Showing 3001 words to 6000 words out of 44853 words

Chapter 2 - NAGA_RAYUWA_BOOK_1

Unknown   

02 Dec 2025

96

ya ce Aysha ta..” Duk da haka ban yi nawar d’agowa ba na zuba masa ido ina kallon yarda yake kallona fuskarsa a ha’de ya mik’a min takardar hannunsa tabbas yanayinsa ya firgita ni…


“Ungo wannan.” Ya fa’da da wata irin shak’akkiyar murya, yana d’auke kallonsa daga gani na. Leda ce ya mik’a min. Daga haka ya juya ya fice a zatona zuwa zai yi shirya ya dawo. Duk da zuciyarta na gaya min akwai matsala ba haka Ustazuna ya kamata ya tare ni ba ni da nayi zaton runguma da kyakykyawan kiss da na da’de ina mafarki…. Ko dai na masa wani laifi ne da ban sani ba?


Ajiyar zuciya na saki ina jan ledar da sauri. K’amshin kazar Yahuza suya ya dake ni da Ice cream masu sanyi. Jikina har rawa yake don idan ban manta ba rabona da abinci tun safiyar ranar don haka kawai sai na samu kai na da fara cin kazar na sha ice cream d’in. Na saka hannu na jawo leda zan d’au lemo idona ya kai kan wata farar enveloped. A zatona mantawa ya yi don haka ban ma bu’de ba na ajiye a gefe ina jan kwalin exotic na fara d’addaka shi a cikina. Na tattare kayan idona ya sake sauka kan enveloped da a bayansa na ga sunana b’aro b’aro. AYSHA IMAM KHALIL… murmushi na saki ina tunanin ko wata kyauta Ustaz d’in ya bani don haka na jawo da sauri na farke enveloped d’in da yake ta zuba k’amshin turarensa.


𝒜𝓈𝓈𝒶𝓁𝒶𝓂𝓊 𝒶𝓁𝒶𝒾𝓀𝓊𝓂.... 𝒩𝒾 𝒜𝒽𝓂𝒶𝒹 𝒮𝓊𝓁𝒶𝒾𝓂𝒶𝓃 𝒮𝒶ℯℯ𝒹 𝓃𝒶 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝓂𝒶𝓉𝒶𝓉𝒶 𝒜𝓎𝓈𝒽𝒶 ℐ𝓂𝒶𝓂 𝒦𝒽𝒶𝓁𝒾𝓁 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝒹𝒶𝓎𝒶 𝒷𝒶𝓉𝒶 𝒹𝒶 𝒾𝒹𝒹𝒶𝓉𝒶 𝒾𝒹𝒶𝓃 𝓉𝒶 𝓈𝒶𝓂𝓊 𝓂𝒾𝒿𝒾 𝓉𝒶 𝓎𝒾 𝒶𝓊𝓇ℯ......


Kasa k’arasawa na yi saboda yarda na ji numfashi na yana neman d’aukewa na dinga ware ido ina jin zuciyata na wani irin bugu..


Tabbas NAGA RAYUWA Me yake shirin faruwa da ni ne? Saki a daren aurena daren da muke d’oki da zakwa’din zuwansa ni da mijina ya da’de yana gaya min yana jiran ranar da zai rungumeni dtazo saboda kiyeye dokar Ubangiji. Me na yiwa Ustazuna ya sake ni? Na shiga uku!! Haka na furta a zuciyata..



To fa! ko me AYSHA ta yiwa Ustaz Ahmad ya zabga mata saki a daren aurenta? Duka yana cikin littafin NAGA RAYUWA da zai dinga zuwa muku daga Alk’alamin…..



𝒥𝒾𝓀𝒶𝓇 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎


𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION




Arewabooks @nazeefah

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 2.



