Showing 36001 words to 39000 words out of 44320 words
sukayi tare dashi sun san halin sanyinsa.
Yakan iya kai 3 minute zaune a cikin motar duk da yasan sun iso, a da can baya ma, bare yau kuma da zuciyarsa ke cike da taraddadin wanne sakamako zai samu, sai kuma ya shaƙi sassayan ƙamshi turaren Ishmah dake gefenshi, lumshe idanunsa yayi saboda duk sanda ya shaƙi ƙamshin ji yake zuciyarsa da jikinsa na samun nitsuwa.
Dai-dai lokacin kuma a can cikin Reception ɗin nasu, Dr Farida ce zaune bisa kujerar office ɗinta, yayinda Dr Abbas ke ƙoƙarin fita, da alamu waya takeyi.
Ɗan juyowa yayi ya kalleta cikin tsokana yace.
“Ga fa Dr Afif a cikin hospital nan ya shigo”.
Cikin lumshe idanu Dr ta ɗan ɗaura tafin hannunta bisa ƙirjinta da take, jin yadda Heart ɗinta ke beating so fast, sai kuma ta buɗe idanunta tare da cewa.
“Zuciyata ta rigaka sanarmin ai”.
Murmushin Dr Abbas yayi tare da buɗe ƙofar ya fita.
Ita kuwa Dr cikin sanyi ta longwaɓar da kanta bisa wuyanta saboda jin yayarta da suke waya da ita tana faɗin.
“Wlh kina bani tausayi Farida, saboda yadda kika ɗaurawa ranki son Dr Afif mutumin da baima san kinayi ba, ke kin hana kanki yin aure kinƙi ki saurari kowa saboda shi”.
Sai kuma tayi shiru jin Dr Farida na faɗin.
“Toh ya zanyi Aunty Hidrah.
Allah ne fa ya jarabceni da son shi a lokacin da ni kaina ban sani ba, dan da fari kafin in fara ganinsa a zahiri nayi zaton muryarsa da karatun Alqur'ani da yake yi yasa nake masifar sonshi, sai daga baya na gane cewa, sone irin na aure nakeyi mishi”.
Da sauri Aunty Hidrah tace.
“To shi baima fa san kinayi ba”.
Cikin sanyi tace.
“Eh ban damu da ya sani ba, ni dai fara aiki na a hospital ɗinsa yasa na fara jin cewa lallai shi miji nane in sha Allah, tunda gashi Allah yana ta kusantani dashi Kinga da ya bar Ethiopia ma, ya dawo Qatar gashi Allah yayi na biyoshi kuma ya amshini ya bani aiki, so in sha Allah zai amsheni a matsayin matar sa, duk da a ta biyu zanzo tunda mahaifinsa ya aura masa ɗiyar aminsa.”
Cikin sanyi Aunty Hidrah tace.
“Duk da ina ganin wautarki a wasu lokutan, Amman a wasu lokutan kuma in naga Dr Afif ko naji Voice ɗinsa nakan ce dole, ƴan mata su rikice su ɗiwauce da sonshi, saboda ya kai a soshi, haibarsa da nagartasa kuma ta isa ta hana ƴan matan samun damar isar da sonsu, toh muma da muke da aure ai sai dan kariyar Allah da darajar aurene yake hana shaiɗan samun damar farma zuƙatanmu wurin sonshi.”
Shi kuwa Dr Abbas a yana murmushin ya fito.
Ganinsa ne kuma yasa ɗaya daga cikin Nurse's dake tsaye cikin Pharmacy
ta fito daga Pharmacy ɗin, ta koma Registry, inda nanne wurin aikinta.
Ita kuwa dayar ta gyara zamanta tayi, dai-dai lokacin kuma Dr Amdaz ya fito daga Consultings room 1, ganinsa yasa duk suka nitsu.
Patients insu wanda a ƙalla sun kai 16 ya kalla tare da yi musu, ya masu jiki.
