Showing 9001 words to 12000 words out of 44853 words
da zamu yi sai naga fik’hu ce. A rayuwata ina kunyar Ustaz shi yasa sam ba zan iya zama ya karanta Fik’hun a gaba na ba, kada a yi irin ta ranar da muka karanta Babul janabati… Don haka yau ina duba littafin naga za’a yi bayani ne akan ruwa kashi uku da yake fitowa daga gaban mace na ji sam ba zan iya zuwa ba. Sanda Asma ta biyo min ta shiga d’akina tana kallona ta furta “AYSHA me ye haka?” Nima kallon nata na yi nace “Me kika gani?” Ta saki tsaki tana kallon agogo “Yau kuma wani sabon abu zaki tsiro da shi, makara? Abinda ba halinki ba. Kin san dai Ustaz Ahmad ya jaddada rashin son makara ko?” D’an yamutsa fuska na yi “Ke makarantar ce fa ba zani ba.” Ta waro ido “Dalili?” “Bana jin da’di ko na je ba fuskantar karatun zan yi ba. Ki ba shi uziri na.” Asma ta ‘d’au jakarta tana furta “Allah ya baki lafiya, amma kamar ciwon naki bai kai inda ba za’a iya zuwa makaranta ba..” Ban mata magana ba har ta fice daga d’akin. Na saki ajiyar zuciya duk ina son zuwa makarantar ko don naga Ustaz wannan karatun da zai yi yau ne zai hana ni zuwa. Allah ya san ba zan iya zama yana zayyano min karatun nan me saka kunya ba…
Kashegari da wuri na shirya musamman ganin maddar Hadith da Tajweed ne da mu. Asma ta biyu muka tafi..
Ajin har ya cika y’an mata sai baza k’amshi suke. Muka shiga muma muka bi ayari muka zauna. Ina ji wata sanda Ustaz ya shigo k’asa k’asa ta saki ajiyar zuciya “Wallahi Zahra mutumin nan ya gama sace zuciyata..” Zahran ta harareta tana furta “Ke ka’dai? Ai kowa nan da kike gani yana fatan ya taya shi…” Wani abu ne ya tsaya min a zuciyata. Na d’aga idona na kai duba na gare shi duk da idona a cikin nik’ab yake ina kallon yarda ya tsuke fuskarsa ya shigo ya ja kujera ya zauna. Fuskar a yamutse ya furta “Kada na sake ganin wata da kwalliya a fuska a ajin nan ba gidan biki za ku ba, kuna jina? Wannan wace irin tarbiyya ce zaku zo Islamiyya ku wani fece kwalliya wa kuke son burgewa?” Gaba d’aya masu kwalliyar k’asa suka yi da kansu na san kunya ce ta rufe su. Wani farin ciki ya rufe ni a raina na ce don ma baka ji k’amshin turarukan da suke ba. Na cije leb’e na ina furta “Marasa aji kawai, ni ko sonsa zai kashe ni Ai ba zan bari ya gane ba…” “AYSHA Imam Khaleel…” Ya fa’da cikin muryarsa da ta ratsa kunnuwan duk y’an ajin. Ni kuwa tunani na tafi na wuncin gadi ina ganin kamar ba sunana ya kira ba. “Ba kya ji ne AYSHA?” Ya fa’da wannan karan da alamar fushi a muryar.. da sauri na mik’e jikina har shaking yake ka’dan. “Me ya hanaki zuwa jiya? Don ban yarda da uzirin da k’awarki ta bayar ba…” Shiru na yi ina wasa da yatsuna.. “Cire abin fuskarki, kada kuma ki sake zama min da shi a aji…” Na d’age nik’ab d’in idanuwa na na son kawo ruwa. Na yi k’asa da kai na… “Bana jin da’di ne..” na furta muryarta