Showing 30001 words to 33000 words out of 44853 words
da Tinysteps_ng ta yi muku na samun duka abinda kike so da ya danganci back to school akan farashi mai rahusa… abin buk’ata kawai garzaya da gudu ki shiga cikin group ‘din, ta hanyar danna link. Zaki ganki tsundum cikin companyn Tinysteps_ng…
Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group fouf updates on our unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more
https://chat.whatsapp.com/
★✍️
Idanunta zubar da hawaye kawai take, tana pointing d’ina da hannunta, bakinta na rawa so take ta furta furucin da yake kan harshenta sai dai da alama harshen nata ya kasa bata ha’din kai. Sai kawai na ji ta kamani ta min wata irin kyakykyawar runguma tana sakin kuka kamar zata mayar da ni cikinta. Zuciyata da ta ta duka a tare suke wani matsanancin bugu. Kukan kawai nake nima don na kasa jurewa. Ban san tsawon lokacin da muka ‘dauka a haka ba. Sai da Mami ta gaji sannan ta ‘dago ni tana share min hawayen ido na. Tana sakin wani guntun murmushi ta furta “Ina miki murna AYSHA, ina wa iyayenki Murna….” Da wani irin zafin nama na rufe mata baki ina girgiza kai. Muryata a shak’e alamar na ci kuka da yawa na furta “Kada kice haka Mami, Wallahi bani da wasu iyaye bayan ke, ke nake wa kallon Uwa tunda ke na bu’de ido na gani a matsayin uwata. Wannan auren nawa tabbas k’addara ce don Allah Mami ki yi hak’uri, ki daina nuna fushinki, kada mutane su yiwa abin wata fassara…” “Fassara?” Ta furta tana cije leb’en bakinta, sai kuma naga ta saki murmushi ta furta shikkenan na san k’addara ce Aysha na kuma yarda da ita, In sha Allah zan daure zuciyata, duk da na san ba zan tab’a iya kawar da damuwar da take zuciyar ba, amma zan yi hakan musamman don idon mutane da kika ce..” Da farin ciki na rungumeta ina sakin ajiyar zuciya. Ta ja ni jikinta ta bani kiss a gefen kumatu. Tana jan karan hancina ta furta “Yanzu AYSHA ke matar aure ce ko? Ustaz zai raba ni da ke da zarar kin gama secondary?” Sai kawai ta ciji leb’enta ta ja hannuna zuwa cikin d’akin. Tana furta “Cire Hijabin nan, abin wani banbarakwai amarya da hijab. Cire maza na gyara miki fuska mu fita a gaisa da mutane, idan da mai hoto a
Mana..”
Duk da ban manta da garga’din Ustaz ba haka na amince Mami ta zauna ta tsantsara min kwalliya. Don Mami gwanar kwalliya ce. Sai ga shi na zuba wani irin fitinannen kyau. Laffaya sabuwa dal ta ‘d’auko ta na’da min. Ta kuma saka min wasu irin turaruka masu mugun k’amshi. Zuwa lokacin naga kiran Ustaz yafi nawa a wayata. K’arshe da ya gaji sai ya turo min text. “AYSHA kina ina ne? Ki zo yanzu mun gama cin abinci tafiya za mu yi. Ban da makeup banda turare pls!l” k’irjina ne ya d’an buga ganin ya sake warning ‘dina a kan hakan, sai dai ban isa na bujirewa Mami ba. Tana murmushi ta ja ni jikin mudubi ta rungumoni muka d’au hoto da wayarta, mun yi masifar kyau sosai. Ta d’an ja hancina, tana furta “You look Gorgeous Ayshan Mami.” D’an murmushi na saki itama ta yafa nata mayafin mai kauri muka fita tsakar gida.
