Showing 15001 words to 18000 words out of 44853 words
cikin sanyin murya. “Cewa zaki yi To menene Habibeey?” Ya fa’da yana koyan muryar y’an mata dariya ya bani sosai na dinga yi kuwa ba k’akkautawa “Tunanin D’an Ugly saurayinki ko?” Na ware ido.. “Ba zaki amsa ba. Zaki iya vedio call please.” Da sauri na girgiza kai ina cije leb’ena na furta “A’a” “Me yasa?” Duban jikina na yi na ce “Ni dai bana so…” “Mhmn..” Ya ce cikin wata irin murya “Allah ya baki hak’uri, amma ki saka Hijab mana mu yi, wallahi son ganin ki kawai nake ko zan iya barci, kin bi kin rufe idona ke kawai nake gani.” “Shikkenan ma, kaga ba sai ka ganni ba kenan…” Dariya ya saki ya ce “Aysha!” Sunan da na ji ya tsarga har k’aramin yatsan k’afata “Kin san sunana?” “Uhm” na ce masa. “Okay fa’da na ji please, ni dage sai fa’dar naki nake kamar ni na ra’da miki. Ya sunana?” “Ustaz!” Na fa’da cikin muryar da ni kaina ban san na iya ta ba. Shiru ya yi tsawon seconds Hamsin har na zata ko ya kashe ne. Na furta “Hello..” ya saki ajiyar zuciya yana firta “Ina jin ki Aysha… kin tafi da numfashi na ne, Allah ya baki wata irin murya da zan yi kishin wasu mazan su gaba da jinta in dai za su yi feeling abinda nake ji yanzu… Ba zan iya ba, ki tashi ki yi sallah yanzu ki rok’a mana dukkan alheran da suke cikin neman auren nan kin ji?” “Toh” na amsa “Kina sallahr ai ko? Ko ba kya sallar dare?” “Ina yi.” To maza ki yi sallahrki zan kira da safe na ji feedback akan maganarmu.” Ya fa’da yana kashe wayar bayan ya furta “I love you…” cikin k’asa da murya. Sai da na ware ido ina tunanin Anya kuwa Ustaz ne.. ashe Ustazan nan suma ba baya ba wajen bawa soyayya hakkinta? In dai kuwa haka ne tabbas na dace.. Sallahr na yi na dinga rok’on Allah musamman akan Mami da niyyar Allah ya karkato mata da zuciyarta ta amince ta kuma so auren nan.
Da sassafe na tashi, cikin matuk’ar karsashi da wani farin ciki da ya kasa b’oyuwa a fuskata.
Idona kawai zaka kalla ka karanta abinda yake k’asan raina na zallar farin ciki. Kasancewar lahadi ce na fita Parlorn Abba inda anan ake zama duk ranar lahadi a karya.
Tun daga tsakargida masu aiki suke bina da kallo har na isa parlorn. Su ma su Abba da mamaki suke kallo na ganin yanayin sauyin fuska a tare da ni ba kamar jiya ba da na tashi fuskar kamar hadarin kaji. Mamaki ya ishi Abba ya kasa shiru har sai da ya furta “Ayshan Mameeyn ta, ta samu ne naga kina wani farin ciki.” Sunne kaina na yi ina dariya da girgiza kai. Na mik’a masa kwalin wayar hannuna don na b’oye turarukan. Wayar ya bi da kallo yana furta “Wannan fa Aysha?” Cikin k’asa da murya ina kallon Mami da take min wani kallo na furta “Mutumin jiya ne ya ba ni.” Abba ya ‘dan ware ido yana furta “Ma sha Allah, labarin zuciya a tambayi fuska. Fateemah ya naga haka kuma? D’iyar take da alama ta yi na’am da zanka’de’den mijinta, ke tun baki tsaya kin ji waye ba kike kumfar bakin ba kwa son sa. Ustaz Ahmad Sulaiman Sa’eed babban Malamin nan, yaro da kwanyar manya shine fa yake son ta…” Cikin wani yanayi Mami ta ‘dago idonta tana furta “Ustaz!” Da mamaki a idonta, ta furzar da wani huci tana furta “Shine ma abinda ba zai yi wu ba cab’di! Kama sake nazari….”
