Showing 12001 words to 15000 words out of 44853 words

Chapter 5 - NAGA_RAYUWA_BOOK_1

Unknown   

02 Dec 2025

98

da na tabbatar suna kitchen d’in. Saboda koda yaushe tare suke girkin su. Wani kallo Mami ta zuba min mai cike da zargi da tuhuma, na lura kwana biyu irin kallon da take min kenan. Na yi k’asa da kai na ina sake gaishesu. Na mik’e ina cewa sai na dawo bayan sun amsa gaisuwar. “Abincin fa?” Mami ta fa’da tana tsare da kallo. Na d’an girgiza kai ina turo baki na ce “Mami, yau bana son yin breakfast fast…” “Wasa kenan, wuce Malama ki ha’da tea ki sha ga chips nan ki cinye tas kafin ki wuce… ina lura da ke kwana biyu ba wani abincin kirki kike ci ba, jiki kamar sillen kara… Uban me ke damunki?” Da sauri na furta “Allah bakomai Mami..” K’wafa ta yi, ta cigaba da aikinta kafin ta furta “Ina fatan Bakoman ta zama bakomai d’in…” Umma da take jin mu dariya ta yi tana furta “Ke ma dai Fateema, kamar AYSHA ce sai an tsaya cewa ta ci abinci sai ka ce yarinya, idan kika ga bata ci ba ta k’oshi ne…” Mami a tunzire ta furta “To Ayshan nawa take? Shekara sha bakwai Ai har yanzu yarinya ce, ko yanzu ta kama d’aukarta zan yi na cafeta na goyata da zani. Gaskiya a daina jawo mata girma balle ido ya dawo kanta…” Umma d’auke kanta ta yi tana furta “Allah ya taimaka, aure dai idan lokacinsa ya yi ko an jawo girma ko baa jawo ba yinsa za’a yi…” Mami wani kallo ta yiwa Umma sai kuma ta furta “Allah Umma kada ki fa’di maganar nan wajen Abbansu ya ji, don wallahi ko sama da k’asa zata ha’de a shekaru dai irin na Aysha ba zan bari a mata aure ba, sai na ‘dauketa mu bar garin ina dalili?” Ni dai ina daga gefe dariya tana son kama ni, koda yaushe drammerr Umma da Mami na kenan.

Na gama kurb’ar tea d’in a gaggauce na fice ina amsa addu’ar da suke min da ameen..


Ina zaune a ajin mu na makarantar boko intercontinental nake zuwa.
Aka turo kira na daga office d’in principal. Ban wani damu ba sanin cewa ina da mik’amin da zaa iya nemane koda yaushe.

A hankali na saka hannu ina knocking d’in k’ofar. Daga ciki principal ya amsa da “Yes come In.” na saka kai na direct cikin office d’in. Daidai lokacin da idanuwana suka sauka cikin na ustaz hancina ya shak’i k’amshinsa. Ji na yi k’afafuna kamar ba a jikina suke. A raina na ce “Nan ma ka biyo ni ne?” “Da principal zai lura lokacin zai ga yarda k’irjina yake bugun gaske idanuna suka tara k’walla. Na shiga office d’in a nutse da sallama. “Good morning sir!” Na furta muryata a nutse. Ina satar kallon Ustaz da ya yi kamar bai ganni ba. “Morning AYSHA Imam. Baki ga bak’o ba?” Na juya ina satar kallonsa murya a k’asa na furta “Good morning.” Ya d’ago daga kallon wayar da yake fuskarsa a ‘dan tsuke ya furta “Morning…” Daga haka bai sake magana ba ya mayar da kansa kan abinda yake na daddanna waya. Principal ya mik’e min wasu files “Maza ki kaiwa Emeka, ki ce masa ya yi signing before a fita break..”

Na amshi files d’in ina d’an durk’usawa. Na fita raina a b’ace. Zuciyata cike da mamakin kallon da Ustaz ya min kamar bai sanni ba. Sai na ji sam ban ji da’di ba.



