Showing 39001 words to 42000 words out of 44853 words
furucin a hankali sai ji na yi kawai ta burkito ni jikinta a hankali ta saka hannunta a gefen cikina ta min cakulkuli da sauri na bu’de idon ina d’an ja jikina ba furta “Kai Mammy, am not that young fa…” Sake janyo ni ta yi jikinta tana ha’da fuskata da tata ta furta “You are still my little Aysha, har yanzu kallon Babyn Mameey nake miki. Sau tari raina ne yake b’aci bana son kusancinki da Ustaz wallahi ina jin haushin hakan sosai a raina. A yanzu ba zan k’i ki auri wani ba ki bar Ustaz ba don komai ba sai don na san zai yi tsauri zai kuma takura miki zamantowarsa Malami, ba zai bari ki mori rayuwarki ba, balle….” Sai naga ta ciji leb’en bakinta na k’asa ta yi shiru bata k’arasa ba. Ta d’an girgiza kai sai naga ta ja pillow kawai ta kwanta ta furta “A dole za’a raba mu abinda bana so, ba yarda zan yi ne, shi yasa nake so mu dinga kwana tare ina jin ki kusa da ni, don na san wata rana ba zan samu damar hakan ba….” Kafin na yi wani yunk’uri naji Mami ta kwanta daf da ni sosai tana sakin ajiyar zuciya… ni dai a ‘darare na yi barci a ranar da mamakin wasu daga halayyar Mamin…
Bayan kwana biyu da faruwar hakan aka ce za’a kawo lefe don haka ranar da wuri na shirya duk raina ba da’di musamman takura ni da Mami take yi na kwana a d’akina ko nata ko itace da girki sau tari sai ta dawo don kawai ta hanani waya da Ustaz. Waya kam sai a sace nake yi da shi.
K’asa na sauka cikin shigar doguwar Rigar abaya da na na’de kaina da mayafinta, na saka nik’ab kuma. Mami da Umma na gani a kitchen sai masu aikin mu suna ta hidimar ha’da abubuwan da za’a tarbi bak’i da su. Bayan gaishesu Umma naga ta zuba min ido kafin ta juya wajen Mami ta ce “Fateemah, wani abu ke damun y’ar taki naga tayi wata Uban rama? Ko dai duk tunanin auren ne?”
Mami ta d’an tab’e baki tana kallon Umma ta furta “Me kike tsammani daga yarinya kamarta da za’a mata aure a k’ananun shekaru, ba dole ta yi tunani ba tunda ta san abinda zata tarar gidan Mijin ba mai sauk’i ba ne…” Umma d’auke kanta ta yi tana furta “Allah ya kyauta, aure ne fa ba rayuwar azaba ba, menene na sakawa kai tunanin? Sanda aka yi aurena shekaru sha biyar gareni kuma ba abinda ya same ni, ku san dai na yi gaskiya ko Sabaya ki fara d’irka mata gaskiya… don ramar ta yi yawa.”
Mami ta tab’e baki ta furta “Idan taje gidan Mijin, ta fara samun abinda kuke so ta samu Ai zata ciko. Zo ki wuce AYSHA kafin mutane su zo su tarar da ke, ki gaida Aseeyar sai kuma yamma zaki dawo. Driver na nan a waje ya sauke ki.” Na d’aga kaina ina fita daga kitchen d’in. Bayan na sake kallon Umma da ta zubo min ido…
A waje na tarar da Asma don tare zamu tafi. Driver ya taso don ya kai mu, na girgiza masa kaina “Bar shi ma Baba, Ustaz zai kai mu, amma don Allah kada ka gayawa Mami na.” Murmushi ya yi ya d’aga kai jin abinda na ce. Da sauri na ja hannun Asma muka fice don Ustaz ya isheni da kiran waya. Muna isa kuwa ya wurga min harara gaisuwata ma bai amsa ba sai ta Asma. Ban wani damu ba don na san laifukan da na yiwa Ustaz a lokutan nan ba zasu lissafu ba. A hanya Asma ta masa zancen zamu je fitar da anko. Ji nayi yana furta “Waye zai je kasuwar? Ba dai AYSHA ba wallahi gwara na rasa miliyoyin naira da na barta ta shiga kasuwa ku fa’di colorn da kuke so da adadin ku zan saka a kawo muku.” Asma murmushi ta yi ta kuma furta “Mun gode Allah ya k’ara arziki.”