Kana ya wuce ya nufi inda Dr Abbas yake gaisawa sukayi tare da juyawa suka nufi hanyar fita.
A bakin ƙofar fita Reception ɗin suka tsaya tare da zuwa aminin nasu idanu suna sakin murmushi.
Shi kuwa Taj cikin nitsuwa ya fito daga cikin motar, tare da miƙawa Ishmah hannun, hannun ta bashi, haɗe tafukan hannunsu yayi tare da harɗe yatsunsa cikin nata, kana yayi mata nuni da hannunsa ɗaya tare da cewa.
“Bismillah fito Babey”.
Sassayan numfashi ta fesar tare da ziro sawunta waje.
A hankali ya ɗan matsa kaɗan tare da jawota ta ƙarasa fitowa.
Dai-dai lokacin kuma Bilal ya buɗewa Laylah dake gaba, marfin motar tare da cewa.
“Sai na fito da kene?”.
Kai ta ɗan jujjuya kana ta fito, ta tsaya gefenshi.
Shi kuwa Taj da Ishmah, tsayuwa sukayi a jere kai kace, wata da zahara ne, sai wani irin ƙyalli da sheƙi gami da sassayan ƙamshi da suke bazawa cikin shigar su da tayi kamanceceniya.
Shi Taj cikin shigar farin wondon jeans ne sai long sleeve shirt black blue color mai masifar kyau da sheƙi, daga sama can wurin wuyansa bai maƙala botur ɗin ƙarsheba hakan ne ya bawa farar fatar wuyansa zuwa saman ƙirjinaa mai ɗauke da yalwataccen gashi kwance lip-pli ya ɗan bayyana.
Daga ƙugunsa tsadadden belt ne shima Black blue ne ɗamare da ƙungunsa wanda hakan ya bawa surar jikinsa damar ƙara bayyana cike da haiba.
Sai siririn glass irin nasu na Doctors dake manne da idonsa, wani irin kekkyawan sheƙi da ƙyalli lips in shi keyi, hakama sajensa da yake kwance lip-pli gwanin ban sha'awa.
sai kuma Half cover shoe dake sawunsa, na kamfanin Gucci shima Black blue.
Ita kuwa Ishmah wata tattausar rigace fara ƙal a jikinta, short sleeve shirt, sai kuma wondon pallazo shima fari, ta ɗaura wandan kan rigar saman cikinta kaɗan hakan ne ya bawa lafeffen cikinta bawa ƙirjinta damar bayyana ra'anul ain.
Sai kuma after dress, black blue collar, data ɗaura a saman shigar tata, wacce ta ɗan haɗe igiyar tsakiyarta kaɗan, sai farin glaye tsiriri da tayi rolling kanta da shi, wanda ya bawa kekkyawar fuska tsaro na musamman da fidda haibar kyanta, pink lips inta kuwa sai sheƙi sukeyi, hakama gashin girarta dake kwance lip kana ya ɗan haɗe a tsakiyar saman hancinta ya bada siffar W. Farin idonta ya ƙara bayyana ne, sabida ɗan kollin data zizara.
Sai kuma siririn glass fari ƙal mai garai-garai data manna a idonta.
Sai takalmi cover shoe mai ɗan karen tsini Black blue da tasa, sai wayarta dake hannunta na hagu yayinda hannunta na dama ke cikin hannun Taj ɗin ya harɗe yatsunsu gam, yana murzawa a hankali.
Sai wani irin ni'imtaccen ƙanshin mai masifar daɗi sha suke bazawa, na turaren kamanin Gucci, intense Oud.
Kusan duk a tare Ƙananan ma'aikatan nasa sukayi mishi zobe, suna kwasar gaisuwa kamar yadda ya saba yiwa ma'akatan TAJMUH, haka ya fara, amsawa yana mai jinjina musu da basu ƙarfin guiwa yake cewa.
“Aikinku yayi, manyan ma'aikatana”.
