Showing 27001 words to 30000 words out of 44853 words
Zaman dafi’an na yi akan sallaya. Ina ta lazimi da addu’ar Allah ya ‘dorani akan Ustazuna ya janye batun auren waccan yarinyar mai kama da zabiya, idan har ya amince ni na yarda ko kashegarin ranar ne a ‘daura min aure da shi. Daga baya zan san yarda na yi muka shirya da Mami.
Ina zaunen akan sallaya Ya. Muhd ya shigo, ‘Dan duba na ya yi sai kuma naga ya tab’e baki ya furta “Ki taso Malama, bak’onki ya zo.” D’aga kai na yi gabana na cigaba da matsanancin bugu. Na mik’e cikin mutuwar jiki da kasala. Dama na jera masa komai a sitroom ‘din.
Fuskata fayau ko kwalli babu na fita wajensa cikin shigar doguwar riga bak’a da na yi rolling da mayafinta. Jikina ruf ba inda ake gani sai fuskata don hatta k’afata a rufe take.
Da sallama na shiga parlorn yana zaune ya tank’washe k’afa suna hira da Ya. Muhd har ya fara cin abincinsa. Ya ‘dago kai ya kalleni ya mayar kan abincinsa. Ya. Muhd mik’ewa ya yi ya fita. Ni kuma na zube a k’asa daga gefensa ‘dan nesa da shi ka’dan. “Ina yini?” Ya ‘dago yana kallona. Kafin ya furta “Lafiya Lau Ukhteey..” Turo baki na yi, na ce “Ni ba y’ar uwarka ba ce..” ware idonsa ya yi ka’dan ya furta “Then ke mecece?” Sunkuyar da kai na na yi ina wasa da yatsun hannuna. Ustaz bai bar kallona ba don ina ‘d’agowa muke sake ha’da ido da shi. “Amsa min mana ke mecece? Tunda kin ce ba kya so na, ni yanzu kallon k’anwa nake miki..” Idona ne ya kawo ruwa na zuba masa idanun nawa da naga ya k’ank’ance nasa idon ya saka cikin nawa ya Kuma lumshe su. Cikin wata irin murya ya furta “Matsayin Yayan ma ba zaki bani ba kenan?” D’aga kai na yi. Ya yi dariya sosai har wushiryarsa na bayyana ya ce “Shikkenan nagode. Matsayin me zaki ba ni? Gaya min AYSHA?” Mutsu-mutsu na fara yi shi kuma ganin hakan bai saka ya d’auke idonsa ba. Kallona yake kawai yana murmushi yana kuma kurb’ar ruwan zob’onsa. “Ba zaki gaya min ba? Ai shikkenan bari na tashi na tafi Habibteey na jira na, na gode da girki ya yi da’di sosai mijinki ya ji da’dinsa Wallahi na masa murna. Nima Allah yasa dai Habibteey ta iya girki…” Turo bakina na yi na furta “Ni ka daina min zancen zabiyar nan…” ware idonsa ya yi yana furta “Habibteeyn ce zabiya? Lallai ma, to idan ita zabiya ce ke kuma mecece?” Ban san sanda na harareshi ba. Na furta “Allah ya sawwake ni Ai fari na ba irin nata ba ne. Fari na yafi nata kyau…” Ya tab’e baki yana dariya ya ce “Ko dai kishi ne? Idan banda haka kiga yarinya zubin larabawa ki ha’da kanki da ita. Zan tafi ta ce ma
Na gaisheki, amma kafin na tafi ina son na san matsayina sannan don Allah a min alfarma ki halarci event ‘dinmu ko guda ‘d’aya ne….” “Wallahi ba zani ba…” Na furta da sauri, har muryata na sark’e wa saboda tsabar takaici da bak’in cikin da zuciyata take ciki. Na lura ba k’aramin so yake mata ba kuma duk ni na jawowa kai na. Da sauri na fice daga ‘dakin ina sake fa’din “Ba zan je ba, sai kace wata mara zuciya…” Ban san sanda hawaye ya dinga rigegeniya a kan fuskata ba…
Ranar kam ba barcin da ya ‘daukeni, ko b’arawon ma hak’ura ya yi ya k’yaleni.
