Showing 6001 words to 9000 words out of 44320 words

Chapter 3 - In Da Rai Book 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

26 Jan 2025

8672

kalli sauran Ummomin sa cikin sanyi yace.
“Alamarin Ubangiji akwai bada mamaki akwai abin tsoro aciki”.
Kallon Aunty Hauwa yayi jin tana cewa.
“Sosai ma Muhammad”.
Cikin sake jinjina girman Ubangiji Aransa yace.
“Al'amarin yanda Auren nan ya kasance da yanda ya faru har tsoro ya bani”.
Hajia Aisha wacce itace babba adakin su Daddy tace.
“Babu komai sai alkhairi in Sha Allahu ”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe da faɗin.
“Nima haka nake ji amma wani sashe na zuciyata sai ina jin tsoron yanda abin ya kasance cikin gaggawa".
Yah Abubakar daje gefe yace.
“In sha Allahu sai alkhairi da izinin Ubangiji".
Mikewa Yah Abubakar da Yah Muhammad sukayi jin Abba na cewa kuzo mu tafi.
Sallama suka musu tare da ficewa.

Nan su Aunty Hauwa da Garkuwa Da sauran duk suka dinga al'ajabi akan lamarin Ubangiji daya saƙƙo da Auren nan lokacin da ba'a yi zato ba ba'ayi tsammani ba...

Acan gefen su Taj kuwa tunda Abba ya danƙa masa hannun Ishmah bai sake ba kana ya kasa buɗe baki yace mata wani abu ba...
Ishmah kam tunda ta Zaurawa ƙafarsa dake yanke ido ta kasa janyewa sai hawaye dake kwaranya daga idanunta.
Jin ya saki nannauyan ajiyar zuciya mai haɗe da zazzafan iska daya fito daga cikin ƙahon zuciyarsa hankali ta ɗago idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kallesa.

Kansa ya fara jujjuya mata ahankali alamar ta daina kuka so yake ya buɗe baki yace ta daina kuka amma yana jin harshensa yayi nauyi ta wace siga ta wane yanayi kana da wani furuci ko laɓe ko harshe ko kalmar zai fara gabatar mata da tsananin sonta da yake yi kana da bata hakuri bisa laifin daya mata na aura masa ita batare da saninta ko amincewar ta ba, abubuwan sun taru sunyi masa yawa azuciya haka yasashin jin ya rasa ta ina zai fara bata haƙuri.
Ga kuma Babbar damuwar dake tattare dashi na abubuwa uku fushin ya Abana! Batun cikin Laylah!! Da lamarin wannan karuwantacciyar yarinya Adaya, da ya baro a Ethiopia wanda ya danne ko wanne kuzari dake cikin zuciyarsa arayuwarsa hakan sai yasa ya zuba mata idanun.

Idanu Ishmah ta zuba masa tana kallon yanda ya rame du-du-du da komarsa kwana talatin da biyu ne amma yayi wata ramar data firgitata ta ruɗa mata hankalinta acikin kwanaki talatin da biyun ma du-du-du sati ɗaya ne baiyi Update na new video saba a Tik-tok wanda har take tunanin meyesa bayayi.

