Showing 12001 words to 15000 words out of 44320 words
duk da yana gefensa.
Aunty Nana kam dariya tayi tare da zama abakin gadon tare da cewa.
“Hmmm ai waɗannan tsofaffin tuzuran sai dai Allah ya taro manasu nifa karfin halin Taj na gani, mutum shiru-shiru fa Ustaz-Ustaz naga mota tasha kwana hanya daban ko ina sukaje suka buya sai Allah watofa gani yake in munzo nan tare ba lallai ne ya samu matarsa kusa da shiba”.
Garkuwa na gyara kwanciyarta akan gadon da yasha shimfida na alfarma tace.
“Koma dai ina suka nufa matarsa ce ba ruwanki”.
Cikin dariya tace.
“Wallahi ji nake kamar in zama ƙuda in liƙu a jikin blanket nasu inga wainar da za'a to”.
Cikin dariya Garkuwa tace.
“Wato ke Bama a ɗakinba har cikin blanket kike son shiga”.
Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
“Hmmm ba doleba zan samu ƙarin darasi Ishmah fa da kike ganin halittar soyyayace shiyasa duk wanda ya taɓa koda hiran sone da ita baya yanke alaƙa da ita dan gwanace a iya tattalin miji wani lokaci har Maryam tai ta mata tsiya tana cewa muda muke matan aure ba ma tattalin mazanmu da riritasu kamar yadda takewa Tajjj.
To kuma shima Tajj ɗin naga alamar Tattabarane shi kuma ɗawisu a fagen iya love ke kiga randa aka ɗaura auren mana da suka ƙule BQ sai Magrib suka fito”.
Sai kuma tayi shiru jin yadda Garkuwa keta dariya.
Hira kaɗan suka taɓa kana daga bisani suka kwanta su kayi bacci...
Washe gari da safe Ethiopia
Aminullah ne zaune agaban Ummi yayin da Abpu ke gefe idanunsa alumshe kamar mai bacci saidai ba bacci yake yi ba, bisa dukkan alamu breakfast suke.
Anutse Aminullah ya kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi Aunty Ada fa?”.
Ummi na ɗan gyara zamanta tace.
“Aunty Ada na kirata amma naji tana waya da Izzin”.
Numfashi ya sauke kana yace.
“Ummi idan munyi Sa'a fa Allah ya kawo sauki, baki ga tun randa mutumin nan yazo ya saki Aunty Ada har yau bata sake fita rawan nan ba”.
Cikin jin daɗi da alamun farin ciki tace.
“Nima abinda nake ta tunawa kenan Aminullah in Allah yaso ma sanadin sakin nan za tayi sanyi ta daina abinda take yi, kasan shi saki yanada zafi da kashe jiki da cushe zuciyar mutum koda ko yana son a sakeshin wannan alƙawarin Allah ne domin abinda zai girgiza al'arshin Allah ai ba wani zuciyar dake da kafircin da zai hanashi girgiza sai dai in bashi da ɗigon imani, gashi kuma tace min ta faɗi ƙugunta ya bugu sosai”.
Cikin jin daɗi Aminullah yace.
“Allah yasa ta shiryu kenan”.
Ummi na Murmushi tace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Aminullah abinda muke ta fama kenan Allah ya shirya mana ita”.
Yana gyara zamansa yace.
“In sha Allahu ai Allah sami'uddu'a ne zai amsa mana addu'o'in mu, in Sha Allah watarana zamuyi farin ciki da rayuwar aunty Ada”.
Abpu da tunda suka fara Magana baice uffan ba ya buɗe idanunsa cikin rauni yace.
“Kayya ina wani shiryuwa awajen Adaya wataƙil ciwo ne kawai yasa ta lafa wataƙil kuma wani abu na daban take shiryawa wanda bamu sani ba”.
Ya kai ƙarshen maganar cikin rauni da takaicin halin data jefa rayuwar ta”
Da sauri Ummi tace.
“Kada kace haka in Sha Allahu Adaya zata shiryu kawai mu cigaba dayi mata addu'a ”.
