Showing 24001 words to 27000 words out of 44853 words

Chapter 9 - NAGA_RAYUWA_BOOK_1

Unknown   

02 Dec 2025

105

AYSHA ce zata je ta mata wahalar laulayin kenan? To ba sai yiwu ba ka samar mata y’ar aiki idan ma bata da y’an uwan da zasu zauna mata.” Muhammad ya d’an rusuna, duk da ba wani girmansa Mami ta yi ba, bai fi 2 yrs ta bashi ba, amma yana girmamata a matsayinta na matar ubansa. “Ki taimaka, ko don nan gaba idan Aysha ta yi aure bata da y’an uwa mata itama fa y’an uwan Mijin ne zasu kula da ita.” Mami ta girgiza kai “Wallahi don dai kai ne, amma da Umar ne Allah ba zata gidansa ba..” Dariya Muhammad ya yi don ya san Mami da Umar sam basa shiri haka ma Usman. Ya dinga dariya yana kallona ya furta “Ke d’ebo kayan da zasu miki kwana biyar, ki yi sauri ina mota ina jiranki…”


Na mik’e na hau sama, a raina sam bana son zuwa saboda ina yawan fita da yamma naga ko zan ga Ustaz amma bana ganinsa. Na shirya kaya na na bi Yaya Muhammad gidansa.


A parlor na samu Anty Khadija daga yanayinta na hango tabbas laulayin take. Gaisheta na yi ta amsa tana murmushi na mata sannu. Da kanta ta raka ni ‘d’akin da zan zauna. Hijab d’ina na cire na fito parlorn ba mayafi a jikina sai hula. Tas na gyara gidan don ya yi k’ura ka’dan. Kafin na shiga kitchen na tuk’a musu tuwon semovita da Yaya Muhammad ya ce shi ka’dai take iya ci.

Tsaf na shirya musu table d’in duk zuciyata ba da’di balle ganin tunda suka shige d’aki basu sake fitowa ba wai bata son k’amshin kayan miya. Mijinta sai wani lallab’ata yake. Haushi ma abin ya bani don haka bayan na yi wanka kawai na fita k’aramin parlorn na kwanta. Ina kallon wani Korean series. Anty Khadija da Ya Muhd suka shigo hannunsu sark’afe cikin na juna sai wani janta yake a jiki, ita Kuma tana sake narke masa. Kunya da takaicin su ma duk suka ha’du suka sake jagule min zuciya ta. Khadija na kallona ta furta “Sannu Aysha..” na amsa mata ina mayar da kaina na kwanta. “My love wallahi duk jikina ciwo yake, so nake ka yi min tausa…” Gani na yi kawai ya sunkuya ya ‘dagata cak tana Zillo tana komai ya fice da ita kamar Babyn roba.
Lumshe idona na yi ina tunanin dama nice da Ustaz a haka, da na tabbata ba wani da zai kai ni farin ciki a duniya. Sai kawai na samu kaina da zurarowar hawaye. K’amshin turarensa da na dinga ji yana sake yawaita ne ya saka ni bu’de lumsassun idanuna…. Da wani irin sauri na mik’e ganin Ustaz ne da Ya Muhd a parlorn. Ustaz d’in a zaune idanunsa akan wayarsa. Hula ce kawai a kaina, itama ta zame don haka gashi na ya bayyana sosai. Kayan jikina kuwa T.shirt ce da ta d’an kamani ka’dan sai siket. Ido na dinga warowa ina k’ank’ame jikina. Sai na lura Ustaz ko kallona bai yi ba, ya cigaba da hirarsu da Yaya Muhd, kamar ma basu san ina wajen ba. “Bari na kawo maka ruwa” Ya Muhd ya mik’ewa yana ficewa. Sai sannan na furta “Ya zaka shigo ba sallama, ai dai ba kyau shiga gidan mutane ba sallama, ga shi nan ka shigo ko Hijab babu a jikina…” Wani irin kallo ya min. Kafin naga ya ‘d’auke kansa ya mayar kan waya ya furta “Ba wajenki na zo ba, kuma mai gidan ne ya bani izinin shigowa.” Raina ne ya sake b’aci a kufule na ce “Sai ka tashi ka fita, ina son zan wuce cikin gida…” “Na hanaki ne?” Ya furta yana zuba min narkakkun idanunsa.. Turo bakina na yi sai ga Ya Muhd ya shigo yana kallona “Tashi ki samo masa snacks a kitchen Malama…” Ji na yi kamar na yi ihu. Na kalleshi na ce “To ka bani Hijab d’ina a cikin gida…” Tsaki Ya Muhd ya yi kafin ya fice sai ga shi ya dawo da Hijab ‘din ya hurga min. Ina kallo Ustaz ya ‘dan tab’e bakinsa na zura Hijabin na fice da sauri. A kitchen na tsaya ina mayar da ajiyar numfashi dafatan Allah yasa Ustaz aurena yazo sake nema.. Ban dawo daga hayyacina ba sai da Ya Muhd ya shigo kitchen d’in yana wurga min harara ya furta “Ki zuba abinci ki kai masa Malama ki ha’da da snacks.” Ya fice da sauri.


