Showing 9001 words to 12000 words out of 44320 words
Aunty Nana ta gyaɗa tare da dariya tace.
“Eh baku da haufi kam baiwar Allah duk sun fece sun barta da ciwon mara in ya tashi yana damunta in nace mata rashin mijine tai ta rantse rantse tana cemin wlh ita kam bashi bane, ita ba namiji a rayuwarta ma, firfa taki yarda kuma wlh shine”.
Sai kuma duk sukayi saurin juyawa kan kofar dakin ganin....
*Littafin INDA RAI na kiɗine ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Mutanen kasar Niger kuma 1000fc jaka ɗaya kenan rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076 Please Dan Allah da Manzonsa kada ki karanta min littafina in kinsan baki biya ba, in kuma kika biya kika rinƙa turawa wasu ko groups wannan kuma keda Allah*
*BY*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286: 📝🕋💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK 2 PAGE 4*
*AYASHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Zira idanunsa kan fuskarta, wani irin sassayan numfashi mai cike da rauni tausayinta gami da danne ƙuncin zuciyarsa yaja, kana ya juya a hankali ya kalli fuskar wayarta.
Status ɗin Hamisu take kallo inda yasa wani hotonta dashi da sukayi a tare tana bashi magani bayan rasuwar Daddy da yayi fama da ciwon kai a saman hoton yayi rubutu da manyan baƙi.
“Munyi rashin uwa na tsawon rayuwarmu amma ta hanamu maraici koda na one second ne, ta maye mana gurmin Daddy tun second ɗaya bayan fitan ran mahaifiyarmu, ta ruggumemu ta hana hawayenmu zuba ƙasa.
Sai kuma yasa emojis na kuka sai hoto na gaba wanda suna Airport ne.
Ak’asan hoton ya rubuta.
Kin yi nesa damu, irin nesan da tasa dole na zubda hawayen maraicin da yau ne ya riskemu.
Nasan gida bazai sake min daɗi ba.
Amman ina jin maɗaukakin farin ciki da aurene yayi mana rabuwar bazata, ke ba yaya bace a garemu ke uwace kamar yadda Daddy tace ki zame mana uwa harda su Yah Muhammad, mu kuma mu zame miki bongo abun jingina.
Abba kance yana tausayinki saboda ƙaddarar mtsalar da Allah ya jarabceki dashi.
Sai kuma ya sauƙi sassayan numfashi a hoto na gaba daya taho.
Wanda ita da Taj ɗin ne wanda sukayi lokacin zuwanshi suna Murmushi ya rubuta.
“Ku tamkar watane da zara, haɗin ku haɗin Allah ne, inayi miki fatan Alkhairi Ammi dan daga yau bazan sake kiranki da Aunty Ishmah ba sai Ammi saboda na fahimci matsayin uwa kike a garemu.
Inayi Miki fatan al'khairi a gidanki.
Zuwa yanzu kam shesh-sheƙan kuka mai sanyi ne ya subce mata da ƙarfi.
Shi kuwa Taj a hankali ya gyara zamansa tare da fuskantar ta da kyau, kana ya manna kanshi ajikin gadon ya zamana goshinsa na gab da kunnenta, cikin wata iriyar matasaciyar murya mafi sanyi ya kirata da sabon sunan daya sanya mata.
“Babe!!”
Yayi mata kiran da cikekkiyar muryar dake nuna ruwan tausayawa, ƙauna da kuma jink’ai.
Kana ahankali ya kuma ƙara kiranta.
“Babe!”.
Jin yadda muryarshi ke ratsa cikin kunnuwanta ne kuma yasa ta ɗan buɗe idanunta a hankali.
Cikin sanyi ya ɗan zaro harshensa ganin hawayenta na tsiyaya har suna gangarowa kan kunnenta.
A hankali ya manna tongue ɗinsa bisa saman kunnen.
