Showing 18001 words to 21000 words out of 44853 words
girgiza kai ina furta “Ai ban san zaka zo ba…” “Ta ya zaki san zan zo bayan kin k’i picking call d’ina, kina hora ni saboda kina tunanin kin yi yarinya sa aure ko?” Ya furta yana d’an murmushi ha’de da cije leb’ensa ka’dan. “Allah ya nuna mana lokacin, Jibi zan wuce Egypt, zan samu one week a can. Idan na dawo kashegari zai kama litinin anan zan sha ruwa. Ina jiran girki mai kyau daga wajen kyakykyawar budurwata, za ki yi min?” D’aga kai na yi da sauri ya yi dariya “Kamar gaske Allah yasa kin iya girkin.” “Allah kuwa na iya..” Ya mik’a min hannunsa “Zamu gani ai, Allah ya kai mu ranar kuma ban amince kowa ya tayaki ba. Kina girkin muna vedio call, ba ni zoben hannunki.” Na waro ido ina girgiza kai. “Ai ya yi maka ka’dan, ji fa hannunka.” Ya kai duba zuwa hannunsa “In dai ba rowa zaki min ba, ai sai ki bani na gwada na gani, ko ya yi min ka’dan ina so zai min rakiya Egypt..” Na zare zoben ya nuna min gefen kujera “Ajiye a nan, Zan d’auka.” Na kuwa ajiye ina sake girmama halin Ustaz na kiyaye dokokin musulunci. Ya ‘d’au zoben ya saka a k’aramin yatsansa sai ga shi kuwa ya ‘dan shiga. Sumbatar zoben ya yi a hankali yana lumshe ido ya furta “Ina sonka zobe, Saboda ka fito a hannun AYSHA ta..” Ban san sanda na saki murmushi ba ina jin kamar ni Ustaz ya sumbata.. Daga haka ya fice daga sitroom d’in yana sakin murmushi…
Tunda na saka k’afata a benen Mami, na ji gabana yana fa’duwa, fatana Allah yasa ta yi barci. Da san’da na tura k’ofar parlorn sai dai ba kamar yarda na yi tsammani ba, Mami na nan idonta biyu. Tana zaune a kan kujera ko T.V bata Kunna ba. K’afarta ta ‘dora ‘d’aya saman d’aya tana girgiza ta fuskarta a ha’de sosai. Jikina a sanyaye na k’arasa kusa da ita na zube a gabanta… “Mami na, don Allah ki yi hak’uri ki yafe min laifi na, wallahi ban yi don na b’ata miki rai ba, na yi ne don bin umarnin Abba….” “Abba ba? Dole ki bi umarninsa tunda shi ya kawoki duniya, ni mecece a wajenki da na wuce Uwar goyo, ba abinda zaki ce min kin zab’i iyayenki a kai na sakamakona kenan a wajen ki Aysha? Duk da tarin k’aunar da na nuna miki?” Ta fa’da wata k’walla na zubo mata. Nima kukan na saki, jijiyoyin kaina suka d’aure na dinga kuka mai tafe da ajiyar zuciya. Ta matsar da ni daga jikinta tana mik’ewa ta nuna min k’ofa “Sauka min daga bene AYSHA ki koma wajen iyayenki da kika fi k’auna….” A tsorace na dinga kallonta jin furucinta kuma na hango tabbas da gaske take har k’asan zuciyar ta . Hannunta na kama da sauri ina furta “Me yayi zafi haka Mami na? Duk duniya ba ni da kamarki, Abba da Umma kawai haihuwata suka yi, amma ke kika ci dukkan wahala da ni, kika bani tarbiyya kika kula da ni da jiki da aljihunki me yasa zan bujire miki?” “Zaki bujire min ne AYSHA saboda d’a namiji, d’a namijin da nan gaba idan ya kuntaka miki iya shege sai kin yi dana sanin ha’duwa da shi, d’a namijin da idan nan gaba ta ciyoshi zai auro wayayyiya mai ilimi ke kuma ya mayar da ke Bagidajiyar gida… Ilimi shine garkuwarki don haka ki yiwa kan ki fa’da ki rabu