Na sauke ajiyar zuciya. Na ha’da abincin da snacks d’in sannan na shiga d’akin da yake zuciyata na wani irin bugawa. Har na ajiye abincin bai d’ago ba. Na ja na tsaya don na kasa fita daga sitroom d’in. “Zuba ka’dan.” Ya furta cikin wata irin husky voice. Kamar ba zan zuba ba, sai dai na zuba tunda neman sulhu nake. Na ajiye akan table ya d’ago yana kallona kafin ya d’au abincin ya tab’e bakinsa. Na rasa dalilin wannan tab’e baki don haka na fara kallon jikina ko wani abin ya gani ban ga komai. Don haka na koma kujera na zauna. “Ki tashi ki koma ba wajenki na zo ba..” Da wani irin zafin rai na ‘dago ina kallonsa sai naga shi ko kallona ba ya yi tuwonsa kawai yake ci. Haushi ya kamani na mik’e da sauri zan fice daga ‘dakin. Na ji muryarsa a waya yana furta “Aysha, zo ku gaisa da zab’in alheri da Allah ya min, ga matar da za’a aura min aure da ita jibi….” Wani irin rawa jikina ya fara na juya da sauri don ganin matar da yake nuna min a vedio call. Zuciyata ce kawai bata fito ba, Saboda tashin hankali. Ya mik’a min wayar ba tare da ya kalleni ba. Take hankali yazo min kada a yi abin kunya na karb’e wayar ina kallon kyakykyawar yarinyar a cikin waya sai sakar min murmushi take. Yarinya kamar ita ta k’era kanta fara jajir da ita. Idan ma zata girmeni da ka’dan ne. “Sannu Aysha..” ta furta cikin zak’in muryarta. Kokawa na dinga yi da numfashi na na ja iska da k’yar na fesar ina k’ak’aro murmushi na ce “Sannunki…” ta lumshe ido tana furta “Yaushe zamu ha’du ki taya ni shirin biki?” Ji nayi kamar na k’unduma mata zagi. Na ha’diye wani abu da ya tsaya min a mak’oshi na ce “Ki yi hak’uri ina school ba ni da time, Allah ya sanya alheri..” Daga haka na mik’a masa wayar da sauri, ina jin zuciyata na wani irin hantsilowa. Bai karb’i wayar ba ya nuna min gefensa “Ajiye min anan, kin ga zab’in da Allah ya yi min ko? Wani baya auren matar wani, she is my cousin jibi za’a d’aura mana aure don a shekaruna ba zan iya jiranki wani degree ba, duk sanda kika gama degree d’in idan kina da niyyar aure na the door is open…” Ya fa’da yana kurb’ar lemo da min kallon da na tabbatar na rainin hankali ne. “Ba wani aurenka da zan yi, ce maka aka yi ni kuma kwantai zan yi da zan auri Mijin wata, ragowar wata Allah ya kiyaye Mijina zan samu Wallahi nima dallele na aura…” na furta ina huci kamar wacce ta yi tsere. Murmushi ya saki yana yamutsa fuskarsa ya furta “Allah ko? Amma dai kin san ba zaki samu wanda ya fi ni ba… Idan haka kika zab’a Ai shikkenan, ina fatan ita dai kin ganta idan bata fi ki ba, ke ba zaki fita ba…” Ya ‘d’au key d’insa yana furta ki turo Min Muhammad zan ba shi Invitation card d’in Abba ya kai masa…..” “Ba zan turo shi ba ‘din…” na furta kai tsaye idona na cikin nasa, duk wata shakkarsa da nake ji ranar ta kau, Saboda tsananin kishi da ya rufe min ido na. Murmushi ya saki ya furta “Bakomai, bari na kira shi a waya…” Cije leb’ena na yi ina ji yana furta “Muhammad idan ba damuwa d’an fito na baka cards d’in Abba na d’aurin aure na special guests…..” Daga haka ya saka kai ya fice ya bar ni a tsaye kamar statue gaba d’aya naji duniyar na juya min na runtse idonsa sai ga wasu k’walla masu turiri sun fara zubo min.. fuskar budurwarsa still a cikin
Idanuwana……



𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ


NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎


𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️

Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION




Arewabooks @nazeefah

https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ


Wattpad@Nazeefah381

08033748387.

★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 13







Tabbas bata inda zan ha’da kaina da matar da zai aura, ta fi ni komai kyau ilimi wayewa, da kuma gata, daga ganin gidansu inda ta d’au hoton in dai ba y’ar feck life ba ce to na san Ubanta yafi Abba ku’di nesa ba kusa ba. Me ya ja min? Na ce na fasa auren Ustaz gashi nan na jawowa kai na sakiyar da ba ruwa.


Da k’yar na mik’e na fita cikin gida, daidai lokacin da na ji Motar Ustaz ta fita daga gidan a guje. Na lek’a ta window sai naga Yaya Muhd ya shigo gidan . Fuskarsa a ha’de yake kallona. Kafin naga ya yi k’aramin tsaki ya shige bedroom d’insa. Da alama haushina yake ji ta yarda nayi watsi da duk abinda suke so na zab’i farin cikin Mami fiye da nasu. Wayata na jawo na fara kiran Ustaz da sauri amma wayar na ringing Ustaz bai ‘d’auka ba. Na ja tsaki ina cilla wayar kan kujera tare da zama dab’ar ina rik’e kaina da naji yana sara min da k’arfin gaske. Idona na lumshe amma still Ustaz da Amaryarsa nake hangowa a wani yanayi na soyayya. Zuciyata ta dinga bugu da k’arfin gaske. Wasu hawaye masu zafi suka dinga zubo min. Ban san sanda na ja wayar na danna masa msg ba. “Ka ‘d’aga wayar magana za
Mu yi….” In seconds ya dawo min da amsa “It’s too late, ki yi barci zan yi magana da safe, yanzu muna discussing da amaryata ne.” Na yi cilli da wayar ina jin wani d’aci har a mak’wagoro na. Cije leb’e na kawai nake yi ina mamakin wulk’ancin da Ustaz yake son ya fara min.


Da dai naga babu sarki sai Allah, sai kawai na mik’e da sauri na nufi bedroom ‘din da nake, direct washroom na shige na sakarwa kaina shower da kayana a jiki da komai, burina naji abinda nake ji ‘din ya ragu. Sai dai ba abinda ya ragun daga zafin zuciya da nake ji. Na ‘d’auro alwala na shiga sallah ba ji ba gani…


