Showing 21001 words to 24000 words out of 44853 words
gidahumanci kamar yarda ke kike yi…” Sai na ji kalmar ta min girma a kai, na kuma samu raina da b’aci Umman ce gidahuma kenan?
Sallamar Abba muka ji a kan mu bayan kusan mintuna 30 da fitar Umma, har a sannan kuma Mami bata fasa zuga ni ba. Ido ya zuba mana cikin tsukakkiyar fuskarsa da ban tab’a sanin yana da ita ba. “Tashi ki je sitroom kina da bak’o…” Mami ta ja hannuna ta rik’e k’am. Ba zata je ba..” Ta furta idanunta cikin na Abba. Wani kallo ya wurga mata mai cike da nuna zallar b’acin ransa ya furta “Kada mu yi haka da ke Fateema, kada ki kai ni bango, abin ba zai mana da kyau ba. Cika mata hannu…” Hannun ya fincike a nata hannun ya ja hannuna muka fice. Har d’aki ya raka ni. “Ki shirya sosai ki same shi a sitroom, idan kin so ki watsa min k’asa a ido ki zubar da martabar gidan nan…” Jikina kawai rawa yake, na kasa aikata komai sai share hawayen fuskata nake. Ga Abba ya ce yana tsaye a parlorn Mamin yana jira na. After dress kawai na zura akan kayan na fita duk zuciyata a furguce take ba ni da nutsuwa ko ka’dan. Don ban manta kashedin Mami ba na kada na yarda da zuwa wajen Ustaz idan kuwa na amince ta san na nuna mata bata isa da ni ba, kuma ba ita ta haifeni ba. Wannan magana ita take firgitani nake kuma rasa nutsuwa tabbas sun saka ni a tsaka mai wuya. Hannuna Abba ya sake ja, muka sauka ina kallon Mami da take tsaye ta saka hannu ta share hawayenta sai na ji nima nawa hawayen sun zubo. Na d’an tsaya Abba ya juyo yana kallona. “Kina son na b’ata miki rai AYSHA? Kada ki saka na d’aura miki aure da shi yanzun nan…” Da sauri na girgiza kai. Sai da ya ga na shiga sitroom d’in sannan ya juya ya koma cikin gida.
Zuciyata kawai bugu take, musamman da na ji k’amshin turaren Ustaz ya mamaye sitroom d’in. Na yi sallama can k’asan mak’oshi. Shima a k’asan mak’oshin ya amsa yana sakin ajiyar zuciyar da tasa na d’ago na kalleshi. Jallabiya ce bak’a wuluk a jikinsa, yau bai saka Alkyabba ba. Kansa dai da farin Ihrami. Idanunsa sanye da farin glass da ya k’ara fito da kyan fuskarsa. “Shigo ki zauna..” Kamar ba zan shiga ba. Sai dai na shiga na zauna a kujerar da take nesa da shi. “Dawo wannan kujerar bana son magana da k’arfi, I feel headache zuwan na dole ne..” Na kalli kujerar da take kallon tasa na tashi na koma na zauna fuskata a tsuke ina wasa da yatsun hannuna. Shiru ya yi kansa a k’asa kafin na ji muryarsa mai cike da rauni yana furta “Ba gaisuwa AYSHA?” Sai na ji kunya ta kamani na d’ago kamar dole na ce “Ina wuni?” Bai amsa ba, wani kallo kawai yake jifana da shi da yasa yanayin jikinsa sauyawa, sai naga ya lumshe ido yana murza goshinsa ya furta “Gaya min laifina Ayshatu? Kike hukunta ni da wannan sigar, na kira waya kin yi rejecting text no answer, makaranta kin k’i zuwa, gaya min me ya faru?” Shiru na masa kawai idanuna na zubar da hawaye da zan iya a lokacin kai tsaye zan furta masa ya janye maganar aurena, amma wallahi na kasa ya min wani irin kwarjini da ba zan iya kallon idanunsa na furta masa hakan ba. Gashi a k’asan zuciyata wata irin soyayyarsa mai zafi ce take sake ragargazar zuciyar. Kallona dai yake kafin na ji ya sake kiran sunana. Kiran da naji har tsakiyar raina. “AYSHA! D’ago ki kalleni ina son mu yi maganar gaskiya, bana son k’unbiya k’unbiya kuma….