na rawa.. kallona yake sosai kafin ya saki wani d’an banzan murmushi ya furta “Ko?” Na d’aga kai na ina kallonsa ya tsuke fuska. “Bayan an idar da sallah ki tabbata kin samu wata ta miki karatun jiya, ki zo office ki same ni zan miki tambaya akan karatun don na tabbatar kin gane bana son tafiyar kura….” Da sauri na furta “Ai na iya, bama sai ka tambayeni ba…” Kallona ya sake yi yana girgiza kai ha’de da murmushi ya furta “Jayyeed, na san kin iya k’wararriya ina son na tabbatar da iyawar ne kamar yarda na tabbatar da na abokan karatun ki…” Yarda kika san na zunduma ihu haka na ji, wani irin mutum ne wannan.. “Malam ka tambayeta mana anan…” wat daga d’aliban ta yi tsagal ta fa’da. Da alama ko haushi ta ji. Kallon Maryam ya yi idonsa cikin nata ya furta “Idan na k’i fa? Maddar Hadith d’in kike so na bari na koma fik’hu. Ko kuwa ma Am I talking to you?” Shiru ta yi tana k’ikkifta ido… da alama ta ji haushin disgin da ya yi mata. “As I told you earlier, ki tabbata kin zo after asr, kuma ina son ki gudu kin ji…” ya fa’da yana d’aukar littafinsa…
Tsit ajin ya yi, ni kuma na zauna ina sauke numfashi. Na sake mayar da nik’ab d’ina. K’afata kuma a d’an mik’e a wajen. Ni da kaina na san ina da kyan k’afa sosai, amma ban damu da rufeta kamar fuskata ba. Yana d’agowa ya kalleni. “How many times zan gaya miki ki cire k’yallen nan a fuskarki.. kin san bonono?” Na yi saurin girgiza kai “To shi kike yi, rufin k’ofa da b’arawo ba. Wannan da kike bari a waje ita yafi kamata ki rufe, don ana ake gane a wani aji mace take.” Ya fa’da yana nuna k’afata. “Duk namijin da ya san abinda yake idan zai so mace k’afarta yake fara dubawa saboda akwai wani karatu na musamman akan k’afar…” Da sauri na ja k’afata na cukuikuye tun kafin na ji ma menene karatun. Murmushi ya yi ya girgiza kai ya kalli y’an ajin “Kuna son ku sani?” Da wani irin ihu da farin ciki suka furta Eeh Malam. Ji na yi kamar na tashi na rufe su da duka. “Ta hanyar k’afa ake gane Mace Khareeja ce ko Mutawassi’da ko Dakhilatun… kun san ma’anarsu?” Cikin karsashi suka furta “A’a” musamman manyan ajin da suna son irin wannan karatun. Na san sun sani don suna ta k’us k’us da murya suna dariya. “Mace Kharija itace mai yawan sha’awa….” Runtse idona na yi ina sake jan nik’ab d’ina. “Baki ji warning d’ina ba kenan?” Hawaye ne kawai na ji suna cika min ido ganin yarda ya tsira min ido cikin wani irin narkakken kallo da na kasa fassara shi. “A k’afafunku yanzu kowacce zan iya gaya mata ajin da take..” Ya fa’da yana d’an ha’de ransa… Da sauri kuwa suka dinga tura k’afafunsu ni da Asma da wasu biyu ne kawai ba mu tura ba. Ya dinga kallonsu yana tab’e baki ya furta “Kunya itace cikar mutuncin y’a mace ku dinga koyi da d’abi’ar y’an uwanku…” Ya fa’da yana nuna mu. Sannan ya sha kunu ya cigaba da karatun sa na Hadith.
