Showing 42001 words to 44853 words out of 44853 words
Na yi wani irin fitinannen kyau da kowa ya gani sai ya tanka.
Ranar da za’a kamu, sanda aka min kwalliya wallahi idan ba fa’da aka yi ba zata zaka yi India ce, Saboda fitinannen kyan da na yi a cikin Indian dress d’in da aka min complete kwalliyarsu. Jikina a rufe yake ruf. Duk da fuskata da walwala sai dai sab’anin zuciyata da take cike da takaicin Ustaz na rashin kulawa da ya kamata ya bani, musamman a irin wannan lokacin da amarya da ango suke buk’atar zuwansa.
Mai kwalliya na gama min Mami ta shigo wajen. Wani irin bu’de baki ta yi ta furta “Wow! Ya subhanallah Ayshata haka kika dawo? Fatabarakallahu Ahsanul
Khaleek’in, Tabbas Allah ya yi halitta…” murmushi kawai na saki ina kallon yarda Mamin ta rungume ni a jikinta ana d’aukarmu hotuna ko ta ina. Na so ace Ustaz ne a madadinta.
“Sai ki kirashi ku tafi.” Mami ta furta fuskarta a d’an tsuke kamar ba ita ta gama dariya yanzu ba. Wayata na d’auka na fara kiransa ta dinga ringing bai d’aga ba kamar yarda ya saba a kwanakin nan. A fusace na ji ya yi furucin “Wai menene?” Mamaki ya kamani jin tambayar rainin hankalin da ya yi min, na dinga kallon wayar ina son na tabbatar da gaske daga shine. “Na gama shiryawa” na furta a hankali. “Ki ce Mami ta kai ki.” Ya furta yana katse wayar. Ido na d’an ware kafin na sake danna wayar na tura masa text “Amma dai ka san kai ya kamata ka kai ni ko?” Ban zaci zai dawo min da amsa ba, sai naga ya turo min da “To ki jira…” na d’ago ina kallon Mami da suke magana da mai kwalliya ta kalleni itama ta ce “Ya taho?” Na d’aga kaina kawai ina furta “Eeh ga shi nan.”
Tun a mota nake kallon yanayin Ustaz d’ina tamkar ba shi ba, fuskarsa murtuk babu annuri ko ka’dan a cikinta, na zata zai yaba kwalliya ta sai dai ko kallona bai yi ba. Ya ja mota muka tafi bayan Asma ta shiga. Hankali ne tashe nake kallonsa na ce “Baka da lafiya ne Ustaz?” Bai ko kalleni ba balle ya amsa min, ya cigaba da driving zuwa inda ake gudanar da shirin. Shiru motar tafiya kawai muke kamar kurame sai sautin k’ur’an da yake cikin motar cikin suratun nisa’i.
Muna isa wajen Dinnerr Asma ta fita. Ni kuwa kasa fita na yi ina bin Ustaz da kallo da idanuwana da suke kawo ruwa. “Ya dai?” Ya furta yana d’an Cijan bakinsa da kawar da kai, na san kwallar da ke idonsa ce baya son na gani. Hannunsa kawai na kama k’am cikin nawa. Na furta “Gaya min ustaz, gaya min ko laifi na maka na baka hak’uri bana son irin wannan horon da kake min zuciyata ba zata ‘dauka ba…” cigaba ya yi da danna wayarsa idanunsa duk sun ka’da sun yi wani iri. “Baka da lafiya ko?” Na fa’da ina son lalubar k’wayar idonsa. A fusace ya ce “K’alau nake Ayshatu, just go and live me alone….” Kallonsa nake yi idonsa a runtse kafin na janye hannuna a hankali na fice daga motar idona na zubar da k’walla ban damu da b’acin kwalliyar ba damuwata sanin wani laifi na yiwa Ustazun Aysha..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️NA GA RAYUWA…21.
Ina neman alfarma Don Allah da Manzonsa 😭🤲 don Allah ku shiga link ɗin nan ku yi mana voting MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
https://www.facebook.com/share/p/ChZaudpRhnBicHZ5/?mibextid=C7JYKg
Idan kun shiga zai nuna requesting ana yin approving sai ku danna mini don Allah.
