Showing 21001 words to 24000 words out of 44320 words
aljanna!”.
Garkuwa kuwa a motar da suke sassayan numfashi ta fesar tare da baza ido tana ƙarewa Qatar kallo tare da ƙudurtawa a ranta in sha Allah sai tayi littafin a Qatar.
Su Garkuwa ɗiɗɗiri sai baza na mujiya ake ana kallon kauyenci to ba fulatanar daji a tsakiyar birni Doha.
Aunty Amina kuwa cikin sanyi tace.
“Allah ɗaya gari bambam”.
A motarsu Ishmah kuwa a hankali ta kalleshi cikin sanyi tace.
“Ya naga sunyi can mu munyi nan”.
Cikin kulawa yace.
“Su gida zasu wuce!”.
Cike da gajiya tace.
“To mufa?”.
Yana ɗan matsota yace.
“Zaki gani”.
Dai-dai lokacin kuma taga driver ya ɗan karya kwana ya fuskanci wani ƙaton gada daya yake gicciye a tsakiyar tekun dake zagaye da ƙasar, da sauri ta rumtse idanunta saboda iya ganinta ruwane a kwance bila haddin.
Tafiya mai tsawo sukayi kana taji an buɗe musu Gate.
Yah Salam shine abinda tace dai-dai lokacin da idanunta suka sauƙa kan wani Mashahurin Hotel Rixos Gulf Hotel Doha, wani irin hotel ne na alfarmar kai da gani ma kasan bana yara bane.
Wanda ke jan motar ne ya fito, tare da ɗaukar trollybag d’in Ishmah, kana suka fito suka bishi a baya.
Sassayan numfashi mai nauyi ta fesar a hankali da ta kutsa kanta cikin Parlour.
Ya ilahi ya mujibat da'awati, sune kalaman da ta faɗa saboda wani irin ni'imtaccen ƙanshin gami da sanyi mai kashe jiki da zuciyar ɗan Adam.
Jujjuya kwayar idanunta tayi tana ƙarewa Parlorn kallo a saman lips inta tace.
“Wannan a duniya ne haka? Ya Allah ka bamu aljanna”.
Sai kuma ta ɗan kalleshi jin ya kamo hannunta tare da amsar trolly bag din.
Shi kuwa driver’n juyawa yayi ya fita.
A hankali suke takawa har suka shiga cikin bedroom ɗin, a hankali ya sauƙe numfashi kana yace.
“Shiga kiyi wonka, kafin a kawo miki abinci!”.
Yess tana son yin wanka Amman jin ni'imomin cikin ɗakin yasa taji wani irin sassayan bacci na diro mata.
Shi kuwa Taj drawer’n dake kafe daga dungu har dungu ya ɗan buɗe mata side ɗaya tare da cewa.
“Ga sleeping dress a nan in kin fito.
Ya ƙare maganar tare da sa hannunsa ya zaro wata tattausan jallabiya Black blue mai sheƙi, kana ya fita Parlour.
Bayan tayi wanka ta fitone kuma ta kimtsa kanta cikin wasu soft sleeping dress na companyn Gucci riga da wondo ne masu kyau da shek’i had’i da ɗan kaurin da zasu kareta daga tsananin sanyin AC’n dake d’akin, rigar pink and white color ce, sai kuma white headband me kyau da tasa a kanta tare da tubke gashin kanta, idanunta ta d’an lumshe alokacin da ta d’au d’aya daga cikin unisex perfumes d’in da ta gani akan tsararren dressing mirror d’in dake d’akin, turaren me suna Symphony na companyn Louis Vuitton ta fesa ajikinta, sosai kuwa kamshin yayi mata dadi.
Cike da gajiya ta zauna a bakin gadon,
Da sauri kuma ta lumshe idanunta saboda jin kamar anayi mata lilone sunkuyar da kanta tayi tana shunshunan kanta da kanta saboda jin yadda take baza ni'imtaccen ƙamshi.