Kashegari da k’yar na tashi na hau gyaran gidan don duk kawai na kawar da abinda nake ji a raina. Da yamma sai ga Mami na tazo gidan. Da sallama ta shigo na yi saurin ‘d’aga kai ina kallonta. Zama ta yi tana tana jikinta ta furta “Ke Baby!
What happened to you na ganki so pale haka?” Daurewa na yi ban sakar mata hawayen da suke son zubo min na ce mata bakomai…” Sai sannan ta amsa gaisuwar da Khadija ta mata. Tana fa’din “Ina Muhammad ‘din?” Anty Khadija ta ce “Ai bai dawo ba..” Gani nayi Mami ta girgiza kai ta ce “Yaushe ya ce zai dawo daga Kadunan?” Khadija ta ce “May be gobe.” Ni mamaki nake yi don dai Yaya Muhd yana nan a cikin gidan nan me yasa Anty Khadija zata ce bata nan… Mami ta ‘dan ja tsaki ta furta “D’an bamu waje Khadija zan yi magana da ita…” Kamar jira take tayi saurin mik’ewa ta fice. Mami ta saki ajiyar zuciya tana jawo wata leda a jakarta. “Dama yana dawowa ki dawo gida, a goben, kin ji na gaya miki.” Na ‘daga kaina ta zaro wata roba mai cike da wani abu kamar rubutu tana furta “Bu’de ki shanye, ban yarda da lamarin wancan mutumin ba..” Na karb’a hannuna na rawa na bu’de na sha duk da sam hankalina ya kasa yarda da rubutun, abu ne da na sani a gidan mu Abba d’an izala ne shi yasa baa ta’ammali da rubutu, zan iya cewa tun tashi na ma ban tab’a ganin rubutu a gidan ba. Yana dai yin tofi. Ina shanyewa ta saki ajiyar zuciya sannan ta ciro wani turare a jakarta ta shafa min. Turaren sam ba shi da da’din k’amshi. Daga haka ta mik’e bayan ta bani chocolates da ta siyo min da biscuit da yawa ta ta ce “Zan tafi AYSHA na gaya miki ki taho yana dawowa gobe..” Na ‘daga kaina ko sallama bata yi da Khadija ba ta fice.

Sai ga Yaya Muhd ya fito daga bedroom fuskarsa a ha’de ya zuba min ido yana kallona. “Me ta baki kika sha?” Na waro ido ina furta “Bakomai fa…” “Bakomai d’in Uwaki, ba ina kallo ta baki abu roba kika shanye ba…” ya furta yana tsare ni da ido.
Yana bu’de k’ofofin hancinsa da alama k’amshin turaren yake shak’a. “Wannan wani irin turare ne kamar na y’an bori? Tashi kije ki yi wanka don Ubanki shashasha da bata san ciwon kanta ba…” Yaya Muhd ya furta a zafafe kamar ya mangare ni. Da sauri na shige d’aki ina turo bakina alamar na ji haushin abinda ya yi min ‘din. Ina ji ya zabga tsaki.


Da na yi wankan, zama na na yi a ‘d’aki fuskata a ha’de don na ji zafin abinda ya yi min. Sai gashi ya shigo d’akin yana kallona ya furta tashi magana zamu yi AYSHA….” Na mik’e na zauna still fuskata a ha’de. “Haushi kike ji ko? Baki da hankali yarinya har yanzu baki san me duniya take ciki ba, ina sane na kawoki nan don ban yarda da wannan matar ba…” Wani irin waro ido na yi na furta “Mamin nawa?” Harara ya zuba min,
Yana fa’din “Saura kuma don Ubanki ki je ki gaya mata, na ce ban yarda da ita ba, tunda da alama ta shanye miki zuciya har kina k’ok’arin gasa taki zuciyar saboda ki sanyaya tata, kan ki
Kika cuta ba wani ba na tabbatar ko gama karatun kika yi ba zaki samu kamar Ustaz Ahmad ba, shi na daban ne ina gaya miki, gashi nan kin cuci kanki zai yi aure ya bar ki, saboda ko farantawa wata k’atuwa rai shi kuma Abba da hakkin ki masa biyayya yake kanki kin bak’anta masa nasa ran a matsayinsa na mahaifinki,
Kin nunawa duniya bai isa da ke ba. Ina sane na kawo ki nan amma nan ‘din ma sai da ta biyoki. To wallahi ki kiyaye kan ki na gaya miki bakomai zata sake baki ki yi amfani da shi ba. Ki ‘dau waya kuma ki kira Ustaz idan ya amince yazo gidan nan sai na tayaki bashi hak’uri, Allah yasa ya hak’ura ya aureki.” “Ameen” na furta ba tare da na san ameen ‘din ta fito ba. Ya Muhd ya bi ni da wani irin kallo kafin ya yi murmushi ya ce “Shashasha, kina so kina kai wa kasuwa..” Na sunkuyar da kai ina d’an dariya. Ya furta “Ki kira shi yanzu.” Ya fita daga d’akin.