Cikin sauri Aminullah ya karɓi maganar da cewa.
“Sosai ko Abpu addu'ar mu Aunty Ada ke bukata in Sha Allahu zata shiryu kada ka karaya”.
Murmushi mai ciwo yayi tare da cewa.
“Ina fatan haka ina rokon Ubangiji ya nuna min ranan da za'a ce Adaya ta nutsu ta zama kamilalliyar mace mai nutsuwa zuciya da jiki”.
Haka dai suka ci-gaba da tattaunawa.
*Nigeria*
Abbane zaune afalonsa yayin da Yah Muhammad, Yah Abubakar ke gefensa sai kuma Hamisu da yanzu ya shigo gefen Abba ya tsugunna.
Kansa Abba ya shafa tare da cewa.
“Ya dai Hamisu?”.
Kansa ya gyaɗa kana yace.
“Lafiya lau Abba?".
Cikin kaunar su Abba yace.
“Ya kewar Boɗɗi?”.
Cikin sanyi da kuma rauni yace.
“Abba akwai ina kewarta gidan ba daɗi ji nayi kamar na ƙaura".
Cikin sauƙe ajiyar zuciya da kewar ɗiyarsa Abba ya saki nannauyan ajiyar zuciya kana ya kwantar da kan Hamisu kan cinyarsa tare da cewa.
“Toh ina zaka kaura inda yafi nan Hamisu? Ai duk duniya babu inda zaka je inda yafi nan. In Sha Allahu zamu saba ai abin farin cikine ya samu Addarka. Aure tayi fa sunnar ma'aikin Allah abinda muke mata fata tsawon shekaru kai kafi son ta zauna anan tare damu ba tayi Aure bane?”.
Kai ya girgiza kana yace.
“A'a Abba bana fatan haka.
Hakan shine abu mafi a'ala in Sha Allahu zan yi ta addu'a Allah ya bata zaman lafiya acikin rayuwar aunrenta”.
Atare Abba Yah Muhammad,Yah Abubakar suka amsa da Ameen.
*Qatar*.
Baki ɗayansu zaune suke bayan sun gama breakfast tare da kimtsa wa sai Adam ne dabai nan wanda suka fita tare da Bilal.
Murmushi Addawa tayi tare da kallonsu tace.
“Toh nima dai tun juya nake kiran Afif bai ɗauka ba gashi Ni kaina na matsu ya kawo min Ishmah kuma shiru dai har yanzu”.
Dariya Aunty Nana tayi tare da cewa.
“Hmmm ai muma mun kira Ishmah Addawa ba'a ɗauka ba wannan dai sai mu zubawa sarautar Allah ido.
Allah andi inda suka ratsa”.
Dariya Khadijah ta sanya tare da cewa.
“Allah dai yasa ba ƙasan suka bari ba”.
Murmushi Addawa tayi kana tace.
“Ya isa ya bar ƙasar da ita bai kawo min ita mun gaisa ba?,Ko zai bar ƙasar ai sai ya kawota mun gaisa”.
Cikin sauri Goggo Dijah ta ɗan zare idanu tace.
“Toh ma sai ya iya barin ƙasar da ita toh su tafi ina?”.
Zama Addawa ta gyara tace.
“Duk inda tace masa tana son zuwa zai Kaita in dai Tajju ne".
Kai ta jingina tare da faɗin.
“Lallai dai kam”.
Adai-dai lokacin kuwa a hotel ɗin da suka sauƙa Ahankali Ishmah ke ɗan jujjuya Idanunta cikin ɗakin jikinta sanye da bathrobe fari kanta naɗe da towel wanda shima ya kasance fari bisa duk kan alamu yanzu ta fito wanda.
Ahankali ta shaƙi numfashi tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin da jikinta ke fitarwa buɗe idanunta tayi kana ta lumshe aranta tace to ina na wurga hand bag ɗina juyawa tayi ta kalli kan gadon kana ta maida idanunta tsakiyar falon still babu, numfashi ta fesar asaman Lips ɗin ta murya araunace tace.