Sosai zuciyarta ta raunata saboda ganin yanda fuskarsa ta rame da kuma yanda sajensa ya burkice ga kuma idanunsa da sukayi Jawur suka sauya launi daga ainihin launin data sansu cikin rauni mai ɗauke da rawa murya tace.
“Tajjjj”.
Kallonta yayi amma baice komai ba saboda bazai iya amsa kiran da take masa ba.
Ahankali ta janye idanunta dake cikin nasa ta mayar kan ƙafarsa dake kumbure yana ƙyalli ga kuma tafin ƙafar da ƙirjin ƙafar da yayi wani irin yanka ahankali taja hannunta dake kusa da ƙafar ta manna akan ƙafar cikin sauri ta Runtse idanunta jin ƙafar tayi zafi jau.
Cikin rauni da bugun zuciya ta maida idanunta cikin nasa tare da cewa.
“Tajj”.
Sai kuma ta fesar da sassayan numfashi tare da lumshe idanunta wanda hakan ya bawa hawayenta damar ci gaba da tsiyayowa.
Shi kuwa Taj tsira mata idanunsa yayi tamkar wahayin kallonta akayi nishi.
Murya ciki da rauni, kulawa, tausayawa da taushin lafazi mai cike da jinƙai tace.
“Tajj me yake faruwa?,Me yasameka?,Tajj meke damunka!?”.
Kai ya girgiza mata kasancewar bazai iya cewa komai ba.
Ganin haka ne yasa ahankali tasa hannunta ta ɗauki wayarta dake gefenta number Rahama ta kira.
Adai-dai lokacin kuma Motarsu Rahama ke shigowa gidan jin Rahama ta ɗauka tace.
“Rahama kawo min First aid box”.
Kai Rahama ta gyaɗa tare da cewa.
“Ina yake Aunty Ishmah?".
Cikin sanyi tace.
“Yana ɗakina”.
“Ok bari na kawo".
Dai-dai lokacin kuma ta shiga cikin Falon bakinta ɗauke da sallama tana shiga Aunty Amina wacce itama ƙanwar Daddy ce ta amsa mata sallamar tare da cewa.
“kin dawo?”.
Kai ta gyaɗa sai kuma ta mayar da kallonta kan Garkuwa dake cewa.
“Ya kuka daɗe haka Rahama?”
Ta ƙare maganar tare da amsar ledan hannunta ahankali tace.
“Wallahi Yah Adam ne yace dole sai mun biya gidan Hajia munyi mata albishir ɗin wannan auren”.
Garkuwa na bude ledar tace.
“Kai haba Shiyasa mana naga kun daɗe baku dawo ba”.
Murmushi Rahama tayi tana kallon Ummominta tace.
“Gaba ɗaya Hajia na gaisheku ta kuma ce tana tayaku farin cikinki Auren ɗiyarku”.
Murmushi Aunty Amina tayi tare da faɗin.
“Mun gode mata itama mun tayata farin cikin Auren Jikarta"
Murmushi Rahama tayi tare da nufar bedroom ɗin Ishmah...

Ita kuwa Garkuwa Da sauri ta miƙe tare da kallon Aunty Nana tace.
“Aunty Nana”.
Aunty Nana dake magana da Aunty Maryam ta ɗago tare da faɗin.
“Na'am”.
“Zan samu kaza?”.
Cewar Garkuwa tana sake buɗe ledan.
Kai Aunty Nana ta gyada tare da cewa.
“Eh akwai wani iri kike so?,na gida kike so ko kuma”.
Shiru tayi sai kuma tace.
“Eh toh tun da dai abin gangawa ne duk wanda ya samu amma in so samune ai Zabuwa muke buƙata”.
Murmushi Aunty Maryam tayi kana tace.
“Ai akwai a wajena”.
Dai-dai lokacin Rahama ta fito daga ɗakin Ishmah hannunta riƙe da First aid box murmushi tayi tare da faɗin.
“Aunty Garkuwa ke dai kinyi farin jini Aunty Maryam bata Miki rowa”
Dariya Aunty Maryam tayi kana tace.
“Rahama cigaba da samin sunan Marowata.
Ta ida maganar tana fita tare da nufar ƙofanta...