Mutane suna ganinmu aka taho wajenmu da sauri ana muna gu’da a kai. Mami murmushi kawai take tana amsa Allah ya sanya alherin da ake mata. Nan aka fara mata d’an biki ana fa’din Mami girma yazo an samu suriki. Ya Muhammad ne ya shigo yana fa’din Ina AYSHA take ne? Ke kizo in ji abokan ango. Na mik’e zuciyata na wani irin bugu na ja hannun Asma da wata k’awarmu muka nufi sitroom d’in. Kaina a k’asa kawai yake, ina jin ‘dan bikin da suke min, bayan amsa gaisuwar su Asma da suka yi. Sai jin hannun Ustaz na yi a jikina yana ja na d’akin su Aliyu da yake cikin sitroom d’in. Aka saka masa dariya gaba d’aya. Bai kula su ba sai da muka shiga cikin d’akin ya kullo k’ofar da k’arfi ya zuba min tsumammun idonsa. Lumshe idon na yi ina jin bugun zuciyata na tsananta don na san ni mai laifice a wajensa. Madadin na ji ya yi magana kawai jin bakinsa na yi saman nawa yana tsotse jambakin bakina kamar ya samu alawa. K’wace jikina nake son yi amma ya k’i bani dama don ya rungumeni tsam a jikinsa. A kunne yake ra’da min cikin wata irin murya “Rashin kunya ko? Da kunnen k’ashi, bana ce kada ki yi kwalliya ba kada ki saka jambaki, ki kuma fito da hijabi shine baki ji ba kika yi kunnen uwar shegu kika na’do wannan abin kika fito?” Ya fa’da yana zagaye hannunsa a shaffafen cikina zuwa saman k’irjina “Ji fa Aysha, ji nan wajen duk sun fito tsaf a cikin kayan, kowane banza ya kallesu kike so? Bayan mallaki na ne….” Tsaf na rufe idona, cikin matsananciyar kunya, kamar yarda na Ustaz ‘din ma suke a rufe, Murya na rawa na ce “Ustaz ka bari kai fa Malamin addini ne.” “Malamin addini baya soyayya? Baki san annabi ma ya yi soyayyar da ta fi wannan ba?” Ya fa’da min cikin wata irin murya yana shinshinar wuya na. “Turarenki Aysha yana jefa ni a wani yanayi ya sunan sa?” Kuka nake son na saka masa don duk wani yanayi nake ji a jikina. “Pls Ustaz ka bari!” “I can’t Aysha, na da’de ina jiran ranar da zan gan mu a haka, pls kice a gida kina so ki tare zaki yi karatun a gida….” Ya fa’da yana bu’de lumsassun idanunsa da suke dawo wata colour cikin nawa… “Your Love gonna make me crazy Aysha…” Ka’dan ya rage ban sume ba, a yanayin da ya yi maganar….
Kasa furta ko kalmar ‘a’ na yi, saboda matsananciyar k’aunarsa. Na Dai d’an janye jikina ina furta “Ustaz, mutane fa suna jiran mu.” ya min wani kallo kafin ya girgiza kai “Ba zaki ko ina ba, a haka zaki wajen maza? Wa’dannan halittun nawa ne ni ka’dai, Allah ni ka’dai ya mallakawa.” Daga haka ya fice da sauri yana jan k’ofa. Ban San ya suka yi ba, ya dai lek’o yana furta min “Wifey zan dawo around 7:30, ki shirya.” Na ‘d’aga kai na. Ina kallo ya fice wani haushi ya cunkushe min zuciya, na san ba mamaki wajen waccan zabiyar zai je… haka na ce a raina kafin na mik’e a kasalance na fice daga ‘dakin jin su Asma suna kira na.