Da safe kam da ciwon kai na tashi. Kuma ko shara ban yi ba. Ina kwance a ‘d’aki Anty Khadija ta shigo tana kallona ta ce “AYSHA kin tashi, naga yau ko fitowa ba ki yi ba. Ki je in ji Yayanki.” Ban amsa mata ba, don haka kawai na samu kaina da k’uncin zuciya da jin haushin kowa ma. Na mik’e da rigar Barcin da take jikina na fita parlorn. Kaina ko gyara babu. Idona ya yi k’ozai-k’ozai.
Zuba min ido Yaya Muhd ya yi kafin ya furta “Ke baiwar Allah, lafiya kike? Kinga yarda kika dawo kuwa?” Kallonsa kawai nake ban amsa ba ganin yarda yake walainiya cikin sabuwar shadda fara k’al da ita. Ya tab’e baki ganin bani da niyyar amsawa ya ce “Allah ya kawo sauk’i, ke Khadija mu je na sauke ki a asibitin tunda ita bata shirya ba, balle ta raka ki, ni zan wuce wajen d’aurin auren Ustaz… Hararar gefen ido kawai nake watsa masa, ina ganin Ya Muhd d’in kamar wani gagarumin mak’iyina. Ganin ba zan amsa ba ina kallo Suka fice shi da matarsa suka rufo min k’ofa…
Na cusa hannuna cikin gashin kaina ina jin zuciyata na wata irin suya. Hawayen ma k’in zubowa suka yi. Kawai wani irin kuka nake na zuci. Ban san iya lokacin da na ‘d’auka a kwance a wajen ba, sai ji na yi wata ta yi k’ara na duba naga msg d’in Ustaz ne ya shigo wayata. Tsaki na zuba kamar ba zan karanta ba sai dai na bu’de sai naga ya saka “Alhamdulillah an ‘d’aura aure na, ina jiran fatan alheri daga k’anwata…..
Duum naji na daina ji da gani…
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group for updates on our unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more
https://chat.whatsapp.com/FuUV3xjAcKgDaquGHnOnjw
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 14
14…..
Tun daga kwanyata nake jin wani irin zafi, har k’asan zuciyata. Jikina ya yi sanyi sosai kukan ma ya kasa zuwa sai wani b’acin rai nake ji mai dugunzuma zuciya, ya raunata gabban jiki. Da k’yar na sulale na zame na kwanta a k’asan carpet ina lumshe idona. Tafarfasar da zuciyata take yi yasa na dinga jin kai na yana neman yin tsawa. Gashin kaina na burkita gaba d’aya ina jan gashin da k’arfi kamar shi ya min laifin. Kuka nake son yi amma kukan ya k’i zuwa. Rigar barci ce a jikina ban kuma damu da na cireta ba, don bata wankan nake ba. Sai yanzu na ji ina jin haushin biyayyar da na yiwa Mameey, kamar na cuci kai na kamar ni na jawowa kai na.
Ina kwancen cikin tafasar zuciya idanu na a kulle. Na ji kamar wani na tsaye a kai na. Da k’yar na dinga bu’de lumsassun idanuna sai na ga Ustaz ne a tsaye sake mayar da idon na yi na kulle don ina tunanin imagination d’in da na saba ne.