Haka dole na koma Islamiyya ba don raina na so ba, sai don zuciyata ta kasa dauriyar rashin ganin ustaz. Ranar ma ko kallo ban ishesa ba, ya yi karatunsa ya fita fuskarsa a d’an tsuke.


Ina komawa gida na tarar da abinda ya kusa fasa min zuciya. Tun daga bakin gate nake jiyo hayaniya a cikin gidan mu. Muryar Mami a sama take sake furta “Wannan ma ai zance ne, kuma ba mai yiwuwa ba, Ayshan nawa take da za’a d’auko maganar aurenta yanzu, to wallahi in dai ina numfashi ba mai aurar da ita a wannan lokacin..komai zai faru sai dai ya faru….

Gabana ne ya yi wani irin mugun fa’duwa na waro ido a hankali na furta “Aure kuma? Ni Ayshan za’a yiwa aure yanzu?” Murya a sanyaye na yi sallama, gaba d’aya suka zubo min ido, kamar sun samu Tv. Take na gasgata abinda zuciyata ta gaya min. Aurar da ni za’a yi. Gefe na ja na zauna idanuna tuni suka fara bulbular da hawaye ina kallon Mami na na ce “Mami aure za’a min?” Mami da itama nata idanun suka yi jajir suna son zubo da hawayen, ta furta “Kul Aysha! Kada ki sake ki zubar min da hawaye anan, wannan maganar ki ‘dauketa tatsuniya wallahi in dai sunana Fateemah y’ar halak kuma cikin iyayena sai na cika burina a kan ki… babu wanda ya isa ya aurar da ke a wannan k’ananan shekarun sai kace a karkara. Ko su karkarar yanzu an daina irin wannan auren. Wuce ciki ki zauna…” Na kasa wucewa cikin zuciyata sai kakkarwa take, ni na san halin Abba yana da kafiya da naci akan abinda ya saka gaba, ba wanda ya isa ya canja masa ra’ayi, baya ma tank’waruwa ko ka’dan, irin mutanannan ne da ake cewa taurin kai kamar mutanen farko. Don haka ban san sanda na kece da wani irin kuka ba musamman da na tuna shikkenan son da nake wa Ustaz ya zama tarihi kenan, ba zan aureshi ba? Mami hankalinta ya sake tashi, ta ja hannu da k’arfi muka hau sama cikin b’acin rai da k’unar zuciya take furta “Ba zai yiwu ba, ki gaya masa ma tun farko kada ya yi abinda zamu zo muna samun sab’ani da shi.

“An da’de baa samu sab’anin ba, aure ne dai ba fashi sai dai ki yi duk abinda za ki yi. Haka kawai ba zan ga samu naga rashi ba. Nagartaccen mutum irin wannan ya zo neman auren y’ata ko a primary take tsigeta zan yi na ba shi…” muka ji muryar Abba a sama yana fa’da yana tsaye a k’ofar shigowa…

Mami ta juya a fusace tana furta “Kada mu yi haka da kai Abban Aysha….


Tsaki ya ja kawai ya shige parlor jin ana kiran sallah.



Bayan Sallahr Isha, a al’ada irin ta gidanmu bazuwa ake, a tsakargida kan tabarma a ci abinci. Yau d’in ma haka ce ta kasance sai dai ni ina daga wani d’an lungu a zaune kamar yarda Mami ta umarce ni. Abba ya juya yaga kowa bai ganni ba. Ya kalli Mami ya ce “Ina Aysha?” “Ina zaka ga Aysha anan? Alhali ka birkita mata kwanya tun d’azu take kuka..” “Ta shirya fara na jini, don aure ba fashi, ki kuma sanar da ita k’arfe takwas bak’onta zai zo. Don Allah ki sata ta wulak’anta martabar gidan nan kiga abinda zan
Aikata.. Babban mutum ne da ba zai juri rashin kunya ba…” Daga haka bai saurari surutun Mami ba ya wanke hannunsa ya saka a cikin tuwo ya fara ci…