Masoya Ustazun Aysha. A nuna mata kara… Daga kungiyata abar alfaharina. In dai kuna son na cigaba da rubutu cikin da’din rai…
Ganin irin yawan mutanen da suka zo wajen kamun biki na, ya wanke min duk wani b’acin rai na da bak’in cikin dake nuk’urk’usar zuciyata. Wani farin ciki ya ziyarce ni, da na tuna duka wa’dannan mutanen sun zo ne saboda ni. Zuciyata ta yi haske walwala da fara’ar fuskata suka dawo. Mai hoto ce ta dinga d’aukata duk inda na saka k’afa, har zuwa sanda na isa wajen zama na. K’awayena suna bina a baya. A haka na zauna ina ta sakin murmushi. Ki’dan larabawa ne kawai yake tashi a wajen, da wani irin k’amshin turaren wuta masu da’din gaske. Ba’a rawa kowa yana wajensa a zaune sai mai gabatar da shirye shiryen bikin ce kawai a tsaye a filin wajen, tana ta yiwa manyan bak’i barka da zuwa. Kowa yana zaune cikin aji kai daga gani ka san mutane ne masu aji da wanda ilimi ya ratsa su suka halarci wajen. Ba wani hayaniya kowa yana zaune a inda aka tanadar masa ya zauna ya hanyar ganin Table no. D’insa a card d’insa.
An ci an sha, kowa ya yi nak, an kuma yi barkwanci Malamai mata suka yi wa’azi sosai. Bayan tsawon lokaci aka tashi daga wajen. Dangin Ustaz ma sun zo sun kuma yi min kamu akan ku’di masu daraja. Ustaz ne ya mayar da ni gida bayan an tashi sai dai ko kallon arziki bai ha’dani da shi ba balle magana ta fatar baki. Tattarashi na yi na watsar don ni sam ban san wani laifi guda da na yi masa ba.
Sai sha biyun dare na kashe wayata saboda naga da gaske dai Ustaz bai kira ba.
Da Asuba kuwa ina kunna wayata kiransa ya shigo. Na saki ajiyar zuciya na saka hannu na amsa kiran cikin matuk’ar farin ciki, don rabon da ya yi min kira irin wannan har na manta. “Hello Habeeby…” Na kira shi da sunan da ban tab’a kiransa da shi ba. Madadin ya amsa sai ji na yi ya yi k’aramin tsaki ya furta “Ina ki ka je jiya da daddare, ba kira wayarki a kashe?” Zuciyata ta wani yunk’oro da tsananin b’acin rai na ce “Ina kuwa zan je da daddare? Wace irin tambaya ce wannan barci nake ji shi yasa na kashe wayar na kwanta… na san ba kira zaka yi ba shi yasa ban ma saka a kai ba.” “Kada ki raina min hankali mana, ki mayar da ni wani sokon namiji wanda bai san abinda yake yi ba, ke…….”
D’if na kashe wayar da sauri, jin mamakin furucinsa, a muryarsa nake jin wani b’acin rai wanda na tabbatar har k’asan zuciyarsa yake. Ba zai yiwu na cigaba da waya da shi ba, don nima tawa zuciyar a hassale yake shi yasa na kashe. Na runtse idona ina jin wayar tana ta ringing kuma na san Ustaz ne don ringing d’insa daban ne. Hannu na saka na d’au wayar ba rubuta masa gajeran sak’o.
“Allah ya huci zuciyar manya, ka yi hak’uri Habibeey idan zuciyarka ta yi sanyi ka kira ni. Ina tura masa na kashe wayar gaba ‘d’aya cikin wani irin tashin hankali naji hawaye na zubo min daga idona. Me na yiwa Ustaz me zafi haka da nake hango jin haushina a tsakiyar k’wayar idonsa?
Ranar ne aka yi Dinnerr bikina a AMANI… Shima tsaf aka tsantsara min kwalliya ta cikin Black material wanda zab’in Ustazuna ne, kwalliyar ta min kyau matuk’a da gaske. Stone peach ne a jikin material d’in don haka aka min amfani da Shoe and clutch peach sai sark’ar wuyana ta zallar Zinare zubin English golden. Baa min kwalliya ba ranar saboda hawaye ya k’i barin idona ba kuma hawayen komai bane, sai na rabuwa da gidanmu Abba na Ummana, da Mami na. Ga su Ya Usman ma duk wai yau zamu yi ban kwana, zan tafi rayuwar da kowa yake gaya min sai hak’uri. Zuciyata ta yi rauni sosai musamman da aka kai ni wajen Abba mu yi sallama. Abba ya d’ago cikin jarumta ya saki murmushin da na tabbatar na k’arfin hali ne. Hannu yasa ya ya fito ni jikin sa. Muryarsa cike da k’arfin hali ya ce “Matso AYSHA ta….” Na matsa kuwa jikinsa na kafa kaina a saman cinyarsa ina zubar da wani irin hawaye. Hannu ya saka ya bubbuga baya na alamar rarrashe cikin wani irin furuci ya ce. “Ki yi hak’uri Ayshatu na, haka kowace mace ta gada kuma shine abin alfaharin ta. Aysha, ina son ki yiwa mijinki biyayya kwatankwacin biyayyar da Rabi’atul Adawiyya ta yiwa Mijinta, ko ki samawa zuri’ar gidanku k’ima da daraja a idanun Mijinki. Ba na son AYSHA ki yi abinda Mijin ki zai tsaneki har ta kai ga yazo yana dana sanin aurenki. Alhamdulillah ina alfahari da iyayenki mata ina so kuma ki yi koyi da su. Na fi son a fito min da gawar Ki daga gidan Ahmad Aysha, haka shine cikar burin Uba na gari, musamman da ke ke ka’dai ce d’iyata Mace da Allah ya bani. Soyayyar da nake miki ce ta saka na aurar da ke da k’ananun shekaru ba k’iyayya ba, Saboda na san Ahmad mutum ne na k’warai zai kuma rik’e min ke tsakaninsa da Allah. Ki kiyaye Ayshan Mami Allah ya miki albarka.” Ameen na ji jama’ar parlorn sun amsa Daga haka Abba ya ja hannuna ya damk’a min Alkur’ani ya saka min wata jaka mai kyau a gefena. “Alk’ur’ani ya zamo abokin hirarki, sallaya ta zama inda zaki sujjada ki kaiwa Allah kukanki, bana son kawo k’ara, mutuniyar kirki bata fiye kai k’arar Mijinta ba gudun b’ata masa suna. Kin ji ko?” Na d’aga kai ina jin zuciyata kamar zata tafasa saboda tsananin b’acin rai.