Daf da ni na dinga jin k’amshin mayataccen turarensa, don haka na ware idona sosai na zuba su a kansa. Yana zaune daf da ni idanunsa a kaina yana sakar min murmushi. Da sauri na mik’e cikin razana ina neman ko Hijab ne da zan suturce jikina don rigar barci ce a jikina itama iya gwiwa mai santsin gaske, sanda suka tafi na ji abin duniya ya min zafi ban san sanda na wancakalar da Hijabin can gefe ba. Hijabin yana daga can bakin k’ofa. Ga shi sam ba zan iya tashi ba. Na takure gefe guda ina rufe jikina duk da na san ba abinda bai gani ba, don ban san tsawon wani lokaci ya ‘d’auka a wajen ba. Murya a sark’e na furta “Ya zaka shigo min haka? Ba sallama ka bani Hijab ‘dina…” Still kallona yake yana murmushi kawai bai kuma mik’o min Hijab d’in ba. “Please Ustaz, ka bani Hijab ‘dina….” Na furta kamar na yi kuka. Muryarsa a sark’e ya lumshe ido… ya furta “Idan na k’i fa?” A tunzire na furta “Amma dai ka san haramun kake kalla ko?” Sake k’ura min ido ya yi kafin murya can k’asa ya furta “Da jikin da Mai jikin yau duk mallaki na ne, Matar Ustazunta…” wani irin ware ido na yi don ni duk ban fuskanci manufarsa ba. “Tashi ki ‘dau Hijabin naki…bari na rufe ido na..” Ya fa’da yana rufe idon nasa. Ban san sanda na wani irin mik’ewa da sauri ba don ‘d’aukar Hijabin, sai ji na yi kawai ya jawo ni na fa’do jikinsa ya saka hannu ya rungumeni sosai yana sakin ajiyar zuciya. Idona a waje nake furta Ustaz me ye haka? Ina matar taka?” “D’aya matar tawa tana gidansu Aysha, ga uwargidan anan.” Ya fa’da min cikin wata murya a kunnena. Da sauri na wani kalar Zillo na bar jikinsa ina kallo ya yi baya ya jingina da kujera idanunsa a lumshe yana sakin ajiyar zuciya… ni kuwa kallonsa kawai nake ina mamakin jin abinda ya ce da gaske an ‘d’aura mana aure shi? Kuma mu biyu da wata. Duk da na yi farin ciki amma kishi bai barni na bayyana farin cikin ba. Zuciyata na sama da k’asa na dinga kallonsa still idonsa a lumshe.. na furta “Wai da gaske aurena aka ‘d’aura ni da kai da wata kuma?” Idanunsa a lumshen ya ‘d’aga kai. A zafafe na ce “Tab’di! Ni Allah ban ce maka ina son mai mata ba…” “Aysha bana son surutu, ki tashi ki shirya mu je gidanku, Abba yana jiranki abokai na suna jira su ga matata za su koma garuruwansu. Ba lallai ku sake ha’duwa ba sai lokacin tariya.” Ya fa’da yana mik’o min wata leda mai kyan gaske. Ledar na bi da kallo ina amsa ya jawo ni jikinsa. Kissing ‘din lips ‘dina ya yi ka’dan yana jan karan hancina ya furta “Am sorry for this, na da’de ina jiran wannan ranar. Sai ga shi Allah ya bani ku ku biyu… “ Turo baki na na yi cikin matuk’ar jin kunya na sauka daga jikinsa. “Wa yace ki sauka? Kin san dai ba haramun ba ne ko?” “Ni dai bana so, ka je wajen waccan matar.” Na fa’da idona na zubar da hawaye. Murmushi ya yi yana furta “Don kuwa baki ga yarda ta yi kyau ba, ta yi kwalliya sai zabga wani irin k’amshi take mai sanya tunani a rai. Ke kuwa ko wankan bana jin yau kin yi, saboda kina
Cikin tashin hankalin kin yi rashin santalelen saurayi irina ko?” Turo baki na yi na shige ciki da sauri. Ina jin sautin murmushin Ustaz.
