatou tin daga wankanta da komai nata tareda tsaftanta da Bata tsananin lokaci da kulawanta,
Da farko itama Bata dauka mahimmancin Ameenatou din ba Saida taga irin ruwan kudin da Dr Adams da Siddeeq suke mata take ta nutsu tasan da gasken gaske Ameenatou din me mahimmancin ce.

Yanda take kulawa da ita tamkar 'yar babyn da baa yarda da komai ya tabata ta fahimci ciwon Ameenatou din kaman ba kaman na sauran patients dinsu bane sbd lura da Babu magani ko wasu allurai Da Dr Adams yake mata hakama Babu Wanda file dinta ya taba shiga hannunsa bayan ita Kuma itama din Bata taba budewa ba sbd Dr Adams Daya Riga yayi mata bayanin Ameenatou ba kaman sauran patients dinsu bane iya abinda ya dorata Akai shi kadai yake buqatan ta tabbatarda Ameenatou din na karba.

Sister Ashley ahankali ahankali ta sabu da Ameenatou da sanyinta rashin hankalinta Wanda kwata kwata ita nata haukan kaman baby ta maidata Dan kuwa komai sai anyi mata Batayi hatta brush itace take taimakawa tayi mata suyi tare hakama tarin panties da undies da aka siyo aka kawo na amfanin Ameenatou din mamaki suke Bata Dan haka komai sakawa Daya take masa ta wanke mata Bata barinta tayi maimaita abu batareda wanki ba dan sosai dr Adams take maimaita mahimmancin tsaftar Ameenatou din badan komai ba sbd sanin waye wanda ya kawota tsaftarsa da kyankyaminsa na musamman ne.


******
Gyara zama Daddy lameenu yayi akan kujeran office dinsa Dayake floor din sama gaba Daya na lafiyayyan kamfanin SEELAHs ya dago idanuwansa ya kalli BB dayake zaune gabansa yana zuba masa cikakken bayanin komai gameda asibitin da Ameenatou jden take.

Yana gama bayaninsa bakon da suke Jira ya iso kofan office din tareda Ben yaron BB.

Ben ne yayi knocking kofar cikin nutsuwa da girmamawa yana Neman izinin shigowa.

BB ne ya miqe tsaye Yana kallan Lameenu Wanda ya gyada masa Kai alaman ya shigo dasu.

Kofar ya nufa ya Bude tareda kallan Dr Dee dayake bayan Ben Yana masa barka da zuwa cikin girmamawa Badan ya cancanta Hakan daga garesa ba sai Dan suna buqatan Aikinsa ne Kuma aiki na kammala zasu batar da sahunsa dan duk abinda zai saka Mam sanin sunyi abubuwa ba da sani ko izininsa bazasu taba barin wannan shedan ba koda ta ran mutum ce se sun kaudata dan gwara ya kashe iyalan lameenu kaf daya kashe rai daya daga cikin rayukan da mam ke tsananin so a gurinsa yanzu dinma tsautsayi ne yariga ya cisa na shiga wannan barnar ta lameenu suka hainci Mam batareda saninsa ba suka aikata illa ga Haroon gashinan sun kasa samun nutsuwa a tsorace suke,
Shi kansa Lameenu kwata kwata Baya cikin cikakkiyar nutsuwan wannan ta'adin da sukai Kuma yanata Dana sani sedai shima kaman yanda idan Mam ya fara aiki ba ja da Baya Shima bayajin zai ja da Baya daga abinda ya fara tinda idan ba lalata komai daga duk abinda zai Saka Mam mallakar dukiyar Omar ta hanyar sirikarsa ba to Yana mallakarta ma zai iya sanin komai daga ranar sunsan qiyamarsu ta gama tsayuwa

hanya BB ya bawa Dr Dee ya wuce ciki shi kuwa Ben kofar ya tsaya daga waje Yana tsaro.


Daga ciki kuwa Dr Dee na ganin Daddy lameenu seelah cikin girmamawa ya iso fuskansa a sake Yana gaidasa cikin mutuntawa sosai.

Daddy lameenu kuwa sbd jansa a jiki Shima fuska ya sake sosai tareda miqa masa hannunsa dayake daure da wata tsadaddiyar ogogon Rolex Yana masa barka da zuwa.

Tsananta sake fuska sosai dr Dee yayi Yana miqa hannunsa suka gaisa da Alh lameenu seelah Yana Jin dadin samun gayyatarsa zuwa gunsa,

Gurin zama Lameenu ya nuna masa Yana cewa,

"Please Sit Dr,
Barka da zuwa,ya ayyuka ya fama?
BB pls a kawowa water,tea or coffee Kokuma Idan akwai abinda yakeso ya fada a kawo masa."

"No am ok bana buqatan komai thank you" Dr Dee ya fada fuskansa a sake Yana Dan ajiye wayoyinsa a gefensa cikin nutsuwa Dan Shima din da abin duniyarsa bawai talaka bane ko mara karfi Yanada nasa arzikin daidai matsayinsa masu yawa ga Kuma matsayi me girman gaske dayake dashi a asibitin da Ameenatou take Dan kuwa shine kusan babba gaba Daya a asibitin.
#MAMUH#
#DR JAMAAL JEEY SEELAH
#AMEENATOU JDEN SEELAH
#MAM SEELAH
#LAMEENU SEELAH
#OMAR SEELAH
#WEALTH/POWER
#BESTLOVE
#HOTLOVE
#ROMANCE


*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
60
BB ne ya matsa Baya ya dawo gefen Alh Lameenu ya tsaya Ya Kallesa kafin ya zauna a natse Yana sake gaisawa da Dr Dee din Yana bayyanarda girmamawansa sosai tareda nutsuwa kafin Shima Alh Lameenu ya sake sakewa suka gaisa sosai Yana tambayarsa aiki suna shiga zantukan rayuwa Dana ayyuka da yanda businesses na mutane ke tafiya kafin a natse cikin Kwanciyar hankali ba boye boye Daddy lameenu ya Kalli Dr Dee daidai lokacinda BB ya miqe tsaye ya ajiye masa Yan 100 100 doller a kan table din gabansa kusan bundle biyu zuwa uku batareda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login