Showing 33001 words to 36000 words out of 44320 words
ne, bacci ya sureta.
Shi kuwa Taj ɗin a hankali yake sauƙe numfashi tare da taune lips inshi na ƙasa, so yake yayi bacci ko ya suma ko Allah zaisa yaji sauƙin zafi da ƙuna gami da raɗaɗin da zuciyarsa keyi masa, to ya zaiyi da rayuwar sa, ina zai shiga ya samu sassauci, kullum tabbatar a yiwa Laylah gyaɗe ƙara bayyana sukeyi ga batun cikin da akace tana ɗauke dashi, shine babbar matsalar rayuwar sa, ganin cewa ya cinye fiye da rabin daren a nazarin da bai samu mafita bane, yasa ya miƙe yaje yayi al'wala kana ya dawo Parlour ya rinƙa nafilfili tare da tilawar Qura'ani mai girma gami da tasbihai da neman sassaucin zafi da ƙunar ƙadaddarorinsa.
Washe gari ranar Friday, kasan cewar yau ba aiki dan a tasu doka da ƙa'idar ƙasar Jumma'a da asabarne ranakun hutun mako, ranar Sunday to Thursday ne ranakun aikinsu.
Tsaye take a tsakiyar Parlour, tare da lumshe kumburarrun idanunta, ringing ɗin da wayarsa keyi ne yasata buɗe idanunta.
“Dr Abbas”. Ta furta saman lips inta lokacin da taga shine mai kiran.
“Na rasa meyasa Taj baya son riƙe wayar nan yanzu wayarda yasha cemin ta family insa ne da shaƙiƙansa makusanta shiyasa bai rabuwa da ita, yanzu kuma sam bai riƙeta ma, sai dai ya riƙe waccar da yake cewa layin ciki na al'ummar duniya baki ɗaya ne.”
Sai kuma tasa hannunta ta ɗauki wayar ganin kira ya kuma shigowa.
A dai-dai lokacin kuma Taj ɗin ne zaune, a balcony dake bayan dinning area ɗinsa, zaune yake bisa kujerar sai System nashi dake gabanshi bisa ɗan madaidacin table ɗin dake gabansa.
Yayinda ya kafa wayarsa yana video, a shafinsa na TikTok inda yake karanta suratul Khaff kamar ko wacce ranar Friday domin tunasarwace ga al'ummar musulmi, kasan cewar yana bin ayoyin daki daki ne, so daga aya ta 59, 60, 61, 62. Yayi kana yayi saki video bayan ya ɗanyi rubutu a sama kaɗan, Don't forget to read suratul Khaff on Friday. Jumma'at Mabrooq to all Muslims Ummah.
A hankali ya gyara zamansa tare da lumshe idanunsa kana ya buɗesu yana kallon fuskarsa a cikin Camerar wayar tasa da yatsarsa ta ɗan taɓa, ya shiga kamar zai yi wani video ɗin.
Cikin sanyi ya kuma lumshe idanunsa da suka sauya launi tun ranar da Yah Abana ya koreshi basu sake dawowa asalin launinsu ba.
Wani irin rauni, bege, so, ƙauna, gami da kewar iyayensa da ƴan uwansa da ahlinsa baki ɗaya yakejin.
Ji yake tamkar yayi fiffige ya ganshi a tsakiyar Parlour Yah Abana wanda ya sani yanzu haka suna can suna cike a Parlour, sun sashi a tsakiya, ji yake tamkar zuciyarsa zata fashe dan so da begen ganin Ummeeynshi da Yah Abana, so yake ya ganshi a tsakiyar yayunsa da ƙannensa, ji yake yi yayi rashin da bazai manceba, da ya kamata yaye kansa da kare kansa da haka bata faruba da yau shi ya limancin Yah Abana kamar yadda ya saba tsawon shekaru in dai yana Ethiopia.
Ishmah kuwa a hankali ta ɗan haura saman dinning area ɗin, ido ta zuba wa ƙofar da zai sadata da balcony ganinta kamar a buɗe da ɗan sauri ta isa gaban ƙofar, tana ɗan jan handily ɗin kuma taga ashe a buɗe take.
Shi kuwa Taj haka nan yakejin.