Ina tsaye ina jin k’afata na rawa. Babban mutum nake ta nanatawa a zuciyata it means mai iyali dattijo. Na runtse idona ina jin wani zafi a k’asan zuciyata. Ina jin yaro ya yi sallama aka amsa masa ya ce “Wai akwai bak’o a waje…” Na ji zuciyata ta wani irin hantsilawa har sai da na dafe k’irjina. Muryar Abba na ji yana cewa “Kai ALIYU jeka ka shiga da shi sitroom, kai kuma Usman jeka ka kira min Aysha… Ji na yi kai na ya wani irin sarawa. Usman da ya nufo inda nake ya tsaya yana kallo na. “Au da kina tsaye kina ji?” Hawayen idona na d’auke na d’aga masa kai na. “Ki je in ji Abba kina da bak’o… Saura ki je masa da wannan banzan hawayen shashasha tun baki san wa ne me neman aurenki ba kin sakawa kan ki damuwa…” Ban bi ta kansa ba na nufi inda Abba yake. Mami kuka take tana sake rok’onsa ya janye maganar sa. Kallona Abba ya yi ya ce “Ki je ki shirya ki je sitroom kina da bak’o saura ki je ki nuna masa rashin tarbiyya…” Na juya jikina a sanyaye madadin na je na canja kayan Wucewa na yi wajen haka idona a damalmale da hawaye na tura k’ofar, muryata cike da k’unci na masa sallama.. k’amshin turaren Ustaz na ji ya baibaye hancina zuciyata na bugu nake son d’agowa naga ko shine ban dawo daga tunanin da nake ba, na ji ya ce “Aysha Imam ya gida?” Ko daga barci na tashi na san muryar Ustaz na yi saurin d’ago kaina idona ya sark’e cikin nasa, yana zaune yana matse yatsunsa cikin na juna fuskarsa d’auke da murmushi…..
Cikin mamaki na furta “Ustaz!” Ya d’aga gira yana murmur ya furta “Ayshatu….





𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️













Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎


𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION




Arewabooks @nazeefah

Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 8



‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR


Kasak’e na yi ina kallonsa, shi kuma sai sakin murmushi yake ya firta “Kin yi mamakin gani na ko? Koda yake na san ba lallai ki yi mamakin ba don tini zuciyarki ta sanar da ke zan zo d’in ko ina so ko bana so, haka ne?” kallonsa kawai nake kafin na
Ankara da abin kunyar da na so aikatawa na runtse idona ina jin yarda zuciyata ke harbawa da k’arfin gaske. Bana son na bu’de idona balle na tarar da
Mafarkin da na saba ne.. “Ki yi hak’uri nazo gidanku ba tare da saninki ba, ban kuma nemi amincewarki ba ko? Na yi hakane saboda koyi da sunnar manzon Allah s.a.w, na fara
Neman izinin iyayen yarinya kafin ita yarinyar. Na san tuni ki fuskanci manufata ba ke ba ma wasu da dama a ajinku sun san inda zuciyata da ruhina suka karkata, kema kuma a idonki na gano zallar son Ustaz da k’aunarsa…” Da sauri na waro idona ina kallonsa. Ya ‘daga min girarsa guda da ta bada wani shape mai kyan gaske. Yana lumshe idon. “Don't pretend Aysha na san kina so na, albushir guda da zan miki ina miki so ninkin miliyoyin naki…” wani sanyi na ji yana ratsa zuciyata ban san sanda na saki wata siririyar ajiyar zuciya ba. “Ba ki ce komai ba?” Na sunkuyar da kai na wani murmushi da ban shirya zuwa masa ba yana kufce min. Cikin siririyar murya na furta “Me Zan ce Ustaz…” “Ki ce I love you too…” Da sauri na saka tafin hannu na rufe fuskarta, ina ji Ustaz ya saki ajiyar zuciya ya furta “Yawaitar kunyata a idanunki ya tabbatar min da zazzafar soyayyata a ranki. Amma naga kafin ki fito kamar kin yi kuka ko dai baki so fitowar ba ne?” “Ai ban san kai ba ne…” Na yi saurin toshe bakina jin abinda bakin ya furta.