Zan baki tarihin kai na da baki tab’a tambaya ba, zan sanar da ke waye ni da k’arfin soyayyarki a zuciyata, idan kin amince da aurena to, idan kuma kin ji ban kwanta miki ba bayan sanin wanene ni sai na k’yaleki na yi fatan Allah ya ha’da kowa da rabonsa….
Ahmad Sulaiman Saeed shine
Cikakken sunana, sunan da iyaye suka saka min, sunan da kowa ya san ni da shi. Sai dai a yanzu a makarantar ku da gidanmu na ji sun canja min suna zuwa Ustazun Aysha….”
Jin abinda ya fa’da ya saka ni saurin d’agowa ina kallonsa. D’aga min kai ya yi “Banda tambaya har sai na gama, abu guda da na sani ina jin da’din Sunan da aka canja min, ina kuma fata ya ‘dore har abada idan da alheri a cikin zama na da ke…
Mu uku kacal na gani a gidan mu, nima ban san dalilin da yasa suka zab’i su haifemu mu ukun ba kamar a k’asar turawa duk da dai d’abiun turawan suke amfani da su… na so a ce gidanmu muna da yawa kamar yarda nake sha’awar duk wani babban gida ya kasance, sai dai hakan bata samu ba. Amma na ce alwashin duk matar da na aura sai ta haifa min yara bila adadin ina son naga y’ay’ana sun kai hamsin…” waro idona na yi ina kallonsa ya ‘d’aga min kai “Don haka sai ki shirya dafatan Allah ya bamu masa albarka….” Runtse idona na yi saboda tsananin kunya a raina nake raya sai kace nace masa zan aureshi?
Ahmad Sulaiman Sa’eed shine Babba, sai Khadija Sulaiman Sa’eed wanda kafin a haifeta sai da na shekara goma cif. Itama tsakaninta da d’an autanmu shekaru goman ne, shi yasa na ce miki su iyayena rayuwar turawa suke ko don a can k’asar masu jajayen kunnuwan suka taso. Mahaifina ya da’de yana aiki a Canada kafin ya dawo Nigeria ya kafa kasuwanci.
Mahaifina su Talatin ne a gidansu ba zan iya jero miki su ba, sai dai na san mutanene masu zumunci masu son kuma auren zumunci, nima bijirewa na yi na musu tsallen baka’dai na gaya musu AYSHA kawai zuciyata take so. A d’akin su Abba na akwai Umma Amina itace Babba sai Umma Jamila, Daddynmu sai Abba Kabeer, Abba Ali, Abba Naseer da Umma Shatu.. autarsu kenan kuma mate d’ina ce mai sunan Ayshata…
A gidansu Umma na kuwa su Ashirin ba biyu ne, sai dai a d’akinsu su biyar ne kacal. Ramla Mahaifiyar Ahmad Sulaiman, sai Saudat Tasleem, Taiba da Nihad. Nan fa wai su mahaifiyarsu balarabiya shi yasa ta sakawa yaranta sunan larabawa don Kakata buzuwar Yamen ce.. sai kin hankali da su idan muka yi aure don mutane ne masu felek’e da iyayi na gaske.
Duka karatu na tun daga matakin yarinta har na girma, na yi su ne a lebanon school, sai da na gama secondary sannan na tuburewa Daddy na ce Jami’atul Madeena za’a kai ni. Ya so ya bujire don shi burinsa na zama iyalen Elizabeth ni kuma na ce nawa burin na zama dangin King Fahad ne, an kai ruwa rana kafin ya amincewa buk’atata na tattara na tafi Jami’atul Madeena ban kuma dawo ba sai a waccan shekarar… Ina isowa Nigeria na tsunduma aikin k’wadago ina ha’dawa da noma da kiwo da kuma safara daga can k’asashen waje zuwa tamu k’asar.