Muka gama tsara bikinmu da y’ay’an Anty Aseeya k’anwar Mami, kafin Ustaz ya sake dawowa d’aukar mu. Sanda muka isa gida Asma tana fita ya saka hannunsa ya rik’e hannuna. Tsawon minti guda yana murza hannun kafin ya ware idonsa a kaina. “Me yasa ba kya amsa wayata da daddare?” Muryata a hankali na furta “Barci Ustazuna barci ne ke hana ni sak’at.” Ya cije leb’ensa yana narkar da idonsa cikin nawa ya furta “Ki yi barci ki more AYSHA, gwara ki yi barcin yanzu don ina tabbatar miki ranar first night d’inmu ba barci till down zamu yi mai zafin gaske….” Da sauri na lumshe ido na. Ya saki hannun yana furta “Good night, abinda bai yi ba a lefe feel free ki gaya min.” Na girgiza kai na ina furta “Na san Ustazu na ya iya zab’e zan kuma yi farin ciki da dukkan abinda ya fito daga hannunka.” “Jikina fa?” Ya furta yana d’aga gira da sakin murmushi… da sauri na fice ina furta “Har jikin…” Sai naga ya waro ido ya buso min iska alamar kiss yana sakin murmushi ya furta “I love you till my last breath…” na shige gida cikin wani irin zallar farin ciki.
Tun a gate Asma ta wani rungumeni tana furta AYSHA ke mai sa’a ce kin ga lefenki kuwa?” Murmushi kawai na saki wata kunya na sake baibayeni wai ni Aysha yau ake zancen aure na a gidanmu. A parlorn Abba na tarar da su da yake na san lefen suke kalla hakan ya saka ni guduwa sama don har ga Allah ba zan iya zaman kallon lefen ba…
Da daddare Mami ta shigo still yau ma cikin shigar wata shegiyar rigar barci sai zabga k’amshin turare take. Gashinta a sake sai baza k’amshi yake da alama ta yi gabbasar gashi. Glass cup ne a hannunta mai d’auke da madara ta zauna a gefen gadon ta mik’a min cup d’in. “Tashi ki sha AYSHA.” Na karb’a na kafa kai na shanye. Mami ta zuban ido tana saki wani malalacin murmushi ta furta “Yau zan sanar da ke abinda baki sani ba Aysha Zan koya miki yarda zaki mallaki Ustaz in a romantic way…. “ Dishi dishi na dinga gani a idona na fara kallon Mami bibbiyu da duk abinda take furtawa yana shiga kunne na kafin na ga ta saka hannu ta baje gashin kanta ta ‘dago tana min wani kallo…..
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️😉
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA…….20.
Gaskiya ku min kara, ku yi dandazo ku nuna wa Littafin mu ja Bright pens na Aysha Cool. K’arfe a wuta….. soyayya wacce zata girgiza media… a fito a siyi k’arfe a wuta ko na yi yajin aikin rubutu na sati guda 😒 yauwa eeehe.
Don samun littafin kai tsaye ka tuntub’i AYSHA COOL MARUBUCIYAR K’ANWAR MAZA. Kowa dai ya san yarda labarin ya kara’de Media.. tuna da sunan K’ARFE A WUTA.
I dedicated this page to my lovely sis Nimcyluv. “Saboda sonki da littafin Na ga rayuwa na mallaka miki wannan page d’in. Really appreciated 🥰.