Ranar kam Ustaz k’in zuwa ya yi ya kai ni wajen dinner, kiran duniya ya k’i d’agawa k’arshe ma sai ya kashe wayar tasa gaba d’aya. Jan bakina na yi na tsuke ban gayawa kowa ba sai su Mami ne suka tafi dani wajen dinner.
Wannan shine labari na da duk wata soyayya da muka gudanar da Ustaz.
Hawayene ya gangaro daga idona na mik’e daga saman kujerar da nake ina bin d’akin Abba na da kallo. Tunani ne ya shiga yi min suntiri a zuciyata so nake na gano dalilin da yasa duk son da Ustaz yake min ya riki’de ya koma zazzafar k’iyayyar da ta kasa b’oyuwa a ransa har ta kai shi ga furta min kalmar saki a daren auren mu. Daren da Ustaz ya da’de yana gaya min ya ci buri iri iri a kansa. Burin ganin Aysharsa a zahirin Aysharsa ba tare da shamakin tufafi ba. Sai ga shi daren yazo mana a wani irin hagunce da namu burin. Menene sila? “MAMIN KI!” Na ji zuciyata ta amsa min a tsawace..
Da sauri na runtse idona ina girgiza kai da k’arfin gaske. Daidai sanda aka bu’de k’ofar d’akin aka shigo. Na dawo hayyacina ina binsu da kallo cikin dishi dishin idona. Yaya Muhammad, Ya Sadik, Ya Umar, fuskarsu a murtuke ba fara’a suke zubo min ido. Suka shigo cikin wani irin taku da yake nuna zallar b’acin ran da suke ciki. Zuciyata ta shiga bugu da k’arfin gaske na dinga bin su da kallo ina kallon yarda suka dogara k’afafunsu akan kujerar suka zagaye ni da idanunsu…
Wani irin kallo suke jifana da shi, wanda na rasa a mizanin da zan saka kallon nasu. Na san dai kallo ne na Allah wadaran halinki…
Sautin zuciyata ya sake bugu da k’arfin gaske jin Ya.Muhd ya kira sunana da sark’akkiyar muryarsa. “AYSHA! Gaya mana laifin me kika yiwa Ahmad ya sake ki a daren farko? Kada kice mana bakomai don hakan ma kin san ba zai yiwu ba. Ba auren k’iyayya aka muku ba, Ustaz kuma bai d’ora miki iddarsa ba balle a ce auren d’and’ano ya yi da ke? Me kika masa?” Ya fa’da a tsawace.
Hawaye ne kawai yake kwarara daga ido na. Na shiga masa rantsuwa da a idonsa ka’dai na san rantsuwa ta ba inda ta je. Na ba shi labarin abinda na sani dangane da canja min da Ustaz ya yi a kwanaki ka’dan da Suka rage na bikin mu.
“Mak’aryaciyar banza, wa kike tunanin zai yarda da wannan tatsuniyar taki? Ta yaya kike tunanin mutum ya aureki yana tsananin son ki Sannan ya sake ki a daren da aka d’aura muku aure? Dole akwai wani abu ki gaya min gaskiya kawai… kada ki bari zargin da nake a zuciyata ya tabbata don ni zuciyata na gaya min tabbas ke da uwarki sun san komai, Mami ba, tabbas akwai saka hannunta a cikin lamarin haka nake ji a raina….
