Showing 42001 words to 44320 words out of 44320 words
gama waya da Addawa duk ƴaƴanta mata ta kirasu ta basu labarin yadda akayi, hakan yasa kaso 40 na ɗarin cikin damuwarsu ya bar zuƙatansu sun huta.
Ajiye cup ɗin tea ɗin yayi bisa Tray kana ya ɗan turashi gefe, ya kalli Baby face ɗin cikin kulawa yace.
“Babey Are you okay?”.
Sassayan numfashi ta fesar tare da lumshe idanunta murya a kasalance tace.
“A I'm so tired, bacci nakeji”.
Ta ƙare maganar tare da buɗe idanunta a hankali ya ɗan gyara zamansa tare da matsowa kusa da ita, hannunshi yasa ya jawota jikinsa, sai kuma ya ɗan jingina bayansa da jikin kujerar dake bayansa.
Ware sawunsa yayi ya sata a tsakiyar sawun nasa kana ya miƙe sawun.
A hankali ya ɗan ƙara jawota, jikinsa tare da kwantar da ita kan cikinsa ya manna kanta kan ƙirjinsa.
A tare suka sauƙe numfashi gami da lumshe idanunsu.
A hankali ya manna lips inshi kan goshinta yayi mata sassayan kiss.
Hmmmmmmmmm suka ja numfashi tare shaƙan ƙamshin jikin junansu.
A hankali ta ɗan gyara kwanciyarta bisa jikinsa.
Gefen lip inshi na sama ya ɗan ciza da ƙarfi saboda yadda yaji lafiyar jikinsa na amsa yanayin da tunda ya shiga iftila'in nan bai sake jinsa ba.
Dogon numfashi yaja tare da maida kanshi ya jingina.
Ethiopia.
“Ummi ce tsaye gefen Adaya dake zaune bakin a Dinnin table tare da matse ruwan Lemon ɗin data yanka cikin peppered chicken da takeci, da sauri ta yamutsa fuska saboda gani take kamar ita ke cin masifeffen yajin da ake gaurayeshi da tsamin.
“Kici a hankali mana”.
Ta faɗa tana zama gefenta.
“Sauri nake zan tafi”.
“Wurin rawa ko?”.
Ummin ta tambaya cike da takaici.
“Tana ɗan matse lemon ɗin tace.
“A'a zamuje ayi mana E passport ne”.
Cikin sauri tace.
“Na zuwa ina”
A taƙaice tace.
“India”.
Cikin takaici tace.
“Da izin waye zakije”.
Miƙewa tsaye tayi tana goge bakinta da Tissue tace.
“Da izinin Ubangiji, in dai Allah ya yarda zanje, yardarsa kaɗai kuma nake buƙata”.
Ta ƙare maganar tana sauƙa daga kan steps Dinnin table ɗin tare da jujjuya ƙugu da ido kawai ta iya rakata, dan tasan Adaya bata tsoronta bare shayinta kai Abpu ma ba tsoronsa takeji ba.
Aminullah dake kwance a Parlour'n ya ɗan ja gajeren tsaki, haransa tayi kana ta wuce ta tafi tana faɗin.
“Ni dai kuyi min addu'a Allah ya bamu sa'a, tunda dai kun san cewa nasarar nan dai ba tawa bace ni kaɗai, ina samun nasara tamkar ku kuka samu, musamman Abpu dan sai na fiddashi waje anyi mishi aiki”.
Kasake kawai sukayi suna kallonta, har ta ɓacewa ganinsu.
Qatar
Da dare misalin ƙarfe goma,
Kwance a kan gado tayi ruf da ciki, ta ɗan ɗaura ƙirjinta bisa pillow tana riƙe da wayarta video call takeyi dasu Khalid a wayar Hamisu sai kuma tace a kaiwa Abba wayar. Bayan sun gaida ne tayi Murmushin cikin jin daɗi tace.
“Abba yanzu dai Hamisu ya daina kuka ko?”.
Yana kallon Khalid da Minat dake matsowa yace.
“Ah sosai ma, yanzu shike tausar Rahama ma kafin su tafi Gombe ita da Khadijah”.
Cikin sanyi tace.
“Yauwa Abba to batun zuwan Hamisu fa, wata biyu kaɗaifa zaiyi ya dawo”.
Ta ƙare maganar tare juyawa da sauri dan jin motsin mutum ya kwanta kusa da ita, kana yayi mgn.
“Barka da dare Abba”.
Murmushin jin dadi Abba yayi tare da cewa.
“Barka dai Tajuddeen ya koke-koken Boɗɗi na”.
Ɗan juyowa yayi ya kalleta ganin ta ɗan matsa gefe.