“Toh bari in duba falo ko acan na bari in ɗauko brush in samu inyi, nayi wanka kuma bazan iya brush da wannan brush d’in nasu mai laushi kamar na jariraiba”.
Ahankali ta ɗan tura ƙofar ta leƙa ganin ko Taj na falon.
Jin Parlourn shiru alamun ba kowa sai sanyin Ac dake ratsa ko ina sai kuma wuta dake kunne wanda ya bawa falon wani haske na musamman da yayi masifar kyau yana sheƙi ahankali ta fito saɗaf-saɗaf ta nufi inda ta hango jakarta akan 2sitter tana buɗe hangbag taga Maclean da brush ɗinta da ta saka, ajiyar zuciya ta sauƙe ta kana ta ɓare ledan brush ɗin ta zato brush ɗin tare da matsa Maclean ɗin juyawa tayi zata koma bedroom sai kuma ta tsaya jin kamar motsin mutum agefen hagunta da sauri ta zira idanunta kan labulayen cikin sauri mai haɗe da tsoro ta zare idanunta muryanta na ɗan rawa tace.
“Waye?”.
Shiru ba wanda ya amsa ahankali ta nufi wajen ganin yanda labulayen keta motsi kamar mutum ne a ciki, saɗaf-saɗaf ta isa wajen sai kuma ta tsaya cikin sanyi tace.
“Taj”.
Sai kuma tayi shiru ganin har zuwa lokacin labulayen na motsi ahankali ta sanya hannunta ta ɗaga labulayen da sauri ta saki sanyayyan ajiyar zuciya ganin ƙoface awajen kana iskane ke kaɗa labulen, wanda tayi zaton Taj ne zai gwada tsoronta, ahankali ta riƙe Handle ɗin tare da murdawa ga mamakinta taga ya buɗu cikin sanyayyan sauti tace.
“Wowww Masha Allah”.
Ta kare faɗan Masha Allah ɗin tana ƙarasa fitowa kan ɗan baranda dake zagaye da ƙarafunan silver, a huta isa kusa da ƙarafun, kana tasa hannayenta ta dafa ƙarfen da aka yiwa Farandar garkuwa dashi idanunta ta lumshe tare da tsira wajen daya fi kama da akira sa da forest dan yafi karfin akira da garden saboda subiruni ne da kuma tsirran da suke bakin kogi wanda akanshi akayi Hotel ɗin duk inda ta ƙyalla idanunta kore ne shar da wani iska mai masidar daɗi dake busawa wanda ke sanya nishadi..
Wani irin shauƙi da farin ciki na musamman take ji wanda yake ratsa sassan jikinta da zuciyarta lumshe idanunta tayi tare da sanya brush ɗin abakinta batare data fara gogawa ba.
Dai-dai lokacin kuma Taj ya buɗe kofar falon ya shigo bayansu kuwa home Deleviry daya kawo musu breakfast ne suna shiga ya nuna masa kan dining ɗin falon alamar ya ajiye abincin akai wanda abinci da sukayi order ne yana ajiye wa ya juya ya fita.
Taj kuwa har ya nufi bedroom ya hango alamar Kofar abuɗe yake ahankali ya nufi Kofar.
Yana isa yasa hannunsa ahankali ya ɗan ɗaga labulayen.
Idanunsa ya sauƙa akan Ishmah data juya baya tana kollon forest ta ɗan Dafa jikin karafunan kana ta ɗan jingina kadan da jikin ginin sam bata ji motsinsa ko alamarsa ba.
Ahankali ya ƙara sa shiga dai-dai bayanta ya tsaya Anutse ya sanya hannunsa ya zagaye dai-dai kan ƙugunta.
Cikin sauri da tsoro ta ɗago kanta ta kallesa ta gefe wanda ya bawa bayanta damar mannuwa da ƙirjinsa a hankali ɗaya ta saki sanyayyan ajiyar zuciya ganin shine dan da farko ta tsorata.
Kanshi ya ɗan zuro ta gefen fuskarta tare da ɗan manna sajenshi da gefen fuskarta ta murya can ƙasan maƙoshinsa a hankali yace.