★…..✍🏽



Kuka ne sosai ya kufce min, irin kukan nan da kake jin d’acinsa har k’asan ranka. Kuka mai sauti da Amon muryar karaya a cikinsa. Me Na masa? Shine tambayar da nake wa kaina na kuma kasa lalubo amsar. Abinda zuciyata take gaya min nake k’aryatawa ko nak’i ko na so dole ne na gasagata zuciyar tawa dole Butulcin d’a namiji ne ya biyo ta kai na. Ko kuma ya yi haka ne don ya gwada mizanin soyayyarsa a zuciyata. Amma ya rasa ta hanyar da zai gwada sai ta kalmar saki? Kai abinda kamar wuya Ustaz da wayonsa ba zai yi wasa da saki ba Halak d’in da ya san Allah baya so, kuma idan aka aikata shi ar’ashi tana girgiza. Dole ba don na so ba na amince da shawarar da zuciyata take ba ni, na danganawa sashensa na je na tambayeshi abinda ke faruwa…

Tsam na mik’e na shiga laliben sashennasa, kasancewata bak’uwa a gidan bai saka na sha wahalar gane k’ofar sashen nasa ba. Daga can corridor tsakanin k’ofar da zata kai ka nawa sashen. A hankali na tura k’ofar na shiga. Shiru babban parlorn nasa baka jin k’arar komai sai na A.c da take ta aiki ba ji ba gani. Fitulun wajen ma a kashe suke. Karatun k’ur’ani ne kawai yake tashi a parlourn cikin k’ira’ar shureim. Na gama zagaye parlorn da idona ban gan shi ba, don haka na isa k’ofa guda da take parlorn da na tabbatar nan ne d’akin nasa.


Yana zaune a gefen gadon daga k’asa saman sallaya ya kifa kansa a jikin gadon. Jin motsina ya saka shi d’aga kai. Wata irin fa’duwar gaba ce ta same ni ganin yarda idanunsa suka ka’da suka yi jawur kamar gaurashi. Idan ba idanu na ne suka min gizo ba sai naga kamar hawaye ne a kwance a k’asan idanun. Mayar da idonsa ya yi ya lumshe bai sake kallona ba alamu sun nuna baya son gani na.

Zuciyata a jagule tana wani irin bugu da k’arfin gaske na k’arasa wajensa. Zama na yi a gefen gadon murya cike da rauni na furta “Ustazuna, wata takarda na gani a cikin kayan da ka kawo, zuciyata ta kasa amincewa hannunka ne ya rubuta ta. Ban kuma fahimceka ba.”

Shiru kamar ba zai amsa ba, idanun dai still a lumshe daga inda nake ina ganin yarda k’irjinsa yake bugu. “Ustaz, magana fa nake.” “Taki ce.” Ya fa’da muryarsa a shak’e. Ido na waro ina furta “Saki Ustaz!” Ya bu’de idon nasa ya nutsasu cikin nawa, a hankali ya d’aga lab’b’ansa kamar baya so ya furta “K’warai kuwa AYSHA, don haka ki tabbata kin fice kin daga gida k’arfe bakwai na safe….”


Ina daga zaunen na dinga jin wani irin jiri yana d’ibana. “Ko zan san dalili?” Wannan karan madadin amsa min mik’ewa ya yi yana zabga tsaki ya furta “Ban sani ba…” Shiru na yi na lumshe idona ina hak’ilo da yak’i da b’acin ran da yake son dannen numfashi. “Tashi ki fita zan rufe k’ofata..” Ya furta yana nuna min k’ofa.. Ya fa’da yana juya min baya… Jikina a salub’e na mik’e ina jin kamar k’afarta wa ba Zata iya d’aukata ba saboda rawar da jikina yake yi na zallar tashin hankali. Da k’yar na ja jiki na isa bak’in k’ofar daidai lokacin da na jiyo ina kallon Ustaz ina cije leb’ena shima kallon nawa yake hawaye ba zuba daga idonsa. Na ja k’ofar da k’arfin gaske na fice daga d’akin.


Zuciyata har Tafasa take saboda tsananin b’acin rai. Na zauna a gefen gadona ina mayar da numfashi tabbas Uztaz ya cuceni a shekaruna sha takwas kacal ya mayar da ni k’aramar bazawara? Shin halaccin da zai yiwa Iyayena kenan? Tabbas ya amsa sunansa Butulu? Yanzu me Zan je na ce a gidan mu? Ya rasa irin sakin da zai yi min sai irin wannan na tozarci da wulak’anci saki a ranar aurenka daren amarcinka? Yaya mutane za su yiwa abin fassara? Dole ne a jefa min ayar tambaya musamman kowa da ya san Ustaz ya san Babban Malami na da ake watsa tafseer d’insa a gidajen sunna na t.v. Babban Malami ne da gwamnatin k’asa baki d’aya take ji da shi duk da dai ba wani shekaru ne da shi ba ba zai wuce shekaru 32 ba.