Sai ya ɗan ƙara matso da kanshi cikin girmamawa yace.
“Abba ta ɗan rage”.
Sai kuma yace.
“Yauwa Abba dan Allah a tsamma mana Hamisu yazo ko wata biyu ne muyi, Please Abba dan Allah”.
Kai Abba ya ɗan jinjina tare da cewa.
“To yanzu dai ga ƴaƴanku sun dameni in basu waya, sai da safe mayi magana Allah yayi muku al'barka”.
Ya ƙare maganar tare da miƙawa Khalid wayar wanda yaketa turo kai yana faɗin.
“Hi Uncle Taj”.
Murmushin Yayi tare da cewa.
“Hello my Son ya kake? Ina my Daughter da Dr Mahamud”.
Yayi mgnar cikin son yaran.
Tsalle Khalid yayi tare da cewa.
“Gasu can suna game ni uncle Hamisu yace in kawowa Abba waya”.
Yana ɗan ƙara matsowa jikinta yace.
“To kace ina gaidasu.”
Da sauri yace.
“Toh Uncle yaushe zaka kawo mana Mamey na. Nayi missing nata, Mamey I miss You so much”.
Murmushi tayi tare da cewa.
“Miss U to autana Mamey, ba kace Daddy ya yarda zaku zo a Ramadan ba”.
Da sauri yace.
“Ehh, kuma nace miki Ni ba auta bane ina son ƙanne masu cemin Yaya in samu ƙanwa muyi ta faɗa kamar yadda Uncle Hamisu da Aunty Rahama sukeyi, kuma ai Kinga Daddy ma da mace tayi auta”.
Ɗit-ɗit wayar ta bada sauti alamun Data ya ƙare.
Da sauri ta ɗan zaro idanunta waje dabida jin yadda yasa yatsunsa biyu ya ɗan matse lips inta fuska a kwaɓe yace.
“Kar ki sake cewa Khalid auta, kinji shima baya so, yana son ƙanne ahli Afisha.”
Ya ƙare maganar tare da ɗan zaro harshen sai ya ɗan lashi lips inta da ta cinno gaba.
Murmushin yayi ganin yadda ta rufe idanunta.
Lips ɗin ta ya zubawa ido, tare da shaƙan ƙamshin jikinta.
Sassayan numfashi ta fesar tare da ɗan turo tongue ɗinta ta ɗan lashi lips inta da.
Allah mai komai maiyin yadda yaso a lokacin da ya ga dama, wai ni da Taj ne a matsayin ma'aurata gamu ƙasa ɗaya gari ɗaya gida ɗaya gado ɗaya.
A hankali ta buɗe idanunta saboda jin ya ƙara matsowa gareta, kanshi ya ɗaura kan pillow da kanta yake, haka yasa suka zama suna fuskantar juna.
Ido cikin ido suke kallon juna, tamkar yau suka fara ganin juna.
A hankali ya ɗan mirgino ya matsota sosai.
Uhmmmm, suka dire numfashi a tare lokacin da ya manne lips inshi da nata.
Sai kuma yasa hannunsa bisa wuyanta, tare da fara mirza babbar yatsarsa ƙasan kunnenta zuwa bayan kunnen.
Yana mai lasar saman lips inta tamkar ya samu lollypop.
A tare suka rufe idonsu kuma a tare suka buɗesu.
Jawota jikinsa yayi tare da yi mata sahihin rugguma a haka bacci yayi awon gaba da su.
Da asuba hankali ya ke kiciniyar buɗe ƙofar Parlour dan so yake ya koma side ɗinsa yayi al'walan tafiya sallan asuba.
Addawa kuwa da tun fitowarsa taji alamun takun mutum ne yasa ta ɗan buɗe ƙofar ɗakinta,
Ido ta zuba mishi ganin ya juyo ya nufi ɗakin Ishmah.
A tsakiyar ɗakin ya sameta tsaye bisa alamu yanzu ta sauƙo kan gadon, a hankali ta ɗan sunkuyar da kanta tare da kallon rigar baccin dake jikinta wacce cibiyar ta ke fili, sai kuma wondon da iyakarsa guiwa cinyoyinta sunyi santal-santal a ciki.
A hankali ya kamo hannunta cikin sanyi yace.
“Babey ƙofar ba key a jiki ina kuke ajiyewa, muje ku buɗe min”.
Kai ta ɗan jinjina tare da yin ƴar miƙa tace.
“Kan Dinnin table Addawa ke ajiyeshi”.
Hanya ya nuna mata tare da cewa.
“Muje to”.
Kai ta gyaɗa mishi kana tayi gaba.