Ranar da na fara ganinki, rana ce mai matuk’ar girma a wajena, da ba zan manta da ita ba. Kamar ba zan fita daga gida ba saboda hadari da ya lullub’e sararin samaniya sai dai wayar da Kabeer yake min ta isheni na zuwa ganin wani gida da Zan gani a layinku. Na mik’e na shiga wanka kamar ba zan yi kwalliya ba sai dai na samu kaina da tsara kwalliya ashe zan ha’du da matata ne…
Ina tsaye da abokina na dinga jin zuciyata na wani irin harbawa. Mamaki ya isheni na juya don ganin dalili sai idona ya fa’da kan wata zuk’ek’iyar yarinya doguwa fara mai suffar larabawa. Numfashina ne ya kusa d’aukewa duk da na Yi matuk’ar daurewa wajen yi miki kallon da shari’a ta amince da shi kallo guda. Sai da kika wuce sannan na saki ajiyar zuciya ina kallon Kabeer na furta “Wacece wannan?” Kabeer dariya ya yi sosai yana cewa “Ai kuwa in dai sonta ka ke ka dace da macen k’warai, Saliha managarciya da kowa ke so.. duk layin nan ba nutsuwar yarinyar can wallahi…” na d’an yi dariya ina furta “Dalilinka na cewa haka Kabeer?” “Saboda kai daga gani shigarta ka san ta ha’da duk qualities d’in da ake son mace ta gari ta zama..” ya furta yana kallona cikin son tabbatarwa. Dariya na yi nace “Idan kuma Basaja take fa?” Kabeer ya ware ido ya ce wallahi ba wani Basaja idan baka amince ba kuma ka yi bincike..” “Bincike ya zama dole Kabeer, don aure nake son mu yi ta zame min Uwar yara na kaga kuwa dole na binciki sahihancin tarbiyyarta..” Kabeer ya jinjina min kai. “Ina tabbatar maka Ahmad duk binciken da zaka yi akan yarinyar nan magana guda zaka samu Mai tarbiyya ce…” Na saki ajiyar zuciya ina d’aga kai na windownku na hango kamar ana lek’e jikina kuma ya bani ke ce ko?” Waro ido na yi ina kallonsa. Ya saki murmushi yana d’aga min gira. “A jikina na san ke ce, na san kuma kema kin fa’da soyayyata daga yanayin yarda idanunmu suka sark’e da juna…”
Daga ranar na kafa d’anbar bincike ka’in da Na’in. Shine dalilin da yasa na je har makarantarku neman koyarwa. Kuma daga ranar kullum a kan idona kike tafiya makaranta duk da ba na bari ki ganni, na kuma lura duk sanda kika zo wucewa sai kin dinga d’an juyowa kina dubawa. Ina sane na dinga miki duk tambayoyin da nake miki a aji sai na samu kina da matsananciya kunya. Wannan ma ya sake k’ara miki k’ima a idona.
Hakan yasa kai tsaye naje gida da buk’atar azo min neman izinin fara zuwa zance wajenki. A take Abba ya ce wallahi in dai nine nake sonki ya ba ni ke, sai dai zai rok’i alfarmar a barki ki gama secondary saura shekara guda. Ba wanda ya ja da haka sai dai ni ba haka na so ba, na so a ce a yi bikin cikin wata biyu idan yaso ki k’arasa makarantar a gida na. Mommy ce ta dinga tausata. Abin kamar almara kullum Aysha k’ara min wutar sonki ake.. Yau da na ganki kina kuka a makaranta da k’yar na k’arasa musu karatun da nake musu. Allah ne ka’dai ya kai ni gida. Na dinga rok’on Daddy yazo a d’aura aure kawai amma ya k’i ya ce dole a bi maganar Abbanki ko shine ba zai aurar da y’arsa bata gama secondary ba. Still yanzu ma nazo naga kina kuka, AYSHA ki gaya min gaskiya ba kya son auren ne?”