Wasu irin zafafan hawaye masu masifar ɗumi suna tsatstsapo mishi cikin jijiyoyin idanunsa, haka nan yaji wasu baitukan na dira kan harshensa cikin harcen Amharic murya can cike da sanyi gami da rauni ya fara baitukan.
“Da Babana nake, nakayin tutiyyyyah”.
Yaja ƙarshen baitin cike da raunin da yasa hawayensa bayyana cikin ƙwayar idanunsa da hakan yasa idanun nasa yin wani irin sheƙi da ƙellin hawayen suka bada wani special collar mai tafiya da hankalin.
Dai-dai lokacin Ishmah ta ƙarasa fito hango shi zaune, ya dasa waya a gaba, kana ga wasu amintattun baitukan da yake yi wanda suka sa zuciyarta raunata har ta kai ga jikinta yayi sanyi, a hankali ta nufi inda yake zaune yana fuskantar ta, sai dai sam bai gantaba saboda zuciyarsa data raunata ga ruwan hawaye daya cika mishi ido.
Sassayan numfashi ta fesar tare da lumshe idanunta saboda taushin da zaƙin sautin muryarsa da ya wadaci jinta, a hankali ta zauna bisa kujerar dake fuskantar tasa dai-dai lokacin da ya sake maimaita baitin da yayi a forkon.
“Da Babana nake, nakayin tutiyyyah.”
Sai kuma ya lunshe idanunsa wanda hakan yasa hawayensa kwaranyowa kana ya motsa lips inshi a hankali yaci gaba da raira baitukan.
“Zamana ɗansa na halal shine kwalliyata, ta rayuwata ta cikin duniya.”
Sai kuma ya ɗan taune lip inshi na ƙasa da ƙarfi murya na rawa yaci gaba da faɗin.
“Yah Abana shine antal sababul zuwata duniyyyah”.
Zuwa yanzu rawar da muryasa keyi ya tsananta bazai iya ci gaba da rairai baitukan ba,
Sai sassayan shesh-sheƙan kuka daya kufce mishi.
Sai kuma yayi saurin ɗago idanusa ya kalli Ishmah da itama kukan ne ya kufce mata saboda tsananin tausayinsa.
Murmushin ƙarfin hali da jarunta yayi tare da miƙa hannunsa zai ɗauki wayar, dai-dai lokacin kuma itama Ishmah ta miƙa hannun ɗaukar wayar, hakan yasa wayar ta faɗi da sauri ta sunkuyo ta ɗauki wayar garin ɗauka kuma yatsarta yayi sending video ya tafi duniyar TikTok.
A kuma dai-dai lokacin kiran Dr Abbas ya sake shigowa, piking call ɗin tayi kafin ta miƙa masa, murya na rawa tace.
“Dr Abbas ne yaketa kira tun ɗazu”.
A hankali ya ɗan ƙara matsowa gaba, ga zatonta wayar zai amsa, sai kuma taga ya kai hannunsa kan kuncinta tare da fara sharce mata hawayenta cikin sanyi da taushin lafazi yace.
“Kiyi haƙuri ki yafe min, inata zama sanadin saki zubda hawaye.
Na kasa cika alkawarin da nayiwa Abba na hanaki zubda hawaye, dole in nemi yafiyarsa bisa kasa cika mushi alƙawarin saki farin ciki”.
Ya ƙare maganar tare da tallabe fuskantar da tafukan hannunsa.
Cikin sanyi ta ɗaura nata tafukan hannunta kan nashi daya tallabe fuskantar murya cike da tautasaya tace.
“Baka gazaba Yah Sheykh dan ba abinda ka rage ni dashi, nice na gaza zame maka mai share ma hawaye.
Nice na ƙasa saka farin ciki, na gaza mantar da kai damuwar zuciyarka na kasa zame makar mar'atussaliha”.
Ta ƙare maganar tana lumshe idanunta saboda jin yadda yake murza yatsunsa kan kumatunta.
Shi kuwa Taj wani irin lumshe ido yayi yana mai jin kalmar mar'atussaliha data kira yana mishi yayyafin sanyi a zuciyarsa.