A hankali take takun Amman duk da haka bai hana mazaunanta yin mazarin da yasashi liƙa idanunsa a kansu.
A haka suka fito Dinning area ta nufa shi kuwa yana biye da ita a baya.
Ita kuwa Addawa ido take binsu dashi fuska ɗauke da murmushin jin daɗi a fili tace.
“In sha Allah farin cikinka zai dawo Taj domin kayi dace da Mar'atussaliha”.
Ta ƙare maganar a hankali.
Sai kuma ta kuma ware idanunta dai-dai lokacin da suka isa bakin ƙofar Parlour.
Key ɗin ta zira cikin ƙofar.
Shi kuwa Taj a hankali ya ƙarayin taku biyu zuwa uku, har dai ya isa gab da ita.
A hankali ta ɗan juyo lokacin da taji ya kife tafukan hannunsa kan hips ɗinta.
Sai kuma ya ɗan manna ƙirjinsa da bayanta, tare da cuso kansa tsakanin wuyanta da kafaɗarta juyowa ta ɗanyi, hakan yasa fuskantar mannewa da tasa cikin yin ƙasa da murya cike da raɗa yace.
“Ganinki a haka zaisa na gaza cika ƙudurina Ma'eesha Taj ɗinki zalamemme ne, Amincin zuciyarki ne burin rai da ruhi da jinin jikina a yanzu, shi kaɗai zai hanani ratsa mallaki na, Please Babey ki soni dan Allah”.
Cikin sauri ta rumtse idanunta saboda jin yadda lfyarsa ke bayyana a jikinta, murya can ƙasan maƙoshinta tace.
“Taj lokacin salla fa yayi”.
A hankali ya juyota gareshi ruggumeta yayi tare da ɗaura hannunshi kan mazaunan nata, ya ɗan mara tare da ɗan matsesu.
“Washhh Allah na Taj zafi fa”.
Tayi tambayar cikin narkekkiyar murya.
Murmushin yayi tare da ɗan lakace hancinta kana a hankali yace.
“Raki ko? Shogoɓatuna ki koyi jarumta fa, saboda ke ba matar ragwo bace”.
Ya ƙare maganar tare da matse cinyoyinsa.
Ita kuwa da sauri ta buɗe mishi ƙofar tare da nuna mishi hanyar fita.
Da sauri Addawa ta janye kanta sabida hango yadda surarsa ke tsaye cir a cikin jallabiyar.
Kan sallayarta ta koma tana istigfari tare da yiwa kanta faɗar abinda tai bai daceba na tsayuwa kallon ma'aurata da tafi kowa sanin zuƙatansu cike da begen juna suke.
Ita kuwa Ishmah ido ta rumtsa kana ta juya da sauri ta nufi ɗakinta.
Washe gari da yamma suna tsakiyar Parlour, miƙa mishi E passport ɗin tayi tare da zuba mishi ido dan so take taji me zaiyi dashi.
“Ina zakuje?”.
Addawa tayi tambayar dan taga alamun tafiya yake so suyi.
Yana mai ɗan taune lips inshi na ƙasa yace.
“Jordan zanmu je, Amman zamu fara ta Dubai?!”.
Da sauri ta kalleshi cikin jin daɗi yes Allah ya sani kuma duk wanda yake tare da ita yasan tana son zuwa Qatar da Jordan, Dubai ne ma bai wani cika damunta ba.
Girarsa ɗaya ya ɗan ɗaga mata.
Addawa kuwa da sauri tace.
“Afif ba Umrah zakuje ba, sai Jordan da Dubai.”
Yana ɗan jujjuya E passport ɗin yace.
“Ehh akwai abunda zanyi a Dubai da Jordan ɗin ne, masu mahimmanci.
Umrah sai mun dawo zamuje”.
Cikin sanyi Laylah dake gefen Ishmah ta ɗan kalleshi a hankali tace.
“Uncle Taj mu kaɗai da Addawa kawai zaku bari”.
Kanta ya ɗan shafa cike da son cire mata tsoronsa yace.
“Uncle Hamisu zaizo, shi zaike kaiku school”.
Da sauri tace.
“Yaushe zaizo?”.
Kai ya ɗan jinjina kana yace.
“Eh Next month”.
Cikin jin daɗi ta fara tsalle.
Ita kuwa Ishmah Addawa ta kalla jin tana cewa.
“Ku kuma yaushe zaku tafi?”.
Yana ɗan juyawa yace.
“Tuesday !”.
Cikin mamaki tace.
“jibi-jibi kuma?”.
Yana ƙoƙarin fita yace.