Rahama kuwa direct BQ ta nufa abakin Kofar ta tsaya tayi Knowking jin shiru yasa ta sake sallama tare da ɗan ɗaga saurin murya.
Daga ciki Ishmah tace.
“Shigo”.
Shiga tayi ganin Taj yasa ta saki Murmushi lokaci ɗaya fuskarta ya koma kalan rauni ganin yanda fuskar Taj ya rame cikin sanyi ta ajiye First aid box kusa da ita kallon Taj tayi cikin sanyi tace.
“Uncle Taj Barka da Yamma”.
Cikin sanyin murya mai gauraye da tarin damuwa ya motsa Lips ɗin sa tare da cewa.
“Barka dai auta”.
Tana tanƙwashe ƙafafunta tace.
“Yasu Ummeey?”.
Kai ya gyaɗa batare da yace komai ba.
Tana sauƙe ajiyar zuciya tace.
“Uncle Taj ina Laylah?”.
Ahankali ya motsa Lips ɗin sa sai kuma ya kalleta yace.
“Tana gida”.
Cikin farin cikin kasancewarsa mijin yayarta tace.
“Uncle Taj Allah ya sanya Alkhairi Allah ya baku zaman lafiya”.
Wannan kalmar ne yasa ya ɗanji sanyi Aransa kallon idon Ishmah yayi sai yaga bashi take kallo ba first aid box take buɗewa sai kuma ya kalli Rahama dake cewa.
“Uncle Taj sai anjima”.
Kai ya gyada a sanda take rufe musu Kofar...

Ishmah kuwa tana buɗe box ɗin taga duk wasu abubuwa da take buƙata suna ciki ɗaya gefen kuwa magunguna ne buɗewa tayi tare da ɗaukar hydrogen kana ta Ciro auduga da karamin almakashi ta kama auduguar kana tasa acikin hydrogen ɗin ahankali ta daga Idanunta ta kallesa sai taga shima ita yake kallo.
Ahankali ta motsa Lips ɗin ta still hawaye na zuba musamman idan ta kallesa sai taji wasu sabbin hawaye na zirya a kuncinta cikin sanyi tace.
“Tajj”.
Zanyi maka dreesing”.
Idanunsa ya lunshe tare da buɗewa alamar tayi.
Baya tayi kaɗan kana tasa ya tsarta manuniya da babbar ta riƙe babban yatsarsa na ƙafa na ta jawo.
Tare da ƙunsa
hauhawar tausayisa cikin zuciyarta da yake motsa mata rauninta

Jin ta jawo ƙafar ne yasa ya ware ƙafan tare da miƙa mata sai ya zamana kafar yana gabanta.
Ahankali ta gyara tankwashe ƙafafunta da tayi ta jawo pillow dake kam kushin ta ɗaura ƙafarsa akai.
A hankali tasa ya tsarta inda taga yankan, ɗan dannan gefe-gefen ya kan tayi.
“Shythhmmmm”. yaja wani daskararren sauti wanda yafi kama da ajiyar zuciya.
Wanda yasa ya daki dodon kunnen Ishmah amma ta gaza fahimtar sautin na menene.
Ɗagowa tayi ta kallesa shima itan yake kallo.
Sai kuma ya nuna mata cikin box ɗin da hannunsa alamar ta ɗauki hangloves ta saka.
Kai ta gyaɗa kana ta janyo hangloves ɗin ta sanya tare da ɗaukar almakashin mai audugan data sama sa hydrogen ta saka abakin yanka.
Atake ciwon ya fara fitar da kumfa duk da cewa bawai datti ciwon yayi ba ga dai yanda yankan yayi ja alamar danye ne babu datti ko alamar ƙura, sai dai saboda bacteria bashi da ƙanƙantar shiga jikin mutum.
Ganin yanda ciwon yayi yasa ta daga Idanu ta kallesa Araunane tace.
“Ka gani fa , Amatsayin ka na likita kaji ciwo kana wasa da lafiyarka da, kake dauka kamar bata da muhimmanci”.
Sai kuma ta lumshe raunatattun idanunta dake cike da hawaye tana sharce hawayenta wasu na turo wasu murya cike da tausayawa taci gaba da cewa.
“Kuma idan ma bata da muhimmanci awajenka tana da muhimmanci awajen Ummey da Yah Abana, Ma'eesha kamata yayi ka kula da kanka ko dan Ummey, Ma'eeshah Meymer, Adaya da kuma Laylah”.
Lokaci ɗaya ya Runtse idanunsa sunan Ummey data kira yasa yaji zuciyarsa ta karye har yana ji kamar wani abu ya fito daga cikin ƙwaƙwalwarsa ya faɗa zuciyarsa sai kuma sunan Meymer da Adaya data kira kansa ya bada sautin Dimmm wanda har kunnuwansa sukayi Dimmm na dan wani lokaci hakan yasa baya jin zafin hydrogen ɗin ahaka ta cigaba da wanke wajen.
Sai yatsunta daya tsurawa ido.
Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago idonsa, tsirawa sirrin sajenta yake kallon yanda ya sake ƙawata kyawun fuskarta.
Sanyayyan ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya maida idanunsa kan zara-zaran eyelashes ɗin ta da suka jika da ruwan hawaye da kuma yanda take ƙifƙiftasu.
Wani irin sanyi da nusuwa ne yaji yana dirar masa tabbatas Ishmah ta musamman ce azuciyarsa da rayuwarsa tana da wani irin matsayi da harshe kansa bai isa ya fade sa ba...