Saman Mami na sake hawa da su, suna ta min iya shege iri iri saman ma ba kowa da alama Mamin ta sauka. Na zauna akan kujera ina kallon Asma da bakinta ya k’i rufuwa. Ta furta “Wallahi lamarinku da Ustaz, AYSHA abin sha’awa, ta k’wayar idonsa ake gane zallar k’aunar da yake miki.” Murmushi kawai na saki ina gyara zama na. Sa’ada ma murmushin ta yi ta furta “Ke mai sa’a ce AYSHA, irin sa’ar da kowace mace take son ta samu. Allah ya baku zaman lafiya amma na san yau fa kin tarwatsa farin cikin y’an mata da yawa, don ko a Islamiyya Ustaz Ahmad ya tafi da zuciyar y’an mata da yawa…” Haka dai muka yi ta hirarmu. Har nake sanar da su zamu fita da Ustaz da daddare Amma ina tsoron na gayawa Mami. D’an waro ido Asma ta yi sai kuma ta tuntsire da dariya “Mhmnm Fa Aysha, ba wai na ji ance ba yanzu zaki tare ba, kada Ustaz…” Ta fa’da tana rufe bakinta tana dariya… Na yi tsaki ina dukanta a cinya na furta “Ni y’ar yarinyata da ni, me Ustaz zai ‘d’auka a jikina…” “Abubuwa da yawa mana, ai shi ya ga mai ya gani ya nace miki, Allah dai ya kai mu next year mu sha biki…” Sa’da itama ta fa’da tana dariyar… shigowar Mami ce ta saka muka ja baki muka yi shiru. Ta ‘dan kallemu tana murmushi ta furta “Aysha ki sauka k’asa, ku gaisa da mutane…” na mik’e su Asma suka bi ni suka saka ni a tsakiya muka sauka. Babban parlorn da ya kasance na Abba nan muka fara shiga, inda y’an uwan Abba suke. Da fara’a duk walwala suke amsa gaisuwata. Umma Dijah ta kasa shiru tana furta “Ai kin dace Aishatu, Ubangiji Allah ya sanya albarka a auren ya nuna mana ranar tariya.” Kaina a k’asa na kasa amsa ameen ‘din sai wasa nake da zoben hannuna. Daga nan muka shiga parlorn Umma. Zo kiga farin ciki yarda suka rungumeni suna ihun ga amarya ga amarya. Murmushi kawai nake saki. Inna laddu kuwa k’anwar Babar Umma cak ta saka ni a cinyarta tana furta “Ma sha Allah tubarakalla dole Ahmadu ya tubure sai an d’aura aure. Haka kika sake zuba kyau.” Na ‘dan yi dariya kawai ina kallon Umma na, da ko kallona ba tayi ba sai dai murmushi sam ya kasa barin fuskarta. Na da’de anan d’in kafin na zame jiki na koma sama, inda y’an uwan Mami suka cika wajen. Suma da farin cikin suka tare ni. Mami kuma
Ta ware a cikinsu sai farin ciki take. Na zauna daf da ita na kwanta a jikinta kaina a saman cinyarta na lumshe ido. Barci mai nauyin gaske ya ‘daukeni, na san barcin da ban yi bane a daren ranar yake d’aukata.
Mami bata tashe ni ba sai daf da la’asar na ‘dan ware idona. Ina kallon wajen, ba kowa sai Mamin da k’awayenta guda biyu. Duk suka zubo min idon da yasa har na ji kunya na mik’e na bar wajen da sauri na shige ‘dakina.