“Afwan na baki tsoro ko”.
Sassayan numfashi ta fesar tare da ɗan lumshe idanunta tana mai jin yadda ni'imtaccen sanyi ke ratsata ga kuma ƙamshin jikinsa.
Taj kuwa hankali ya murza hannayensa tare da murza ƙugunta ya juyo da ita suna fuskantar juna har lau kuma hannunta na kan Brush ɗinta.
Ahankali ya sanya hannunsa dai-dai haɓarta na dama, gefen fuskantar ya ɗan shafa tare da ɗan sayatsunsa biyu yana ɗan shafa sajenta tare da ɗan kwantar dashi, sassayan numfashi suka fesar a tare, sai kuma duk suka ɗan tsaida idanunsu cikin na juna.
A hankali ya ɗan kamo kunnenta kaɗan ya shafa zuwa ƙasan habarta cikin wani irin yanayi ya tsira mata idanu yana mai sakin sanyayyan numfashi.
Itama Ishmah idanu ta tsira masa tana mai jin wani abu mai masifar nauyi yana fita daga cikin ƙwayar idanunsa zuwa nata.
Cikin wani irin yanayi Taj ya saki nannauyan ajiyar zuciya, sai kuma yasa hannunsa na dama ya zaro brush ɗin daga bakinta.
Ido ta ɗan lumshe kana ta buɗe.
Shi kuwa ɗan murmushi gefen baki yayi tare da sanya broch ɗin cikin bakinsa.
Ɗan wara idanunta tayi kana muryanta can kasan maƙoshi mai cike da shauƙi da kuma sanyi ta fesar da numfashi laɓɓanta ta motsa tare da cewa.
“Brush ɗina kuma kasa abakinka?”.
Idanunsa ya tsayar akanta batare da yace komai ba yana dan motsa hannunsa kamar yana goga Brush ɗin murmushi tayi cikin mmkin lamuransa, shi kuma cikin jin sanyi a rai ya ɗaga mata girarsa ɗaya tare da zaro Brush ɗin daga bakinsa.
Ahankali ya motsa Lips ɗin sa alamar ya ɗan tsosti zaƙin brush ɗin da kuma garɗin yawunta.
Cikin sakin sanyayyan Murmushi mai haɗe da wani irin shauƙi na musamman ta fesar da iska mai sanyi tace.
“Ka bani tsoro”.
Fuskarta ya shafa yana mai jin wani irin yanayi na musamman atare dashi yace.
“Farar kura ga tsoro ga ban tsoro”.
Ya ƙare maganar yana haɗe yawunsa daya haɗe da zaƙin makilin da garɗin yawunta.
Sai kuma yasa hannunsa na dama ya tallaɓe fuskantar ido ta tsira mishi shima tsira mata nasa yayi, da sauri ta lumshe nata saboda ganin ya haɗe bakinsu wuri ɗaya.
“Yah Salam wai ni kam me lips ɗina sukayiwa Tajj”.
Tayi mgnar zuci sabida jin yadda yakeyiwa lips inta wani irin fitinenne lasa kamar ya samu lollypop”.
Sai kuma tayi saurin zamewa daga gareshi tare da juyawa tana kallon Forest ɗin still fuskarta na ɗauke da Murmushi.
Sake matsar da ita jikin ƙarafunan yayi kana yasanya hannunsa ya shafa lafeffen cikinta cikin sanyi sauti yace.
“Jiya ba kiyi Lunch ba gashi yanzu har kusan ƙarfe goma bakiyi breakfasts ba, muje Kiyi in baki abinci, kada Ulcer ta illata min ke”.
Cikin lumshe idanu da yanda hannunsa ke yawo asaman cikinta ta saki sanyayyan numfashi tare da faɗin.
“Toh”.
Kana suka fito falon ƙofar yaja ya rufe.
Ishmah kuwa kai tsaye bedroom ta wuce tana shiga ta wuce bathroom tayi brush tana fitowa ta ganshi tsaye.
Cikin lumshe idanu tace.
“Ya dai?”.