Toilet na shiga bayan da zuciyata ta tabbatar min ba ni da wanda zan fuskanta a wannan gab’ar sai Ubangiji. Don haka na yi alwala na fito na tada sallah akan daddumar da Abba ya bani d’azu da safe ita da Alk’ur’ani da Riga da Hijab na sallah farare tas har da carbi da wani turare mai k’amshin gaske, yana furta “AYSHA, kin ga wa’dannan sune garkuwarki a gidan miji idan kika rik’esu kin samu makamin k’are dangi.” Ina sallahr ina hawaye na kaiwa Allah kuka na, na bayyana masa rauni na na kuma rok’eshi ya shige min gaba a dukkan lamari na.”


Ban tashi daga sallaya ba sai k’arfe uku da naji kaina ya fara ciwo abin mamaki sai na ji na samu k’arfi da nutsuwar zuciya. Na ji komai ya faru gareni daga Allah yake duk da tabbas Ustaz ya cuceni. Abu guda nafi buk’ata a yanzu na ji dalilin sakin da ya yi min, sai dai na yi alk’awarin ni da kai na ba zan sake tambayarsa ba don ko don ganinsa bana yi.



Barci ne sosai ya d’auke ni, kasancewar garin sanyi ne dare yana tsawaita don haka sallar asuba sa daf da k’arfe shidda ake yi, shi yasa na samu barci sosai duk da ba wai zance na yi isashshe ba ne. Ina sallame sallahr ko kayan sallar ban cire ba na fice da su da sauri a jikina.


Shiru layin amma a haka na dinga tattaki har na je bakin titi. Allah kuma ya taimakeni na samu adaidaita sahu. “Shara’da phase 2 kawai nace masa.



Har k’ofar gidanmu ya ajiye ni ta hanyar kwatance da na masa.

Duk da a tsorace nake da ganin Abbana hakan bai hana ni shiga gidan da k’warin gwiwata ba. Y’an biki ko watsewa ba su yi ba, don wasu daga garuruwa daban daban suka zo. Sai dai gidan shiru da alama kowa gajiyar biki ta saka ana sallah an kwanta sai wa’danda suke aiki a bayan gidan ta can na dinga jin d’an hayaniya da sautin kwanuka na tashi.


Jama’ar da suke kwance a
Parlor wa’danda duk k’annen Mami na ne da na Umma na suka dinga bi na da kallon mamaki baki a sake. Anty Sharifa ta ce “Ke AYSHA lafiya?” Mami da fitowarta daga d’akinta kenan itama hangame bakin ta yi tana ware ido ta furta “Ni Fa’dima me Zan gani haka? Ke Aysha Uban me ya fito da ke da sassafe haka?” Ta fa’da tana jan hannuna hankali a tashe ta furta “Ai dama sai da na gayawa Abbanku kin yi k’ank’anta da aure, shekara sha bakwai don ko sha takwas d’in baki cika ba, yanzu haka wani bak’on al’amari kika gani da yafi k’arfinki yasa kika gudo?” Anty Sharifa k’anwar Umma ta ce “Ah haba! Sai kace ba y’ar yanzu ba, ai duk da take k’anwar Maza na san ta san me aure ya k’unsa ko da ta hanyar k’awaye da karance karancen littafine…” Mami ta d’an harareta “Me AYSHA ta sani? Karatun littafin take ita? Ko k’awayen arziki AYSHA bata da su balle su sanar da ita aure da abinda ya k’unsa…” Ta fa’da tana jan hannuna muka shige Uwar d’akinta.


Zaunar da ni ta yi a bakin gado, bayan ta koma ta rufe d’akin da key tana furta “Bana son saka ido da munafunci yanzu duk ido zai dawo kan ki, kema kin yi wauta Aysha. Me ya kai ki fitowa don kawai Mijinki ya kusanceki Ai shine auren muma duk haka ake mana da haka kuma kowa yake sabawa… kowace macen aure da kika gani haka ne yake faruwa da ita koda yaushe, don haka tun kafin sauran mutane da Ubanki su ji ki tashi maza naje na mayar da ke, bana son na ji komai wannan sirrinki ne ke da Mijinki. Maza tashi mu tafi kafin mutane su fara miki kallon mara wayo mai gudun
Miji.”