da shi ki zab’i karatunki…” Runtse idona na yi na furta “Ya ce zai bar ni na yi karatun har sai na ce ya isheni…” “K’arya yake AYSHA yana samunki, zai manta da wannan alk’awarin, bana burin nan gaba ki zama k’ask’antacciya nafi so ki zama tauraruwa a cikin duniyar mata masu ilimi, ta yarda zaki shiga ko ina a goga da ke… Ki bijirewa auren nan AYSHA in dai ba so kike na ‘d’auka har a raina don kun san bana haihuwa ba ne bani da kuma y’ar da zata shafe min hawaye…” Fa’dawa jikinta na yi ina furta “Zan share miki Mami, wallahi zan share miki kuma na hak’ura da Ustaz ko da hakan na nufin rasa dukkan farin ciki a rayuwata…” Murmushi ta saki tana sake rungume ni a jikinta. “Ba wani farin ciki da zaki rasa Aysha, farin ciki yanzu ma kika fara in dai zaki rabu da wancan mutumin ni kuma zan baki farin cikin da har sai kin dinga mamaki, zan maye miki gurbin Uba, Uwa da shi kansa Mijin…” na d’aga kai ina sakin ajiyar zuciya a hankali. “Ba ni wayar da ya baki?” Hannuna na rawa na mik’a mata. Naga ta danna wajen kashewa ta kasheta tana murmushi “Bak’in mugu sai dai ka auri wata ba AYSHA ta ba…” ta fa’da tana mik’ewa ta shige d’akinta “Ki je ki yi wanka ki kwanta, Maganar wannan mutumin close har abada…” wani irin yawu na ha’diye da k’yar ina mik’ewa na ji kaina ya sarawa na rik’e kan da k’yar na isa cikin d’aki, ina ji kamar Mami ta raba ni da wani sashe ne na rayuwa ta..
Tun daga ranar na rasa duk wani farin ciki da walwala. Sai dai ina k’ok’ari sosai wajen danne hakan don kada Mami ta gane. W
Ranar kwana uku da faruwar lamarin Mami ta fita, Umma ta hawo sama, ta shiga d’akin da nake a kwance ta sameni idanuna na kallon ceiling ta tsaya a gefen gadon. Ganinta ya saka ni yin firgitgit ina kallonta. Ajiyar zuciya ta saki ta zauna a gefen gadon tana furta “Ta shi Aysha magana za mu yi, a matsayina na uwar da ta haifeki na san kin kwana da sanin cewa ba zan cutar da ke ba.” Jikina a sanyaye na mik’e na zauna idanuna na kawo ruwa sai na ji kawai ina son na yi kuka a jikin Umma na. Fa’dawa jikinta na yi na saki kukan bata hana ni ba sai ma sake rungume ni da ta yi a jikinta. Na yi kukan sosai kafin ta ‘dago ta share min hawaye ta furta “Me ke damunki?” Girgiza mata kai na yi “Bakomai Umma.” Murmushi ta saki tana gigiza kai “Ba zai zama bakomai ba AYSHA tabbas Akwai komai, ni na san kina son mutumin nan Kuma kin amince da aurensa, me yasa kuma kwana biyu kika canja? Ga shi kullum kina d’aki ba kya walwala, Aysha ina son ki bu’de kunne ki ji ni da kyau. Bin Umarnin mahaifinki wajibi ne gareki, ki amince da auren nan kafin ki zo kina nadama, me yasa ba kya amsa wayarsa alhali kin san baya gari? Ya kira Abbanku yana tambayar lafiya idan ya kira wayarki bata yi? Ina wayar taki take?” Umma ta furta tana min kallo mai cike da k’auna da rarrashi. A hankali na furta “Tana wajen Mami.” Murmushi naga ta yi ta mik’e tana fa’din ki tashi ki yi wanka ki sauko ki ci abinci bana son zaman ‘d’akin nan.” Na mik’e a hankali na shige toilet d’in. Umma har ta tara min ruwa na shiga wankan sannan ta fita daga d’akin.