Sai da na murza key a ‘d’akin don naga kamar Ustaz yau ya cire kunyarsa gaba d’aya. Wankan na yi sosai har kamar fatata zata futa, don duk dole ina son nafi waccan matar kyau. Ina cikin zura rigar lace a jikina na ji muryarsa a bakin k’ofa. “Bu’de Aysha..” wani irin waro ido na yi na furta “Na bu’de na
Maka me?” “Idan ba zaki bu’de ba, answer your phone..” Sai sannan na kai idona kan wayar naga numberrsa da na yi saving da Ustazu na, tana ringing. Amsa wayar na yi. “Kada ki yi kwalliya, kada ki saka turare kuma don zaku gaisa da abokaina…” Ya furta yana kashe wayar. Ban saka turare ba, amma na yi kwalliya don haka kawai ba zan bari wata can ta fi ni kyau ba. Na fito tsaf da ni cikin laffayar da ta zauna das a jikina ta fitar da shape ‘dina sosai. Idon Ustaz a kaina yake kallona ya furta “Cab a hakan zaki fita?” Na ‘dan turo bakina “To ba kai ka kawo kayan ba?” Mik’ewa ya yi ya isa kusa da ni, yana jana jikinsa da sauri na fara turjewa ya rik’e ni sosai yana furta “Bana ce kada ki yi kwalliya ba, wa yace ki yi, tsaya na goge jambakin nan.” Cak na tsaya a zatona gogewar zai yi sai na ji bakinsa a saman leb’ena yana tsotsa a hankali. Da sauri na waro ido. Ya sake ni yana murmushi ya bushe min idon da iskar bakinsa. Yana furta “Gobe ma ki sake k’in bin umarnina, ki je ki sako Hijab, ba zaki fita da wannan abin ba, Ji k’irjinki ji yarda ta fitar da zahirin Suffar Aysha…” Ya fa’da yana shafa gefen Hips ‘dina. “Anya Aysha zan iya jira ki gama secondary ‘din nan, kamar yarda Abba ya buk’ata? Ba zan iya ba zan wahala sosai wallahi, duk da dai ina da wata matar, amma kuma zuciyar tana nan…” Ya fa’da yana ‘dage min gira ka’dan. Turo bakina na yi ina jin zuciya ta na shirin tafasa na furta “Ni ka daina min zancen matarka.” Yatsansa ya saka yana zagaye leb’ena da su, yana murmushi ya sake ba su sumbata sannan ya lumshe idonsa ya furta “I like those kissable lips, na da’de ina mafarkin wannan ranar.” Shiru na masa ina jin sauyawar yanayi tare da ni. Sakin ajiyar zuciya ya yi yana furta “Wannan karatun boko…. Shikkenan maza ki je ki saka Hijab Madam, ana jiran mu.” Na juya d’akin Anty Khadija. A drawernta na samo Hijab mai kyau da ya shiga da kayan na saka. Ina fitowa na tarar Ustaz har ya mik’e yana waya k’asa k’asa na ji yana furta “Ki jira na ce, zan zo yanzu ko Habibteey…” Wani irin duum na ji a raina. Ya mik’o min hannu yana furta “Zo Aysha ku gaisa da Habibteey…” Banza na masa idona na shirin zubo da hawaye na fice daga gidan da sauri. Sai ga shi ya biyo bayana na kulle k’ofar. Banda ina son zuwa gida cewa zan yi ba zan bi shi ba. Ya shiga mota ni ma na shiga fuskata a ha’de shima bai min magana ba ya ja zuwa gidan mu.
Sai da na ganni a k’ofar gida sannan hankalina ya dawo jikina na tuna da batun Mami ko ta amince da auren? Gaba na ya fa’di sanin cewa ba lallai ta amince ba tunda ko jiya da ta je gidna Ya Muhd ban ga alamar haka a tare da ita ba. Zan fita daga Motar ya ja hannuna ya rik’e cikin nasa yana kallona. “Idan baki saki fuska ba zan mayar da ke.” Na ha’diye tashin hankali na na furta “Ba wajenta zaka ba?” “Ina ruwanki, ki yi abinda yake gaban ki, and kada ki sake ina magana ki yi gaba hakan raini ne, kin ji ko? Idan baku gaisa kun saba ba sai yaushe zaku gaisa, idan na gama da ke, zan tafi wajenta da daddare kuma ki shirya zan zo na kai ki wajen su Mommy kafin su yagalgala nama na…” Yawu na ha’diye ina sauka daga motar bayan na sake nik’ab ‘din fuskata don haka kawai sai na ji ina jin kunyar ha’duwata da jama’ar gidanmu ban san kalar tsiyar da suka tanadar min ba.