A k’aida idan aka fita sallah, sai duk y’an aji sun fita sannan Malam zai fita. Haka kowa ya mik’e amma ni na kasa mik’ewa sai mutsu-mutsu nake a Hijba bana son tashi ne don kada Ustaz yaga k’afata. Ina kallon yarda yake dariya k’asa k’asa. “AYSHA tashi ki fita sallah.. ko kina Off?” Waro ido na yi na yi saurin sakin Nik’ab d’ina, ina martaba rashin kunyar ustaz a cikin zuciyata. “Jira fa nake ki tashi ki fita..” Asma da ta ga ban fita ba ita ta sake dawowa tana kallona. “AYSHA taso mana.” Na yafito ta da hannu. Ra’da na mata. “Pls ki samo min safa ko a k’afar waye don Allah..” Asma ta k’unshe dariyar da take son yi ta fita tana kallon ustaz. “Me kike ce mata? Ko kina needing wani abu ne?” Na yi saurin girgiza kai. Zama ya yi yana danna wayarsa har sanda Asma ta dawo ta mik’a min sucks d’in. Na yi saurin amsa na dinga zira wa ta cikin Hijab d’ina. Ina kallon yarda Ustaz yake min wani kallo… Sai kuma girgiza kai ya fita..” Na sauke ajiyar zuciya. Asma ta zauna kusa da ni tana furta “Kamar Ustaz fa ya fa’da son ki..” Ban amsa mata ba saboda kiran sallah na ik’ama da aka yi. Muka fita da sauri.
Ana idar da sallah ina zaune a harabar makarantar muna
Jiran yara su gama shigewa. Wata yarinya tazo tana kallona. “Anty Aysha, Ustaz Ahmad yana kira…” waro ido na yi ina kallon Asma da take ta dariya na harareta na ce “Don Allah ki raka ni?” “Wa? Ni? Ai idan kika gan ni a lahira kai ni aka yi.
Me ya aikeki fashin makaranta jiya? Ga shi nan abinda kika gujewa shi kika tarar yau har Gwara ma jiya a cikin mutane ne, yau fa daga ke sai shi…”
Ban manta magana ba saboda haushi da ta bani. Na tashi cikin sanyin jiki da na zuciya na bi step d’in da zai kai ka Office d’in Ustaz Ahmad. Duk da ban
Tab’a shiga ba na san nan ne, don ina jin yarda y’an mata ke wassafa kyau da tsaruwar office d’in. Sai da ya saka aka kashe masa ku’di sosai kafin ya fara zama cikinsa.
Knocking na yi sosai kafin daga can a ce “Shigo kafin ki saka min ciwon kai.” Zuciyata na bugu na mur’da handle d’in k’ofar na shiga. Shiru office d’in sai wani irin azababben sanyi da k’amshin turarensa da ya zauna ra’dam a office d’i.
K’ofar na bari a bu’de, sai dai tun kafin na kai ga zama ya furta “Ita k’ofar zata rufe kanta kenan?” Tsaye na yi ina wasa da yatsuna don kam ba zan wani kulle k’ofa ba, a haka ma ji nake kamar zuciyata zata fito don tsabar tsoro. Bai kulani ba ya mik’e ya isa k’ofar ya rufe ya dawo ya zauna. Yana d’aukar cup d’in Hot coffee d’insa idanunsa akai na dana kasa zama sai rawa k’afata take. Tsawon mintuna biyu yana shan tea d’insa ya lumshe ido ni kuma ina tsaye… “Na gama ganin surarki idan ita kike son ki nuna min sai ki zauna Ai…” Ban san sanda na zauna ba.. Ina haki kamar wacce ta yi gudu tsabar firgicin da maganarsa ta saka ni. A yanayin fuskarsa naga yarda yake ha’diye dariyar da yake son yi. “Mun yi karatu jiya, akan ruwa uku da suke zubowa daga gaban mace, sababinsu da hukuncinsu Islamically.. su nake son yanzu ki jero min ki kuma gaya min me
Ke sabbabasu da hukuncinsu a musulunce tunda kin ce kin sani…” “Cabd’i…” na furta a hankali ina jin wani irin bugu da zuciyata take yi… wayarsa ya ‘d’auka ya danna yana furta “Ina jin ki, ina son in san da gaske kin iya orally kafin lokacin da zan sani a aikace…..”
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢✍️
https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR
Group 1 ya cika. Ga wanda bai samu damar shiga ba ya danna link d’in nan ya shiga group 2 daga gobe In sha Allah a iya groups d’in zan dinga posting. Kada a dinga bina private ana na bayar daga farko. Allah ya sani bani da jumurin hakan…
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 7.