Sallah na yi ina idar da sallahr na sauka k’asa wajen Umma. Har lokacin jira nake na ji Ustaz ya kira ni amma bai kira ba. Kawai sai zuciyata ta dinga bani yana can wajen amaryarsa. Don takaici har wata k’walla ce ta so zubo min. Na matse ha’de da tura k’ofata parlorn Umma. Ba kowa a parlorn da alama duk bak’in sun tafi. Sai Umma ita ka’dai da k’anwarta suka ‘dago suna kallo na. Umma ta d’auke kanta. Sai Anty Zee ce ta ce “Shigo mana Aysha kin ci abinci?” Na ‘d’aga kai na “Na ci Anty.” Ta yi murmushi tana fa’din amaryar da ba lalle, wannan aure naki Aysha Ai shine bagatatan. Yaushe ya ce zaki ki gaida iyayensa?” Wani farin ciki ya shige ni don abinda nake son na ce kenan, amma ba kasa gayawa Mami balle Umma. Na gyara zamana ina furta “Yau ya ce Anty..” Ta saki murmushi tana fa’din “Kin ji ko Yaya, ai na san wallahi kawai zan ce ne, ace kawai mutum ya auri mace sai ya zuba mata ido alhali sabon shiga ne a aure a ce wani sai ta k’arasa karatu, karatun me Allah na tuba a gidanta ba zata yi karatun ba, wallahi kada ki bi ta wani karatu ki tattara y’a ki mik’a d’akin Mijinta….” Umma ta waro idonta tana furta “Rufa ni ki saya, ni meye nawa da za’ace ni zan saka a kaita d’akin Miji, ki bar uwarta y’ar a lallab’a da yaya ma aka samu aka shawo kanta a yau d’in. Shekara kamar yau ne, Idan Allah ya kai mu.” Anty ta yi d’an tsaki tana kallon Umman ta ce “Allah ya kai mun, idan da rabon an yi taron suna ne ba taron biki ba sai mu ce san barka…” Da sauri na mik’e na fice daga ‘dakin cikin matsananciyar kunya. Na koma saman Mami. Bak’in sun tafi sai ita ka’dai zaune ta zuba hannunta a k’unci. Har na zauna daf da ita ba ta sani ba sai da ba dafa ta sannan ta juyo a razane tana d’an kallo na. Ta furta “Aysha ce?” Cike da tausayinta na ce “Mami kin ci abinci?” Ta ‘d’aga min kai tana d’an murmushi. Na yi shiru ina wasa da yatsuna na furta “Mami Ustaz ya rok’i alfarmar yana son na je gidan su yau after magriba….” Mami ta ‘dago tana kallona, idanunta suka bayyana tashin hankalin da zuciyarta take ciki. Ta gyara zamanta tana sakin ajiyar zuciya sai kuma ta kama hannuna murya a raunane ta ce “Ba zan hanaki bin sa ba AYSHA, don yanzu duk duniya ba wanda yake da iko da ke sama da shi. Sai dai zan rok’i alfarmar ki tsare jikinki, don maza mayaudara ne idan dama jikin naki yake so da zarar ya kusanceki zai iya sakin ki tun kafin ki tare…. Ki min alk’awarin ba zaki bari Ustaz ya kusanceki ba..” Na d’aga kai na, ina ji har a zuciyata na amince da abinda Mamin ta ce. Ta sakar min murmushi ta furta sai ki shirya da wuri kada yazo yana jiranki amma banda saka turare… na d’aga kai.
Da magriba ina idar da sallah Mami ta shigo d’akin hannunta d’auke da wata leda. Ta zauna a gefen gado. Tana bu’de ledar wata doguwar Riga ce mai masifar kyau kalar bak’a da stone golden ta yi matuk’ar kyau. “Ki saka wannan, sai ki je gidan nasu, idan kin je kuma bana son rawar kai ki nuna musu ke mai tarbiyyace.” Na amsa ina godiya. Bata amsa ba ta wuce ta fita.
Da wata irin murna na zura rigar a jikina na shafa powder sama sama, sai na yi rolling. Ba k’aramin kyau na yi ba ni da kai na na sani. Sanda na fita parlor sai naga Mami bata nan. Na san tana k’asa na sauka k’asan don Ustaz ya isheni da kiran waya.
Yarda na zata kuwa suna tsaye a kitchen ita da Umma. Suka juyo suna kallo na. Anty Small ta furta “Ma sha Allah, Allah ya yi halitta.” Mami ta dafa ni tana furta A dawo lafiya, and take care AYSHA. Ga wata leda nan ki kaiwa Inlaw d’inki abinda ke ciki…” Na d’au ledar ina murmushi na fita k’ofar gida don na san Abba yana masallachi sai dai su Umma su gaya masa.
Cikin takun nutsuwa na isa bakin motar na saka hannu na bu’de k’ofar gaban motar. Gaba na ya yi wani irin mugun fa’duwa ganin Habibteeyn Ustaz a gaban motar, ta sha kwalliya ta yi masifar kyau tana zabga k’amshi. Murmushi ta ‘dan saki ni kuwa fuskata a tsuke na juya da nufin komawa gidanmu don wallahi in dai da wannan za’a ba zan je ba…. Kai bana jin ma zan iya kishi da zanka’ded’iyar mace irin wannan habibteeyn ta Ustaz ba. Ta ko ina ta fi ni….