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 9
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
“Kamar ya?” Abba ya furta yana saka k’wayar idonsa cikin ta Mami. Amma sam yau Mamin wannan kallon na Abba na da alama bai ratsa ta ba, don tab’e bakinta ta yi murya a sama ta furta “Kamar komai ma Abban Aysha.. Ta yaya za’a aura mat Uztaz hakan na nufin makarantar da na ci buri akanta ba zata yi ba kenan? Wani Ustaz ne zai bar matarsa tana yawo a titi fisabilillah, da ma wani d’an boko ne da sauk’i. Amma wannan ha’din sam bai ha’du ba, in dai za’a min adalci akan Aysha a tuna bani da wata da nake gani a matsayin y’ata a bar Aysha ta yi karatu…” Ta fa’da idanunta suna zubar da k’wallar da ta sanya duk jikina sanyi. Amma ban hango sanyin gwiwa a wajen Abba ba, kamar yarda na hango shi a wajen Umma, don a raunane ta ce “Abban Aysha ka yi hak’uri ka janye maganar auren nan….” wani kallo ha hurgawa Umman da ya sata shiru da bakinta tana kallon Mamin a raunace. “Ba zan janye ba, har abada kuwa, don ba zan ga samu naga rashi ba, wani irin solob’iyon Uba kuke so na zama? Allah ya kawowa y’ata nagartaccen Mijin da kowane Uba yake fata sai na masa butulci sabida wani karatun boko na banza da na wofi. Mutumin da ko y’ay’a d’ari yake so za’a ba shi a rana guda, duka ta tsallake ya ce Aysha ce ta masa Aysha yake son aure sai na zuba masa k’asa a ido, Saboda wata maganar banza da wofi. Ita ka’dai ce fa y’ata mace da nake fatan ta yi dace da Mijin k’warai.. ko yanzu yake so na tsame ta a boko na mata aure wallahil azeem na shiryawa haka, ba abinda kuma zai saka ni fasawa. Karatu dai idan ya ce zata yi a gidanta falillahil hamdihi idan ya hanata ma gaba d’aya wallahi ba zan tursasa shi ba. Saboda ku iyayen banza ne ku da zaku saka ta ta yarda ku rarrasheta ku ke sakata ta bijire min? To ku je ku yi na da ku a ga wanda zai ci riba…” Daga haka yaja bakinsa ya tsuke ya kuma wanke hannunsa ya tsoma cikin tuwo ya cigaba da ci. Fuskarsa a ha’de sosai alamar duk abinda ya fa’da har k’asan zuciyarsa hakan yake. Mami ta ture kwanon tuwon da muke ci ni da ita da Umma ta mik’e fuska a ha’de ta fice daga parlorn.
Jikina a sanyaye na mik’e zan bi ta Abba ya saka baki ya kira ni muryarsa a dake. “Dawo Ayshatu, zauna ki ci tuwonki, ba cutar da ke zan yi ba, har ga Allah alheri nake hango miki game da aurenki da Ahmad..” Na d’aga kai na ina wasa da zoben hannuna. “Ki kuma bu’de wayarki ki fara amfani da ita, na san ba zai cutar da ke ba. Ban kuma amince da duk wani tarkacen social media ba…” Na d’aga kaina don shima Ustaz garga’di da ya min kenan. Na san tunda suke ta jaddada min to social media d’in ba abu ba ne mai kyau. Cin tuwon kawai nake ba tare da ina fahimtar d’and’anonsa ba, don dai kada Abba ya yi magana ne na zage na ci tuwon kafin na mik’e cikin mutuwa jiki na haye sama. So nake na je naga Mami da halin da take ciki.