Sai da na yi addu’a sosai sannan na kira shi, Ringing ta yi sosai kafin ya ‘d’aga. Cikin Husky Voice ‘d’insa ya ce “Assalamu Alaiki, K’anwata AYSHA ya aka yi?” Wani irin waro ido na yi raina ya b’aci da sunan da ya kira ni da shi. Wai k’anwata ina ma laifin Habibteeyn… da yake fa’da. Ba dai ji haushi ba na furta “Ina yini?” Sai da ya yi ‘dan jum sannan ya furta “Lafiya lau, Babyn Mamy me ya faru na ji muryarki so weak…” Hawaye na ji sun silalo min na yi k’ok’arin tsayar da su ina furta “Zaka zo yau please…” “Ina zan zo?” Ya furta a hankali cikin k’asa da murya “Gidan Ya Muhd please Ustaz…” Sai da ya ja fasali sosai sannan ya furta “Me Zan zo na yi? Ko kin shirya amincewa aurena ne?” Shiru na masa zuciyata na bugawa da sauri na ce “Ni dai kazo don Allah…” ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya. Yana fa’din. “Sai dai gobe yau a gidan su Habibteey zan sha ruwa..” wani irin wuntsilawa zuciyata ta yi don haka naja baki na tsuke ina hucin da na tabbatar yana jin sa ta cikin waya.. “Kada ki fashe, don naji fushin ya bayyana har ta numfashinki, zan zo Amma ina son a min irin funkaso da masar rannan ki saka man shanu a cikin miyar.” Ya furta a hankali. Wani farin ciki naji na ce “Ai baka ci abincin ran nan d’in ba, ta ya aka yi ka gani? Bayan baka bu’de ba…” Y’ar k’aramar dariya ya saki ya furta “Little girl, bayan kin gama kuka a sitroom na saka Drivernku ya ‘dauko min Warmers ‘din na tafi gida da su, ranar duka kowa a gidan mu sai da ya ci abincin AYSHA Momeey na ta mamakin iya girkin ki da murnar ki zama surikarta ashe ba zaki zama ba….” “Wa yace ba zan zama ba?” Na furta da sauri. Na ‘dan Jim ya yi bai ce komai ba, kamar ma ba zai ce ‘din ba sai kuma ya ce… “Ke kika zab’i rabuwarmu Aysha… Ga shi Yanzu it’s too late, koda yake sai nazo za mu yi magana, take care ki ha’da min zob’o bana son kunun aya…”Ina ji ya kashe wayar. Nima ajiye wayar na yi cikin sanyin jiki, ina runtse idona wasu zafafan hawaye suna zubo min..


Na dubi agogo naga akwai sauran lokacin da zan iya masa da funkaso, tunda sai a lokacin ma 3:30 ta yi. Da sauri na mik’e na isa kitchen ‘din Anty Khadija. “Alhamdulillah” na fa’da ganin duk abinda nake buk’ata akwai shi a kitchen d’in.
Nan da nan na fara shirin girki, don kam Alhamdulilah Umma da Mami sun hora ni da girke girke iri-iri, don haka duk inda na je basu da fargabar a bani girki. Sai shidda daidai na gama girkin. Gidan sai zuba k’amshi yake. Wanka kawai na yi na samu kaina da tsantsara kwalliya ta fitar hankali, wai duk don na kamo matar Ustaz a kyau. Amma still walainiyar fuskarta kawai nake gani. Don haka na saki tsaki na goge makeup ‘din tas hawaye na bin idona. Sanda aka yi sallah kuwa dabino kawai na samu na ci, don nima na yi azimin.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login