Da hannu ya nuna mata durowa dake cikin dakin yace.
“Ga kaya acikin nan ki saka”.
“Toh”.
Tace dama aranta tana tunanin wani kaya zata saka.
Shi kuwa Taj juyawa yayi ya fita kana ita kuma ta buɗe durowar ɗan wara idanunta tayi tare da faɗin.
”Wow Masha Allah”.
Ganin kayan dake shaƙe ajiki an shiryasu gwanin ban sha'awa wanda bisa duk kan alamu dogayen rigunane masu masifar kyau da sheƙi.
Sai kuma wanduna masu kamar Palazo da top wanda suma suke shirye gefe ɗaya sai kuma takalma wanda mafi akasarin su Snickers ne da hill masu shegen tsini.
Murmushi tayi aranta tace lalle ma Taj zan iya tafiya da wannan takalmin ne ahankali ta zaro wata tattausar abaya mai laushi ƙiran samfurin Qatar Abayas Maroon color ta ɗaura gefen gado sai kuma taja drawer ƙasa nan kuma Undoies ne kama daga Brassier, Pant, Skin tied, Boxer na mata, da dai sauransu ahankali ta zaro Brassier cikin mamaki ta wara manyan Idanunta tare da jujjuyawa asaman Lips ɗin ta tace.
“Ya akayi Taj yasan Size ɗin Brassier na?”.
Ta ƙare maganar cikin matsanancin mamaki ganin gaba ɗaya Brassier size ɗin ta ya sayo sai kuma ta janyo Pant cikin sauri ta rufe fiskarta ganin su manya-manyan aranta tace ya akayi Taj yasan har size ɗin Pant ɗina ahankali ta zaro Pant da Brassier duka farare ta ajiye kana ta ɗauki Skin tied ta sanya ta kimtsa kanta tare da komawa cikin Weldrop ta dauki turaruka masu daɗin ƙamshi kana ta fito.
Akan dining ta same sa already yayi serving abinci.
Ganinta yasa ya mike tare da jan hannunta ya zaunar da ita akujeran dake facing dinsa kafin shima ya koma ya zauna.
Yana zama ya miƙa mata fork ɗin abincin.
Ajiyar zuciya ta sauke kana ta karɓa ganin acikin abinci akwai cheaps yasa ta sauke numfashi tasan ko bata iya cin saura ba zata iya cin cheaps ganin ya zuba mata idanu yasa ta lumshe Idanunta cikin langwaɓar da kai mai sanyi gami da rauni tace.
“Toh kaima Kaci mana”.
Cikin sanyi yace.
“Nafi bukatar naga ke kinci shine babban matsalata inga kin daina zubda hawaye sannan kina cin abinci shine abinda zai iya samin farin ciki arayuwata”.
Numfashi ta fesar muryanta cike da sanyi da kuma rauni tace.
“Toh yanzu ina yin hawayene?”.
A hankali ya ɗan daura rafin hannunshi kan sajensa yana ɗan shafawa tare da cewa.
“Ko ba kiyi yanzu ba kinyi daren jiya kuma har yanzu ga idanuki akumbure alamun yau da safe ma kafin kishiga wanka kinyi”.
Ya ida maganar yana kallon yanda Idanunta sukayi luhu-luhu dasu .
Shiru tayi batare da tace komai ba.
Muryar can kasan maƙoshi yace.
“Kinyi ko?”.
Kanta ta girgiza alamar batayi ba,
langwaɓar da kai yayi tare da cewa.
“Kinyi mana faɗa min gaskiya?”.
Idanunta ta lumshe tare da buɗewa tace.
“Toh ai ɗazune da nayi waya da Hamisu gaba ɗaya yasa Naji nayi kewan gida yana cewa gidan mu ba daɗi ”.
Murmushi yayi kana yace.
“Ina ga zan hanaki yin waya da Hamisu ”.
Da sauri tace.
“Kayi haƙuri”.
Cikin ɗan murmushi da langwaɓar da kai yace.
“Toh ai yana samun ke kuka.
Ni kuma bana son abinda zai saki kuka ”.