Jikina a sanyaye na murd’a k’ofar d’akinta don bata parlour kamar yarda ta saba zama. A saman gado na sameta hannayenta dafe da k’unci da alama ta yi zurfi cikin tunanin da take. Zama na yi daf da ita ina d’ora kaina a saman kafa’darta. Sai na ji ta saki ajiyar zuciya. Ta rungumoni sosai a jikinta tana furta “Aysha, yanzu kin amince d a auren da Abba zai miki?” K’asa na yi da kaina idona na zubar da k’walla. “Mami kema ki yi hak’uri please…” Janye jikinta ta yi tana sakin wani malalacin murmushi “Na yi hak’uri Aysha? Na yi hak’uri Ustaz ya cuceni ya raba ni da duk wani farin cikina? Ya kuma ruguza min da duk wani shirina a kan ki da na shekara da shekaru ina shiryawa?” Ta girgiza kai tana taune leb’enta ta furta “Wallahi bai isa ba, mu zuba ko ni ko shi?” K’asa na yi da kaina saboda ba zan iya sake cigaba da juriyar kallon idanun Mami ba, don wani abu nake gani a cikin idon… Zamewa ta yi ta kwanta tana mayar da numfashi idanunta a lumshe. “Tashi ki tafi AYSHA, ta shi ki wuce d’akinki…” Ta fa’da a zafafe da sauri kuwa na mik’e ba fice don ban saba ko na ce ban tab’a ganinta a irin wannan yanayin ba… na lura daf take da fara Aljannu…
Da safe har na shirya na gama shirin makaranta Mami bata tashi ba. Hakan yasa na nufi d’akinta ina nocking a hankali. A zafafe ta furta “Waye ne?” “Nice Mami…” ta bu’de k’ofar tana kallona idanunta kuwa da k’yar take lumshe su. Ta ja hannuna tana murzawa a hankali cikin wata irin murya ta furta “Ayshatu…” Na d’ago ina kallonta ta d’an sunkuyar da kai sai kuma ta saki hannun nawa. Tana sakin Malalacin murmushi ta furta “Har kin yi shirin makaranta?” Na d’aga mata kai “Ina kwana Mami?” Amsawa ta yi tana d’an ja baya ta furta “Wuce ki tafi AYSHA, ni ba abinda zaki ce min tunda kin zab’i farin cikin iyayenki a kaina. A jiya na yi takaicin rashin haihuwa da ni na haifeki da kaina na san ba zaki bujire min ba….” Kuka ne yazo min sosai ban san sanda na fa’da jikinta ba na saki wani irin kuka. Mami ta rungumeni sosai a jikinta ina jin yarda take sakin ajiyar zuciya. A kunne ta ra’da min “Kada ki bujire min Aysha, kada ki guje ni zan shiga wani hali AYSHA….” Da k’yar ta zame jikinta daga jikina ta juya bayanta tana furta “Je ki ki rufe min k’ofa…” Jikina a sanyaye na fice daga d’akin nata.
A kitchen na tarar da Umma na tana ta aikinta ita ka’dai. Sai na ji duk ban ji da’di ba don koda yaushe tare suke aikinsu da Mami. Da wayona dai ba zan tab’a cewa ga ranar da suka yi aiki ba tare ba. Kallo guda ta min ta d’auke kanta tana amsa gaisuwata. Na juya zan fice ta furta “Ba zaki k’arya ba ne?” “Umma na k’oshi…” Umma ta bi ni da kallo mai kama da harara tana furta “Ki yi ta k’oshin mana Aysha? Cikin wa? Kin zata ni d’in uwarki ce da zan ta bin ki ina lallab’aki, kin bi kin k’i ki kwantar da hankalinki balle na uwarki ya kwanta sai kace a kan ki aka fara auren early marriage, sanda Ubanki ya auro ni 15yrs nake, ban ma kai ki ba me ya same ni? Mahaifinki dai kaifi d’aya ne, ba mai saka shi ba mai hana shi don haka ki nutsu ki san abinda ki ke. Ban tab’a jin kan Fateemah da Abbanku sai a yanzu da take son ta bujire masa, me ye ribarki idan kin haddasa sab’ani a tsakaninsu? Na ce meye ribarki AYSHA?” Shiru na mata ina bulbular da hawaye. Me yasa Umma zata ga laifina ce mata na yi bana son Ustaz? Bata san nafi kowa son haka ba? Tashin hankalin Mami ne kawai bana so nake b’oye hakan a raina.. “wuce ki bani wuri, ki shirya bujire masa kece zaki wahala don kin san ko magagin mutuwa kike Ubanki sai ya sadaki da gidan mutumin nan…” Na ja k’afata na fice daga kitchen d’in zuciyata a k’untace ranar na isa makaranta.