Ajiyar zuciya na sauke a hankali na d’aga kai na. Waro ido ya yi har yana mik’ewa ya iso gaba na a tsayen da yake hannayensa a k’irji ya furta “Ki gaya min gaskiya, da gaske ba kya so na, idan Kika sake tabbatar min zan hak’ura…” Jikina ne yake rawa na sake d’aga kai na.. Zama ya yi yana rik’e kansa naga sai murza goshinsa yake. Sai kuma na ji cikin sark’akkiyar murya ya furta “Ki furta da bakin ki, cewa ba kya so na…” Na d’aga leb’ena a hankali ina kallon k’wayar idonsa muryata na rawa na furta “Na ba yanzu zan yi aure ba sai na yi ko degree ne, am too young to marry…..”
Ga mai son next page ya duba shafina na arewa zai samu page d’aya ko biyu bayan wannan.
Page 11 @ ArewaBooks Danna link d’in nan Zai kai ka har page 11.
https://arewabooks.com/chapter?id=669d122dc1b845b878dad215
Saboda yawan complain d’inku yasa na yi haka… dafatan za’a ni ha’din kai.
Group 1 and 2 ya cika ga group 3 nan wanda bai samu ba ya shiga.
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
********************** ! **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ! **************************
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 12
Kashegari na lallab’a na yi shirin makaranta, don kawai na zame na je gidan su Mami na. K’arfin hali kawai nake don ko barcin kirki ban samu na yi ba. Don ma a ‘d’akin Umma nake kwana tunda Mami bata gidan. Ganin juye juyen da nake ya yi yawa, hakan yasa ina ji Umma ta saka baki ta kira suna na. “Mik’e AYSHA ki shiga toilet ki yi alwala ki yi sallolin nafila tunda barcin ya gagara. Na mik’e kuwa jikina a sanyaye na aikata abinda ta ce d’in, sai naga na samu sauk’in abinda nake ji a cikin raina.
A kitchen na sameta tana dama kunun gya’da. Na furta “Umma zan tafi.” Ta ‘dago tana kallona kafin ta mik’o min cup d’in hannunta mai cike da kunun gya’da mai zafin gaske. “Shanye shi tas kafin ki tafi, kina nan kin sakawa kan ki k’wazzaba duk kin bi kin rame.” Ban mata musu ba na sha kunun don ni da kaina ina ji a jikina na matuk’ar ramewa don har kamar iska zata kwasheni.
Ina shiga motar na ce da Baba Driver “Gidan su Mami zaka kai ni ba makaranta ba Baba.” Ya juyo yana kallona ya ce “Yau ba zaki makarantar ba Ayshatu?” Na d’aga masa kai, sai bai ce komai ba ya ja mota ya nufi da ni court road don anan gidan su Mamin yake.
Shiru gidan har na shiga cikin harabar gidan ba kowa, don gidan sam ba yara sai Maman su Mamin duk an musu aure mazan gidan kuma wasu suna k’asashen waje karatu. Na shiga Parlorn gidan da yake k’asa inda anan step d’in benen yake.
Mama ta dubeni tana bu’de baki. “Yarinyar Mami ce a gidan nan da safe haka, ina makarantar?” D’an murmushi na saki ban yi mata wasan da na saba mata ba ni jika da kaka. Na zauna a gefenta ina furta “Mama ina kwana?” Ba zan amsa ba Aysha, kin ga yarda kika dawo kuwa? Wace irin masifa ce kuka jefa kan ku haka ke da Uwar taki, ita ba nutsuwa ke ba nutsuwa, ku wato ba zaku yarda da hukuncin Allah ba kenan, dole sai kun ja da mahaifinki alhali dukkanku a k’ark’ashinsa kuke, ai ni ya min daidai wallahi wani Sokon Uba ne shi da alheri na binsa zai saka k’afa ya doke saboda wani bokon banza da wofi… ai idan nice a ranar da aka zo neman auren ma zan d’aura auren kowa ma bai ji ba bai gani ba. Mutum kamar Ustaz Ahmad da yake burge kowa, a cikin lafazin karatunsa zaka gane mutum ne mai nagarta…” idanuna ne suka kawo k’walla na yi shiru kawai ina jin zancenta. Ina ma y’arta zata zauna ta gane abinda Maman take fa’da. Amma Ai mun bari gini tun ran Zane, ni na san Ustaz ya yi zuciya ya bar ni daga yanayin kallon da ya min jiya. Ai shi ba k’aramin mutum bane da zai zauna ina masa walagigi da hankali. “Tashi ki je can wajen Uwarki, kada ki min kuka anan ba zan wani lallasheki ba, don ni bana bayan rashing gaskiya..” Na
Mik’e kawai ina harha’da hanya na hau saman don na san a can zan samu Mami har yanzu yaran gidan kowa da d’akinsa.