Duum haka na ji maganar Ustaz ta min saukar bazata a kunnena. Na sunkuyar da kaina ina mamakin yarda shi Sam ba ya Jin kunyar fa’dar duk abinda ke bakinsa. “Ina Jin ki…” Ya fa’da yana sake sanya idanunsa cikin nawa. Muryata na rawa na furta “I can’t..” kafin na yi aune hawaye ya fara zubowa a fuskata don har ga Allah ya fara takura min. Shi bai san duk sanda ya rutsa ni ba, Wani irin yanayi nake shiga mai wuyar kwatance… “Kuka ki ke? Daga tambaya?” Ya furta muryarsa a k’asa sosai. Na sake runtse idona na k’ara k’arfin kukan nawa. “Ki min shiru.. tunda ba amsa just wipe your tears..” ya fa’da yana mik’a min handky d’insa. Amsa na yi na shiga goge idon nawa amma hawayen still basu tsaya ba. “Ki tsayar da hawayen nan yanzun nan bana son shagwab’a. Me aka miki daga cewa ki yi karatu..” Ya furta a hankali cikin wani husky voice da zan iya cewa yana sane yake min magana da ita.. “Zan gaya miki Laa Haya’u fiddeeni, idan baki tsaya kin koya ba ta ina zaki iya? Ko ni ne ba kya son na koya miki?” Da sauri na d’aga kai, murmushi ya saki mai kyan gaske.. yana furta “Why?” Yana shigar da idonsa cikin nawa “Gaya min dalili sai na k’yaleki..” Shiru na masa idona a k’asa ina cigaba da wasa da handky d’in hannunsa.. ina ji ya saki ajiyar zuciya bayan ya gama k’are min kallo tas, don a jikina na ji ni yake kallo… “Dole zai fito muku a exam don haka dole ki saurareni na miki gamsashshen bayani. Kuma bana son ki rufe min ido. Ki tsaya ki kalleni kamar yarda kowace d’aliba take sauraran malaminta idan yana mata karatu. Tunda ni ba saurayinki ba ne, balle ki ce kina jin kunyata…..AYSHA..” Na d’ago da niyyar kallon nasa sai dai sam idanuna sun kasa ba ni dama. “Kalleni ki saurareni..” Na girgiza kai “Don Allah Ustaz ka yi hak’uri zan je Asma ta koya min, inda ban gane ba..” ta gefen ido naga ya tab’e baki. “Ban yarda ba Aysha, na Riga na d’au alk’awari zan karantar da ku don haka dolena ne na yi miki yarda na yiwa kowa..” “To ka ha’da ni da wani Malamin.” Na furta muryata na rawa. “Saboda ni surikin ki ne? Ko saurayin ki?. Ruwa uku ne yake fitowa daga al’aura akwai Maniyyi, akwai wadiyyi akwai maziyyi kina ji na? Maniyyi shine ruwan da yake fitowa mutum yayin babbar sha’awa, saduwar aure wato jima’i….” Ban san sanda na kai kaina bakin k’ofa ba, na fice da sauri don na lura Ustaz so yake kawai ya kashe ni da salonsa. Saboda wani irin abu da na dinga ji a jikina. Ina ji yana k’wala min kira amma na k’i komawa na shige wani lungu ina mayar da haki. Ina goge hawayena da handky d’insa da ya cika da k’amshin turarensa sai sannan ma na lura da handkerchief d’in. Na cusa shi cikin aljihun hijab d’ina ina mayar da haki. In dai zan shiga aji a haka dole ne ma a fuskanci bana cikin nutsuwa don haka kawai na fice daga makarantar don ba zan iya sake ha’da ido da Ustaz ba, a dai ranar yau…
Ina zuwa gida d’aki kawai na shige ba tare da na bari su Mami da suke kitchen su ganni ba. Na shige toilet saboda wani irin fitsari da na ji ya matseni. Ban yi mamakin ganin discharge mai yawan gaske a undies d’ina ba. Kwanciya na yi saman gadon ina sakin haki tare da shak’ar k’amshin Ustaz da yake jikin Handky d’in. Murmushi nake saki ni ka’dai ina tuna drammerr da muka sha da Ustaz d’in. Gwara ya dokeni akan na zauna yana min wannan karatun nasa… na raya a zuciyata.