Masu bina private kan na mayar da shi na ku’di saboda na dinga musu posting 2 times a day. Ku yi hak’uri Na ga rayuwa dai kyauta na bada shi don haka In sha Allah zamu gama cikin nasara idan ku'din ne ya muku yawa ku siyi books 'dinmu na Bright pens. 🤗
_____________
Cikin lumsassun idona nake kallon abubuwanda Mamin take min a sunan tana koya min yarda zan mallaki zuciyar Ustaz. Har k’afata ta ja a hankali tana matsawa cikin wani salo. “Hakan da nake miki Aysha shine romantic tausa kuma haka ake son ki yiwa Mijinki, ba kunya tsakanin Miji da Mata ki zage ki nemi zuciyar Mijinki ko ta wani hali….” Wasu abubuwan daga baya sam kasa fahintar su nayi, sabida wani irin barci da ya dinga fisgata k’arshe dai ban san ya aka yi ba sai wayar gari nayi naga asuba ta yi. Har gari ya fara haske. Na juya Babu Mami a d’akin idona na lumshe duk abinda ya faru a daren ranar ya shiga dawo min daki-daki. Ajiyar zuciya na sauke kafin na mik’ na shiga toilet don abin na Mami ya girmi kwanyata.
Da yake na san alhamis ce ban wani damu da neman abin kari ba. Still bayan naje ba gaishesu barcin na ji ina sake ji don haka na koma d’aki kawai na sake kwanciya. Daga ranar ya zama kullum Mami sai ta bani wannan madarar na sha da daddare ina sha kuma barci mai nauyin gaske zai d’auke ni ba zan farka ba sai asubahi. A haka kwanakin bikin suka dinga matsawa na dinga zuba wani kyau ga k’irjina ya cika k’ugu na ma haka na yi k’iba ta ban mamaki. Don bana manta wata rana muna zaune a parlorn Abba ana auna ni d’inkin da za’a min wata k’wararriyar tela da ta yi shuhura a ‘dinkin Amare cike da mamaki Umma yake kallo na ta ce “Fateema kin ga yarda AYSHA ta cika ta yi k’iba kuwa kamar ma har ta tare a gidan Mijin? Ko dai har kun fara shan sabayar?” Mami murmushi kawai ta yi ta ‘d’auke kanta tana kallona k’asa k’asa.
Da yamma kuwa ina dawowa daga Islamiyya na shiga parlorn Mamin sai naga ta yi bak’i wasu manyan mata, da kana ganinsu kaga y’an duniya… Sak na yi ina kallonsu a zaune sun ci matsatstsun kaya dole na yi mamaki don ban saba ganin irin su ba a gidanmu. Gaba d’aya k’irjinsu a waje yake, sun baza gashi ga sark’a a k’afarsu. Mami na gani na ta tsuke fuska, k’ok’arin Gaishesu na yi amma sai ta dakatar da ni. “AYSHA sauka k’asa wajen Umma na gama da bak’i tukun.” Sak na yi na juya sai na ji d’aya a cikinsu tana furta “Ma sha Allah, Fateema wannan yarinyar fa komai ya ji akwai kaya gaskiya…” “Ita nake baku labari…” Shine kawai abinda naji. Na sauka k’asa jikina a sanyaye saboda mamakin abinda Mami ta ce na yi. Bata tab’a ce min na sauka k’asa don na yi bak’i ba, sai yau bak’in ma irin wa’dannan marasa kamun kai.