————
Kashegari da safe naga duk k’annen Abba maza sun zo gidan. Ban san me ake ba ni dai na shirya na tafi makaranta. Da na dawo kuwa rigima na tarar a gidan wai ashe ku’din aurena aka kawo da sa rana gaba d’aya..
Shine Mameey ta fito tana masifa a tsakargida na ganta da Umma tana janta da akwatin ta tana furta “Wai Fateema meye haka kina cikin hankalinki kuwa? Saboda za’a aurar da Aysha zaki bar gidan nan…” A zafafe ta janye hannunta. “Cika ni, gwara na tafi meye amfanin zama na a gidan da baa san daraja da k’imata ba, ashe dama kun bani y’ar ne don ku wulak’antani ku nuna min bani da iko da ita. Zan bar gidan tunda ba Uban da na ajiye, ku je ku yi ta aurar da ita….” Da gudu na iso wajen na zube a jikinta, jikina yana kakkarwa na furta “Please Mamy ba inda zaki, ba Zan aure shi ba wallahi, tunda dai baki amince ba…” “Ashe kuwa sai dai idan ba ni Iman ba ne na haifeki Aysha, aure ba fashi..” Mami ta juyo tana kallonsa “Kada Allah yasa ka fasa Imamu, ga y’arka nan ka aurar da ita, amma ni na gama zaman gidanka…” Hanya ya nuna mata yana juyawa a zafafe cikin parlorn sa. Mami ta wancakalar da ni ta ja akwatin ta da sauri zan bi ta Abba ya daka min tsawa da sauri na durk’ushe a wajen ina jin tashin motar Mamin. Na runtse idona da k’arfin gaske, ina jin wani irin b’acin rai Yana dugunzuma zuciyata…
Wannan wani irin bal’ai ne tabbas zuwan Ustaz rayuwata ba abinda ya haifar sai fitina a cikin gidan mu, abinda ban tab’a gani ba, sa’insa tsakanin Iyayena da Abba. Ranar sam zuciyata bata da nutsuwa na ji a raina sam na shirya rabuwa da Ustaz.
Nan da nan labari ya kara’de danginmu an bada ni an saka min rana. Aka yi ta zuwa Allah ya sanya alheri. Mami kuma bata dawo gidan ba tashin hankalina kenan…
Ranar lahadi Ina zuwa makaranta naga motar Ustaz. Mamaki ya kama ni na fara tunanin a yau d’in da ya dawo yazo kenan. A aji na same shi a zaune da wasu tsirari daga cikin ajin. Ido ya ‘dago yana kallona sai naga kamar har rama ya yi a ido. Na rusunar da idona kawai na isa wajen zama na na zauna.
Sai da ya gama karatu wanda duk rabi ba fahinta nake ba sannan ya ‘dago yana kallon y’an ajin ya furta “Bissalam, ku je ku yi sallah.” Ni ce ta farkon fita.
Ana idar da sallah aka ce koda kowa ya mik’e, anan muke jin ashe yau ustaz zai yi sallama da makarantar. D’alibai da yawa ba su so ba, musamman y’an mata da suke ta maganar k’asa-k’asa. Ustaz ya yi alheri sosai ga makarantarmu. Sanda Malam Kawu ya masa godiya a madadin y’an ajinsa na Ibn Kaseer ta cikin loud speakerr Ya furta “Bayan jaddada kalmar godiyar mu, sannan ina son y’an makaranta su taya Ustaz Ahmad murnar samun matar Aure da ya yi, a cikin makarantar nan. An saka musu rana da hazik’ar mu, Hafizar mu Aysha Imam Khaleel, Head girl d’in mu ta wannan makaranta. Duk da nik’ab ne a fuskata sai da jikina ya fara rawa musamman da kabbarar mutane ta dinga shiga kunnuwa na. Na runtse idona a hankali. Ina hango yarda bakin Ustaz ya kasa rufuwa yana ta sakin murmushi. Y’an mata kuwa duk fuskokin wasu ba walwala. Har gaba na aka dinga zuwa ana sake taya ni murna. Ni dai kasa bu’de fuskata na yi na samu na na silale na gudu…
Ina zuwa layin gidan mu naga yarinya ta biyo ni da gudu “Malama Aysha take ta furtawa. Na tsaya ina kallonta sai da ta d’an yi haki na alamar gudun da ta ci sannan ta mik’o min envelope ‘din mai matuk’ar kyau. Da tun kafin na bu’de na san waye saboda k’amshin mayen turarensa. “Ba ruwana da fushinki, duk da na ji haushi amma abu guda na sani dole a cika min alk’awarina zan zo shan ruwa gobe around 7:30pm.