Yayi mgnar da iya kar mutumtaka tare da ɗan jujjuya ƙwayar idanunsa ganin ko ina na cikin Hospital ɗin yayi fes-fes gwanin kyau sai ƙyallin sabunta yake.
Bilal ya ɗanyi murmushi tare da gyara riƙe hannun Laylah kana yace.
“Yah Afif karfa su Yah Amdaz suce kana bawa cliners matsayinsu fa”.
Kai ya ɗan jinjina tare da cewa.
“Hmmm Bilal ai matsayin su ya ɗara na Doctors da Nurse's, domin in babu su a asibitin, ƙazanta zata sa babu Dr da zai yarda yayi aiki anan, bare kuma patients su zo ko ba haka ba Ma'eeshah?”.
Yelwataccen murmushin da yasa dimples ɗita duka biyu lotsawa tayi, tare da amsa gaisuwar da cliners ɗin keyi mata kana tace.
“Sosai ma kuwa, dan duk Kyan wuri in ba gyara lalacewa yakeyi”.
Cikin jin daɗin karramasun da sukayi, suka rinƙa godiya kana suka juya kowa ya koma bakin aikinsa.
Shi kuwa Bilal kai ya jinjina cike da gamsuwa.
Shi kuwa Taj juyawa yayi ya ɗan fuskanci gefen gabas, inda wani tamfatsen gini na musamman yake shimfide daga sama an rubuta Reception. Da manyan baƙi,
Cikin sauƙe numfashi suka nufi ƙofar shigan. Bilal da Laylah na biye dasu a baya, riƙe da briefcase inashi.
Murmushin mai nuna cikar jin daɗin Dr Abbas da Dr Amdaz sukayi tare da cewa.
“Wow Masha Allah, kaga wani haɗin Allah a nan”.
Kai Dr Abbas ya jinjina tare da zaro wayarsa ya fara yi musu hoto, a duk taku da motsin tafiyarsu suna masu nufarsu.
Shi kuwa Taj tsuke fuska yayi dai-dai lokacin da suka isa gab dasu, cikin sanyi yace.
“Kai kana nan kamar yaro duk motsin ka sai kayi hoto”.
Murmushin Dr Amdaz yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah patients ɗin yau zasu samu ganin Sheykh Dr Afif dan da yawa ma suna zuwa ne da yaƙinin zasu samu ganinka, dan haka yau zamu huta tunda ga uban gayya”.
Shi kuwa Taj fuskarshi ya ɗan kwaɓe tare da yi mishi irin kallon nan na.
“Toh bani hanya”. Fahimtar hakan ne yasa Dr Abbas yin saurin juyawa suka shiga cikin Reception ɗin.
Yana faɗin.
“Ya naga kamar Madam ɗin ma tamuce”.
Da sauri suka kalli juna jin Taj yace.
“Tawa dai”.
Cikin sakin fuska Dr Amdaz yace.
“Eh yana nufin kamar itama likita ce ko?”.
Ɗan mirza tafin hannunta yayi cikin nasa tare da cewa.
“Itace ma mai Hospitals ɗin ai”.
Kai suka jinjina tare da biyo bayansu.
Sassayan ajiyan zuciya, Ishmah ta sauƙe lokacin da taga duk ma'aikatansu suna ta fitowa.
Ido ta zuba wa, gabansu inda nanne Registry, sai kuma gefen hagu inda Nurse's Station ke jere da Pharmacy, sai kuma gefen dama inda Consultings room 1 2 and 3 ke jere, sai kuma Pay Point, dake tsakanin su.
Parlour ƙatone wanda ke ɗauke da wasu irin tsala-tsalan kujeru na al'farma, masu taushi, ke jere daga tsakiya, wanda zai iya ɗaukan mutum 20 zuwa 30, sai kuma babban TV dake manne jikin gini, sai AC daga can sama dake fesa sassayan iska mai sauke ƙasala.
Cikin yin ƙasa da murya yadda shi kaɗai zaijita tace.