Har na dawo daga makaranta ranar Mami bata mik’e daga saman gadonta ba. Ko kayan barcin bata cire ba. Na shiga na sameta na sanar da ita na dawo. Ta bi ni da kallo kafin ta saki ajiyar zuciya ta nuna min gefenta. “Zo AYSHA ki kwanta ki huta…” Ban k’i tayinta ba don ina buk’atar hakan na san kwanciya kusa da itan ne kawai zai saka na daina jin b’acin ran da nake ciki. Sau tari idan na saka jikina a jikinta ina samun nutsuwa idan ina cikin tashin hankali ko b’acin rai. Ta jawo ni na shiga jikin nata sosai. Hannu ta saka a bayana ta shafawa a hankali kamar yarda ta saba min. Muryata a k’asa sosai ta furta “Aysha me yasa kike son bujire min? Kada ki cuci kanki ki yi aure at your young age, zaki cuci kanki, zaki yi nadama nan gaba rayuwa ta canja. Ke ka’dai nake da hope a kanki AYSHA don Allah kada ki bujire min, ko me za’a miki kada ki amincewa auren Ustaz.. kin yarda.” Na d’aga kai sai naga ta saki ajiyar zuciya ta bani peck a kumatu tana sakin murmushi ta furta “Thanks my beautiful Baby, I love you..” Shiru na yi sai da ta d’an ja kumatu na ta furta “Ba zaki mayar min ba? Ko fushi kike da ni?” “I love you too Mamy..” na fa’da kamar yarda na saba fa’da koda yaushe idan ta furtar kalmar. Ta lumshe ido tana sake jana jikinta ta furta “Oya sleep…” zan yi magana ta furta “Shsssh!” A kunne na hakan yasa na lumshe idon dole. Take ni da Mamy barci ya d’auke mu. Barci da ba mu tashi farka wa ba sai da aka yi kiran sallahr la’asar. Na bu’de ido da sauri don na san tabbas yau na makara a makaranta. Mami bata san Ustaz yana koyarwa a makarantar mu don haka bata saka ido a kaina da zuwa makarantar ba. Ta bu’de idonta da k’yar tana kallona “Ya dai Aysha?” Na sauka daga gadon ina furta “An yi sallah Mamy, kuma zani Islamiyya.” Kanta ta rik’e a hankali tana d’aga min kai. Na fice da sauri.
A gaggauce na watsa ruwa na yi shirin Islamiyya na fito da sauri. A d’aki na samu Mami daga ita sai rigar wanka. Ta mudubi take kallona ta furta “Kin shirya Aysha?” Na d’aga mata kai. “Zo ku shafa min mai a baya na.” Na isa wajenta da d’an sauri na zuba nan a hannuna ta zame rigarta na fara shafa mata. Ban wani damu ba don na saba shafa mata d’in. Kuma Mami ba ta damuwa da suturce kanta koda ina wajen abinda ya danganci k’irjinta kam bata damu ta b’oyeshi ba. Tun ina jin kunya har na saba. “Ada lafiya ta fa’da tana mik’o min chocolates masu d’an yawa. Tana furta “Ki tabbata kin cika min alk’awarina Aysha, kada ki sake ki amince da auren Ustaz..”. Na amsa na fice da sauri..