Your’s Ustazun Aysha.
Ajiyar zuciya na saki. A raina ina tunanin ta inda zan rabu da Ustaz ba tare da na saka shi a damuwa ba..
Kashegari nima tashi na yi da azimin kawai na samu kai na da son yiwa Ustaz d’in girki, duk da ina ji a raina a ranar zan rok’e shi ya janye daga maganar aurena ko don dawo da farin cikin gidan mu, kuma Mami ta dawo gidan mijinta. Girkin na masa, Masa da sinasir sai miyar taushe na kuma yi kunun tsamiya da zob’o da ya ji kayan k’amshi. Haka kawai na ji gwara na masa abincin mu na gargajiya. Umma dai sai kallona take kafin ta gaji da shirun ta furta “AYSHA wa kike wa girki ne?” Kunyace ta kamani na ce “Umma cewa ya yi zai zo ya sha ruwa.” Gani na yi ta yi murmushi ta d’an’dana girkin da lemon ta girgiza kai ta furta “Kin yi k’ok’ari, sai ki ha’da masa da zogale tunda naga harkar gargajiya kika masa. Ko ke fa? Ki rabu da Mami zata dawo da ikon Allah, gobe ma Na ji Baffaninku suna za su je gidan…” Na d’aga kai kawai ba wai don zan janye maganar rabuwa da Ustaz ba da na shiryawa a yau.
Daidai lokacin da zai zo kuwa sai ga Yaya Ali ya shigo d’akina yana kallona ya furta “Bak’onki ya zo kandala.” Turo baki na yi ina fa’din “Kai Ya Ali me ye haka? Kai ma ya kamata ka yi aure ka bar gidan nan.” D’alle min baki ya yi yana furta sai ki aurar da ni, ashe dai kina son mutumin ji wani uban kwalliya da kika yi har da su jambaki?” Harararsa kawai na yi na shige na sauka k’asa. Kafin na je ma har Umma ta saka an kai masa abincin sitroom. Ina shiga yana zaune na same shi. Idonsa a lumshe sai dai daga yanayin fuskarsa na tabbatar akwai abinda ke damunsa. Sallamar da na yi bai saka ya bu’de idon ba ya dai amsa nima na ga haka ne ta hanyar d’aga lab’b’ansa da ya yi. Tsawon mintu biyu bai bu’de idon ba duk da a jikina na ji yana kallona da lumsassun idanun nasa. “Zuba min ruwan tea.ban sha ruwa ba dabino kawai na ci.” Ya fa’da still idanunsa a lumshe. A daburce na fara ha’da masa shayin. Ina shirin sake zuba sugar ya furta “Enough madam, wa ya gaya miki ana son maza su dinga shan zak’i sosai?” Ya fa’da yana ware idonsa ka’dan a kai na. Maik’on k’wallar ido yana k’arawa idonsa kyau. Hawaye naga sun d’an gangaro masa. Hakan ya saka jikina ya yi sanyi. Na ajiye cup d’in shayin a kan table da ke kusa da shi. “Na gode” ya furta cikin raunin muryar da ta saka har na ‘dago na kalleshi da sauri na ce “Kuka ka ke?” Ya ‘d’aga min kai. “Kuka nake AYSHA, dole na yi kuka me yasa ba kya so na? Kike wahalar da ni, kin san kalar azabar da kika bani a kwanakin nan, Sana’a na je yi k’asar mutane amma na zama sam bani da nutsuwar da zan gudanar da sana’ar na kira waya a kashe har na gaji na kira Abba. Amma still you don’t on your phone why? Me na miki da na yi deserving this kind of purnishment a wajenki? Kin san bana k’asar balle nazo na ji dalili. Ki gaya min gaskiya me ya faru kin daina so na ne?” Da sauri na d’aga kai ina kallon sanda ya matse tea cup d’in hannunsa duk da zafinsa na