“Masha Allah komai yayi kyau”.
Yana ɗan ƙara jawota kusa dashi yace.
“Alhamdulillah tunda kin yaba nasan kowa zai yaba”.
Kusan duk a tare suka fito, yayinda har hada baki sukeyi wurin cewa.
Good morning sir. Morning sir. Kai yake ɗan gyaɗa musu tare da ɗan motsa lips inshi a hankali yana faɗin.
“Morning”.
Daga nan kuma suka nufi Office ɗin Dr Abbas dai-dai lokacin kuma Dr Farida ta fito daga cikin Office ɗinta.
Da sauri ta mara musu baya.
Ta shiga da sallama tare da faɗin.
“Good Morning sir”.
Ta ƙare gaisuwar cikin yauƙi da kwarkwasa, sai kuma ta tsaida idanunta kan fuskar Ishmah dake ɗauke da yelwataccen murmushin mai fidda haiba da kwarjinin da yasata dole ta janye idanunta, ta maidasu kan Taj ɗin tare da yi mishi kallon dake bayyana zafin sonshi dake cikin zuciyarta.
Sai kuwa tayi saurin
rumtse idanunta tayi da ƙarfi ganin Taj ɗin ya ɗan jawo hannun Ishmah ya ɗaura kan lips inshi tare da ɗan sumbata kana ya ɗan fara goga bayan hannunta kan sajensa zuwa saman lips inshi, sai kuma yasa hannunsa ɗaya ya jawo kujerar baya kaɗan, kana ya ɗan juyo ya kalleta cikin narke ido da murya ya ɗan motsa lips inshi a hankali tare da ɗan ɗaga sauti yadda Dr Farida zata iya jinsa yace.
“So sorry Babey na barki a tsaye ko, Afwan my life zauna”.
Wani irin yam yam tsikar jikinta ya amsa saboda jin sautin muryasa har cikin kwanyarta.
Dr Amdaz kuwa kauda kai gefe yayi.
Shi kuwa Dr Abbas ido ya zuba wa Dr Farida data ƙara diriricewa tuni launin fuskantar ya sauya.
Shi kuwa Tajj har ranshi yana hakane dan Dr Farida ta samawa ranta salama ta daina bibiyarsa da kallon kura yaga ɗanyen nama.
Bilal da Laylah kuwa gaida Dr Farida sukayi sai dai ina ta gaza amsawa saboda firgincin ganin kyaun sura da haibar Ishmah da kuma ganin zallan zazzafan so da ƙaunarta cikin ƙwayar idanun mutumin da tafi so fiye da kowa a duniya.
A hankali ta zauna tare da kallon Dr Farida cikin girmama kai tace.
“Dr Farida ko?”.
A diririce Dr Farida ta gyaɗa mata kai tare da gaida ta, ta ɗaura da cewa.
“Kin sanni ni kuma ban san ki ba”.
Da sauri ta maida kallonta kan Taj ɗin daya ɗan shafi gefen fuskar Ishmah yace.
“Matatace. Aysha Abdallah Matawalle, Mrs Dr Afif Muhammad Taj.”
Wani zazzafan numfashi Dr Farida ta fesar tare da rumtse idanutan kana a hankali tace.
“Masha Allah”.
Ta ƙare faɗar hakan da nazarin, to dama wannan ce matar da mahaifinshi ya aura masa, kuma Dr Abbas yace mata baya sonta bata sonshi, kenan ƙarya Dr Abbas yayi mata, ai waɗanan ko mahaukaci ne ya kallesu yasan akwai true love a tsaka ninsu.”
Shi kuwa Taj files ɗin patients dake jibge kan Table ɗin Dr Abbas ya kalla kana ya kallesu tare da ɗan gyara zamansa yace.
“Kamar akwai patients da yawa, ayiwa Dr Priter mgna taji dasu, ku kuma ga patients ɗin ku.”
Ya ƙare maganar da nuna musu Laylah dake gefen Bilal.