Hawaye ne suka fara zuba min, ganin ita Mami na inda take hange daban da abinda ya kawo ni gidan. Na turo bakina ina furta “Ni fa ba wannan bane, ko hannu bai rik’e min ba fa.”

Mami ta d’an bu’de idonta ta furta “To menene idan ba wannan ba?” “Ya sake ni…” Wani irin ja da baya Mami ta yi idonta a waje tana kallona baki a bu’de ta shiga shock sosai cikin wani irin yanayi ta furta “What? Ya sake ki Aysha? Shi Ahmad d’in ne ya sake ki? A kwana guda da kika yi a gidansa to Uban me kika masa?” Hawaye ne suka fara ambaliya a fuskata na gayawa Mami duk abinda ya faru ban b’oye mata komai ba. Dariya Mami ta yi tana furta “Sharrin D’a Namiji! Ga abinda nake gudu ya zo. Sai ki tashi mu je wajen Abbanki na bashi tukuicin alheri da Ahmad ya kawo masa, ya mayar masa da y’a k’aramar bazawara Ahmad dai mai nagartattun halayen da Ubanki yake faman b’ab’atu akai.” Ido na waro waje ganin tana ja hannuna “Tashi mu je mana.” Na ja hannun ina girgiza kai “Mami, ba zan iya zuwa wajen Abba ba, Allah ina tsoro, ban san yarda zai d’au lamarin ba.” Wani kallo ta min cikin b’acin rai ta furta “Tashi na ce miki mu je ko? Iyakacinsa dai dake fa’da, tunda ba zai iya zare miki ranki ba.” Ta fa’da a fusace ta kuma fincikeni muka fita wajen.


Abin haushi Jama’a an fito gaba d’aya kowa sai baza ido yake ana kallon mu. Kallo guda Mami ta musu suka dinga bajewa suna ba mu hanya. Ban yi mamaki ba don ni da kai na na san an samu topic.



Abba na zaune yana lazimin safiya. Umma ce a gefensa tana ha’da masa coffee da ya saba sha duk safiya. Da alama shi bai san abinda ya faru ba. Balle Umma da tun jiyan bata fita daga sashensa ba.


A razane duk suka zuba mana idonsu musamman Umma da har Cokalin hannunta yake fa’duwa. “FATIMA lafiya kuwa? Naga Aysha da sassafe.” Umma ta fa’da tashin hankalinta na sake bayyana a saman fuskarta.

Zama Mami ta yi a gefen Kujerar da yake kusa da Abba, ta saka ni a gefenta ta furta “Lafiyar kenan Umma, sai dai d’an gaban goshin naku ya muku Aiken tukuicin sakamakon alherin da kuka masa…”

Abba da yake laziminsa ya d’ago ya d’an zubawa Mami ido don ya san halin kayarsa sarai danger ce wutar baya. Umma kuwa cup d’in ta ajiye tana sake furta “Me ya faru to? amma fa Mammin Aysha ya kamata ki yiwa y’ar taki fa’da ta san fa ta girma, aure kuma ba wasan yara ba ne. Idan ban da shashashanci menene na dako wannan Uban sammakon, koma menene ba ga waya ba me yasa ba zata sanar miki ba? Sai ta d’ebo jiki ta taho ta saka y’an biki su tafi da ita a bakin duniya tunda ko gama watsewa ba su yi ba. Aa sam wannan wauta ce da shirme.” Mami wani kallo ta mata sai kuma ta cije baki.

“Kamawa ta yi, ta dako uban sammakon babu gaira ba dalili ba abinda zai sakata fitowa daga gidan Mijin da aka kai ta jiya.” Mami ta fa’da tana hura hanci da jijjiga k’afa. Umma dai shiru ta yi don ba mamaki ta lura idan ta cigaba da magana tata ce zata yi zafi.


Abbana yana jin su bai yi magana ba ya cigaba da laziminsa. Sai da ya idar sannan ya ‘d’au coffee d’insa ya shanye ya zuba min kallon da na kusan jin kayan cikina suna shirin fitowa. “Ke wace irin shashasha ce Aysha? Daga kai ki gidan Miji jiya yau ki fito? Kin d’auka auren wasa ne? Me ya fito da ke?”