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 16.
16…
AYSHA! Na ji Ustaz ya fa’da cikin muryarsa da take bayyana ginshira. Na ja na tsaya sai dai ban jiyo ba, Saboda bana son na jiyo d’in naga Habibteeyn Ustaz. Rufe k’ofar Motar da aka yi ya tabbatar min da ya zo wajen. A daf da ni ya tsaya. Kafin na juyo na ji hannunsa a cikin nawa hannun. Da kansa ya juyo da ni yana k’ok’arin lalubar idanuna ni kuwa na ja na runtse idon. “Wuce mu tafi.” Ya ce cikin wani cool voice da ta so ta saka raunin da yake zuciyata ya bayyana… “Ni ba zan shiga ba..” “Me yasa?” Ya fa’da bayan jin abinda na ce. Na d’an turo bakina ina furta “Ka je kawai, ka je ka kaita ni na hak’ura..” wani murmushi ya saki yana furta “Tafiya da ita ne ba kya so?” Na d’aga kai na. “Me yasa zaka zo da ita?” Na fa’da hawaye suna son zubo min. Ustaz murmushi kawai ya saki ya ce “Maza ki yi kuka a gabanta ta raina ki.” Na matse hawayen ina kallon cikin idonsa da suke lumshewa kamar me… “Ku je zan saka Ya Aliyu ya kai ni a motar Abba..” cute smile d’in ya sake yi yana jan hannuna har kamar zan fa’da jikinsa. Ya furta “Yanzu dai ba kya son Third Party a
Cikin tafiyar mu ko?” Da sauri na d’aga kai. Sai naga ya saki hannuna yana murza goshinsa a hankali. Kallon k’asan ido yake min kafin ya jefa min tambayar da ta so saka ni zubewa a k’asa tsabar yarda jikina ke rawa. Cewa ya yi “Kina so mu ka’daice, in har kika yarda muka tafi mu ka’dai zaki min deep kiss a cikin motar…” ya fa’da yana murza hannuna. Da sauri na janye hannun ina furta “Mu je kawai, amma ta koma baya tunda nice Uwargida.” “Done wifey ya furta yana dariya k’asa-k’asa. “Hannunki AYSHA so soft, har bana son na daina tab’awa…” Da sauri na janye hannun ina dubawa naga ko Maigadi ya ji, sai na ga ma baya wajen. Muka isa bakin motar hannuna cikin nasa yana ta murzawa. Ja na yi na tsaya ina jin zuciyata kamar ta buga, ganin yarda Ustaz ya durk’usa daf da ita yana gaya mata magana. Sai naga ta ‘dan ha’de rai ta fito tana min wani kallon banza ta shiga bayan motar. Murmushi na saki ina jin duk wani bak’in cikina ya yaye. Na shiga gaban Motar cikin jin haushin yarda da ta zauna a motar…
“Baku gaisa ba?” Muka ji muryar Ustza daga sama bayan
Mun fara tafiya. Shiru kowa ya yi har sai da ya sake furta “Ba kwa ji ne ina magana…” Sannan ta furta “Ina yini?” A ciki na amsa don sai naga kamar ta fini sauk’in kishi.
Wani irin wawakeken gate muka shiga, inda muka tarar da makeken fili. Ustaz ya yi Parkin ina kallo ta fice cikin takun isa da son ta nuna min ita ta san gidan tunda cousin ‘d’insa ce. Na d’an ha’de rai ina cije leb’ena idona suka kawo ruwa. Ustaz ya sunkuya yana kallona ka’dan, tunda mu ba mu fita daga cikin motar ba. Ji na yi ya kaiwa bakina sumbata ya kuma lashi d’an guntun hawayen da ya zubo min. “Kukan menene?” Ya furta a cikin kunnuwa na. Da sauri na rintse idon, don na lura Ustaz so yake ya kashe ni da salonsa. “Mu je mana Zauj, ko sai na d’aukeki..”