Ishmah kuwa cikin nutsuwa take gyara masa ƙafar bayan ta gama wankewa tasa auduga tare da bandeji ta matse.

Ahankali ya sauƙe nannauyan ajiyar zuciya a lokacin da yaga ta rufe First Aid box ɗin.
Anutse ta ture First aid box ɗin tare da juyawa ta kalli kan dining idanunta suka sauka akan Warmers data shiryasu ne sunan Bappa Kawu da komai da komai da ke kai.
Miƙewa tayi ta ɗauko try ta ajiye agefensa kana ta buɗe fridge dake dining ɗin ta dauko plate data haɗa friut da kuma Fresh da Swan water sai Cock bayan ta ɗauka ta zauna a gabansa.
Shibkuwa kallon wayarsa yayi dai-dai lokacin kiran Abokinshi Dr Amdaz ɗan Qatar ya shigo wayarsa.
Kansa ya kawar gefe.
Ita kuwa Ishmah hawayenta yaƙi tsayuwa ahankali ta cire ledan data rufe fruits ɗin sai kuma tasa fork ta tura masa Bowl ɗin kusa dashi.
Idanu ya zuba mata batare da yace komai ba ganin haka yasa ta ɗauki glass cup ta zuba masa ruwa ta miƙa masa...

Cikin sanyi ya ɗaga kansa ya kalleta sai kuma ya sunkuyar tare da karɓan cup ɗin ya kai bakinsa shi kansa yasan cewa akwana biyun nan da ruwan ne yake rayuwa dashi a cikinsa sai kuma ɗan fruits da yake sha time to time ahankali ya ajiye cup ɗin bayan yasha kusan rabin ruwan.

Kallonsa tayi bayan ya ajiye cup ɗin tace.
“Taj”.
Idanunsa dake cike taf da tarin damuwa ya dago ya kalleta da ido ta nuna masa Bowl ɗin fruits dake gabansa.
Kansa ya jujjuya mata.

Da sauri ta girgiza masa kai murya cike da sanyi kana hawaye na taruwa tace.
“Na roƙe ka da Allah koma menene matsalar ka, kada ka hora kanka da yunwa, Please dan Allah kaji tausayin zucciyata.
Kaci abinci kada kayi fushi da ƙaddarar da zata iya riskarka a ko wani yanayi a ko wani lokaci Kaci abinci ka samu karfin da zaka yiwa Allah godiya da addu'a sannan ya kawo maka sauyi acikin rayuwarka”.
Jin abinda ta faɗa yasa ya zuba mata idanun batare daya iya cire idanunsa akanta ba yana kallonta.
Ganin haka yasa ta ɗauki fork ta soka yankekkekken kankana data zuba madara akai ta ɗago.
Idanunsa ya ɗaga ya kalleta sai kuma ya sunkuyar da kansa ahankali cikin rauni tace.
“Karɓi”.
Ta ƙare maganar tana miƙa masa fork ganin yanda tayi maganar da kuma yanda hawaye ke zuba a idanunta yasa ya karbi fork ɗin yasa abakinsa.