Kiran Dr Abbas daya kuma shigane yasa ta ɗan janye fuskantar tare da cewa.
“Ayyah ka amsa tun ɗazu yake kiranka”.
Kai ya gyaɗa mata kana, ya amsa kiran tare da ƙara wayar a kunne yace.
“Wa alaikassalam, kun iso ne?”.
Cikin kufula Dr Abbas yace.
“Ban saniba”.
Ɗan guntun Murmushin yayi tare da cewa.
“Dr Amdaz da Bilal suna Airport ɗin ai tun da aka sauƙa sallan jumma'a suna can”.
Cikin tsuke fuska Dr Abbas yace.
“Na fika sani ai, tunda sun ɗaukoni har gani a Parlour Addawa harma naci abinci.
Kai da kai na jira sai in bushe a can ko”.
Ɗan gyara zamansa yayi tare da cewa.
“Barka da isa lfy”.
Da sauri Dr Abbas yace.
“Kaga kada ka kashe min waya, ka sauƙo ina jiranka, ga Dr Farida tana son isa masauƙinta”.
Cikin mamaki yace.
“Ha'a wai da gaske tahowa tayi?”.
“To ka sauƙo ai zaka ga zahiri”.
Cewar Dr Abbas.
Yana ɗan tsuke fuska yace.
“No kada ta jirani, Dr Amdaz zai bata key Bilal ya kaita, kai kuma da Dr Amdaz ku jirani”.
Yana ida faɗin hakan ya katse kiran.
Cikin sanyi Dr Farida ta miƙe tsaye bayan da Dr Abbas ya gaya mata yadda sukayi.
Da sauri Addawa tace.
“Bari a kawo miki abinci ki tafi dashi”.
Ɗan Murmushin kirsa tayi tare da cewa.
“A'a barshi kawai in naji yunwa zanzo nan ɗin muyi dinner in kuma banji yunwaba sai da safe zanzo muyi breakfast”.
Cikin murmushi Addawa tace.
“To a huta gajiya”.
Daga nan Bilal ya ɗauketa suka tafi.
Tsakanin gidanta dana Taj ɗin a ƙalla akwai gidaje 8, kuma two bedrooms ne sai big Parlour and dinning area sai kitchen da ɗan ƙaramin store, kusan haka gidajen Doctors ɗin suke, sai dai akwai masu 3 bedrooms.
Suna shigowa Parlour'n Dr Abbas yayi murmushi tare da kallon Ishmah dake cikin Dubai Abaya onion color kai ya jinjina cikin jinjina kai ya ɗan rungume Taj tare da cewa.
“Masha Allah, ka iya zaɓi Allah ya baku zaman lfy ya sanya alkhairi”.
Yana ɗan buge ƙeyar Dr Abbas ɗin yace.
“Amin ya Allah”.
Sai kuma ya sakeshi tare da rungume Dr Amdaz.
Murmushin Addawa tayi jin Dr Abbas nacewa Ishmah.
“Ƴar sa'a ko ince sarkin sa'a, kin samu mijin da matan duniya ke ribibi in one time kinyi dace da nagartaccen miji ina tayaki murna, duk da kinyiwa abokan aikin mu shigar sauri”.
Ɗan murmushi mai cike da kamala tayi kana tace.
“Haka shima yayiwa wasu bugun kwab ɗaya”.
Cikin dariya Dr Amdaz yace.
“Ai shima dama tun a school bugu ɗaya yakeyiwa komai ya kwashi abinda wasu suka shekara suna bugawa basu samu ba, baya cewa yana son abu ya rasa”.
Suna zama Taj ɗin ya ɗan kalli Laylah da ta miƙe da sauri tabi bayan Ishmah data nufi ɗakinta.
Addawa da Zulaihat kuwa kitchen suka nufa.
Washe gari ranar asabar.
Mexico.
Arfah ne kwance bisa gadon yana riƙe da waya, video da Taj yayi na baitukan akan mahaifinsa ya tura Family group insu, yayi playing video yafi sau shida,
Hawaye ne keta zuba daga idanunsa.
Imran dake zaune gefensa ne ya ɗan kallesa cikin disashewar murya yace.
“Yauma ina ta kiran Uncle Taj baya piking call ɗin”.