Murmushi Ustaz ya saki ya furta “Ni na sani ai, da kin san ni ne kwalliya mai kyau zaki cab’a min ki fito kina iyayi irin yarda budurwa take wa Habibinta ko?” “Kai Ustaz!” Na furta ina d’an satar kallonsa “Kai ko gaskiya, next zuwan da zan yi dama ki tabbatar kin fito min a y’an matanki caras a bu’de min kuma jiki tunda ya halatta ko sau d’aya ne kaga matar da zaka aura ki saka min kaya mai kyau.. Kin ji ni ina ta surutu ban tabbatar ma ana so na ko a’a ba…. AYSHA d’ago ki kalleni…” na d’ago a hankali ba don zan iya kallon nasa ba, sai don bana son na masa gaddama. “Kina so na za ki aure ni?” K’asa na yi da kai na in furta “Kana da mata?” Wata irin dariya ya yi da har sai da ya bayyana wasu points a gefen hancinsa. Ya furta “Kishi kumallon mata, kada dai ace AYSHA na da kishi?” Girgiza kai na yi “Ni ba ni da kishi, ni dai kawai ba zan auri mai mata ba..” Dariya ya yi sosai ya furta “Mhmn, ba amsa kenan, don wannan amsar bata cika gamsashshiya ba.” In a serious tone ya furta “I have a wife AYSHA da yara biyar…” wani irin waro ido na yi, k’walla na taruwa a k’asan idon nawa. Na girgiza kai. Ustaz kuwa idanunsa ya kafa min yana sakin murmushi k’asa k’asa. “Gaskiya na gaya miki, ki je ki yi shawara zan dawo jibi idan kin amince sai ki gaya min. Ko ta cikin waya ne.” Ya fa’da yana ajiye min wani kwali a cikin leda “Idan kin kunna akwai layi a ciki, na yi setting komai, ban amince da Instagram da duk wasu tarkacen Social media ba sai whatsapp kawai. I repeat Whatsapp only AYSHA…. Anjima zan kira na san a waya dai may be zaki amsa min sosai ba za’a dinga min maganar bebaye ba, mai rowar murya kawai…” Murmushi kawai na saki ha’de da fa’din “Na gode.” Cikin sanyin murya don kam Ustaz ya sanyayar da ita, tunda ya gaya min yana da mata. “Numberta kawai, Sai Siblings d’inki da parents ban da su bana son ganin any number.” Na ce “Toh!” Ya ‘dan kalli table ya tab’e baki “Budurwar k’auye ba ruwa ba lemo haka ake saukar saurayi ko?” Da sauri na girgiza kai ina y’ar dariya ka’dan. Na lura Ustaz sam bai da bak’unta. Komansa free yake. “Ki gaida kowa na cikin gida sai na dawo.” Ya fa’da yana ficewa daga d’akin. Sakin ajiyar zuciya na yi, ina lumshe ido. A wata duniya na dinga ji na, mai girman gaske. Da na san Ustaz ne yazo wajena ba ta yarda za’a yi na zubar da hawaye na a banza, tunda Burina ne dama burina zuwan wannan ranar. Abu guda ke fa’dar min da gaba Mami na! Ban san yarda zata fuskanci lamarin ba. Ni kam ina son Ustaz kuma na shirya Aurensa koda Ba Abba ne ya ce ba, balle shi ya ce.