Lokaci d’aya kuma sai ta kalli wayarta jin alamun an turo mata saƙo a WhatsApp.
“tana buɗewa kuwa taga Hamisu ne, sai kuma ta ɗan kalli saman profile picture d’inshi ganin alamun yasa abu a status ɗinsa.
A hankali ta danna kanshi.
Cikin wani sanyi mai cike da gajiya kasala, ta zame ta kwanta a bakin gadon tana fuskantar ƙofar shiga.
Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara silalo mata.
Dai-dai lokacin kuma Taj ɗin ya shigo sanye da jallabiya sai faman baza fitinannen ƙamshi mai kashe jiki da zuciya yake.
Ido ya ɗan zuba mata ganin alamun bata ma san ya shigo ba, da fari yayi zaton tayi bacci ne, sai da ya ɗan matso kusa kuma yaga idanunta na zubda hawaye.
Cikin sanyi ya fara takawa yana matsowa bakin gadon.
Tare da yawo da kwayar idanunsa akan dukka sassan jikinta.
Ahankali ya zauna a ƙasan gadon dai-dai inda kanta yake, cikin nutsuwa ya daidai ta fuskarsa da tata fuskar.
Kana asanyaye cikin wani irin fitinannen yanayi mai hana zuciya sukuni ya kusan to da fuskarsa tare da zira....
********************** ? **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************? **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ? **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ? **************************
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286: 📝🕋💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*AYASHA ALIYU GARKUWA*
*BOOK 2 PAGE 7*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
“Bazan iya zama a gaban ka ba, kana suffanta min kanka da waɗanan mugaye, ƙazaman, lalatattun, halayyar da nasan ba naka bane, kuma bazaka aikata ba, Wallahi tallahi bazan taɓa yarda da kaiba koda zaka kwana dubu kana faɗa min waɗanan kalaman ne.
Please dan Allah Tajj kace min wasa kake min, kace min ƙarya Addawa tayi min, kasan na sani cewa kai maitsarki ne kuma tsarkakken da zuciyata tasashi a sahun masu cikar imani kuma nagartataccen da bani da haufi kan nagartarka Please dan Allah kada ka faɗa min kalaman da zasu fasa min zuciyata”.
Taƙere mgnr cikin Muryar kuka tare ysyyarfa hannu ɗaya, ɗaya kuma na bisa ƙirjinta.
Shi kuwa Tajj da sauri ya tashi tsaye tare dasa hannunsa ya kamo hannunta da take ta yarfawa tamkar wacce ta ƙone.
Wani irin nannauyan numfashi ya fesar mai zafi tare da sakin ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya dake nuni da kaso 50 na cikin dari na damuwar dake nuƙurƙusar rayuwarsa ya bar zuciyarsa.
Addawa kuwa tun sanda yacewa Ishmah yayiwa Laylah fyaɗe ta shigo da sallamar da basu jitaba bare su amsa mata, gefensu ta tsaya a duk da basu gantaba.
Shi kuwa Taj cikin sanyi ya jawota jikinsa tare da yi mata amintaccen ruƙuma murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Babe haka akace wai ni nayiwa Laylah fyaɗe, kuma har Ummeey na da Yah Abana sunyi fushi dani”.
Cikin jujjuya mishi kai da zubda hawaye tace.
“Karya ne Tajj wlh ƙazafi akayi maka! Ban yarda ba, baka aikata hakaba waye ce kai kayiwa Laylah...”.
Sau kuma ta gaza ƙarasa kalmar.
Shi kuwa cikin sanyi kamar a narke mgnar ta fito.
“Meymey ce tacewa Yah Abana ni nayiwa Laylah fyaɗe, kuma Laylah ta tabbatar gashi tsorona takeji”.
Da sauri ta ɗan janye jinkinta daga gareshi tare da jujjuya kanta tana faɗin.