Ina shiga makarantar na tabbatar Ustaz na nan don ga motarsa nan, gaba na ya fa’di don na san na makara ba ta wasa ba. Amma haka na d’aure na nufi ajin. Harabar makarantar shiru duk an yi sallah an koma aji. Zuciyata na bugawa na isa k’ofar ajin fuskata a ha’de don ya kamata na fara janyewa Ustaz don na cikawa Mami alk’awarinta, ya zama dole na mata halacci musamman ganin ita bata haihuwa kada zafin ya mata yawa…
Idanu y’an ajin suka zubo min, Har shi Ustaz d’in da ya tsayar da karatun da yake yana kallona. Na sake ha’de raina na nufi wajen zama na. “Aysha Imam Khaleel kin makara.” Ya fa’da cikin dakakkiyar muryarsa cak na tsaya ban k’arasa inda zan zauna d’in ba. Fuskata a ha’de na d’ago ina kallonsa. Ina ji kallon ne ya bashi mamaki. “Me yake damunki?” Juyawa na yi na fice kawai daga ajin. Ustaz na ji yana kiran “Aysha!” Na k’i na juyawa na koma saman step d’in na zauna kawai kaina a saman cinyata idanuna suna zubar da hawaye. “Tashi ki shiga aji.” Na ji muryarsa a kaina. Ban d’ago ba, ban kuma shiga ajin ba. “Ba kya ji ne Aysha?” Na d’ago a zafafe ina kallonsa na furta “Ni ba zan shiga ba, ka k’yale ni…” Cak ya tsaya yana kallona cikin narkakkun idanunsa ya furta “Ma Asabaki?” Wanda akan lab’b’ansa kawai na ji furucin. Ya lumshe idonsa ya furta “Tashi ki shiga..” Ba musu na mik’e jikina a sanyaye kamar zan shiga ajin sai na yi hanyar fita daga gate d’in. Ina ji Ustaz yana fa’din “Aysha tsaya…” Amma Ina na bawa banza ajiyar sa na fice har da d’an sauri na… Ina fita gate na juya naga Ustaz ya d’an rik’e kansa yana kallo na yana cije leb’ensa…..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://www.arewabooks.com/chapter?id=669e462086c5cb5aff79fe08
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 11
Runtse idonsa naga ya yi da sauri, kafin ya girgiza min kai, “Kada mu yi haka da ke Aysha, kada ki sakawa zuciyata ciwon da zai yi wahalar warkewa.” Sai naga ya durk’ushe a gabana idanunsa sun tara wata k’walla da ya k’ara idanun nasa kyau. Duk da akwai tazara a tsakani na da shi sosai ma, don na lura yana taka tsantsan k’warai da gaske wajen ganin ya kiyaye dokar Allah. “Ki taimaka min don Allah ki amince na aureki, ba yarda idan kin gama secondaryn sai Ai mana auren, duk da haka ma sai na yi k’ok’arin gaske kafin na iya daurewa, ni ka’dai na san me nake ji a kanki, ni na san irin yarda girman son ki yake a zuciyata, Please AYSHA will you marry me?” Runtse idona na yi ina jin yarda zuciyata ke matuk’ar gudu da tarin k’aunarsa a ciki, da gaske dauriya nima kawai nake da kuma son cika alk’awarin da na yiwa Mameey Amma ina ji a raina rashin Ustaz a rayuwata daidai yake da rasa rayuwar tawa. “Ki amsa min AYSHA, please za ki aure ni?” Wallahi ban san sanda na d’aga kai ba, Saboda wani irin kallo mai azababben kyau da Ustaz ya dinga zuba min da narkakkun idonsa. Gani ya yi ya dunk’ule hannunsa duka biyun yana sakin ajiyar zuciya ya furta “Shukran ya Rabbi, Shukran ilaiki Ayshata…”
Ya mik’e yana sake kallon Table bayan ya ajiye wata leda a kusa da ni. Ya furta “Yau ma AYSHA ko ruwa babu?” Sai kunya ta kama ni na yi k’asa da kai na, ina wasa da zoben hannuna. Murmushi mai sauti ya saki. “Shikkenan tunda rowa kike min, na gode..” ya yi furucin da karyayyiyar murya. Da sauri na