Na tura k’ofar na shiga, Mami tana kwance a saman carpet idanunta a lumshe kamar mai barci. Ta bu’de ido tana kallo na. Da sauri na isa wajenta, mik’ewa ta yi zaune tana bu’de min hannunta alamar na shiga. Na kuwa shiga ta Mayar ta rufe i ruf tana sakin ajiyar zuciya. “I missed you Mami na.” Ta lumshe ido tana furta “I mish you too Baby na.. Ina school d’in baki tafi ba kika biyo nan.” Hawaye na fara yi. Ta saka yatsa tana wasa da hawayen fuskata tana sakin murmushi a hankali ta kai min sumbata a gefen k’unci. “No more crying Baby na..” “Zaki koma gidan? Ni na yarda ba zan aure shi ba.” Ta saki murmushi ta ja hannuna ta matse cikin nata ta furta “Zan koma Aysha, don ba zan iya rayuwa ba tare da Baby na ba..” Murna na fara yi ina jin abinda ya tsaya min a zuciyata yana tafiya. So nake na tambayeta ta amincewa alak’ata da Ustaz amma sai na ja baki na yi shiru don bana son b’acin ranta. Ina kallo ta shiga wanka ta fito ta shirya a gabana sannan ta zura hijab d’inta muka sauka k’asa. Mama bin mu ta dinga yi da kallo ganin yarda nake jan akwatin Mamin. Murmushi kawai ta furta “Lallai Fateema, yanzu ba wanda bai rarrashekiba aka dinga baki hak’uri kika k’i komawa gidan mijinki sai yanzu da Aysha ta zo? Ai shikkenan Allah ya kiyaye hanya..” Mami murmusawa kawai ta yi muka fice daga gidan. Muka shiga cikin motar Mamin sai gida.
Umma tana tsakargida tana ware kayan miya da naman da za’a saka a freezer ta ji sallamar mu. Da mamaki ta ‘dago tana kallonmu. Mami murmushi ta saki tana furta “Kallon fa?” Umma ta ce “Ba dole na kalleki ba Fateema, yanzu ba wanda bai je biko ba har ni kishiya, amma kika k’i dawowa Mahaifinki ma ba yarda bai yi da ke ba, shima kika ja kika kafe sai yanzu kawai naga ficilar yarinyar ta dawo da ke..” Mami
Murmushi ta saki. Ta ce “Hakan zai nuna muku mahimmacin ta gareni a rayuwa ta…” Umma ta ce “Ba shakka, To Allah ya kyauta na gaba…”
Daga ranar da na furta masa ba zan aure shi ba, bai sake nemana ba har tsawon kwanaki biyar. Zuwa lokacin duk na fige na lalace sai kace wacce ta yi watanni tana ciwo. Ba wanda ya sake bi ta kaina balle a min zancen Ustaz.
Da yamma sai ga Yaya Muhammad ya shigo gidan muna tsakargida duk muna aiki. Ya d’an dubi Mami yana sosa kai ya furta “Hajiya Mami, Aron Aysha zaki bani, Khadija na fama da laulayi ni kuma tafiya kaduna ta kama ni zan kwana biyu a can…” Mami ta masa wani kallo kafin ta furta “Muhammad bana son jaye jayen magana, ita ina y’an gidansu ba za’a kai mata su ba, sai Aysha?