“Allah ya isana ban yafe mataba, tayi ma ƙazafi mafi muni, ta rabaka da mutani mafi soyuwa a gareka, tayi maka illar da har abada zuciyata bazan taɓa iya yafe mata ba”.
Sassayan numfashi Addawa ta fesar domin itama da fari taji tsoron ƙarshen kalaman Ishmah kar tace bazata zauna da Tajuddeen ɗin ba”.
Ita kuwa Ishmah a hankali ta zame ƙasa ta zauna, wanda haka yasa shima ya zame ya zauna.
Suna fuskantar juna, guiwowinta na manne da guiwowinsa cikin sanyi da alamun ta fara dawowa gayyacinta, tunda yace mata ance ne bawai shi da kansa bane yake jaddada mata cewa yayi fyaɗen ba.
Murya a sanyaye tace.
“Allah ya isana bazan taɓa yafewa duk wanda yayi maka wannan ƙazafinba, Saboda an sawa Al-AHLI AFISHA tabo mai wuyar mancewa, zan ƙare ragowar rayuwata dayi maka addu'o'in neman sakkayar duk wanda yayima ƙazafin nan, da yi mishi addu'o'in tonon asirinsa da rashin samun duk kwanciyar hankali a cikin burinsa kai harda addu'o'in ganin azab...”
A hankali ta lumshe idanunta hawaye masu zafi na kwaranyo mata saboda jin yasa tattausan tafin hannunsa ya rufe mata bakinta.
“A'a Babey banda addu'o'in azaba domin Bama fatan ko wanne musulmi ya faɗa cikin azabar Allah”.
A tare suka kalli Addawa jin tana cewa.
“Alhamdulillah Ishmah kin kasance yadda muka zata, kin ƙarfafa yaƙini da Amincin Tajuddeen a kanki, ko duniya duk zasu gaza fahimtarsa ke zaki fahimceshi.”
Shi ma Taj a hankali yace.
“Mar'atussaliha”.
Da sauri Addawa ta miƙe ta fita.
Ita kuwa Ishmah cikin sanyi tace.
“Tajj wannan ƙazafin ne yasa duk rayuwarka ta ƙuntata?”.
Kanshi kawai yake jijjiga mata dan baya jin zai iya mata cikekken bayanin a yanzu saboda yafi son sai ƴan uwanta sun tafi baya kuma jin zai iya faɗa mata hukuncin Yah Abana na cewa in ya sake yiwa Ummeeyshi mgn ko suka haɗu a kan auren iyayen nasa.
Shigowar Addawa da trayn abincin da ta shirya musune yasasu ɗan gyara zama a plate ɗaya ta zuba musu tare, da ajiye musu spoon guda biyu kana ta tace.
“Bismillah kuci abinci shine abinda zai sama min nutsuwa, bari inje in kawo muku tea.”
Jim kaɗan da fitan ta dawo ga mamakinta ko taɓa spoon ɗin basuyi ba koda ta matsa suci abincin tea ɗin suka amsa suka sha.
Suna gama sha ana kiran sallan azahar, wanda haka yasa shi Taj yin al'wala ya fita tare da Adam da Bilal da yanzu suka shigo.
Bayan sunyi sallan azahar, a ɗakin Ishmah inda nan Aunty Amina da Goggo Dijan suke, ta nufa.
Zaune ta samesu da jakukkunansu a gabansu suna shiryawa, cikin sanyi tace.
“Ayyah Aunty Amina me kuke sauri haka tunda ance goben ma sai gab da Magrib jirginku zai tashi”.
Aunty Nana da yanzu take shigowa ne tace.
“Yo ni da zan samu ma mu tashi yau ai da yafi min”.
Sai kuma tayi ƙasa da murya tacewa Garkuwa dake bayanta.
“Saboda nayi kewar mijina”.
Ɗan dungure kanta tayi tare dayin ƙasa da kai suna dariya.
Nan dai suka shiga sukayi ta hira, sai da aka kira sallan la'asar kana suka tashi sukayi salla.