Baki ta ɗan tura cikin shagwaɓa da rauni tace.
“Toh Kaci abinci mana”.
Kai ya girgiza mata alamun bazaici ba.
Cikin kwaɓe fuska tare da ɗan ture plate ɗin gabanshi tace.
“Nima bana son cin sannan kuma nima Taj”.
Sai kuma tayi shiru Idanu ya tsira mata yace.
“Kema me?”.
Kallonsa tayi sai kuma ta sunkuyar da kai.
Ahankali ya sake motsa laɓɓansa yace.
“Kuma me ki faɗa min”.
Batare data kallesa ba tace.
“Kuma mai ya hanaka bacci da daddare?”.
Kansa ya sunkuyar cikin rauni da sanyi yace.
“Bana jin bacci.
Bacci ya ƙauracewa idanu na Ma'eeshah na rasa yanda akayi bacci ya ƙini bansan ya za'a yi in samu inyi bacci ba”.
Cikin sauƙe numfashi da tarin tausayinsa tace.
“Baka da lafiya ne?”.
Kai ya girgiza mata zazzafan Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa.
“Ka faɗa min mana”.
Araunane yace.
“Nima ban sani ba Ma'eeshah”.
“Toh Ni dai Kaci abinci”.
Ta ida maganar tana miƙa masa fork kusan tare suka ci abinci.
Jim kaɗan da gama cin abincin su,
su kaji ana knowking miƙewa yayi ya buɗe kofar ganin Dr Amdaz ne yasashi ɗan sakin fuska tare da mishi sannu da zuwa.
Cikin alamun sabo da shaƙuwa da alamun yawan magana Dr Amdaz yace.
“Barka da safiya Dr”.
Anutse Taj ya amsa tare da bashi hanya.
Sai kuma ya maida kallonsa kan Ishmah tare da cewa.
“Ma'eeshah tashi ki shiga ciki”.
Kai ta gyada tare da mikewa Akuma dai-dai lokacin Dr Amdaz ke cewa.
“Barka da safiya Amarya”.
“Barka dai Dr”.
Ta faɗa tare da shiga bedroom...
Dr Amdaz kuwa kallon Taj yayi kana yace.
“Dr naxo da duk Doctors ɗin fa ”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Ba matsala ka shigo dasu ai zama zamuyi dasu gaba ɗaya ne za muyi meeting ɗin”.
Fita yayi jim kadan ya sake shigowa mutum tara na biye dashi shida daga ciki maza ne sai mata uku. shine cikon na goma suna shiga suka zauna a Falon.
Dr Amdaz kuwa gefe sa ya zauna tare da cewa.
“Wa'annan sune manyan Doctors ɗin mu ko wanne da fanni daya karanta akwai Brain Dr, Skin Dr, Eyes Dr, Teeth Dr, heart Dr, ko wanne problems muna da Dr'nsa da kuma magungunansu maganinsa.
Kai Taj ya jinjina cikin gamsuwa yace.
“Masha Allah”.
Dr Amdaz kuwa zamansa ya gyara tare da faɗin.
“Dama nace yau kayi zama da Dictors gobe kuma Norse's.
Sai Jibi kuma in Allah ya kaimu kayi zama da Cleaners da sai sauransu”.
Cikin gamsuwa Taj ya jinjina kansa kana yace
“Eh hakan ne yayi abi komai step by step”
Daga nan suka Cigaba da tautauna sauran abubuwa daga bisani ya ɗauki key ɗin office da muhallin ko wani Dr ya basu tare da tsaida ranakun zuwansu da lokaci da kuma dakarun su daya kasance mai gwaɓi, ya ƙara da faɗin satin firko da zasu fara aiki komai kyautane zasuyi duk nauyin ciwo da maganin da zaici.
Sosai sukaji daɗin haka mussaman da suka kasance duk musulmaine sai biyu daga cikine ɗaya ba India ne da addinin hindu ɗaya kuma ahlul kitab ne, wanda da kyar Amdaz yasashi ɗaukarsu sabodo kwarewar su da kuma nuna mishi ai zasuyi