Murya can ƙasa Arfah yace.
“Imran kalli yadda Uncle Taj yake kuka, wai wanne irin zuciya ne a ƙirjin Malam, wlh ni na tura masa video nan sai dai yayi min duk abinda yaga dama, wai so suke baƙin ciki ya kashe Uncle Taj ne, meyasa duk basu da imani”.
Da sauri Imran yace.
“Me malam ɗin yace? Yaga video ne?”.
Yana tashi zaune yace.
“Eh ya gani, baice min komai ba, a group ɗin mafa sai imojis na kuka kawai akayi ta turawa babu wanda yace ko ƙala”.
Cikin sanyi Imran yace
“Arfah ya za'ayi suyi mgn mahaifinsufa cewa yayi duk wanda yayi alaƙa da Uncle Taj ko ya kira sunansa bai yafe masa ba”.
Ya ƙare maganar tare da kiran Taj ɗin.
Qatar.
Zaune yake bisa Sallaya duk hankalinsa na kan System nashi bisa alamu abu mai mahimmanci yakeyi.
Ita kuwa Ishmah kwance take bisa 2 sitter dake bayansa.
A hankali ta ɗan buɗe idanunta ta zubasu kan System ɗin nashi, sai kuma ta kalli wayarsa.
“Imran ne fa kayi piking call ɗin kullum sai ya kirafa”.
ta faɗa cikin muryar bacci, kai ya jujjuya mata alamun a'a, sai kuma yayi piking call ɗin tare da miƙa mata kana yayi magana a hankali.
“Kice masa na tura musu kuɗi, in akwai abinda suke so ba sai ya kirani ba”.
Jin Muryar Imran na faɗin.
“Hello Uncle Taj, kayi haƙuri bazamu iya nesanta da kaiba”.
Jin haka ne yasa Arfah saurin amsar wayar tare da cewa.
“Uncle Taj kasan saura mana wata biyu fa muyi huhu kuma bazamo Ethiopia ba, zaka zo ko”.
Kallon juna sukayi da sauri jin muryar Ishmah tana mgna cike da kulawa da alamun ta sansu.
“So sorry Imran Arfah Uncle Taj, ya fita ya bar wayar a gida, Amman in ya dawo zai kiraku”.
Da sauri Imran yace.
“Afwan wacece ke?”.
Wani sassayan numfashi Taj ɗin ya fesar lokacin da yaji tace.
“Aysha Abdullahi Matawalle, Aunty Ishmah.
*Mrs Uncle Taj”.*
Sake kallon juna sukayi da sauri sai kuma Imran yace.
“Ayyah Aunty Ishmah da gaske, ke matar Uncle Taj ne? yaushe kukayi aure? Yanzu a ina kuke?”.
Cikin son cire musu shakku tace.
“Wallahi kuwa ni matarsace ta Sunnan, last two weeks ago aka ɗaura mana aure A Adamawa Nigeria.
Yanzu kuma muna Doha Qatar.
Cikin sauri da jin gamsuwa da kalaman Ishmah Imran yace.
“Toh My Aunty na yarda, Amman Uncle Taj na kusa ko?”.
A hankali tace.
“Eh”.
Ta faɗi hakanne saboda alama da Taj ɗin yayi mata na cewa ta faɗi eh ɗin.
Da sauri Arfah yace.
“My Aunty kice yayi haƙuri ya amsa kiran mu, mu yana da mahimmanci a rayuwarmu, kuma ba ruwanmu da shara ɗin Malam dan mu ba yayansa bane jikokine, yayi ikonsa iya yayansa bandamu jikoki”.
Ɗan sunkuyar da kai Ishmah tayi kaɗan dan taji me yake cewa.
“Kice musu suyi haƙuri komai nada lokaci kada su rinƙa kirana, ki basu number'nki su rinƙa kiranki ke ko Addawa suna jin labarin mu, in kuma akwai abinda suke so, su rinƙa gaya Miki sai ki gaya min, kice kada su damu, ina cikin lfy dani dake matata da Laylah da Addawa da Zulaihat ɗin ta”.
Kusan a tare Imran da Arfah suka rungume juna dan sunji duk abinda yake faɗa.