“Eh saboda akwai zaman da zamuyi da shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na U.A.E da Qatar Airline, shiyasa sukayi min komai na tafiyar, basu san inada mataba, sai yanzu da na gaya musu to suke neman E Password ɗin nata, dan su haɗa tafiyar tamu”.
Ya ƙare maganar yana fita.
Yana kuma mgnar zuci.
Dole in samu lokaci na musamman a ƙasa ta musamman a wurare na musamman domin in adana soyayyata a zuciya ta musamman, in tabbatar da Ma'eesha na a matsayin matar aurena ta musamman da fatan samar da zuriya ta musamman”.
Ita kuwa Ishmah ɗakinta ta nufa, tana shiga ta amsa kiran Garkuwa, a bakin gado ta zauna tare da gaisawa kana ta ɗaura ta ce mata zasuyi tafiya.
Cikin Murmushin Garkuwa tace.
“Ko kin fahimci cewa, mijinki na son samun dukkan lokacinki ne, da kulawarki, wata ƙil gani yake Qatar tayi muku matsin kusancin su Addawa shiyasa yake son ku arce Dubai da Jordan.
Saboda so yake ku gina rayuwar da har gaban abadan bazaku manceba, Ishmah Taj yana da tsari a kanki, kiyiwa Allah da Manzonsa ki ɗauki magungunan ki da baki shanyeba ki tafi dasu.
Ki kula da kanki”.
Cikin sanyi tace.
“Ni banda lfy ma fa, kwanan duk marata ke fitinata wlh dauriya kawai nakeyi”.
Da sauri Garkuwa tace.
“To kiyiwa Allah da Manzonsa ki ki samawa kanki da mijinki lfy, kayyakine, na ɗura ma ki su kin shasu kin tsumi, sannan kin hanasu damar fidda aikinsu, dan Allah ki bada himma kiga amfanin gyara”.
Ta ƙare maganar cikin yin ƴar dariyar da tafi kama data mugunta.
Tana ɗan kwanciya tace.
“Nifa ba wani abu bane ni wlh ba ruwana”.
Cikin dariya sosai Garkuwa tace.
“Eh ai nima bance da ruwanki ba, ai Taj ne kaɗai zai gane da ruwanki ko ba ruwanki”.
Daga nan dai kuma tayi ta bata shawarwari na musamman.
Washe gari zaune suke ita da Addawa Laylah na tsakiyar su, cikin kulawa da son cire mata mugun tunanin da aka sawa yarinyar ta kamo hanunta cikin sanyi murya tace.
“Laylah ki daina tsoron Uncle Taj, shi ba mugu bane! Kuma ba shi bane yake zuwa ɗakinki, ke kin sani Uncle Taj yana sonki bazai so abinda zai cutar da keba, bare har yace zai kasheki, ko akwai wani abu na mugunta da ya taɓa yi Miki!?”.
Da sauri ta fara jujjuya kanta cikin yaƙini tace.
“A'a bai taɓa min ko tsawa ba, kuma na sani shi ba mugu bane”.
Da sauri tace.
“To ki daina tsoronsa babu abin da zai miki wancan ma ba shi bane sharri akayi mishi”.
Cikin sanyi ta ɗan jinjina kanta tana tunano wasu abubuwan da suka gabata sai kuma ta kalli Ishmah tare da cewa.
“Allah ko Aunty Ishmah?”.
Cikin son sama mata nutsuwarta tace.
“Wallahi sharri ne Laylah ki yarda dani”.
Cikin sanyi tace.
“Na yarda Aunty Ishmah nasan Uncle Taj ba mugu bane”.
Cikin jin sanyi Addawa tace.
“To ki daina tsoronsa ba abinda yayi miki kuma ba abinda zai miki”.
Cikin sanyi ta gyaɗa kai alamar to.
Washegari ranar Tuesday.
Da safe misalin ƙarfe bakwai saura jirginsu ya ɗaga Hamad International Airport Doho Qatar, suka miƙe zuwa Dubai kasan cewar tafiyar.
1 hour and 12 minutes ne Qatar, Doho to Dubai, shiyasa ƙarfe takwas da kwata dai-dai jirginsu yayi landing.
Suna isa suka samu tarba ta musamman daga shugaban Dubai Airline ɗinsu da zai shugabanci taron da zasuyi na yankin Larabawan.
Cikin sauri ta juyo ta kalli Taj ɗin dake zaune gefentan dai-dai lokacin da taga sun kutsa cikin...!
*Littafin INDA RAI na kuɗine ki biya kuɗinki ki karanta cikin aminci ba haƙƙin kowa a kanku. 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276*
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
********************** ? **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************? **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ? **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ? **************************