runtse idona. Sai na ji ya saki ajiyar zuciya ya ajiye cup d’in. Ya furta “Na gode AYSHA, amma may I know the reason?” Ji na yi na kasa b’oye masa na ce “Mami na bata son relationships d’inmu da kai, ta fi so na yi karatu…” “Maminki?” Ya furta yana kallona kallon da yasa na ji wani mugun tausayinsa ya kamani. Sai naga ya cije leb’ensa ya mik’e kawai ya ajiye cup d’in ya fice. Ji na yi kamar na bi shi amma k’afafuna sun kasa sai b’alle war hawaye na ji daga cikin idona. Ai kuwa na saka kukan sosai ina yi ina mayar da ajiyar zuciya….
Shikkenan na san na rabu da Ustaz idan ba’a yi wasa ba rabuwa ta har abada!
𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢.
Kin fara karanta k’arfe a wuta kuwa? Kin ji da’din labarin Arfa da Viper? Idan baki fara ba maza ki fara tunda ke kan ki kin san Alk’alamin Aysha cool baya rubuta shirme. Rubutu ne take yi mai inganci wanda take rubuta abubuwan da suke faruwa zahiran da hanyar warwaruwar matsalar. Kada ki manta marubuciyar k’anwar Maza ce gaba da gabanta, cutarwa… maza ki fara ana kan free pages ina tabbatar muku ba zaku yi nadama ba.
K’ARFE A WUTA……..
Don samun page 12 na Naga rayuwa ga wanda ba za su iya jira ba, ku duba arewabooks an saka. Ga link d’in nan.
Nagode
[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎
𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️
Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION
Arewabooks @nazeefah
https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ
Wattpad@Nazeefah381
08033748387.
★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 10
Da daddare muna zaune a ‘daki ni da Mami. Kalba take min tana sake zuga ni akan kada na yarda na auri Ustaz. Umma ta yi sallama ta tura k’ofar ta shigo. Idanunta zube a kan mu. Mami kuwa tana ganinta ta tsuke fuska. Zama ta yi a gefen gadon Mamin tana furta “Yanzu Fateema abin har ya kai haka? Ni ban ga abin d’aga hankali a wannan maganar ba, har kike neman ki tsiro da wasu halaye na daban da ba masu kyau ba. Wa’dannan abinda kike bakomai ba ne sai raina Abban su, kin koma san sarai makomar macen da ta raina Mijinta. Ni ban ga aibun Abinda Abbansu zai yi ba. Kamar fa gata ya yi muku ke da y’ar taki, auren namiji kamar Ustaz Ai duk uwa ta gari zata so wa d’anta……” Kallon da Mamin ta mata ne yasa ta tsuke bakinta tana kallonta da mamaki a fuskarta… “”Ke ce dai baki ga abin tada jijiyar wuya ba, ni na hango shi, kuma kuka d’auki maganar nan k’arama ni na shirya fito na fito da duk wanda ya ce zai mata aure a wannan y’an shekarun nata, wallahi ko Human right sai na kai mutum, in dai da gaske har zuciyarku kun bar min y’ar, ai sai ku bar ni na yi abinda zan yi da ita, sai dai idan nuna min za ku yi, ban isa da ita ba don ba ni na haifeta ba….” “A’a Fateema, duk maganar bata kai ga haka ba, Allah ya baki hak’uri.” Umma ta fa’da tana mik’ewa ta fice daga d’akin. Wani tsaki da ya tab’an zuciya Mami ta ja tana furta “So kike ta yi zaman aure da