Bayan an idar da salla Khadija ne ta kalli Aunty Nana da Garkuwa tare da cewa.
“Bari mu shiga kitchen nida Zulaihat me zamu dafa mana?”.
Da sauri Aunty Nana tace.
“Kuyi mana fried rice tun jiya naso muyi shi”.
Kai Khadijah ta gyaɗa kana ta fita, a Parlour ta samu Laylah da Zulaihat.
“Mu shiga kitchen ko!”.
Tace musu tare da wucewa kitchen ɗin suna biye da ita a baya.
Bayan fitan Khadija da kaɗan Addawa ta shigo gefen Ishmah ta ɗan zauna tare da kallon yadda ta zauna tsakiyar yan uwanta tana tayi musu magiyar bata gaji da suba.
“Hmmm to yanzu dai tashi kije ki ɗan samawa Tajuddeen,abinda zai ɗanci”.
Cikin kulawa da son ɓoyewa ƴann uwanta damuwarta da sirranta matsalar mijinta da ƙaddararsa tace.
“Ya dawo ne?”.
Addawa na miƙewa tsaye tace.
“Eh yanzu ya shigo ya haura sama”.
Ta ƙare maganar tana fita
Ita kuwa Ishmah juyowa tayi ta kalli Garkuwa jin tana cewa.
“Muje to kiyi wani ɗan abin”.
Miƙewa tayi tare da bin bayanta ganin tuni tayi waje.
Cikin kulawa ta ɗan kalli Ishmah tare da ɗaga marfin fridge dake kitchen kana tace.
“To me zakiyi mishi”.
Tana ɗan kallon Khadija dake gyara fruits tace.
“Abu mai ɗan sauƙi dai, dan yau tunda gari ya waye ba abinda yaci”.
Kai Garkuwa ta jinjina tare da buɗe fridge numfashi mai sanyi ta fesar tare da ɗan juyowa ta kalli Ishmah tana faɗin.
“Ya matsalar rashin bacci akwaita har yanzu?”.
Da sauri Ishmah ta gyaɗa mata kai.
Kai ta jinjina tare da dacewa.
“To in sha Allah yau zaiyi bacci, zo ki haɗa mishi giyar fulani”.
Zare ido Khadijah tayi tare da cewa.
“Ya Salam giya kuma?”.
Da sauri tace.
“Eh ta Fulani ba, kuma halattacciya ba haramtacciyaba”.
Ta ƙare maganar da fito da wani roba mai ɗan girma wanda ke cike da kindirmo, sai kuma ta kalli Ishmah tare da cewa.
“Ɗauko blanda can”.
Juyawa tayi ta ɗauko tare da ɗauraye cikinsa kana ta ajiyeshi.
Ita kuwa Garkuwa cup tasa ta ɗiba cikinsa uku tasa a bulandan kana ta kalli Khadijah tare da cewa, bani Ripe bananas guda huɗu!.
Ke kuma Ishmah ɗauki coconut ɗin nan ki goge bayanshi”.
To sukace baki daya.
Ita kuwa juyawa tayi ta ɗan ɗauki, robar vanillah Essenes cikin marfin ta ɗan saka a ciki kana ta ɓara Ripe bananas guda huɗu ta saka a ciki, sannan ta haɗa rabin coconut ɗin nan da Ishmah ta goge bayanshi sai kuma tasa sugar tea spoon shida dai-dai misali, kana ta watsa ice a ciki, sannan ta rufe tare dayin blanding inshi dai yadda takeso.
Sai kuma ta kalli Ishmah tare da cewa, kawo Bowl guda biyu masu ɗan girma, ki sasu a tray da kuma table spoon biyu”.
Kai ta jinjina mata tare da ɗaukar Bowl ɗin da yafi ɗaukar hankalinta, ita kuwa meda robar nonon tayi kana ta ɗauko na samansa da ta ajiye a gefe wanda furane a ciki.