Da sauri ta lumshe idanunta saboda jin ɗumin harshensa na ratsa fatarta wanda hakan yasa sautin muryar ta fara sanyi.
Cikin numfashi mai cike da rauni ya fara magana a hankali.
“Babe I know Make many mistake!.
Wata ƙil kinaga kamar na cutar da keko?.
But trust me. Banyi da nufin cutar da keba.
Ki sani cewa you are the most important person in my life”.
Ya ƙare maganar can ƙasan maƙoshinsa tare da sake manna tongue ɗinsa ya lashi sabbin hawayenta dake siyayowa.
Sai kuma ya fesar da sassayan numfashi da yasa ta ja wani dogon numfashi saboda jin kalamansa suna sakar mata da wani irin masifeffen kasala da ƙaƙƙarfan bacci mai cike da tsumin zuci wani irin numfashin ta kuma fesarwa mai sanyi jin yana faɗin.
“And if I am saying so sorry Babe.
Zuciyata bazata iya jurar ganin hawayenki ba.
Saboda nayiwa Abba al'ƙawarin bazan bar wahayenki ya sake zuba ba”.
A hankali ta ɗan sauƙe hannun ta dake kan goshinta saboda bacci ya sa gaɓɓanta sun fara sakewa, cikin baccin da ya fara surarta ne take jiyo kalaman nasa tamkar sauƙan sautin sarewa.
“Babe you know what? I lovo You more than I love my self, then ni ko bakya sona nasan zan rayu da soyayyarki”.
A hankali ya ɗan kuma sake numfashi kana a hankali ya ɗan kalleta jin tana sakin sassayan ajiyan zuciya.
Murya ya ɗan gyara cikin sanyi da zaƙin muryasar ya fara karanto suratul Mulk saboda duk daren duniya sai ya karanta.
Gyara kwanciyarta tayi lokacin da taji yayi basmala ya fara kawo ayoyin cikin ranta ta fara binshi daga aya ta ɗaya.
Zuwa ta biyar daga nan bata sake sanin me yake yi ba, saboda baccin da yayi nasarar danneta.
Shi kuwa Tajj a hankali ya gyara zamansa tare da ci gaba da karantawa har dai ya kai ƙarshen surar.
Sai kuma ya karanto Ayoyi 10 na forkon Suratul Khaff.
Sassayan numfashi ya fesar tare da haɗe tafukan hannunsa, ya karanto Ikhlas,nasi, palaƙ, sannan ya daura da ayatul-kursy da kuma amanarrasulu, a hankali ya kife tafukan hannunsa kan fuskarta tare da shafa mata kana ya fara yin ƙasa da hannunsa yana shafa mata a dukkan sassan jikinta.
Bayan ya kammala janye hannunsa yayi tare da jan dogon numfashi, kana ya haɗe tafukan hannunsa tare da yiwa kansa addu'a.
Koda ya shafa a hankali ya juya tare da manna bayansa da jikin gadon ya zamana yana fuskantar alƙibla.
Tanƙwashe sawunsa yayi tare da yin gyaran murya gami da basmala ya fara karatun Suratul Al,Baqara...
*Littafin INDA RAI na kud’i ne ki biya ki karanta cikin aminci da salama ba haƙƙin wani a kanku 1k ne kacal 0661110170 Gtbank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276, mutane Niger kuma 1000fc zaku biya jaka ɗaya kenan rak zaku tura ta wurin Mommy +22790899076. Kun dai ji kun kuma gani da idonku kun kuma sani littafina na kuɗine in baki biyaba kika karanta ke da Allah, in kin biya kuma kika ta turawa wani group ɗin ko groups wannan ke da Allah*
Acan wurinsu Garkuwa kuwa tafiya mai ɗan yawa kaɗan sukayi.
“Wow”
Aunty Nana dake gefen Garkuwa ta faɗa a daidai lokacin da suka kutsa kansu cikin wani tamfatsetsen gini na alfarma wanda daga saman sa can aka rubuta.