Sai kuma ya miƙa Bilal key tare da cewa.
“Kai kuma kaimin briefcase ɗin Office na sai kaje ka dauko Dr Priter”.
Da sauri Bilal ya amshi key ɗin tare da cewa.
“To”.
Kana ya juya ya fita,
Dr Amdaz kuwa da ido ya rakashi kana ya jujjuya kai tare da cewa.
“Hmmm Bilal ya samu abinda yakeso shiyasa ko gida baya komawa, shi a rayuwarsa in dai za'a bashi mota yayi taja to burinsa ya cika”.
Kai Taj ya jinjina tare da cewa.
“Naji kuma ya yace min ya kusa komawa school”.
Da sauri Dr Abbas yace.
“A ina yake karatu ne?”.
Dr Amdaz na ɗan riƙo hannun Laylah yace.
“AL-Jami'atul Madina yake, karatu ni naso a rinƙa hanashi zuwa hutun ma”.
Cikin sauri Dr Abbas yace.
“To ku daina biya mishi kuɗin dawowa mana”.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Taj jin yana faɗin.
“To ai hukumar makarantar ne suke biya dalibansu kuɗin zuwa Hutu suga iyayensu duk shekara-shekara kuma ma yaro nason ganin iyayensa a hanashi dawowa.”
Murmushin Dr Amdaz yayi kana yaja hannun Laylah tare da kallon Dr Farida dake kallon Ishmah tamkar madubi yace.
“Mutafi ko”.
Da sauri tace.
“Ok Laylah zo mu tafi”.
Ɗan kwaɓe fuska Laylah tayi tare da kallon Ishmah cikin sanyi tace.
“Aunty Ishmah muje tare”.
Cikin kulawa Ishmah ta miƙe tsaye tare da cewa.
“To Laylah”.
Cikin ɗan tsuke fuska Dr Farida tace.
“To ke me kika sani akan aikin likitanci? Ai sai dai Dr Afif yazo muyi aikin tare dashi”.
Cikin tsuke fuska Taj ya ɗan kalleta a fakaice kana yace.
“She's a big Gynecologist Dr, ki san abinda zaki faɗa”.
Yayi mgnar cikin kausasa murya.
Da sauri ta ɗan rusunar da kanta tare da cewa.
“Sorry Sir”.
Kai ya kauda gefe tare da kallon Ishmah Innocent face ɗinta ya kalla tare da sakin murmushi gefen baki kana ya kalli Dr Abbas da Amdaz yace.
“Kuje kuyi aikin da kulawa”.
Sai kuma ya ɗanyi ƙasa da murya yace.
“Babey kuje, Allah yasa muyi farin ciki da zuwan”.
Ya ƙare maganar tare da ɗan jawota yayi mata yar ruggumar gefen nan da yasa Dr Farida juwa ta kama hanyar fita.
Ita kuwa Ishmah murmushi tayi tare da cewa.
“In sha Allah zamuyi farin ciki”.
Daga nan taja hannun Laylah suka bi bayan Dr Farida, da Dr Amdaz,. Dr Abbas kuwa ya mara musu baya.
Kai tsaye ɗakin gwaje-gwajen su na musamman suka nufa wanda yake tsakanin Laubor room, da ɗakin Tiyata.
Ɗakin ɗauke yake da sabbin gadaje biyu, sai sabbin na'urorin na musamman, na gwaje-gwaje da kuma na haske.
Cikin 40 minutes suka gama shiryawa komai da zasu buƙata.
Cikin kulawa Ishmah ta jawo Laylah tare da yin hikinar ɗan ɗaure hannunta ta samu ta debi jininta.
Shett tace lokacin da taji zafin zira mata allurar da akayi.
Shafa kanta Dr Abbas yayi cike da tausayawa yace.
“Sorry”.
Ita kuwa Ishmah miƙawa Nurse's ɗin dake gefentan tayi tare da bata umarnin taje a goda komai na lfyar jikinta tana jiran result.