Kwaya shida ta ɗauki tare da marmasasu cikin nonon kana ta ɗan ƙara yin blanding enshi kaɗan.
Sai kuma ta kalli Ishmah tare da cewa.
“Goge min sauran coconut ɗin”.
To tace kana ta fara gogeshi sir-sir.
Ita kuma Garkuwa Ice ɗin ta kuma ɗaukowa ta watsa kusan guda takwas takwas a cikin bowl ɗin kana ta juye damun akai kusan cikasu tayi.
Dai-dai lokacin kuma Ishmah ta miƙo mata coconut ɗin data gogeshi.
Amsa tayi ta watsa akai sai kuma ta ɗan tsinki Grapes kusan guda goma jere guda biyar-biyar tayi kan damun, tare dasa ƴan marafensu ta rufe, kana ta ɗan ƙara gyara killace tsabtar komai na saman trayn sannan ta miƙa mata.
“Gashi ki kai kusha”.
Tana ɗan lasan lip inta na sama tace.
“Hmmm harda ni?”.
Kai ta jinjina mata tare da cewa.
“Yanada amfani jikinki ai”.
Kai ta jinjina kana ta fita.
Ita kuwa Garkuwa sauran ta juyo a Bowl ɗaya, kana tasa guntun a cup Khadija ta miƙa ita kuma ta kaiwa Addawa na hannunta.
A hankali ta gyara zamanta tare da ɗan ƙara matsowa gaba kujerar Dinnin table ɗin.
Spoon ɗin tasa mishi cikin bowl ɗin tare da ɗan motsa ice ɗin da tuni ya narke saura kaɗan-kaɗan cikin sanyin murya da tausasawa tace.
“Dan Allah kayi haƙuri kasha, wannan koda bakaci abinciba, wannan dai ka sha”.
Kai ya ɗan gyaɗa mata tare da amsar spoon ɗin ya ɗan motsa shi ya ɗebo rabin spoon tare da Grapes ɗaya da diddingin coconut ɗin, a hankali ya matso gaban kujerar.
Lumshe idanunsa yayi lokacin da yaji garɗin nono da ɗanɗanon banana ga kuma garɗin coconut da na grape, sai ɗan zaƙi da sanyi daya fito mishi dai-dai yadda yake buƙata.
Cika spoon ɗin yayi a karo na biyu yasa a bakinsa.
“Masha Allah, Babe so sweet”.
Ya faɗa a hankali.
Sai kuma ya tura mata daya Bowl ɗin gabanta cikin sanyi yace.
“Sha, kiji yayi daɗi sosai”.
Tana ɗan lumshe idanunta ta jawoshi tare da fara sha.
Tas ya shanye nasa, sai kuma ya kalleta ganin ta ɗan ture Bowl ɗin gabanta gefe kaɗan alamun ta ƙoshi.
“Ki ƙarasashi Babe”.
Yace cike da taushin lafazi.
Ɗan miƙa tayi tare da cewa.
“Cikina ya cika”.
Sassayan numfashi ya fesar tare da cewa.
“Annabi yace, al'barkar abinci shine na ƙasan kwano fa”.
A hankali ta turo mushi bowl ɗin tare da juya idanunta kana tace.
“Ayyah to ka ƙarasa mana, ni ɗazuma nasha fruits bayan fitanka”.
Kai ya gyaɗa tare da jawo bowl ɗin, fes ya shanye rogowar nata.
Tana Murmushin jin dadi tare da tattaresu tace.
“Taj me zan dafa maka kaci da dare?”.
Ta ƙare maganar tare dasa hannunta kan Tissue box ɗin dake gefen hannunta Tissue ɗin ta zaro tare ɗan ƙara matsowa gaba, a hankali tayi mishi alamar ya matso da kanshi.
Ɗan matso da kansa yayi sai kuma ya ɗan lumshe idanunsa saboda jin ta ɗaura Tissue ɗin kan lips inshi tana goge lips ɗinshi.
Sassayan numfashi ya fesar yana maijin cikinsa yayi haniƙan a hankali yace.
“No kada ki wahal da kanki, ba inda wani abin zai kuma shiga cikina a dai yau”.
Ya ƙare maganar tare da ƙara matsowa da kyau, jujjuya ƙwayar idanunta tayi saboda ganin yayi mata alamun ta matso.
Kai ya jinjjina mata alamun eh matso.
A hankali ta kuma matsowar da ta basu cikekken kusanci.
Cikin sauri ta lumshe idanunta saboda jin ya manne tongue ɗinsa gefen lip inta na sama wanda nono ya ɗan taɓa kaɗan.
Hmmmmmmmmm suka ja numfashi tare.
Sai kuma ya haɗe tafin hannunsu yana mai ɗan lasan lip ɗinta.
Sai kuma tayi ɗan sauri janye kanta jin yana ƙoƙarin haɗe lips ɗintu baki ɗaya.
Cikin sanyi ta miƙe tsaye tace.
“Zanyi maka ɗan abu mai sauƙi dai kaci”.
Ta ƙare maganar tana fita.
Shi kuwa a hankali ya kife kanshi bisa table ɗin tare da yin pillow da hannunsa yana mai lumshe idanunsa.
Bayan sallan isha'i zaune suke suna cin abinci.
Kai Goggo Dijan ta ɗan juya tare da kallon Ishmah dake zaune ba komai a gabanta.
“Ya dai Boɗɗin Abba, kici abinci mana”.
A hankali ta buɗe baki murya a narke tace.
“Cikina kamar zai fashe, ji nake kamar ma iska ake ɗura min ƙoshin na ƙaruwa”.
Aunty Amina ce ta ɗanyi murmushi tare da cewa.
“Ai dama haka damu yake”.
Addawa ce ta amshi zancen da cewa.
“Wlh kuwa nima ji nake kamar ƙoshin ake ƙara min”.
Cikin sanyi Ishmah ta
Miƙewa tsaye tare da cewa.
“Ga ɗan karen kasalar mayataccen bacci, bari inje inyi wanka ko zan samu baccin ya watse idona ya watstsake dan wlh yau dai so nake muyi kwanan zaune musha hira”.
Aunty Nana ce ta ɗanyi ƙasa da murya cikin raɗa tace.
“Ke dai faɗi gsky kwanan zaunen kashe arna da oga ba, ba kwanan zaunen hira da muba, in kin haura sama ai ko motsinki bazamu kuma jiba”.
Hararanta tayi da idanunta dake cike da bacci daga nan ta wuce bedroom ɗin dasu Garkuwa suke dan taga nan akwatunanta suke.
Tana shiga ta wuce bathroom dan yin wanka.
Su kuwa a Parlour suna gama cin abinci, Khadijah da Zulaihat suka tattare Wurin kana Zulaihat tayi wanke-wanke tare da kimtsa komai na kitchen ɗin.
Kusan duk a Parlour suka zauna.
Juyowa Garkuwa tayi tare da kallon Laylah dake kwance gefen Khadijah tayi pillow da cinyarta.
“Jekice Ishmah tazo ta kaiwa Uncle Taj dinner ɗinsa kar ta mance dashi”.
To Laylah tace tare da miƙewa da sauri ta nufi ɗakin.
Tsaye ta samu Ishmah cikin tattausan sleeping dress royal blue da ratsin white da akayisu da zanen heart, sleeping dress ne da zasu tafi da AC weather.
Riga da wando ne, wondon iyakarsa ƙasan guiwa ne kaɗan wanda yake da roba daya kama wurin sai kuma samansa da roba mai ɗan faɗi da ya lafe ya manne kan cikinta da ƙugunta, hakan yabawa mazaunanta damar sakewa sar-sar ciki, rigar kuma mai gajeren hannuce, sai hula, wanda itama ƙasanta keda ɗan