Madadin amsa masa jiki na ne ya dinga rawa kamar yarda zuciyata take bugawa. “Ba magana nake miki ba?” Ya sake fa’da da Tsawar gaske, hakan da yasa har ban san sanda na rik’e Mami da kyau ba ina makyarkyata “A’a Alhaji, kada ka sake hargitsata Ai ba laifinta ba ne fitowar dole ne ta fito tunda ya saketa…..” Gaba d’aya bakinsu a ha’de suka furta “Saki Fatima?” Ta jijjiga kai tana murmushi ha’de da furta “Sakamakon halaccin da kuka masa ne, duk duniya kuna ganin ba wanda ya cancanta kamar Ustaz Ahmad. Kullum zancenku nagartaccen mutum ne mai ilimin addini da ya shahara a duniyar Malamai. Yau ga ilimin nasa nan ya fara nuna muku….” D’akin tsit ya yi Abba jikinsa har rawa yake. Umma kuwa zama ta yi jab’ar a k’asa ta rik’e kanta kawai jikinta na rawa….



𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR


NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎


𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION




Arewabooks @nazeefah

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 4..



Da mamaki Umma take kallonta su Yaya Muhammad suma suka zuba mata ido. Ya Usman da ya kasa shiru ya ce “Au ke kuma auren ne ba kya son ta yi? Shi yasa zata ke k’unshe fuskarta, amma kamar wannan ba dabara ba ce..” Harara ta watsa masa tana furta “To kanari Uban surutu, ni na ce maka bana son ta yi aure? Auren ne dai ba yanzu zata yi shi ba sai ta yi dogon karatun da na tabbatar zata iya k’watar y’ancin kanta a
Wajen namiji sannan zan amince ta yi aure, haka kawai ba za’a aurar da ita da duhun kai ba shikkenan ta zama sai kace baiwa wajen namiji…” Cikin mamaki suka zuba mata ido, Umma kanta ta yi mamakin furucin Mamin, sai dai data tuna Mamin gidansu gangariyar y’an boko ne sai bata yi mamaki ba ta saki ajiyar zuciya kawai tana furta “Allah ya taimaka, ya nuna mana lokacin…” Yaya Muhammad gyara zama ya yi yana tab’e baki ya furta “Amma dai wannan kamar ba shawara ba ce mai b’illewa, Saboda kowa yanzu burinsa a ce y’arsa ta yi aure sai ta yi karatun a nata gidan Mijin….” “Sai ka bari sai ka haifi taka y’ar Muhammad ba wannan ba…” ta fa’da a zafafe tana nuna ni. Ta ja hannuna muka wuce samanta.
Tana banbamin fa’da har da rantsuwar nan gaba idan Muhammad bai yi wasa ba sai ta mare shi.


A kashegarin ranar kuwa bayan na yi wanka Mami ta tsantsara min kwalliya cikin shigar kayan hausawa da suka min matuk’ar kyau. Murna na dinga yi don kam dama ina son su Mamin ce bata ba ni damar sakawa ba.


Sanda na fita tsakargida idanun masu aiki duk a kaina suke, sunan ta dariya ganin kwalliyar da aka min. Har Iya ta kasa shiru ta ce “Lallai Aishatun Mami ta girma… Ma sha Allah a yi shekaru irin na dabino.”


Abba da yake zaune daga can gefe shi da su Yaya Muhd, baki sake ya dinga kallona yana furta “Inye Aishatun ba, irin wannan
Kwalliya haka? Waye ya siyo
Miki kayan hausawa…” ina dariya na zauna daf da shi an furta “‘Mami na ce, ita ta siyo min su da yawa ta ce na daina saka wa’dancan kayan yahudun.” Jan hancina Abba ya yi ya ce “Ai ke ce Yahudun.” Sannan ya juya yana kallon su Ya. Muhd ya furta “Kun ga abinda na gaya muku ko? Na gaya muku kada ku tada hankalinku a kan yarinyar nan Fatima ba zata yi sanadin gurb’acewar tarbiyyarta ba..Fateema mace ce data san abinda take yi.” Shiru su ka yi suna cigaba da shan kununsu Ya Ali ne ya furta “Ba shakka, to Allah yasa dai ba da wata manu…” wani kallo naga Umma ta masa sai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login