Alhamdulillah yanzu sun ƙara gamsuwa Ishmah matarsa ce, gashi sunji yana Qatar kuma tare da Addawa da Laylah ɗin harda Zulaihat.
Sun ji sauƙin raunin gane yana da makusanta.
Cikin jin daɗi suka haɗa baki wurin cewa.
“Yess Uncle Taj, muji muryarka, kuma zamuyi yadda kace, zamuke kiran our Aunty, in mun samu hutuna zamuzo Qatar”.
Murmushin Ishmah tayi ganin shina Taj ya ɗan saki fuska sun mance cewa zasu iya jinsa tunda ta matso da wayar.
Cikin sakin fuska tace.
“Uncle yace karku zo”.
Da sauri Arfah yace.
“Our Aunty ai wurinki da Addawa zamuzo ba wurinsa ba”.
Sai kuma Imran yayi sauri cewa.
“Yauwa Our Aunty dan Allah ki bamu number, ki kulan mana da Uncle Taj”.
Tana Murmushin ta basu number sabon sim ɗin daya mata na Qatar ɗin, daga nan sukayi sallama.
Numfashi ya ɗan fesar tare da ci gaba da abinda yake yi.
Cikin sanyi tace.
“Naga kamar takardar barin aiki kake rubutawa Ethiopia Airlines?”.
Yana ɗan lumshe idanunsa yace.
“Eh”.
Da sauri tace.
“To me yasa Taj pilot fa burinka ne! Ya za'ayi ka bar aikin!”.
ɗan juyowa yayi kalleta kana a hankali yace.
“Ba barinsa zanyi dukaba, Ethiopia Airlines ɗin zan bari, zan dawo Qatar Airways, dan har sun bani gurbin aiki”.
Sassayan numfashi ya fesar kana yace.
“Hakan yayi Miki?”.
Tana tashi zaune tace.
“Eh, fatan Allah ya bada Sa'a”.
Ta ƙare maganar tare da zama a gabansa, shi kuwa Amin yace yana kallonta cikin kulawa dan yaga zaman da tayi alamun so take suyi mgn.
Cikin sanyi tace.
“Dama so nake muje Al-AHLI AFISHA da Laylah, ayi bincike kan lafiyar ta akan fyaɗen da akace anyi mata da kuma batun cikin da akace, in ka yarda ka bani dama”.
Tunda ta fara mgna ya yi ƙasa da kanshi Saida yaji tayi shiru kana ya motsa lips inshi a hankali yace.
“Binci ken me kuma za'ayi bayan ita da kanta ta tabbatar miki da abinda akace nayi mata, kuma Doctors sun tabbatar da batun tana ɗauke da ciki.
Ma'eeshah wani binciken ya rage?”.
Da sauri ta fara jujjuya kanta cikin yaƙini da yarda na gsky tace.
“Ban yarda cewa kayiwa Laylah fyaɗe ba, kuma bazan taɓa yardaba, kawai ina tsorone kar wani yayi mata fyaɗen da gaske ne, shiyasa nake son tabbatarwa, sannan batun cikin kuma shine babban damuwata gwara mu tabbatar da sahihancin mgnar”.
A hankali ya ɗan gyara zamansa tare da jingina kansa da jikin gadon a hankali yace.
“Meyasa kika cika yarda da yaƙinin a kaina? Meyasa kike ganin cewa banyiwa Laylah fyaɗe ba?”.
Tana taune gefen lip inta na sama tace.
“Sabida nasan bazaka aikata hakanba, kuma baka aikata ɗinba, dan zuciyata bata yarda cewa ka aikata ɗinba, domin banji tsarkin ruhinka ya ragu a rainaba, domin na gamsu kai tsarkakekkene, kuma amintacce, ka yarda min muje asibitin in Allah ya kaimu gobe!”.
Cikin sanyi yace.
“Ma'eesha tsoro nakeji kar mgnar likitocin ya tabbata cewa tana da cikin Ma'eesha infa aka samu da gaske anyi wa Laylah fyaɗe zuciyata zuciyata zata buga, da wanne hujja zan kare kaina gaban Ubangiji da bisa amanar ta da na ɗauko a ƙasarsu da alƙawarin kare maraicinta”.