Dariya Ustaz ya yi ganin yarda sam na kasa sake jiki na fita. Ya juya yana kallon cikin harabar gidanmu. Kafin ya furta ko na kira miki Muhammad ya shiga da ke?” Da sauri na ‘d’aga kaina. Don hakan zai fi kin sauk’i akan na shiga da kai na. Ina kallo ya dannna wayar hannunsa ya kira Ya.Muhd. Bai ko d’au lokaci ba, sai ga shi ya fito fuskarsa d’auke da murmushi yana kallo na. “Amarya..” Turo bakina na yi na furta “Ya.Muhd, bana so, shine baka gaya min ba sai da aka d’aura auren.” Murmushin ya sake yi ya ce “Ba gashi yanzu kin sani ba, gaya min are you happy or not?” Ya kama hannuna muka nufi cikin gidan. Ina ji Ustaz yana fa’din idan na gama yana jirana a sitroom.
Tsakargidan taf da mutane, ta cikin nik’ab ’dina na dinga ganinsu, y’an Uwan Umma, Y’an Uwan Abba da y’an Uwan Mami sai hira ake cikin annashuwa da farin ciki. Har sama Muhammad ya kai ni bai bari an ganni ba, ya shigar da ni parlorn Mami. Parlorn nata shiru ba kowa. Sai k’arar Tv. “Ki shiga Mamin tana ciki, ki san yarda kika yi kika kwantar mata da hankali, don tun safe ta k’i bari kowa ya ganta, ta yi fushi sosai don har kuka yau ta yi a gaban Abba, ta furta Kalmar da ta tsayawa kowa a rai, don an ga ita Allah bai bata haihuwa ba….Jikin kowa kam ya yi sanyi, don haka ki rarrasheta..” Ya Muhd ya fa’da yana saka yatsansa guda a idonsa ya ‘d’auke k’wallar da ta tarar masa a k’asan idon. Wani irin fa’duwar gaba na shiga, idona a waje cikin tashin hankali na furta “Ba da sanin Mami ba, aka ‘d’aura min aure?” Muhammad ya ‘d’aga kai “An yi kuskuren da kowa yake dana saninsa, don kam baa kyauta mata ba, shi kansa Abban zan iya cewa ya yi nadama, amma ba hak’urin da bai bata ba ta k’i saurararsa ta ce sai ya saketa tunda bata da wani amfani a wajensa…” Wannan karan sai dana dafe k’irjina jin abinda ya ce na zube a kan kujera ina mayar da ajiyar numfashi. Ina ji Yaya Muhammad ya fice yana sake jaddada min na aikata abinda ya ce ‘din.
Na kai mintuna biyar kafin na daure na isa d’akin nata cikin tashin hankali na mur’da k’ofar. Sai na jita a kulle, a hankali na fara nocking in kiran sunan Mamin cikin tashin hankali.
Tsawon lokaci kafin ta bu’de k’ofar, na ‘dago idona ina kallonta hawaye ne yake zuba a idon nata ya yi jajur, cikin tashin hankali na zube a jikinta, amma sai naga ta janye ni tana min wani kallo da ya kusa ‘d’auke min numfashi na…..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
Kin shirya Siyam lunch box ko duk wasu kayan yara na buk’ata musamman yanzu lokaci ne da za’a koma makaranta. To akwai tanadin da Tinysteps_ng ta yi muku na samun duka abinda kike so da ya danganci back to school akan farashi mai rahusa… abin buk’ata kawai garzaya da gudu ki shiga cikin group ‘din, ta hanyar danna link. Zaki ganki tsundum cikin companyn Tinysteps_ng…
Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group fouf updates on our unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more
https://chat.whatsapp.com/
https://www.arewabooks.com/chapter?id=66a2a58ee86f6001e809b915
Akwai page 15 a arewa, ku duba ku Karanta a can. Gobe ina biki ba zan samu posting ba. Na gode
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 15.
Kin shirya Siyam lunch box ko duk wasu kayan yara na buk’ata musamman yanzu lokaci ne da za’a koma makaranta. To akwai tanadin