Parlorn Umma na shiga sai na sameta tana waya. Da ido ta bi ni da kallo har na zauna a kujerar da take kusa da ita. Sai da ta gama wayar ta juyo tana kallona ta furta “Ke AYSHA lafiya? Naga kin shigo sukuku da ke.” Girgiza mata kai na yi “Bakomai, Mami ce ta ce nazo nan saboda ta yi bak’i.” “Ki zo nan?” Umman ta furta cikin mamaki don itama abin da bata saba gani ba ne. Na d’aga kaina a hankali. Sai naga taja ajiyar zuciya ta ce “Tashi ki je kitchen maza cikin fridge ki d’auko min wasu jarkoki guda uku suna nan. Ki ha’do da cup.” Na mik’e na shiga kitchen d’in Umman da yake cikin parlornta. D’auko biyu na yi saboda da d’an girmansu kafin na koma na d’auko d’aya da cup. Umma ta bu’de ta farkon ta zuba Rabin cup ta mik’o min “Karb’i ki sha, ba kuma wai don da’di ake shan irin wannan kayan ba don na san ki da shegen kwa’dayi.” Na runtse idona na shanye. Ta sake zuba min na sauran gororin tana furta “Kullum ki dinga zuwa cikin fridge kina bu’desu ki sha, Ko Mamin naki na baki?” Na girgiza kai bata bani komai. Na so gaya mata sai madarar da take bani duk dare da take saka ni barci sai dai na kasa. Ina kallo ta d’an cije leb’enta ta furta “Ai shikkenan, da ni da ita duk d’aya ne, ki dage sosai wajen shan su, akwai wasu ma da zan saka a kawo miki duk da dai na san ko da wannan kika tsaya kin fita zarra Magungunan Anty Surayya mai Bojuwa herbals ba k’arya ba ne, suna da amfani k’warai a jikin mutum. Zan kuma baki numberr wayarta don ki dinga tuntub’arta don samun ingantattun magani na gyaran zamantakewar aure…. Ta mik’e sai gata ta dawo da wata roba. Zuba y’an k’wayoyin maganin ta yi a hannunta ta ha’da min da dabino tace na taune. Sauran kazar sababi tace a satinnan zata kawo miki. Na san komai don haka kunya ta kamani don ina karatun litattafai saboda haka na san magungunan da Umman ta bani da dalilin ba ni su. Da Mami ce ba zan ji kunyarta ba kamar Umman don ita Umma sam bata saki jiki da ni ba. “Gyaran jiki dai ba kya buk’atarsa don fatar ki mai kyau ce ba abinda kike buk’ata, sai zuwa saloon a miki predicure da manicure zuwa jibi ki shirya ki je.” Na d’aga mata kai. Daga haka ta mik’e ta shige kitchen na san ba kunya ce ta saka ta barin wajen. Na d’an saki murmushi kawai ina jin soyayyar Umman da wani irin tausayinta a raina. Ni kenan y’arta mace amma ta iya kyauta da ni ta kuma d’auke kanta a kaina. Lallai Umma ta cika fulanin k’warai masu kunya kara da d’auke kai.
Sai dare sannan bak’i Mami suka tafi. Ina shiga parlorn naga sun yi kaca kaca da shi. Tab’e baki nayi na shige mai aikin da take gyarawa.
Wata litinin abubuwan suka fara faruwa tsakanina da Ustaz, litinin d’in ana saura kwana hu’du a fara bikin. Na san anan yake shan ruwa in dai ya yi azimi. Shirin bikin bai hanani tashi na fara shirya masa abin shan ruwa ba, duk da yinin
Ranar sam bai kira ni ba. Nima kuma na shiga busy shi yasa ban kira shi ba. Azimin ne nima a bakina, amma haka na daure na fara shirin yi masa abin bu’de baki. Kunun kwakwa nake son masa, rashin ganin flavour ya saka ni fitowa daga kitchen d’in zuwa d’akin Mami. A bakin k’ofa na tsaya ganin ba Riga a jikinta tana shafa mai. “Shigo” na ji ta ce. Kamar ba zan shiga ba sai kuma na shiga kaina a k’asa. Tsaki ta zabga tana furta “wani munafuncin kuma kika tsuro da shi na tsayawa a bakin k’ofa?” Girgiza kai na nayi na ce “Aa naga kina saka kaya ne..” ta d’an yi tsaki kafin ta ja towel ta rufe k’irjinta “Yau kika saba gani na ba riga?” Na girgiza kai. “Flavour nake so Mami zan saka a kunun kwakwa..” na furta don son barin d’akin. “Yana gidan Uban Ahmad…” Mami ta furta cikin wata irin murya mai bayyana tsananin b’acin rai. Na d’ago ina kallonta idona yana kawo ruwa, ta iso gaba na cikin b’acin rai ta ce “Kike kallo na, na ce yana gidan Ubansa Sulaiman Sa’eed ba, ko da abinda zaki yi?” Hawaye ne kawai suka shiga zuraro min na saka k’afa da sauri na juya na bar d’akin jikina har rawa yake yi. Da k’yar na koma kitchen na k’arasa girkin a gaggauce na fa’da wanka. A raina ina jin ko me Mami zata yi ba zan rabu da Ahmad ba, amma fa zuciyata sai suya take yi.