A kwancen nake har 6:30. Daidai lokacin da na ji shigowar Mami da Asma. Tana fa’din “Wani irin ta taho gida, ni ban ganta ba amma bari na duba d’akinta.” Turus ta yi tana kallona “Ke lafiyarki kika taho daga Islamiyya tun kafin a tashi.” Lumshe idona da ya yi nauyi na yi na furta “‘Mami bana jin da’di ne.” Ta saki ranta tana kallon Asma da take tsaye da Jakata a hannu. “Shine zaki shigo d’aki ki kwanta? Anan wa ya san baki da lafiya?” Ta yi tsaki tana ficewa daga d’akin “Dama ki taso ki sha magani yanzunnan, don na san rashin son magani ne yasa kika k’ulle kanki a d’aki.” Asma Mami na fita ta tuntsire da dariya “Daga zuwa wajen Ustaz kuma sai ki gudo gida.. ko ya fasa miki sirrin zuciyarsa ne?” Na wurga mata harara “Mhmn” ta furta tana zama gefen gadon “Ni sai na ji ma d’akin kamar k’amshin ustaz d’in yake..” Da sauri na danne handky d’insa da k’afata ina furta “A’a Ustaz d’in ne na b’oye ba k’amshinsa ba, y’ar rainin hankali kawai…” “Zaki ga y’ar rainin hankali, Dama ya ce na gaya miki gobe kada yaga k’afarki cikin ajinsa..” “Ta fi Nono fari wallahi, Sai na canja aji..” Asma ta tsira min ido tana furta “Ke ce zaki iya barin Ibn kaseer? Ki dai ba shi hak’uri kawai ki koma. Wai me ya miki?” Zama na yi na bata labari ta dinga tuntsira dariya tana kifawa ta furta “Wallahi Aysha mutumin nan sonki yake, shi kuma tasa salon soyayyar kenan, kan bala’i Amma fa ya burgeni…” kallo na watsa mata ina nuna mata k’ofa. “Maza ki ta surutu Mami ta ji ta tsireni, ni ba wani so na da yake.. kawai dai ya lura ina jin kunyarsa ne..” “Kema aI sonsa kike tunda kina jin kunyar ya miki irin wannan karatun…” Ta furta tana dariya duka na kai mata ina jan hannunta na furta “Fice min daga d’aki Malama..” Ta fita tana furta “Ko baki ce ba, amma wallahi kun dace wai! Ai kuwa zuciyar y’an matan ajin nan zata buga don yau ma baki ji zagin da kika sha ba, da kika bi shi office..” Na tab’e bakina ina furta “Y’an wahala, su suka ga zasu iya. Don Allah Asma tafi gida kawai..” ta fita tana murmushi.. Na zauna ina nawa murmushin nima. Ina ma ya furta yana so na da nafi kowace mace sa’a…
Kashegari ma k’in zuwa makarantar na yi na fake da bani da lafiya don sam ban ji zan iya zuwa na kalleshi ba. Tsawon kwana uku ina k’aryar ciwo kullum Asma ta dawo sai ta biyo gida ta koya min abinda aka yi. Ranar laraba ta shigo d’akina tana murmushi ta ce “Aysha yau fa Ustaz ya kasa dauriya, sai da ya tambayeni ina kike bayan ya kira ni office d’insa. Na ce masa baki da lafiya baki ga murmushin da ya saki ba na irin na raina masa hankali ya furta “Ki gaya mata ranar asabar ta dawo makaranta…” Murmushi kawai na saki na ce “Allah ya kai mu. Asma ta fita tana furta “Ke mutumin nan da gaske ya faller kawai furtawa ne bai yi ba..” samun kai na na yi da sakin murmushin nima ina furta “Allah yasa.
Kashegari ya kasance ranar alhamis ce, na tashi da wuri na yi shirin makaranta don Exams zamu fara third term SS 2.
A gaggauce na sauko daga sama ganin lokaci ya ja. Na isa kitchen wajen Umma da Mami