Ji muka yi an turo k’ofar da k’arfin gaske, an shigo, idanuna suka fa’da cikin na Mami da suka ka’da suka yi jajur. “Umar! Ni kake zargi da mutuwar auren Aysha?” Ta furta a tsawace idanunta suna zubar da hawaye… Umar ya cije bakinsa yana jijjiga kai ya furta “Ai ba abin mamaki ba ne, tunda kowa ya san kina adawa da auren….” “Faruk!” Umma ta fa’da a tsawace tana nuna shi da yatsa. Tashin hankalin da kake son ka jawo mana kenan a gidan nan. Ta yaya kake tunanin Fateema zata cutar da Aysha ta hanyar kashe mata aure? Kada na sake ji… bana so wani irin zancen banza ne wannan..? Kana cikin hayyacinka kuwa…
Gani muka yi Mami ta juya zata fita daga ‘dakin, sai dai shigowar Abba ya hanata don da k’arfi ya turo k’ofar shima idanunsa akan Umma ya furta wai menene?” Nan Umma ta shiga ba shi labari Mami dai bata ce komai ba illa ficewa da ta yi tana hawaye. Madadin Abba ya yi fa’da sai naga ya girgiza kai ya kalli su Ya. Muhd ya furta “Ku tafi masallaci Muhammad an yi sallah.” Suka fice a hankali. Umma ta dubeshi yana zama yana danna waya ta ce “Amma ka barsu suka fita baka wa Umar fa’dan abinda ya yi ba?” Jingina ya yi da kujera yana lumshe idonsa ya furta “Nima ina tunanin da Umar yake….” Ba shiri Umma ta zauna tana furta “A’a Abban Aysha kada ka fara irin wannan maganar don Allah…” wani kallo ya mata kafin ya cije bakinsa. Ya furta “Ina zargi na ce, kuma tabbas idan na tabbatar da zargina wallahi sakinta zan yi, ina jiran feedback d’in Ahmad, mun yi waya da mahaifinsa ya gaya min su basu san labarin sakin ba, amma sun yi waya da Ahmad ya sanar masa yana airport d’in Abuja zai wuce egypt, amma Babansa ya dakatar da shi ya ce ya juyo lalle a daren nan zai zo ya gaya mana koma menene…” Umma jikinta a salub’e ta mik’e tana furta “Allah ya kyauta.” Ta bar ‘d’akin. abba ya sake d’agowa a karo na biyu yana kallona ya furta “Kin tabbata baki san komai ba?” Na d’aga masa kai na. Ya girgiza kansa shima ya mik’e ya fice daga d’akin. Tausayin kaina ya sake kamani. Kuka nake sosai ba wanda ya sake bi ta kaina, tun bayan da Umma ta shigo ta kawo min tea ta rutsa ni sai da na shanye. Sannan ta fice daga d’akin.
Har dare gidanmu tsit ba wani mai walwala, y’an biki tuni suka watse bayan an sanar musu ba wani abu bane, Ustaz ne tafiyar gaggawa ta same shi.
Bayan Isha’i Iyayen Ahmad suka zo, Abba ya saka aka shiga da su parlorn sa na cikin gida. Ni dai gaba na kawai fa’duwa yake. Ba su wani da’de ba suka tafi. Sai ga Ya.Umar ya shigo da gudu yana furta “Umma fito Abba ba lafiya jikinsa rawa yake…” Da wani irin sauri Umma ta fito nima ban san sanda na fito daga d’akin Abba ba, na bi bayansu sitroom d’in Abban. Da wani irin tsawa Abba ya ce min “Fice Aysha haihuwar ki ba ta min rana ba, ku d’auka ku dubi hotunan nan ku ga irin b’atancin da cutarwar da ta yiwa nagartar gidan nan…..”
K’afafuna na rawa na zube a wajen ina kallon takardun da Ya Muhammad ya zubo min, ido na ware ganin ba abinda ya b’uya a hoton daga tsiraicina komai na a waje, k’irji and everything gefe guda wani mutum ne zaune kusa da ni yana shafa k’irjina…. Na zunduma wani Uban ihu, ina jin numfashina na neman barin gangar jikina…
Kash! Ina mai baku hak’uri, anan Book 1 ya k’are, sai dai ba zan yi jumurin kawo muku shi a kullum ba ta kafar whatsapp saboda wani dalili mai girman gaske, zan mayar da posting Litinin talata laraba da alhamis. Wato sau hu’du a sati. Sauran ranakun zan dinga posting a arewabooks. Y’an Arewabooks zasu dinga samu kullum In sha Allah. Dafatan za’a min uziri. Na gode sosai.
Masu so arewa ku yi searching @nazeefah ko kuyi searching sunan Book d’in. Labari yanzu aka fara AYSHA bata ga komai ba sai nan gaba. Akwai book 2 akwai Book 3. Ganin rayuwar yana gaba…
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢✍️
********************** ? **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************? **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ! **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ! **************************