*Al-AHLI AFISHA HOSPITAL*
Still “Wow” shine abinda Adam ya kuma fad’a.
Aunty Amina ko.
“Masha Allah”. Ta faɗi tana mai karewa tamfatsetsen ginin kallo, wanda yake tsaye iya ganinka benaye ne na alfarma wanda akayishi da fasalin wf.
Gaba ɗayansu ido suke bazawa suna kallon tsarin farfarjiyar Asbitin.
Inda daga farkon shiga ƙaton filine ta gefen hagu, wanda ya kasance parking spaces ne da zai iya ɗaukan motoci 30 zuwa da biyar,
Sai kuma gabanshi da akayi wani Raund about ɗin flowers koraye shar masu furanni pink and yellow color sai ɗan ratsin red.
Ya kasance yana gaban faffadan steps ɗin da zai sadaka da cikin asibitin wanda suke da faɗi sosai aƙalla ko mutum hamsin zasu shiga kana hamsin su fito hanyar zata ɗaukesu.
Steps ɗin guda 8 ne, sai gefenshi kadan da akayi wurin shiga wanda ko da gadon nan marasa lfy ko keke.
Sai kuma gefen dama wata hanya ce ke shimfiɗe tsakanin flowers.
Wacce mota biyu zasu iya haɗewa wannan na shiga wannan na fita.
Yah Salam shine abinda Aunty Nana ta furta a saman lips inta dai-dai lokacin da taga sun kusa kai cikin wani gate da aka buɗe musu.
Ganin tsarin wurin da ƙawatuwarsa da flowers da kuma bishiyoyin dabino da yelwar hasken wutane yasata lumshe idanunta tare da shaƙar sassayan iska mai ratsa jiki.
A hankali motocin sukayi parking a gaban wani dantsatsen gida na alfarmar ginin zamani mai nuna ruwan kuɗin da aka binne wurin gina shi.
A hankali suka fara shiga bayan an buɗe musu ƙofar.
Suna kutsa kansu cikin Corridor kusan duk atare suka saki Numfashi gami da lumshe Idanunsu jin wani ni'imantaccen ƙamshi mai masifar daɗin shak’a tare da cire duk kan wata damuwa dake azuciyar ɗan adam.
Babban Corridor ne mai fadi wanda koda mota ce zata iya bi ta wurin, cike yake da yelwar haske daya wadaci wajen tamkar rana saboda haske, sai wani irin sheƙi da walwali da kasan tiles ɗin keyi dana jikin rabin ginin.
Tafiya kaɗan sukayi suka isa wani kofar dakin dake gefen damansu ɗakin ya kasance ciki da falo ne sai toilet gabansa kadan kuwa shoe rug ne na ajiye takalma awajen samansa kadan wani ɗan table ne wanda bisa alamu idan zaka ajiye key, hula, jaka, da dai sauransu gaba kadan daga gefen dama step ne haka ajere wanda za'a haura zuwa sama ne gidan.
Da yake sashine na musamman da aka shiryawa Taj.
Babban falone mai girma asama wanda ya wadatu da komai aciki komai na cikin falon Neavy blue and white color ne kama daga Cottons, Carpet, kujeru, masu masifar kyau, daga jikin bango kuwa wani babban plasma tv ne da kuma Ac dake makale daga ɗaya gefen.
Sai kuma dining area, dake tsakiyar ɗakuna biyu wanda aka shirya dinning table mai kujeru shida, sai fridge da ɗan madaidacin show Glass da aka shirya cups, flack's, mugs, plate's, bowls, spoons da dai ababen buƙata, sai gefensu kaɗan da washing hands beby ke maƙale.
Daga gefen hagun dinning area ɗin kuwa,
wani daki ne da yakasance Library na musamman, domin babu irin littafin da babu acikinsa na addini, da kuma na karatunsa na Likitanci, had’i dana Pilot.