Cikin ƙarfin guiwa tace.
“In sha Allah alkhairi zamu jiyo kuma Alhamdulillah ko yanzu na ƙara samun yaƙini bakayiwa Laylah komai ba kawai gadar zare aka saƙa maka ita kuma aka tura tunaninta da yarintarta ta yarda kaine, ka gayawa Dr Amdaz da Dr Abbas su shiryawa aikin sai kuma Dr Sahra duk su shiryawa aikin”.
Kai ya jinjina cikin jin taraddadin tunanin hakan bai taɓa zuwa mishi ba.
“Dan Allah kira Dr Abbas da Amdaz ka gaya musu tun yanzu, kadama ka mance!”.
Cikin sanyi ya kira Dr Abbas yayi mishi bayanin kaɗan tunda shi yasan komai dama Yah Aryan ya gaya mishi.
Cikin gamsuwa da shawarar Ishmah Dr Abbas ɗin ya kira sauran duk yayi musu bayanin.
Washe gari ranar Sunday ƙarfe tara dai na safe suka isa nufi *AL-AHLI AFISHA CONSULTINGS HOSPITAL.*
Suna shiga harabar Asbitin B.....!
Alhamdulillah Allah ya nufa munci gaba. Yah Allah ya nuna mana ƙarshen littafin nan left dani daku makaranta da iyayenmu, yayunmu, yayanmu, ƙannnenmu, da dukkan dangin mu, harda maƙotanmu, da dukkan musulmai.
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286: 🍇🍇 *INDA RAI* 🍇🍇
*BOOK 2 PAGE 9*
Ku danna link dinnan dan shiga Group din Hausa Novel mai suna ANA ZATON WUTA A MAKERA: https://chat.whatsapp.com/GOia2rQSpDk3ewFUbK1JoL
A hankali Bilal yayi parking cikin harabar tamfatsetsen asibiti na gani na alfarmar, irin asibitin nanne mai tsari na alfarmar ba matsin ko cunkoso kusan komai na asibitin yana kamanceceniya da.
*TAJMUH CONSOLATION HOSPITAL* asibitinsu na Ethiopia.
Sai banbancin suna da abubuwan da ba'a rasaba.
Daga can saman benen aka rubuta.
*AL-AHLI AFISHA HOSPITAL*
da manyan baƙi masu sheƙin zinari.
Harabar asibitin yalwataccen ne domin parking spaces ɗin nasu, mai faɗine, wanda a ƙalla zai iya ɗaukan motoci 25, zuwa 30 ba tare da wata ta matsi wata, ko ta gogi wataba.
Sai kuma doguwar katanga da tayiwa asibitin garkuwa, yayinda bishiyoyin dabino ke zagaye dashi iyakar ganinka, sai kuma ƙasansu wasu ƴan dagwai-dagwai ɗin bishiyoyin grapes ne guntaye, masu masifar ƴaƴa da ɗan karen zaƙi, gasu ringiz gwanin ban sha'awa.
Sai daga ƙasan farfajiyar kuma, tsirran flowers ne masu ƙamshi ke zagaye da lungu da saƙo.
Daga saman Benin dake fuskantar gate ɗin kuma an rubuta.
Admin Maternity and Surgery block.
Gaba ɗaya fuskar wurin marafen Glass ne mai garai-garai wanda zaka iya ganin kanka ras a ciki.
A dai-dai gaban wurin Bilal yayi parking, yayinda Mai gadi da masu bawa flowers ruwa, sai kuma ma cliners dake ƴan share-share da goge-goge wanda tuni sun kammala aiyunkasu domin da dama moppa suke wankewa, masu tura duzbin na turawa gaba ɗaya Asbitin sai sheƙi da kyallin sabunta da gyara da ƙamshi yakeyi.
Da sauri Bilal ys fito tare da zagayawa ya buɗe masa marfin motar, sai kuma ya ɗan jingina gefe kaɗan hannunsa riƙe da briefcase ɗin uban gidan nashi, tare da ɗan tsayawa gefen ƙofar, sukayi jim suna jiran fitowarsa.
Yess in da sabo ai ya kamata ace sun saba a ɗan kwanakin da