Ahankali ta sauƙe ajiyar zuciya ganin yasa abakinsa shi kuwa Ahankali ya tauna ya hadiye yana ji kamar maganine sai kuma ya sake soko kankanar saboda ganin ta tsareshi da ido, ahaka yaci kusan yanka biyar Na kankanar kana ya ajiye fork ɗin.
Banana ta ɗauka ta bare masa sannan miƙa mishi.
Amsa yayi tare da fara ci.
Ita kuwa fork ɗin ta ɗauka ta soka shi jikin apple, kana ta miƙa masa kansa ya girgiza ya kalli grapes yanzu yana jin zai iya shan grapes.

Ganin haka ne yasa ta kama saman Nonon grapes ta mika masa ahankali ya amsa kana ya maida kansa ya jingina da jikin kujeran ya cigaba da tsinkar ƴaƴan grapes yana tauna yana hadiya.
Ita kam idanu ta zubawa ƙafarsa tana kallon wani irin tausayinsa na bin magudanan jinin jikinta zuwa zuciyarta tuni lokacin Maghiba ta ƙara to....

*Littafin INDA RAI na kiɗine ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Mutanen kasar Niger kuma 1000fc jaka ɗaya kenan rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076 Please Dan Allah da Manzonsa kada ki karanta min littafina in kinsan baki biya ba, in kuma kika biya kika rinƙa turawa wasu ko groups wannan kuma keda Allah*