Baki ɗaya ɗakin cike yake da kanta, waɗan da, ke cike da littafai iri da kala, an jerasu tare da kimtsasu daki daki ko wanne sashin da abinda ya ƙunsa.
Daga tsakiya kuwa wani table ne dake zagaye da kujeru huɗu, sai AC dake ciki da yelwar haske.
Idan an fito Parlor kuma ta gefen dama wani ɗan madaidacin Corridor ne bisa alamu ɗakinsa ne.
Wani ƙasaitaccen gadone aciki wanda ya amsa sunansa gado na al'farma, yana kuma ke waye da abubuwan more rayuwa komai na ɗakin fari ne tas, kama daga kan gadon, labulaye, carpet had’i da da two cushions dake gefe suna d’auke da d’an k’aramin stool a tsakiyarsu, duk komai fari ne a d’akin sai ɗan ratsin golding color mai ɗan karen sheƙi da ƙyalli.
daga gefen gadon kuwa drawer’n kayansa ne daya cinye fiye da rabin bango sai kuma mirror dake facing gadon da suketa walwalin madubai dake maƙalle a jikinsu.
Tsakanin Libraryn sa da kuma bedroom d’in dining area wanda yake da step uku ana hudun zaka hau, daga gefen dining area akwai wata ƙofa ana buɗe kofar kuwa wani balcony ne wanda kana tsaye daga wajen kana iya hango farfajiyar wajen ta baya wanda ya kasance kamar Garden saboda shuke-shuke dake wajen bisa dukkan alamu wajen shakatawa ne wanda aka tanada saboda ma'aikatan wajen da kuma majinyata da ake bukatar asamar musu nutsuwa da kuma shauƙi da rage radaɗin ciwo da damuwar dake ɗawainiya dasu iya abin da yake cikin falon kenan.
Idan an sauk’o ƙasa kuwa daga cikin Corridor ta gefen hagu wani daki ne ciki da falo ne sai bathroom idan aka cigaba da tafiya cikin Corridor kuwa za'a hango wata babbar ƙofa dake facing shigowa.
Kusan baki d’ayansu atare suke murmurshi kana suna gyad’awa Addawa kai wacce keyi musu maraba lale cikin harshen Amharic wanda yake shine general language na Ethiopia dashi da Oromo.
Fuskarta d’auke da yalwataccen murmushi mai cike da aminci.
Ganin kamar basu fahimtar abunda take cewa ne kuma yasa ta juyawa zuwa harshen Fulatancin Ethiopia kana tana mai kare musu kallo tana son sanin su wayene saboda Tajj yace mata akwai baki na musamman zasu zo a karramusu Akuma
Mutuntasu.
shin wa'anan su waye ne ina Taj ya samosu shin me suke tafe dashi?.
Duk da wannan tunanin bai sa murmushin fiskarta ɗaukewa ba cikin mutuntasu ta cigaba da cewa.
“Bismillah ku ƙara so ga wajen zama”.
Ta ƙare maganar da nazartar fuskokinsu duk ba wacce ta gane a cikinsu.
Su kuwa kai suka gyada suna masu cigaba da kallon tamfatsetsen falon wanda yasha kayan ƙawa na more rayuwa komai na cikin wannan falon Blue Black da golden. kama daga Carpet Cottons da dai sauransu bisa duk kan alamu 3bedrooms ne a Falon daga gefen dama wani bedroom ne da aka kimtsa kana aka ƙawatashi sosai yayi kyau wanda bisa alamu na Ishmah ce daga gefen hagu shima bedroom wanda bisa duk kan alamu Dakin Addawa ce kusa da bakin Kofar shigowa nan ma bedroom ne bisa alamu ba kowa aciki da alamu Addawa, Laylah da kuma Zulaihat duk daki ɗaya suke.
Sai kuma dining area tsakanin dining area kuwa kitchen ne dake ƙawace da kayan ayyuka na zamani da sauƙaƙa ayyukan rayuwar yau da kullum, wanda duk wata ƴa mace zata buƙata daga cikin kitchen ɗin kuwa wata ƙoface da zata sadaka da Balcony iya tsaruwa ginin ya tsaru ta ko ina wajen sai ƙyalƙyali da ɗaukar ido yake bisa duk kan alamu komai na wajen sabone dal dan sai sheƙi da ɗaukar hankali...
Addawa kuwa cikin mutuntawa da sakin fuska ta k’ira sunan.
“Laylah da kuma Zulaihat”.
Da sauri suka amsa kana suka fito Laylah na kallon Garkuwa ta ware idanunta tare da ɗebawa da gudu ta rungumeta tana me cewa.
“Laaaa Aunty Garkuwa kece”.
Rungumeta Garkuwa tayi had’e da cewa.
“A'a Laylah yan mata”.
Cike da farin ciki Laylah ta saki Garkuwa ta rungume aunty Nana tana faɗin.
“Laaaa Aunty Nana ”.
Sai kuma ta maida kallonta ga Adam tare da cewa.
“Uncle Adam”.
Lokaci d’aya kuma ta maida kallonta ga Addawa still tana murmushi tace.
“Addawa su Uncle Adam ne fa”.
Da sauri ta kalli Khadija tace.
“Aunty Khadija ina Aunty Ishmah na!?”.
Murmushi Khadijah tayi tare da cewa.
“Aunty Ishmah tana tare da Uncle Taj”.
Tsalle Laylah tayi kana ta rungume Addawa tare da faɗin.
“Addawa munji daɗin mu Aunty Ishmah tazo”.
Sai kuma ta juya ta kalli Auty dake murmushi tana kallon yarinyar data shiga ranta Laylah kuwa cikin farin ciki tace.
“Aunty Garkuwa kun kawo mana Aunty Ishmah ko duka ko ta dawo wurinmu ko?”.
Kai aunty Amina ta gyaɗa mata tare da cewa.
“Eh sosai ma”.
Laylah kam cikin jin daɗi ta kuma riƙe hannun Addawa tace.
“Munji daɗin mu Addawa kinji an kawo mana Aunty Ishmah”.
Kallonta ta mayar kan Khadijah tace.
“Aunty Khady ina Aunty Rahama baku zo mana da ita ba?”.
Kai Khadijah ta jinjina tare da cewa.
“Ai mun kawo muku Aunty Ishmah ta dawo gidanku da zama, bazamu haɗa muku da Rahama ba Laylah kun rabamu da Aunty Ishmah dai ya isa”.
Cikin jin daɗi ta riƙa ƙyalƙyala dariya had’i da cewa.
“Alhamdulilah munji daɗi kuma in sha Allah sai mun sa Uncle Afif ya ɗauko mana Aunty Rahama ma ko Addawa”.
Fuska ɗauke da Murmushi Addawa tace.
“Aikam munji daɗi tashi ku kawo musu ruwa”.
Ta ƙare maganar tana kallon Zulaihat.
Kai Zulaihat ta gyada kana ta miƙe ta kawo musu ruwa, dasu drinks,snacks,fruits ta jere agabansu.
Kallon Aunty Amina Addawa tayi jin tana cewa.
“Tafiya dai ko yaya tana da wuya”.
Kasancewar da Fulatancin tayi maganar yasa Addawa ta fahimta kasancewar itama Bafulatanan Ethiopia ce cikin mutumtaka tace.
“Sosai ma kam gashi kuma na tsaidaku a falo baku samu kun shiga ba Zulaihat maza-maxa ku dauki kayayyakin su ku shigar musu ”.
Sai kuma ta maida kallon ta kan wanda adai-dai lokacin yake shigowa da jakankuna cikin alamun dan sanin juna tace.
“Bilal ka shigar da jakunkunan ciki kasa wasu ɗakin nan wasu kuma dakin can”.
Sai kuma ta Kalli Aunty Amina tare da cewa.
“Aunty Amina wasu su shiga ɗakin nan wasu su shiga wancan wasu kuma suzo nan”.
Kai Aunty Amina ta girgiza tace.
“A'a ai biyun ma sun ishe mu ai”.
Murmushi tayi tare da faɗin.
“Toh bari in kawowa Adam key”.
Ta faɗa tare da shiga dakinta Jim kaɗan ta fito ta miƙawa Adam key tace.
“Akwai wani ƙofa da yake kallo. Ƙofar dama ka buɗe ka shiga ciki”.
”Toh”.
Ya faɗa kana ya juya ya fita dai-dai lokacin suka miƙe aunty Amina,Goggo Dijah daƙi ɗaya suka shiga Aunty Nana, Garkuwa, Khadijah suma daki ɗaya suka nufa...
Koda suka shiga wanka suka farayi kana suka cac-canza kayansu kasancewar duk sunyi sallah acikin jirgi yasa suka fito falo bayan sun gama komai.
Ganin sun fito yasa addawa sauke ajiyar zuciya tace.
“Yawwa Bismillah ku iso dining tunda kuka zo ba kuci komai ba”.
Kusan baki ɗaya atare suka zauna a dining ɗin kallon Laylah Addawa tayi tare da cewa.
“Ɗauki ki kaiwa Uncle Adam”.
Kai ta gyada tare da ɗaukan Food flask, da kuma plate bowl spoon da aka jera acikin basket, ta nufi dakin Adam tana shiga ta sameshi zaune a Parlour bisa alamu yayi wanka ya shirya cikin Black jallabiya, cikin girmamawa tace .
“Uncle Adam ga abinci ”.
Kai ya gyada kana yace.
“Sannu Laylah”.
Acan gefen su Garkuwa kuwa sosai suka yaba da mutunci da karramawar Addawa bayan sun gama cin abincin ne kuma suka dawo tsakiyar Falon.
Sai alokacin Addawa tace.
“Yawwa yanzu sai mu gaisa ko?”.
Murmushi Goggo Dija tayi tare da cewa.
“Aidai kam sai mu gaisa tun da tun da muka zo bamu gaisa ba mun bige da cin abinci”.
Dariya Addawa tayi tare da faɗin.
“Ai dai kam matafiyi sai da abinci”.
Cikin mutumtaka da girmamawa suka gaisa bayan sun gama gaisawa tace.
“Na sani yau kam kun ɗebo gajiya ku shiga daga ciki ku samu ku huta in Sha Allahu muna nan tare zamu sha hira kam”.
“Toh shikenan”.
Suka faɗa tare da mik’ewa.
Aunty Nana ce ta kalli Aunty Amina tare da cewa.
“Aunty Amina nifa shiru har yanzu fa basu iso ba”.
Ɗan hararanta Garkuwa tayi kana murya kasa kasa tace.
“Ina ruwanki da jiran sai sun iso mata da mijinta tana tare da mijinta kice sai kin jirata taxo?”.
Murmushi tayi kana tace.
“Ai Yakamata dai mu san inda suke kuma gashi har yanzu basu zoba har zamu kwanta kallifa yanzu kusan ƙarfe biyun dare”.
Dariya Aunty Amina tayi mai haɗe da hamma tace.
“Um wannan dai damuwar kune”.
Ta ƙare maganar tana jan hannun Goggo Dijah suka wuce dakinsu...
Khadijah na dariya tace.
“Toh bari na gwada kiran Addah Ishmah ”.
3 missed calls tayi mata amma duk ba'a ɗaga ba.
Adai-dai lokacin kuma Taj ne zaune yana karatu kasancewar yana karatun da ɗan sautine yasa baiji vibrating ɗin da wayar Ishmahn keyi ba