Na ‘d’au kwalin wayar, ba kowa a tsakargida shiru gidan, dama Mami ce mai son hirar tsakargida da alama tunda bata da sukuni a zuciyar ta sai kowa ma ya kama kansa. Umma dai itace da girki na san tana wajen Abba. Step na fara hawa ina jin tsoro na yana sake yawaita. A hankali na tura k’ofar parlorn Mami, Kamar yarda na zata tana zaune tana kallon tashar Arewa24. Ta amsa sallamar ba tare da ta kalleni ba. Jikina a sanyaye na zauna a gefenta ina nazarin fuskarta na ji ta furta “Yaya kika ganshi? Wani dattijo ko? Mai gemu buya-buya tunda na ji ance Ustaz ne, yanzu haka ma k’azami ne..” Kallon Mami ina mamakin kalamanta, tabbas bata san Ustaz ba, da bata yi wani furucin ba, ba mamaki da zata gan shi taga kamanninsa itama ta so ya zama surikinta.. ina cikin ko a cikin maza millions za’a tsame Ustazu na a matsayin wanda yafi kowa kyau da tsafta.. Mami ta zaci in dai ance mutum Ustaz ne sai ya zama wani mara fasali. Ai yanzu Ustazai akwai d’aukan wanka da kwalliya sosai ma. Ban san me yasa ba sai na ji wasu siraran hawaye suna zubo min, wanda na san ba hawayen komai ba ne sai na zallar farin cikin cikar burina, tunda na ji sanyinsu har k’asan raina da cikin jikina..

A zaton Mami kukan bak’in ciki nake. Ta mik’e tsam daga kujerar ta ta dawo inda nake ha’de da dafa ni, ta furta. “Daina zubar da hawayenki a banza Aysha, in dai ina numfashi babu mai miki wannan auren tozarcin ko me ma zai faru ya faru… wani irin tsalle zuciyata ta buga, na ‘dago da sauri ina kallonta na furta “Mami, kada ki ce haka, Mu yi hak’uri kawai mu yarda da k’addara, Saboda ba mu san abinda Allah ya b’oye ba….”

“Rufe min baki Aysha…” Ta furta cikin wani irin zafin rai, da har huci take fesar wa. “Kada kice min zuciyarki har ta amince da wannan mutumin? Wato har kin ji a zuciyarki zaki iya aurensa? So kike ki ba’da min k’asa a ido? Duk da yak’i da hak’ilon da nake na nema miki y’anci a wajen iyayenki da ba su san mutuncin ki ba? To bu’de kunnenki ki ji da kyau, ko son sa zai kasheki ba zaki auresa ba…” Ta fa’da tana fancakalar da hannu na ta mik’e a zuciye ta shige d’aki. Shiru na yi zuciyata na harbawa na zubawa hanyar da ta bi ido. Ina mamakin duk furucinta. “Anya Mami tana cikin hankalinta kuwa?” Ras take” zuciyata ta bani amsa tsabar son boko ne da ak’idar bokon yaja mata haka.

Na d’an tab’e baki ba ina tunanin tabbas za’a samu matsala, don yarda nake son Ustaz bana jin wani hargitsin Mami zai saka na rabu da shi. Na shige d’akina. Ina bu’de ledar da ya ajiye min. Waya ce mai kyau IPhone 13 sai turaruka masu kyau guda biyu. Na shinshina turaren d’aya irin turarensa ne sak, a jikinsa ya rubuta “For Night only…” Murmushi na saki, ina tunanin sabida me zai ce sai dare kawai zan saka.. Na san Abba ya kwanta, don haka sai da safe zan kai masa wayar ya gani, idan ya amince sai na cigaba da rik’ewa idan kuma bai amince ba sai na mayar wa Ustaz.


Wanka na yi na saka sleeping dress sannan na fesa turaren da Ustaz ya sanar da ni sai dare kawai zan dinga sakawa. Sai da na kwanta sannan na gane dalilinsa na cewa For Night d’in. Don k’amshin sosai ya dinga tuno min da Ustazun. Na dinga sakin murmushi ni ka’dai. Kafin na ji wayar na vibrating. Idona na kai kan screen d’in wayar sai ga hoton Ustaz a ciki yana sakin murmushi an rubuta “Farhatul K’alb..” (Farin cikin zuciya) ina sallama ya saki ajiyar zuciya kafin ya amsa ya furta “murya mai da’di…” shiru na yi “Ba gaisuwa AYSHA? Me ya hanaki bacci k’arfe d’ayan dare?” Da zan iya cewa zan yi Tunaninka. Sai dai na ji na kasa na furta “Bakomai…” “Gaskiya ban yarda ba.. ni na san me ya hanaki barci..” “To menene?” Na fa’da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login