Acan cikin gida kuwa Garkuwa ce tsaye a kitchen yayin da Aunty Maryam ke gefenta cikin dariya sosai tace.
“Wai nikam dan Allah Garkuwa me haka son kai afili so nake na ture Ishmah in maye gurbinta ajikinki amma kinƙi, kuma fa nima yar ɗakinki ne tunda dai Makkan nan tare mukaje ɗaki ɗaya”.
Murmushi Garkuwa tayi tare da cewa.
“Toh son kan me nayi
Maryam kemafa kadaki manta lokacin aurenki haka Naita dibi-dibi dake yanzu ke kin tsufa gashi har kin bugo Hafiz da Hafiza”.
Maryam na gyara tsayuwar ta tace.
“Ki gani fa daga ji an ɗaura auren Ishmah kiga wasu abubuwa da kike ki dafa wannan ki ajiye ki dafa wancan yanzu wannan me yenene dan Allah in ba son kai ba tunda ni lokacin zabuwa kawai kika dafa min”.
Ƴar dariya Garkuwa tayi tare da sauƙe tukunyar data dafa Zabuwa a ciki wanda yaji hadin magunguna na musamman masu kama jiki sauƙe wa tayi ta juye a Warmer kana ta kalli Maryam tare da cewa.
“Ba wani son kai aciki ita fa Amarya ce ke kuma amarya ce. kuma ita Ishmah abu yanzu a ƙurarran lokacin da son samune in tsumata na wata ɗaya zuwa biyu, to wannan Tajj ɗin yayi mana shigar sauri, dan ma dai Allah yayi kwanaki mun ɗan fara kaɗan akan batun Dr Nafi'u da magana ta fara rawa kuma dole muka bari”.
Maryam na matsar da warmer gefe tayi Murmushi tare da cewa.
“Aikuwa tare dani za'a ci”.
Wara Idanu Garkuwa tayi da faɗin.
“Ki yiwa Allah da Annabi ki bari ita kaɗai zata cinye Kuma yau bazan bar gidan nan ba sai ta cinyesa a Idona yanda Auren nan yazo mana a bazata in ba dage mata akayi ba bazata ciba”.
“Kar ki damu ai Maryam na nan zata nace mata dan Maryam nada naci akan magani babu kamar ita duk da cewa itama batasan maganin amma idan ta nace mata dole sai taci”.
Cewar Aunty Nana dake shigowa yanzu.
Cikin jin daɗi Garkuwa tace.
“TOh Alhamdulillah”. Ta ƙare hamdalar suna
ƙarisabfito falon ta ajiye akan dining tana ajiye wa ta fito tare da kallon Rahama tace.
“Ki miƙo min ruwa mai sanyi a fridge”.
Kai Rahama ta gyada tare da ɗauko mata goran ruwa a fridge dake dining tana kawo mata ta karba tare da buɗe ledan da suka kawo mata ta fito da wani ɗan kwanon China tare da cewa.
“Ina su Aunty Amina fa?”.
Rahama na ɗan danna wayarta tace.
“Sun shiga ɗakin Daddy zasuyi alwala sallan Maghiba ya ƙara to”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Nima bari nayi sauri na dama lokaci ya ƙara to".
Juyawa tayi ta kalli Maryam dake gyara zaman da Kulolin data kawo kan Dinnin table.
“Yauwa Maryama gwara fa ki matson nan dan abubuwa nake so in bar Miki aiki zan baki na bawa Ishmah magani dan Allah ki nace mata".
Dariya Maryam tayi tace.
“Kada ki damu dama nice dai-dai da ita akan magani ”.
Murmushi Aunty Hauwa tayi tare da cewa.
“Toh Ni dai bari na shiga tunda lokacin sallah ya ƙara to".
Kai ta gyaɗa Garkuwa kana tace.
“Toh nima bari na gama tunda lokaci yayi”.
Ta ƙare maganar tana ɓare sabon kwanan ɗan China wanda ke ɗauke da rubutu mai kyau ajiki wanda aka rubuta _Walaƙad Alaihi muhabbatu_ ba rubutune na tsafi ba ko sammu ba ko wani saɓoba, tissue dake gefenta ta zare kana ta goge rubutun sai kuma ta ɗauki goran ruwan tasa ruwa kaɗan ta wanke kana ta ɗauki murfin kwanan shima ta kaɗe sai kuma ta ɗauki robobin data fitar daga cikin kwanan garuka ne kala biyu da gumbuna suma kala biyu sai kuma peak ta ɗauka ta miƙawa Rahama tace.
“Rahama fasa min wannan”.
Karba Rahama tayi tare da nufar kitchen
Ita kuwa roban farko ta buɗe ta ɗebo garin mallaka cokali ɗaya tasa a ruwan rubutun kana ta sake ɗiban ɗaya garin ilanwaddihi ta zuba aruwan sannan ta ɗebo gumbar ɓelɗamhi ta saka tare da gumbar da ba'a baiwa mai kishiya dai-dai lokacin Rahama ta fito daga kitchen ɗin karban madarar tayi ta juye acikin sannan tasa cokalin data ɗiba aciki ta dama lokacin ɗaya ya damu sai ya zama tamkar damun fura da nono ne wanda kuma ta kai har tsakiyan kwanan saboda yawan garurrukan da gumba nan ga kuma ruwa da aka ɗan wanke rubutun tana gamawa tasa murfin ta rufe tare dasa cokalin asama ta miƙawa Rahama da cewa.
“Ajiye min shi a fridge”.
Aunty Maryam dake gefenta tace.
“Nayi zaton yau zata shanye?".
Kai Garkuwa ta faɗa da cewa.
“Eh ganan wannan zan Miki bayani ga paper nan duk bayanin yanda za'a yi amfani dasu na bari aciki kuma ma ai wasun kam kin sansu”.
Kai ta gyaɗa tare da miƙewa itama Garkuwa mikewa.
Sai kuma duk sukayi dariya jin Maryam na cewa.
“Toh Allah dai yasa ma kar suyi mana riga Mallan masallaci.
Abu kusan awa biyu da rabi bata fitoba, karfa yayi mana ba zata irin na auren tun kafin muyi gyaran ta dawo da laulayi”.
Dariya mai sauti Aunty Nana tayi tare da cewa.
“Kai haba dai ustadz ne fa”.
Cikin sauri Maryam tace.
“Ustazan nanfa sunfi iya salsala”.
Murmushin Garkuwa tayi tare da cewa.
“Yo ai mu bamu da haufi ko yanzu yazo tun yaushe muke gyara tun kan Barrister Kamal fa, mukayi na Bappa Kawu mukayi na Salis nan baya kusa kusa mukayi na Dr Nafi'u.
Kawai dai dama bamuyi na sabbin bane, Amman ai bamu da haufi”.
Kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login