Shima bayan magribar da yazo sai naga fuskarsa sam ba annuri, kallona kawai yake da k’yar ma ya amshi cup d’in da ba zuba masa Kunun, naga yana kurb’a a hankali kamar yana shan magani, idonsa da suka jirkita zuwa brown colour a kaina. Kawai sai na samu kaina da rushewa da kuka. Bai hana ni kukan ba kamar yarda bai fasa kallona ba, abin mamaki shima sai naga gangarowar hawaye a nasa idon. “Me ya sameki?” Ya ce cikin wata irin murya da yasa na d’ago ina kallonsa… ban amsa masa ba illa cigaba da kukan da na yi, ya saka hannunsa ya mik’o min “Zo ki gaya min…” Ji na yi ba zan iya masa musu ba na isa wajensa jikina a sanyaye na zube a gabansa. Durk’ushe wa ya yi a gabana ya d’ora cup d’in kunun a bakina.
A hankali na fara sipping. “Gaya min damuwarki?” Ya furta min a hankali. Na ce “Kai zan tambaya Ustaz, kai zan tambaya ji fa k’walla a idonka. Kana cikin damuwa yau gaba d’aya fa ko kira na baka yi ba…” ya saka hannunsa a goshina yana murzawa a hankali bayan ya jani jikinsa bakinsa ya saka a saman nawa yana lasar lips d’ina. Kafin ya lumshe idonsa yana cigaba da shafa goshin nawa ya furta “Ki yi shiru baki da lafiya ga kanki nan yayi zafi jijiyarsa ta tashi.” Ni da kaina na yarda ba ni da lafiya sai dai shima na ji nasa hannun shima ya ‘d’au zafin. Tafin hannunsa na kama na rungume a fuskata ina shak’ar k’amshin turarensa na furta “Ustaz kai ma jikinka zafi.” Idonsa a lumshe ya d’aga min kai. “Bani da lafiya ne AYSHA, wani irin ciwo zuciyata take min, ina kika je jiya da daddare, na kikkira wayarki baki d’aga ba?” Girgiza kai na yi ina mamakin furucinsa na furta “Ina zan je ban gaya maka ba, kaima ka san ba inda zan iya zuwa.” Still idonsa a lumshen ya sunkuya ya sunbaci tsinin hancina ya janye ni daga jikinsa sai naga ya mik’e yana kallona ya furta “Good night, idan kinga baki ji sauk’i ba ki fa’da a gida a kaiki asibiti..” Da mamaki na ce masa “Baka ci abincin ba ai?” “Am okay.” Ya fa’da yana fita da sauri kamar har a lokacin da k’walla a idonsa. Na mik’e zuciyata na bugawa na shige cikin d’aki duk hankalina a tashe.
Tun daga ranar Ustaz ya canja gaba d’aya, baya kira na sai dai na kira shi. Khadija ma har waya take min ta ce sun rasa kansa a gida. Amsa guda nake bata nace nima anan d’in ban san me ke damunsa ba. Sau tari ma idan na kira shi cewa yake yana busy ya kashe wayar. Tun jikina na bani bakomai har nazo na yarda tabbas akwai wani abin da Ustaz yake b’oye min.
Mami kuwa hankalinta kwance cikin zallar farin ciki take gudanar da shiryen shiryen bikin. Dukiya yake kashe min bata wasa ba, lamarin har ya fara firgita tunani na. Kullum kulawa take bani ta musamman.