Amsa tayi ta fita, daga nan su kuma ita da Dr Farida da Dr Amdaz suka fara bincikan lfyar budurcin ta...
Shi kuwa Taj, tunda suka fita ya koma ya zauna bisa kujerar, tare da lumshe idanunsa ya fara karanta suratul Yusuf daga forkonta.
Haka nan yake jin masifar bege da kewar iyayensa na sakar masa raunin dayayi sanadin sinkowar ruwan hawayensa.
Sosai hawayen nasa suka tsananta zuba a dai-dai lokacin da yake karanta aya ta. 11.
“Qaalu yaa Abana malaka laa ta'amanna alaa Yoosufa wainna lahu lanasihuu”.
Kalmar Ya Abana da kuma fassarar ayar da take mgn kan yayun Annabi Yoosufa d suke yiwa mahaifinsu daɗin bakin ya basu Annabi Yoosufa suje kiwo dashi, yasashi tsananta rauninsa da hawayensa.
Suma kenan Banu Israel bare kuma yayunsa da ba komaiba mai zai hana shaiɗan nasara a zuƙatan wasunsu.
Da sauri yaci gaba da karatun domin baya son ya zargi wasu daga cikin yayunsa akan ƙaddararsa,
Musamman da yayi tuni da hadisin nan da Manzon Allah Sallallahu alaihi ke cewa.
“Azzannu zambu walau kana haqoon”.
Ethiopia.
Malam ne zaune a tsakiyar Parlour'sa yayinda duk ƴaƴanshi mazan ke zagaye dashi duk suna zaune gabansa sunyi ƙasa da kawunan su.
Doha Qatar.
Bayan fitarsu Ishmah da kamar awa ɗaya da rabi.
Yaji an banko ƙofar Office ɗin da ƙarfi.
Cikin sauri ya ɗago kansa,
Idanunsa ya zaro baki ɗaya ganin wani irin taku da Ishmah keyi tare da nufosa gadan-gadan.
Tana riƙe da takardun Result's ɗin gwaje-gwaje da sukayi wa Laylah.
Wani irin kiɗimemmen numfashi ya fesar da ƙarfi tare da rumtse idanunsa da azaban ƙarfi lokacin da yaga ta watso mishi ta....!
Kuyi haƙuri ba editing zakusha typing errors.
*Littafin INDA RAI na kuɗine 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin aminci ba haƙƙin kowa a kanku 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276.*
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286: 🍇🍇 *INDA RAI* 🍇🍇
*BOOK 2 PAGE 10*
*Yauwa Lahadi 😭😭😭28/04/2024. Wanda yayi dai-dai da cika watanni uku cib da rasuwar ɗan uwana! Ƙanina Hamisu Aliyu Garkuwa, Yah Allah kaine mahaliccinmu kuma kai mai yawan gafara da rahama ne a garemu duk da yawan zunubanmu. Ya Allah ka jiƙan wannan bawa naka Hamisu kayi mishi gafara da rahama ka yafe mishi kura-kuransa ya rabbil alamin ka yalwata makwancinsa ka faɗaɗa mishi ka haskaka mishi, ka ni'imta mishi kasa kushewarsa ta kasance mishi dausayin Jannatul Firdausi dashi da mahaifiyarmu da ƴan uwanmu Abubakar da Auwal. 😭😭😭 Ya zuljalalu Wa ikrami ka yafe dukkan magabatanmu musulmai*
*mu kuma ka bamu lafiya da nisan kwana da imani da dauwamemme. Ka bamu kekkyawan rayuwa da ƙarshe kasa mucika da kyau da imani. Ya Allah kasa mana haƙuri da juriyar rashin iyayenmu da yan uwanmu🙏🏻🙏🏻😭😭😭 yan uwa makaranta inayiwa Ɗan uwana Hamisu barar addu'a Qulhu ƙafa uku uku a gareku Allah ya kai haske kushewarsa*
*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga