Showing 18001 words to 21000 words out of 44320 words

Chapter 7 - In Da Rai Book 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

26 Jan 2025

8678

tsohon ciki. Baza muso a barta ita ɗaya a gida ba babba ba”.
Cikin gamsuwa yace.
“To Allah ya sauƙeta lfy”.
Amin suka amsa sai kuma yace.
“To sai kaje ka amso E passport ɗinsu duk masu zuwan dan ayi duk abinda ya dace”.
Daga nan dai suka gama tsara komai.

A Parlour Daddey kuwa cikin murmushi Yah Muhammad yake kallon E passport ɗin Ishmah tare da cewa.
“Masha Allah saura wata uku yayi expire, da yanzu sai munyi sungular sabunta shi, Kinga yanzu an huta mijinki yayi sungular in kunje.”
Ba tare da ta fahimci mgnar saba, ta juyo tana kallon Aunty Maryam dake miƙo mata bowl ɗin data zuba mata dahuwar jan naman.
Amsa tayi tare da cewa.
“Amman sai anjima yanzu bana jin yunwa”.
Cikin kulawa Yah Muhammad yace.
“Toh me kikaci ɗazumafa ina ganinki ba abinda kikaci”.
Cikin sanyi tace.
“Ji nake ina ƙoshe”.
Kai ya jujjuya mata tare da cewa.
“A'a Goggani kada kiyi haka”.
Da yake yakan kirata da goggini a wasu lokutan yadda Khairat ɗinsa ke kiran Ishmah kafin ta gama iya magana.
Kujera ya nuna mata tare da cewa.
“Zauna kici, ke baki ga kin zama yar lelenmu ba”.
Kai ta ɗan sumkuyar tare da cewa.
“Toh”.
Daga nan ya fita yana faɗin bari inje in amshi na Aunty Amina da Garkuwa.
Cikin sauri Aunty Nana tace.
“Abban Ikiram ya yarda zata je?”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Eh Amman fa saida Abba da Sheykh Tajuh da Tajj ɗin sukaje har wurinsa tukun ya yarda”.

Adam kuwa da bashi da E Passport Abubakar yasashi a gaba sukaje ayi mishi.

Hakan kuwa akayi.
Cikin kwana biyu aka gama komai, to abune na kuɗi da kuma sa bakin manya, shiyasa tuni komai ya kankama ya haɗu.
Aunty Maryam kuwa da Garkuwa wani irin shiri da tsumi na musamman sukeyiwa Ishmah da har yau mgnar kalmar auren nan bai haɗata da kowaba.
Har gobe jin kalmar take a baƙuwa a cikin kunnuwanta.

Taj kuwa tamkar ma gudunsa takeyi, ko sun kasance wuri ɗaya ma kuma zama take tamkar ba itace surutacciyar abokiyarsa nan mai tsananin shaƙuwa da shiba sai dai tana kula da ƙafarsa duk dai har yanzu yana ɗan ɗingisa ta.

A tsakanin kwana kin kuma ya amsa gayyatar sauk’an karatun wasu ɗalibai a jihar Bauchi a ƙaramar hukumar Azare.

Ita kuwa Ishmah gani take Taj ɗin tamkar ba Taj ɗinta bane, kamar wani ne da ban aka ajiye mata.
Saboda tsananin nauyin shi da takeji wanda yasa ko sunanshi nauyin faɗi yake mata.
(girma da darajar aure kenan.)

Khadijah da Goggo Dijan kuwa da Aunty Maryam tuni suketa shirya komai na tafiya.

Ethiopia
Yau talata Ummi ce zaune tare da tsurawa Adaya idanu tana kallon yadda take tahowa wurinta cikin sanyi da lallaɓa takun ƙafar tamkar ba Adayarta data sani a bayaba wacce ko tafiya take sai ta rausaya ba.
Numfashi mai nauyi ta fesar dai-dai lokacin da Adaya ta zauna gefentan a hankali tace.
“Adaya nafa ce Miki, na san akwai abinda kike ɓoye min, ki faɗa min menene matsalar ki?”.
Cikin sauri da karsashi tace.
“Ummi ba abinda ke damuna fa! Kawai zazzabin da nayine, kuma na gaya miki faɗuwar da nayi a BQ lokacin da zan fita ne, ƙuguna ya bugu shiyasa nake tafiya a hankali dan har yanzu yana min ciwo, shiyasa ma ko fita rihazal banayi”.
Cikin rashin gamsuwa Ummi tace.
“Toh Allah ya sauwaƙa”.

Gidansu TAJJ.

Ummey ce zaune gaban Addawa cikin sanyi tare da tsiyayar da hawaye masu zafi
Murya na rawa cike da rauni tace.

“Ko ina yayi min zafi a duniya ji nakeyi, bani da wani sauran farin ciki tunda Malam ya nesantani da Afif ya cika zuciyata da duniyata da baƙin ciki mara yankewa.
Nayi niyar zanyi mishi mgnar Afif in yaso ta zama sanadin aurena, in rabu dashi inje in kansance tare da ɗana, in killace shi in cire mishi ƙuncin rashin mahaifin nasa.
Amman kin hanani kana kin ƙara min wuta a kan ranar da malam ya sani”.
Cikin sanyi Addawa ta ƙara matsowa kusa da ita.
Sassayan numfashi ta fesar tare dasa hannunta ta sharce mata hawayenta da wani ke korar wani cikin hikima da hangen nesa na manyan mutane tace.
“Eh ko yanzu zan ƙara jaddada Miki ban amince ki kira masa sunan Taj a gabansa kamar yadda yace ba”.
Har suna haɗa baki ita da Halima sukace.
“Toh saboda me?”.

“Saboda yace in kin kira masa sunansa a gabansa ko kinyi alaƙa dashi a kan aurenki”.
Da sauri tace.
“Toh me zanyi da auren Malam me ya rage min dashi”.
Tana maida hawayenta dake tsatstsafowa tace.
“Nasan idan har kikayi mgnar Afif a gabansa tabbas zai sakekin, sakinki kuma shine abinda zaifi yiwa Afif ciwo fiye da komai, yace min bazai taɓa yafewa kansaba in har ya zama sanadin rabuwar auren iyayensa.
Sannan kuma ai in kikayi abinda zaku rabu da Malam kin yiwa magauta abinda suke so, shike nan sunyi nasarar korar ɗanki. Kema sun fidda ke gidan Zakiya nayin aure shike nan baki da ko tsuntsu a gidan
Zai kuma tabbata cewa Afif ya aikata laifin kenan?!”.
Da sauri Ummeeyshi ta saki shesh-sheƙan kuka.
Dafa kafaɗarta Addawa tayi tare da cewa.
“To in dai bakya son haka ya tabbata, to kiyi haƙuri kada ki sake mishi mgnar Afif, kuma daga ke har su Maryam kada kuyi alaƙa dashi, saboda kada Allah ya isan mahaifinsu ya hau kansu”.
Cikin kuka Halima tace.
“Yanzu shike nan an rabamu da ɗan uwanmu an maraitar dashi duk da yawan danginsa!”.
Cikin ƙarfin hali Addawa tace.
“Tajuddeen bazai maraitaba, zan kasance tare dashi, kamar yadda na gaya muku dani da Laylah, da Zulaihat yau da dare zamu tafi Qatar zamuje can.
Yace min shima zuwa dare baƙi zasu isa in rigasu isa in marabcesu, sai dai bansan wasu baƙin bane, kuma bansan ina yake ba.
Dan haka ki kwantar da hankalinki zanje in kasance dashi zan bashi dukkan kulawar da kikega in kuna tare zaki bashi.
Wani sassayan kuka Ummeeyshi ta kuma sakewa tana faɗin.
Yanzu ko a waya kenan ya haramta inyi mgn da ɗana”.
Da sauri Addawa tace.
“Kwarai ma kuwa, don kiyaye igiyar aurenki, ki zauna a nan mu jira ranar da gsky zatayi halinta domin ai INDA RAI to tabbas da Rabo.
Ki zauna a gaban idonki gsky zatayi halinta kiga yadda kwayar idanun magautansa zasuyi.”


Nigeria.
Yau Laraba tun safe suke gama shirin su, duk masu tafiyar sun haɗu.
Garkuwa, Aunty Amina, Aunty Nana, Khadijah, Adam Goggo Dija.
Kasan cewar ƙarfe tara jirginsu zai tashi daga Adamawa to Lagos.

Ƙarfe biyu dai-dai kuma zasu tashi daga Logos Nigeria to Doho Qatar.

Cikin sanyin da tunda gari ya waye ta tashi dashi, da ji take da ganin abin kamar wasa ko almara koko mafarkin da zata farka ta ganshi a sawarware.
Rauninta yayi ruɓanya da kaso 90 bisa ɗarine, a lokacin da taga anata fidda dukkan kayayyakinsu durƙushe take a gaban Abbanta da kuma Uncle Bello sai Yayunta.
Wani irin sassayan kuka take yi mai tsuma zuciyar duk mai imani.
Sai kuma kawai ta rarrafa a hankali ta ɗaura kanta bisa cinyar Hajia kakarta wacce tun safe tazo don yin sallama dasu.
Sunkuyar da kai Abba yayi domin shima kansa hawayen ke zubar masa.
Da sauri Rahama tazo ta raɓa jikinta jin tana cewa.
“Yanzu in na tafi waye zai zauna dasu Rahama, waye zaike hanasu kewa da maraicin Daddy, Waye zai rinƙa hana Hamisu kuka in ya tuno Daddynmu”.

Wani irin azabebben numfashi Taj ya fesar a hankali, tare da rumtse idanunsa ji yake yi kukanta na ƙona mishi ƙahon zuciyarsa tamkar zata narke.
Uncle Bello ne ya ɗanyi ƙarfin halin farayi mata faɗa mai haɗe da nasiha nasiha.
“Toh Shatu YAR FULANI. Kin mance cewa Duk wanda baya yarda da ƙaddara MI WASMITI shine kalmar da zata yi abota da harshensa.
Ki tuna fa cewa NAMIJI BAYA KAƊAN.
Ai duk sonki da su Hamisu iyakar na BANDIRAWO ne baki kai Allah daya haliccesu sonsuba.
kuma dai TAUSAYAWA JUNA da kuke bazai hanaki yin aure ki raya sunnar Manzon Allah ba.
Tunda da baku isa ku kauda RUBUTACCAN AL'AMARI ba.
Mutuwa kuwa ai RIGAR KOWA ce, Mamana ya zamuyi Allahn da ya bamu ita shi ya ɗauke mana ita, kuma ya fimu sonta.
To ma wai zakiyi butulci da HUKUNCIN ALLAH ne Mamana?
Kin sani cewa Babu Maraya sai rago ko, to ai ko NAKASA MA BA KASAWA BACE, bare kuma ga
Ga yayunku da mahaifinku wanda yake GARKUWA a gareku.
Kuma TUBALIN jin daɗi rayuwarku.
Kada ki mance cewa Allah yayi miki SAKAYYAH nefa da maɗaukakin aure a bisa haƙurinki da kikayi tsawon shekaru kina riƙe da kanki
Dan haka ki share hawayenki ai INDA RAI to ai ana tare duk inda kike a faɗin duniyar nan.”
Ina ta kasa tsaida hawayenta saboda jin murya Khalid wanda Hamisu ya ɗaukosu dan suzo suyi sallama da ita wani irin sassayan kuka yaron yakeyi harda Shesh-sheƙan kuka.
A hankali Taj ya jawoshi jikinsa cikin son yaron tare da jin tausayinsu zai ɗauke musu uwarsu ya nesantasu da ita.
Wani irin tausayin Minat dake gefe tana sharar kwallane ya rufeshi.
Ji yake yi shi da yake babba ma daga shi sai Allah ne kaɗai suka san irin ƙunci da ciwon da yakeji na rabuwa da iyayensa da yayi, inaga su yara.
Cikin sanyi yace.
“Zo nan my Daughter”.
Ya ƙare maganar yana jawo hannunta a hankali ta matso gareshi sai kuma ya jawo Mahamud da yayi ƙasa da kanshi cikin sanyi yace.
“Kada kuyi kuka, kuyi mana addu'a, kai My boy kana gama Secondary School zaka dawo wurinmu kaci gaba da Karatu.
Kema My Daughter zaki dawo kuyi karatu tare da Laylah ɗinki ko.
Kai kuma Mahmoud ai kama kusa tafiya Mexico kayi karatu a can ko?”.
Cikin jin daɗi duk sukace masa.
“Yess Uncle Taj”.
Yana sharewa Khalid hawaye yace.
“To kuje ku rarrashi Amminku kuce tayi haƙuri”.
Kusan a tare suka koma gabanta da sauri ta ruggume su.
Sai kuma tayi murmushi mai haɗe da hawaye jin Khalid na cewa.
“Ammi ki dena kuka, nima ina gama Secondary School zan taho Qatar mu zama larabawa”.
Kanshi Abba ya shafa tare da cewa.
“Yauwa Khalid haka nake son ji”.
Da sauri duk suka ɗaga hannayensu jin Uncle Bello na cewa.
“To muyi musu Addu'a.”
Nan fa yayi ta kwararo musu addu'o'i.
Bayan sun shafa ne, kuma Ishmah ta sake sakin wani kukan.
A hankali Abba ya miƙe tsaye tare dasa hannunsa ya kamota ya tsaida ita cikin kuka tace.
“Abba wa zai zauna da Rahama da Hamisu”.
Da sauri ta sauƙe nannauyan numfashi jin Hajiabna cewa.
“Ki kwantar da hankalinki Ni zan zauna dasu, sai Abbanku yayi aure zan koma gida”.
Cikin jin ɗan sanyi a ranta ta ruggume Hajia.
Yah Muhammad ne ya ɗan sharce hawayen da suka zubo mai gami da cewa.
“'Lokacin tashin ku ya kusa fa”.
Aunty Amina ce ta kamo hannunta suka fito ganin alamun bazata saki Hajia ba.
Cikin sanyi da tsokana Maryam ta sharce hawayenta tare da cewa.
“Fisabilillahi ke ba yarinya ba duk kiyi ta samu kuka da shogwabarki ki karya mana zuƙata.”
Ruggume Maryam ɗin tayi tare da cewa.
“Aunty Maryam zanyi missing naku ga amanar su Rahama”.
Sai kuma ta sake Maryam ta ruggume Hamisu.
Murmushin ƙarfin hali yayi tare da kamo hannunta suka nufi motar Abba buɗe mata yayi ta shiga kana ya sunkuyo a hankali ya raɗa mata wata kalma.
Kawai sai gani akayi tana Murmushin tare da dukan kanshi.

Daga nan duk saura suka shiga motocin akaja aka tafin.
Suna zuwa Airport ba dadewa suka tashi, suka yi Lagos.

Suna shiga cikin jirgi a jere cike da nitsuwa wayace maƙale a kunnensa bisa alamu da Addawa yake mgna.
“Mu yanzu zamu tashi!”.
Tana gyara zamanta bisa ɗaya daga cikin hamshaƙan kujerar tace.
“Mufa tun sha biyu muka isa”.
Kai ya ɗan jinjina tare da cewa.
“Eh ai ba nisa Ethiopia to Qatar 3 Hours and 18 minutes ne!”.
Tana lumshe ido alamun bacci tace.
“Kuma zaku iso kafin la'asar ko?”.
Suna haurawa saman first class, ya ɗan girgiza kai tamkar yana gabanta kana a hankali yace.
“Nanfa Nigeria to Qatar 8 Hours and 55 minutes ne, kin ga tafiya ce mai nisa sosai”.
Ya ƙare maganar tare da zama bisa kujerar dake gab da window, a hankali Ishmah kuwa data lumshe idanunta hawayen da suke ciki suka zubo, Saboda jin irin nisancin da zatayi da ƙasarta da yaranta mahaifinta Yayunta da kuma ƙannenta hakan yasa kukanta ya sabunta,
Tana mai zubda hawayen ta zauna.
Yayinda Garkuwa kuwa da Aunty Amina suke gefen daman su.
Sai Khadijah da Goggo Dijan dake bayansu.
Adam da Aunty Nana kuwa na can baya.

Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan gyaɗa kansa tare da cewa.
“Uhmmmm”. Saboda jin Addawa na cewa.
“Kace inyi baccina sai tsakiyar dare zaku iso, ni da nufina zan jira isowarku ai”.
Ƙosawa da surutunta ne ya sashi katse kiran tare da kashe wayar saboda sanin dokokin su na cikin jirgi.

Ƙarfe biyu dai-dai jirginsu ya ɗaga zuwa Qatar.

Wani irin kukane mai sassayan sauti ya kubcewa Ishmah lokacin da taji jirginsu ya rabu da ƙasarta ta haihuwa.
Lallai wanda baiji tsoron Allah ba ya wahala.
Cikin kwanaki biyar rayuwarta ta sauya salon ƙaddararta ya juye yazo mata a baibai, ko kusa ko zato ko tsammani fita ko cikin Jimeta batayi ba sai gashi wai ƙasar zata bari Bama ƙasar ba Africa baki ɗaya.
Dama ace Ethiopia ne da tasan ko ba komai yankin nahiyarta ne Africa.”

Shi kuwa Taj a hankali ya lumshe idanunsa, tare da fara tariyo shekarun baya, yana mai tunowa haɗuwarta dashi da halin da ta shiga, tuno da wannan ne ya sashi ɗan gyara zamansa tare da ɗan matsowa kusa da ita.

Dai-dai lokacin kuma tayi saurin rumtse idanunta da ƙarfi saboda jin hanjin cikinta sun fara walle-walle irin dai yadda taji a shiganta jirgi na forko a rayuwarta.
Murya cike da rauni tace.
“Innalillah”.
Da sauri yasa hannunsa ya kamo nata ganin ta yunƙura bisa alamu so take ta kafa goshinta a jikin set ɗin da yake gaban nata.
Da ƙarfi ya ɗan matse hannun nata cikin nashi tare da sarƙafe yatsunsu wuri ɗaya.
Sassayan numfashi ya fesar tare da ɗan jawota gefenshi, dai-dai lokacin kuma jirgin ya ɗanyi marisar ɗaukar asalin hanyarsa.
Cikin tsananin tsoron ta raɓa jikinsa gefen kafaɗarsa ta manna kanta bisa damtsenshi tare da rumtse idanunta da ƙarfi.
Shi kuwa Taj cikin fesar da sassayan iska ya ƙara matse hannunnata tare dasa hannunshi ɗaya ya gyarawa kanta zama, cikin sanyi ya lumshe idanunsa tare da ɗan sunkuyar da kanshi kaɗan lips inshi ya manna bisa goshinta tare da liƙa mata wani amintaccen kiss mai sauk’ar da nitsuwa.
Ajiyar zuciya mai nauyi taja kana ta sauƙe tare da direshi da ƙarfi, saboda wani irin sanyi da taushin lips inshi da ya ratsa mata goshi.
Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan ƙara matsowa kusa da ita, sai kuma ya ɗan sunkuyo ya leƙa fuskar ta ganin hawaye na zubowa ne yasashi sa yatsunsa biyu ya sharce mata hawayenta, sai kuma ya ɗan ƙara sunkuyowa sosai ya kai bakinshi dab da kunnen ta.
Sassayan numfashi ya shaƙa tare da motsa lips inshi a hankali murya cike da raɗa yace.

“Shima iri ɗaya ko Ma'eeshah!”.

Sai kuma ya ɗan cije gefen lip inshi na ƙasa yana mai ƙara yarda cewa haɗinsu daga Allah ne, shiyasa komai nasu yake zuwa iri ɗaya, jin hawayenta na ɗisa bisa cinyarsa ne yasashi ci gaba da cewa.
“Allah ne ya ke kusanta ƙaddarorinmu da kamantasu, kin rasa Daddy a lokacin ban alaƙan ta kamanceceniyar ƙaddararmu ba, sai gashi ni ƙaddara ta rabani da Ummey na, wanda gwara ke mutuwace ta rabaku”.
Haka nan taji hawayenta sun tsananta domin tunda yazo basuyi wani zaman kirkiba jin abinda yake faɗane kuma yasata fahimtar cewa ya shiga cikin jarraba mai tsanani.
Shi kuwa Taj a hankali ya motsa lips inshi tare daci gaba da faɗin.
“Akasi kuma yasa mutumin da yafi kowa sona a duniya ya nesanta kanshi dani, ya barrantani da yaransa yace, ya barwa duniya ni, kinga gwara ke zaman aurene sunnar Manzon Allah ne yasa na rabaki da Abba, Ma'eeshah dani dake bamu da banbanci, nima tamkar maraya nake, bani da kowa duniya sai ke da Addawa da Laylah, Ma'eesha kece kaɗai sauran hope d’ina, in bake a kusa dani ba amfanin rayuwata gwara kawai in mutu in hut”.
Shiru yayi ba tare da ya ƙarasa mgnar ba jin yadda take jijjiga mishi kai.

Aunty Amina ce ta ɗanyi murmushi tare da nunawa Garkuwa inda suke da idanu.
Itama Garkuwa murmushin tayi tare da cire idonta.

Khadijah kuwa tuni tayi baccinta mai daɗi.
Adam kuwa kurui yayi da idanu yana kallon yadda suke keta hazo da gajumare, suna fesa gudu.

Ita kuwa Ishmah a hankali ta fara jin bacci saboda.
Yadda yake ɗan jijjiga ƙafafunshi a hankali hankali wanda wannan halittarce in dai yana zaune sai yayi ta haɗa guiwowinshi yana ɗan rabawa.

Fahimtar tayi bacci ne kuma yasashi gyara mata jingina.
Kana shi kuma ya faɗa duniyar nazarin rayuwar da zai fuskanta.
“Zan rayu dake tamkar abokiyar da kika kasance min Ma'eeshah bazan taɓa kusantar ki a matsayin matar aurena ba, har sai ran da naga sona a matsayin mijin aure ba aboki ba a cikin kwayar idanunki, kuma harshenki ya furta min, dole in fara sauya matsayin soyayya ta a zuciyarki kafin sauya matsayin abota zuwa miji”.

A haka sukayi ta keta hazo har karfe huɗu.
A hankali ta ɗan yunƙura zaune.
Sai kuma ta ɗan kalleshi jin yana cewa.
“Je kiyi al'wala kizo muyi sallan la'asar, ki gayawa su Adam ma duk suyi al'wala suyi niya suyi sallah.
Kai ta jinjina kana ta miƙe tare da nufar wurinda taga yana nuna mata.

Bayan ta fitone duk suka sabunta al'wala bandashi dan yasan al'walarsa na nan.

Koda suka idar da sallan, hannunshi ya ɗago tare da jera musu addu'a.

Daga nan suka ci gaba da tafiya.
Hakama sukayi Magrib da isha.
Koda aka kawo musu ɗan abin taɓawa kowa yaci abinda aka bashi, amma ita babu yadda baiyi da itaba tak’i ci shima kuma baici ba.

Ƙarfe takwas ne ta ɗanyi hamma tare da ɗan lumshe idanunta kana a hankali tace.
“Mun kusa isa? Saura awa nawa?”.
Yana ɗan jawo hannunta yace.
“Saura mana 2 Hours and 35 minutes, bacci kikeji ko?”.
Ya ƙare maganar cike da kulawa, kai ta gyaɗa mishi, ganin haka ne yasa ya jawota jikinsa tare da cewa.
“Zo kiyi baccinki”.
Da sauri Goggo Dijan tayi sauri cire idonta daga kansu.

Ita kuwa yana jawota ya manna kanta a damtsen hannunshi lokaci d’aya bacci yayi awon gaba da ita.

Ƙarfe 9 da minti 35 dai-dai jirginsu yayi landing a Qatar Airways tower.

Bayan duk sun shiga motocin.
A hankali ya kamo hannun Ishmah tare da nufar ɗaya daga cikin motar suna shiga.
Akaja motar tare da bin bayan sauran.

Tafiya mai tsawo sukayi.
Yayinda gaba ɗayansu suka ware idanunsu suna kallon tsari da shaharar ƙasar Qatar da da ta wuce tunanin mai tunani.
Cikin buɗe ido Adam ya kalli Khadijah tare da cewa.
“Yah Sallam Anty Khadi Kinga duniyar da Allah ya kawo mu”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Ai ni nama rasa abin faɗa, wannan abu kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login